Author : Jamila Umar Tanko Category : Romance
zan sake ba. Babu maganar dukan mace a cikin tsarina. Dan Allah ki dinga kiyayewa ke ma ki daina takura ni har in aikata abinda zan yi nadama."
Na matse hawaye na ce "na yafe maka Sweet nima ka yafe min."
Fitowar yara daga cikin daki da gudu ita ta sa ya sake ni, ya gyara zama. Su ka fara ihu Abba, Abba gaba daya suka rungume shi. Ya na yi musu magana cikin karshen larabci kamar yadda ya saba su na bashi amsa. Su ka tabbatar masa cewar sun shirya sun sha cornflakes. Ya ce to su tashi su tafi zai sauke su a makaranta sannan ya wuce wajen aiki.
Na dauki jakar laptop din sa na rataya na riqe lunch box Naziru, shi kuma ya dauki Naziru shine qarami dan shekara 3, Ahamd shine babba dan shekara bakwai ya rataya jakarsa ya dauki lunch box dinsa shima, Nazifi shine na biyu dan shekara biyar ya dauki jakarsa da lunch box dinsa.
Mu ka dunguma muka fito tass da mu gwanin sha'awa kowa na sha'awar yarana saboda su na da kyau sosai sun biyo ni sun biyo babansu dan haka farare ne qal-qal, gasu su na da qoqari a makaranta kowannensu na daya yake yi, shiyasa ma Usman ya daure ya ci gaba da biyan maqudan kudi a makarantar suke yi. Sai yayi kamar ba zai iya ba sai ya daure daure idan ya ji yadda malamai ke yabonsu.Biyu ce ta hadar musu ai uwa na da kokari uba daman gifted ne.
Babu abinda zance da Ubangina sai godiya ga Allah dan Ya yi min komai a duniya.
Usman ya san darajata ya na sona har son yana bani mamaki kullum salon qaunar da yake nuna min daban ce. Dan ba haka nake gani a maqwabta ba, su Dr. sai su yi wata basu zauna a waje daya ba, Safiya da Umma su na qorafi ko mazan sun wuni a gidan ma babu hira babu lallashi sai ma dai su yi ta chating da waya. Amma Usman dina komai dare idan ya dawo sai ya faranta min da kalamai masu dadi ko da yaushe mu na manne, kuma baya kan social media ko daya nima ya ce kada in yi. Ina shan texe massages dai ta waya idan qaunar ta matso daga wajen aiki nima kuma ina yi masa. Ta ina? Ta yaya kuwa zan bari wata ta matso kusa da mu?
Mu na fitowa da maiyar lauyar nan muka yi kicibus wato Bar.Mufidah ta fito tsaf itama a cikin riga da siket na suit sai wani dan qaramin gyale da ta rufe qashinta amma ga gashin nan ana hango shi a tufke baqiqirin. Ina kishin gashin nan, ban taba ganin baqar mace mai gashi irin na ta ba, ga yawa ga tsawo amma bashi da laushi sosai ya fi kama da na 'yan sudan ko Ethiopia. Wannan daddadan qamshin nata ne ya cika koridon.
Ta kalle ni na kalle ta, ta kalli Usman shima ya kalle ta kowa ya tsuke fuska. Ta na rataye da jakar laptop din ta itama a kafada da alama sauri take yi itama ta makara. Ta kalle mu ta kawar da kai sannan ta gyara wani hadadden farin gilashi da ta saka a fuskarta, sai na ga ta qara kyau da aji.
Naziru shine ya fi sabawa da ita ko na dake shi sai ya shige gidanta da gudu, daga ya ga qofarta a bude sai yayi wuf ya fice idan qofarta ma a kulle har bugawa yake yi, sai ta zo ta bude masa tana son yara daga dukkan alamu su ma kuma su na sonta saboda tsadaddun alewoyi da biskit din da take basu.
Ahmad da Naziru sun fi shi wayo su na son zuwa amma su na tsorona sai dai duk da haka su kan faki idanuwana su fada. Duk abin nan da ake yi Usman bai taba sani ba, sai yau da su ka so su tona min asiri.
Nazifi ne ya daka tsalle daga hannu babansa ya fado jikinta, cikin murna da fara a ya ce "oyoyo Aunty Good morning. "
Usman da Mufida riqe da yaro rabin jikinsa a hannun Mufidah qafafuwan kuma a hannun Usman suka tsaya daf da daf, su na kallon juna shi bai sakar mata yaron ba ita bata tunkude shi ba.
Haqiqa na tabbatar Usman ya ji qamshin wannan hadadden turaren na ta, hakan ma ba zai bari ya matsa da wuri ba. Na ji wani yaji yana yi min zugi a cikin idanuwana, kwakwalwata ta dinga tafasa, zuciyata na zabalbala. Da yake ni ce a gaba har na fara sauka na juyo da gudu na tukarosu. Sai da Usman ya ga na taho sannan ya janye yaron daga hannunta.
Mufidah ta yi murmushi ta shafa kan Nazifi ta ce "Morning my darling son. Good luck ayi karatu sosai."
Ta bude jaka ta zaro alewa za ta raba musu, tuni na fisgo yaran na musu tsawa ku wuce mu tafi, Usman kai ma wuce mu tafi mana.
Sai ya fara tafiya cikin sanyin jiki da mamaki yadda wannan shahararriyar maqiyiyar ta mu wacce na tabbatar masa ta tsani yara har yaransa su ka shaqu da ita.Ta ina? Yaya aka yi hakan ta faru?
Na fara magana cikin kissa da kisisina " Hmmm Sweety ka ga abinda nake fada maka ko? Yaran nan sun koyi kwadayi kullum sai na ce ka siyo musu alewa sai ka ce ka manta. Da gayya fa take zubar da ledojin alewa a shara ta zubo sharar qofar falonmu su kuma sai su dinga tsinta su na sudewa.
Usman ya murtuke fuska da alama ya ji haushin abinda Mufidah na ce ta na aikatawa yaransa.
Kawai sai Ahmad ya zabura sai yi magana, zai ce tana basu. Wani uban muntsini na sakar masa na zare musu ido, ai sun san halina su qara yin magana mana su gani, sai su ka yi shiru.
Usman yana huci kamar kasa dan shi bai yarda a baqantawa yaransa ba, zai iya yin komai a kansu. Ya bude bayan mota ya dura yaran a ciki ya rufe. Ya zagayo gefen direba ya bude sai ga Mufidah ta fito da sauri, wata uwar harara Usman ya sakar mata itama ta mayar masa.Ya shiga mota a fusace itama ta nufi motarta a fusace ta shiga.
Fuskata cike da faraa na zagaya gefen direba na bude na ajiye masa jakar laptop na mayar da qofa na rufe, na zagayo gefensa ina magana cikin kwarkwasa. Gumi na ga yana yi kamar yadda ya saba yi idan ransa ya baci, na saka hannu na goge masa gohinsa, gami da jero masa kalamai masu dadi. Gyada kai yayi kawai ya kunna mota, sannan ya bar motar tana dimamuwa.
Mufidah ta taho a cikin wata tsadaddiyar mota baqa ban san ma ta canja waccan jar motarta ba, ta rage tafiya ta tsura mana ido tana harara, mu ma mu na harararta, sannan ta wuce.
Tanimu mai gadi ya bude mata get ta fice da gudu, sai Usman ya zabura zai bi bayanta, na yi sauri na tsayar da shi na dauko masa wasu lissafin kayan cefane da suka qare nan kuwa akwai basu qare ba, dan dai kawai kada su fita tare a hade a hanya. Sai da na tabbatar ta yi nisa sannan na bari ya tsafi, yara na daga min hannu ina daga musu hannu.
Na duba cikin jerin motocin da suke farfajiyar ban ga motar mijin safiya ba sai kawai na afka gidanta. Na tabbatar zan same ta a kicin dan haka ta qofar baya na bi.
Safiya na ganina ta san da labari sai ta tare ni da murna muka tafa. Na tambaya ina mijinta da danta mus'ab ta ce sun fita tun dazu, idan ya sauke shi a makaranta Dr. zai shiga asibiti yana da tiyata. Na shaida mata na bar Haidar yana bacci wataqila ma ya tashi, dan haka ta zo mu hau sama kawai don labarin da yawa.
Ta rufo gidanta muka hau sama. Mu na hawa Safiya ta lumshe ido ta ce "ina son in hawo benen nan na ku wallahi qamshin gidan Mufidah ya ratsa ku."
Na tsuke fuska nace "ni dai Allah Ya jiqaina kawai amma wallahi na dauko ruwan dafa kaina,ni na kawo Mufidah kusa da ni. Da har ta so ta zauna a qasa tsabar son 'yan gayuna na ce dole sai ta hau sama, dan na ganta tsaf da mijinta sai bayan da ta tare na gane ashe wai yayanta ne bata taba yin auren fari ba ma, sai da ta fada ma na ga mamarsu daya. Innalilahi wa inna ilaihi rajuun.
Safiya ta yi dariya , na ce Safiya na ga kina dariya wallahi abin nan ba abin dariya ba ne, mu je ciki ki ji tashin hankalin da nake ciki.
Safiya ta zauna a falo tana kallon talabijin na shiga daki na leqa Haidar, ya sami bacci daman shi gwanin bacci ne in dai babu hayaniya zai yi ta yi, sau daya ya farka cikin dare ya sha nono ya koma. Na ji dadi da ganin hakan dan zamu sake mu yi hirarmu.
Safiya na ganina ta gyara zama ta ce "Aminiya fada min labarin. Me kika yiwa Usman jiya ya kai ku ga duka da mari? Ni dai na jiyo kamar hayaniya amma ban tabbatar ba, kawai na ga giftawar Mufidah ta wundona, kai tsaye na ga ta tunkaro mijina, dawowarsa kenan ko fitowa daga mota bai yi ba.
Na zabura na fito saboda tsaro. Allah sai da gabana ya fadi, na ce toh ina ni ina Mufidah? Gogaggun 'yan duniya. Wai ashe zuwa ta yi ta kira shi ya zo su ceto ki mijinki na dukanki kun rufe gida. A gigice fa take kin san tana da tausayi."
Na tabe baki na ce "tausayin me? Gulma ce wallahi. Kin ga rigar baccin da ta saka a jikinta kuwa, da ita ta je mu ku jikinta ne?"
Safiya ta girgiza kai ta ce "da hijabinta har qasa, ni ban ma taba ganinta ta saka hijab ba sai a ranar."
Na ce " hmmm da ace zata bude hijabin, da kin ga wata crazy rigar da ta saka a ciki, dole maza su susuce in suka ga abinda na gani.
Safiya ta gyara zama ta ce " ban gane ba fa?"
Na bata labarin abinda ya faru daga farko har qarshe har zuwa yau da safe. Sai Safiya ta dora hannu akai ta ce wannan yaqin ba ke kadai ya shafa ba, idan ta kasa da ke kaina za ta dawo. Shi mijinki ma a cije yake amma nawa mijin yana ganin mace yake washe baki. Yanzu Mufidah daga ta fake da ciwon ciki cikin dare, zai haura gidanta da gudu ya ce zai taimake ta."
Na cewa Safiya toh meye abin yi? Mu ka yi Jugum kowacce ta na ta saqe-saqe a ranta. A haka muka rabu da Safiya mun rasa mafita fatanmu dai Mufidah ta tashi daga gidan kawai, kuma mu tabbatar babu wata alaqa da ta gifta tsakaninta da mazanmu.
*** **** ****
Gidana shine yake kallon get, kai tsaye nake hango har bakin titi. Shigowar Mufidah na hango da yamma, gefenta kuwa wata qawarta ce. Bahaushiya ce 'yar Hausawa amma babu maganar mayafi balle dankwali a cikin lissafinta.
Gara Mufidah komin yaya dai tana yafawa. Na tsani qawar nan ta ta mai su na Murjanatu Bibi, haduwarta da wayewarta har ta yi yawa. Ta na da iya yi, ta na da yanga, tana magana tana gatsine amma fa kamar ita ta yi kanta, ba kyau gare ta da yawa ba kawai dai qanqararriyar 'yar kwalliya ce.
Dole ta yi kwalliya mana saloon gare ta, duk wata mace da ta isa can take zuwa a gyara mata jiki, a gyara gashi ga kunshi da kitso. 'Yar gidan wani babba ce dan haka kudi ba matsalar su ba ce su na kashewa sosai, aure ne baya gabansu. Irin wannan idan su ka kama mijinki Allah Ya jiqanki.
Tabbas na san a cikin daya zaa yi biyu ko Mufidah ta bar gidan nan ko ni in bari. Ni Fatiti ina zan kai Mufidah balle qawarta Murjanatu? Sun fi Corona da Ebola illa tabbas.
Hankalina ya tashi matuqa na shiga zurga- zurga tsakanin daki da falo. Ina ta saqe-saqe yadda zan yi da wannan gubar da na dauko da hannuna na kawo gashi tana qoqarin halaka ni.
Ina jinsu su na ta qaqalen turancinsu su ka shige gidanta, kanka ce kwabo sautin kida ya hargitse a matattakalarmu. Wato su a rayuwarsu basu da matsala, basu ajiye wani ba balle su yi fargabar zaa kwace, sai dai su da zasu dauke na wata ma idan sun ga dama.
Ana kiran sallar magruba sai ga Usman yana shigowa, na ga sanda ya tsaya da mota ya fito. Ya na fitowa sai kuma na ji motsin su Mufidah su na fitowa daga gidansu dan haka zaa zaa hadu a kan matattakala kenan. Na ji hankalina ya tashi na rasa wanda zan tsayar a cikinsu.
Ko kwalliyar ban gama ba na shafa hoda a rabin fuska ban shafa a rabi ba, na yi wuf na fito muka yi kicibus da su a bakin qofa. Daman na san ba zasu gaishe ni ba kamar yadda sun tabbatar ba zan gaishe ba. Na shige gabansu na fara wucewa, su na biye da ni a baya. Hira miliyan dallars ake da Paris da America.
Basu dame ni ba fatana kada ayi arangama da mijina, bai ga ta in da na fito ba, bai yi tunanin zai ganni ba kawai ya ji an rungume shi.
Ya dube ni da sauri a firgice ya ga ni ce. Sai ya yi mamaki amma da alama ya ji dadi.
" wow nice couples, perfect match, gasu farare, amma wadannan ma'auratan sun birge ni. A arewa daman ana samun masoya haka?"
Murjanatu Bibi ce ta fada yayin da Mufidah ta zabura ta fisgi hannunta suka yi kwana. Su ka nufi wajen motarta.
Murjanatu ta sake cewa "Mijjn yana da kyau fa and very Gentle."
Nan fa Mufidah ta sake fisgo hannunta ta sake qarawa tayoyin qafafuwanta gudu, suka yi can bayan mota.
Usman ya dube ni ya sakar min wani murmushi na so da qauna ya ce " kin ji ana cewa mun dace sosai, shiyasa nake sake sonki."
Cikin shagwaba na ce "ga shinan tana cewa ka hadu kana da kyau. Ban sani ba ko za ta biyo ka."
Ya girgiza kai ya ce " Haba me zan yi da irin wadancan matan? Allah Ya kiyaye ni ma ya tsare. Ke kadai kin ishe ni. Dadi ya lullube ni, cikin rangwada na karbi jakar laptop dinsa na kama hannunsa zamu hau sama, sai ya ja ya tsaya ya ce ki je ni zan tafi masallacin qofar gida an kira magrib."
Ga Murjanatu da Mufidah sun dawo ashe ba tafiya zasu yi ba abu suka dauko a mota. Murjanatu na waya tana cewa ya tsaya a bakin get ba sai ya shigo ba da alama direbanta ne ya zo daukarta. Wato dai dinguma zaa yi da su da Usman su fita waje tare. Sai hankalina ya tashi na riqe hannunsa gam na ce gaskiya sai dai yayi sallar a gida.
Wannan karon wata uwar harara ya danno min ya fisge hannunsa a fusace, ya fada cikin tsawa "Fatiti kin san abinda kike fada kuwa? Sallah fa na ce zan je in yi kike qoqarin hana ni. Saboda me? "
Sai karaf a kunnensu Murjanatu ta dube mu cike da mamaki har da bude baki ta ce " Ikon Allah ba yanzu na wuce wadannan su na ta soyayya ba, har nake ta yabon su. To yaya haka kuma, har soyayyar ta qare kenan an koma fada? Ah na yarda cikakkun Hausawa ne wadannan don soyayyar su ba dorarriya ba ce temporary ce tabbas."