Author : Jamila Umar Tanko Category : Romance
abinda ya yi min ne so yake ya leqo dakina ya ga halinda nake ciki amma ya kasa.
Ya wankewa yara hannu ya wuce da su cikin dakinsu, gadaje uku ne kowanne ya dora shi a kan gadonsa yana yi musu tatsuniya har suka yi bacci. Daman qaramin mai shan nono ya dade da yin bacci a cinyarsa shi baa dakin yake kwana ba dan haka ya dauko shi ya fake da kawo min shi dakina. Daman na tashi na kashe fitila na hada kai da guiwa a zaune akan gado ina sharbar kuka gami da shidewa da ajiyar zuciya. Tabbas na yi kukan gaske amma daga baya babu hawaye kukan kissa ne.
Ya kunna fitila ya kalle ni sannan ya wuce zuwa gadon yara ya kwantar da Haidar. Ya shiga dakinsa ya abar ni anan a zaune. Na cika da fargaba yau ni ce nake kuka amma Usma bai damu ba? Tabbas akwai gagarumar damuwa. Na ji yana waya, tun yana daki har ya fito falo sannan ya shigo dakina.
Mataimakin gwamnan garin ne da matarsa akan waya. Haquri Usman yake basu da alama sun qi yarda.
Sai ya miqo min wayar a fusace ya fada cikin tsawa "ki karba ki bata hakuri ita ce matar da kika dauki lambarta a wayata ki zazzaga jiya."
Na karbi waya cikin shesheqar kuka da nuna nadama na ce " Hajiya dan Allah ki yi haquri ki yafe min. Kuskure ne na dauka 'yan matan nan ne da suke sonsa....."
Wani dogon tsaki matar ta ja sannan ta kashe wayarta.
Usman ya karbi wayarsa ya dade a tsaye a kaina yana yi min kallon takaici.
Na sulalo qasa na durqusa na riqe qafarsa ina neman da ya yafe min wannan karon kuka ne mai tsanani ya tunkaro min, mai zubar da girgijen zafafan hawaye .
Ya dunkule hannu daya ya daki daya tafin hannunsa da shi ya cije baki ya dafa kai yayi shiru. Yana tsaye dai ni ina durqushe riqe da wafarsa har zuwa lokaci mai tsayi, can ya saka hannu ya tashe ni tsaye abin mamaki sai ya jawo ni zuwa qirjinsa ya rungume ni tsam kamar zai huda qirjin ya zura ni.
Wannan soyayya da tausayi irin na Usman shi yake saka ni qara qaunarsa da mugun kishinsa.
Ya fara magana yana zubar da wasu zafafan hawaye ya ce " na yi miki alqawarin zan siya miki mota sabuwa fil wacce za ki dinga kai yara makaranta, da sauran buqatunki, na yi miki alqawarin sake funiture gidan nan, kin ce irin gidan Mufidah kike so gidan nan ya zama. Ac har kicin da korido.
Na taba kai ki wani wani katafaren fili a GRA size (100 by 100) na ce zan siya in yi mana ginin gidab sama da qasa.
To a yau komai ya rushe a dalilin zagin matar nan da kika yi jiya. Mutanen nan su na da kudi an hada ni da su akan zasu kawo a ajiyar kudinsu a bankinmu kuma duk wanda ya kawo abokan ciniki yana da wasu kaso (percentage) ga qarin girma da zai samu na girma a wajen aiki. Mahaukatan kudade ne zasu kawo ajiya bankinmu, ta hanyata bayan haka zasu hada ni da sanatoci da gwamnoni. Fatiti kin rusa komai na tashi bani da komai, babu irin haqurin da ban basu ba har gidansu na je da kaina amma tuni har sun kai wani bankin. Ashe bayan zagi a waya kin wuni kina aika mata sakon rubutu, da aka bani in karanta kasa qarasawa na yi saboda nauyi da kunya har da ashar da maganar karuwa 'yar iska 'yar madigo. Innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Na yarda da qaddara amma Fatiti me yasa kike yi min haka? Wannan shine karo na goma sha shida kenan kina zagin manyan mata kostomomina, na rasa alkhairai da yawa a sanadiyyar hakan da kike yi. Haka kike so mu dauwama babu ci gaba daga albashi sai albashi,duk wata hanyar samu kin hana ?"
Na runtse ido na qanqame shi na rusa kuka na ce " kishinka na ke, tsananin sonka ne ya hana ni sukuni bana son in ga wata mace na mu'amula da kai. Ka yi haquri."
Ya girgiza kai ya ce " ina sonki fiye ma da yadda kike sona amma bana shiga personal life dinki in hana ki komai, kin san bayan kishin ma kin hada da zargi, kin qi zama mu yi soyayyar cikin kwanciyar hankali ke baki huta ba ni ban huta ba. Kin kasa yin qiba, kin kasa sauke wasu haqqunana da ya wajaba a kanki. Idan kishinki ya tashi zama kike kina fushi kina kuka har in je aiki in dawo in tarar baki yi shara da wanke-wanke ba alhali kin san gyama gare ni, ina son mace mai tsabta. Yanzu wannan kishin me ya amfane mu kenan?
Babban takaicina ma da ban cika miki burinki ba, na yi alqawarin siya miki dukka wadannan abubuwan da kike so saboda maqwabtanki kowacce tana da mota kuma funiture gidansu ya fi namu..."
Na saka hannu na toshe masa baki na ce " in dan haka ne kada ka damu zan zauna da kai ko da a dakin bukka kake zaune, farin cikina in ganmu tare daga kai sai ni."
Ya yi min lallausan murmushi ya ce "Alhamdulullah tunda ba ke na rasa ba kuma ban rasa soyayyarki ba, kudi ne kawai na rasa kuma ba rabonmu ba ne. Amma dan Allah ki daina, kada ki sake daukar min waya ki dauki lambar wata ki kira ki zage ta. Ba dan su na ganin mutuncina ba da yau sai kin kwana a bayan kanta. Ta ce bata yarda ba sai ta sa an kama ki. Ga zagi a wayarta ta yi recording kuma ga massages."
Na ji dadi na lumshe ido na jawo hannunsa muka zauna a gefen gado na ce "daman zan baka labarin Mufidah ne."
Ina ambatan sunanta sai na ga ya hade girar sama da qasa da alama ya qara tsanarta fiye da wacce yake yi mata a baya.
Yauwa daman haka nake so in gani na ci gaba da cewa " in ka ga qaton arnen da ta shigo da shi gidan nan yau za ka sha takaici, mai sarqa da dan kunne wai shine saurayinta, su na ta sunbatar juna abin takaici suka shige cikin gidan, wuni guda a cikin gida sai disko kawai kake ji, gidan nan ya koma kamar club."
Na sirnano da hawaye na ci gaba da cewa "yaranmu nake tausayi su tashi su ga abinda ake yi a maqwabtansu daf da daf din da muka yi nema matsala ga qofa ga qofa. Ko na qi Allah dole in dinga jiyowa kuma ina gani. Darling, gara mu tashi mu bar gidan nan kawai ."
Usman ya yi shiru yana tunani cike da takaici ya ce "daman niyyata daga kudin nan ya samu ba zamu wuce shekara ba zan gama ginin filin can mu koma mu bar yawon gidajen hayar nan. Ai yau na qara tsanar matar nan ma tunda har ta na kirana da wanda bai san darajar mata ba. Ita har macen da ta san darajar kanta ce ma. Matar da bata kama kanta ba, ballagaza ma irinta, ina so ta kai ni kotun ma in kwance mata zani acan?"
Ya miqa hannu ya dauko robb ya jawo fuskata shatin marin yayi jajawur abinka da farar fata, sai ya fara shafa min robb kalmar " I am sorry" ce kadai ke fita daga bakinsa. Ya yi addu'ar kada Allah Ya sake kawo ranar da zai qara aikata abinda ya yi yau. Kwalla ta cika masa ido yayi nadama matuqa. Ya na shafa min robb a hankali yana hura min ciwon, ni kuma na shakwakwkwabe na koma kalar tausayi.
A daren nan dai kamar kwai haka yake ririta ni shine ya gyara mana shinfida ya kaini na yi wanka, ya zaba min rigar baccin da zan saka. Amma wani abu da ya ban mamaki sai na ga ya zabo rigar da ta yi shige da ta jikin Mufida, fara mai dan qaramin hannu. Daman kitson qari (attachment) na yi, sai na ga ya barbazo min da kitson ya zubo bayana kamar yadda gashin Mufidah ya yi.
Innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Me zan gani?zuciyata ta fara ci da wutar kishi bal-bal.
Cikin in-ina muryarta na rawa na ce "Usman zan canja rigar nan ta 'yan iska ce."
Ya cika da mamaki ya ce "ki na tare da mijinki wanne iskanci kuma, dan kin saka masa wannan rigar? Kin ga ta ki ma baa tsaga cinyar ba."
Wato har ya lura da ta Mufidah cinyar a bude. Ashe dai damben nan da aka yi ya na cikin hayyacinsa tana kallon komai na jikinta tare.
Na zabura na miqe tsaye na ce "Usman da rigar jikin Mufidah ka ke siffatawa fa. Ashe komai ka gani, har da bajewar gashinta sai da ka yiwa nawa gashin irin na ta. Burge ka ta yi kenan?"
Ya yi shiru ya rasa abinda zai ce min, da alama ransa ya baci sai ya jawo filo ya kwanta. A fusace na cire rigar na saka wata zunbuleliyar rigar baccina, na dauko almakashi na daddatse kitson qarin gashin (atattchment) din na zubar. Gara ya ganni da kan a gwaguiye da in zubo gashin in yi masa kama da Mufidah. Ina ta shiga ina fita ina ta bambamin fada ina zagin Mufidah, ko uffan bai ce min ba ya juya min qeya ma. Miskilancin na sa ya tashi. Yanzu duk wadannan mugayen halin na ta da na bashi labari bai isa ace ya tsane ta ba kenan amma har ya zo ya gyara ni tsaf, na dauka a cikin soyayya ne sai na ga yayi min Dressing irin na ta.
Sai da na tabbatar yayi bacci sai na duba agogo qarfe daya saura minti biyar. Na san ba ta yin bacci da wuri dan haka na fito na fara qwanqwasa qofar falonta, daman ga qofa ga qofa ne.
Abin mamaki sai gata ta zo ta bude. Wannan karon wata hadaddiyar rigar bacci ce a jikinta kalar ruwan hoda (pink) an jere fulawoyi a gaban qirjin, kalmar Love ta bayyana a jikin fulawar, wannan rigar ta fi waccan ma hatsari saboda shatin komai ya bayyana. Na dube ta cikin takaici ta dube ni cike da mamaki.
"maman Ahmad lafiya kuwa?" Koro ki yayi? Ya sake dukanki ne? Na ga kin bunjima wata riga kuma a bai-bai kamar ba lafiya ba." Mufidah ta tambaya cikin kulawa.
Ta tunkaro ni a gigice ta rungume ni cike da tausayi. Wani qamshi mai sanyi ya daki hancina, ni mace ma kenan ina ga namiji idan ya ji wannan qamshin. Qamshin jikinta, qamshin tufafinta, shine kuma irin qamshin gidanta. Duk ranar da ka shiga gidanta kaima sai ka kwaso qamshin nan, haka idan yara suka shiga gidanta yini suke su na irin qamshin ta, baya barin jikinsu, sai in wuni ina shinshina su gwanin dadi. Tsabar tsafta ce da kuma yin turare wuta akai-akai masu tsadar gaske, humra da turaren wutar ma show glass guda gare ta, amma ba irin namu ba ne ko kadan.
Na sulale na fisge jikina daga jikinta na fada cikin falonta a fusace na sami kujera na zauna. Ta rufe qofar falon ta zo ta zauna a kan hannun kujerar da nake zaune, ta ci gaba da tambaya ta cikin tausayi da kwantar da hankali, har ta shafa wajen da yayi ja shatin mari gami da yi min sannu.
Takaici ya sake rufe ni na ce " ni fa duk ba wannan ne ya kawo ni ba, mijina mun shirya kuma ma dukka fadan da muka yi dazu na wasa ne, ba na gaske ba ne."
Mufidah ta miqe tsaye kamar an tsikare ta, ta ci gaba da kallona galala. Kallo mai cike da rashin fahimta gami da tuhuma.
Na tabe baki na ce ta zauna za mu yi magana ne. Ta ja da baya ta laluba wata kujera a kusa da ni ta zauna da alama kanta ya daure. Ta zuba min ido ko qifatawa bata yi. Sai a lokacin na qare mata kallo ma, daman akwai wadatattun fitulu da suka haska falon kamar da rana.
Tabbas Mufidah ta hada komai da komai da mijina yake so, ga ta wankar tarwada (black beauty) ya na son baqar mace , ya na qaunar mace mai gashi, mazaunai, qugu , cikakken qirji, ga dogon hanci da ido dara-dara, ta na son qamshi da tsafta. Ga idanuwanta masu kalar kallon so wato (sexy eye) ga su dara-dara amma sun risina. Gashin gira da na ido zara-zara kai ka ce ta saka eye lashes masha Allah a cike kamar yadda gashin kanta yake a cike. Laushin jikinta kamar auduga, hannu kamar na jarirai da qafa babu alamar qaushi da faso.
Wata lafiyayyiyar qafa na hango mai qirar koka-kola a dire take ita ta qara bawa shape din jikinta diri. Mufidah a miqe take sanbal doguwar mace, ita ma kuma bata da tunbi kamar ni. Wadannan abubuwa dukka Usman ya na sonsu gaba daya.
Da alama ta qagu ta ji abin da ke tafe da ni da tsakar daren nan. Na harare ta na kawar da kai gefe, na dora qafa daya kan daya na fara magana daya bayan daya irin ta su ta masu aji.
Mijina yana da kyau kuma ya na da qirar da kowacce mace take so a wajen da namiji. Dogo mai dan fadi mai 'yar qiba ga shi bashi da tumbi a tsaye yake qem, ga shi fari qal mai yawan suma da qasumba wacce ta zagaye bakinsa wato quater million. Idanuwansa dara-dara, Idan yayi dariya sai ka ga wushirya 'yar siririya, ga dimples a kumatun hagu da dama. Ga shi da ilimi, ya karanci accountant yayi masters ma, bangaren ilimin addini ma tun muna yara yake koyar da littafi mai tsarki qur'ani, daman gidansu gidan malamai ne, ya dade da yin sauka da hadda tun yana matashi. Ya sauke dukkan wasu littafai na sunna da ki ka sani. Uwa uba mutum ne da bai cika magana barkatai ba, ya na da aji.
'Yan mata sun so shi kamar me har da wacce zata fada rijiya da ya ce baya sonta da kyar aka riqe ta. Tun ba mu zama cikakkun 'yan mata ba muke jin labari a bakin yayyanmu.
Soyayya gamon jini shi kuma a duniyar babu wacce Allah Ya jarraba ya ji yana so sai ni. Tabbas babu wacce zata ga Usman bata ji dama mallakinta ba ne musamman wacce ta yi alaqa da shi ta ji sanyayyiyar muryarsa, nasihohinsa cikin nutsuwa da ratsa zuciya, kallonsa tafiyarsa tsayuwarsa, ga kyauta, yawan murmushi, ya iya daddar kalma, ita kuwa sadaka ce.
Amma ni ban kai kaina inda Allah bai kai ni ba, ashe shi ya na sona ban sani ba har sai da qawayena da 'yan gidanmu suka fargar da ni, duk da haka ban yarda ba.
Na tambayi kaina me yasa Usman zai so ni alhali ga 'yayan attajirai a layin, ga kyawawan 'yan mata cikakku 'yan boko. To me ya gani a wajena? Ina da tsayi siririya kamar taliya, fara ce tas bani da hanci bani da gashin kirki. Ni ce koma baya a cikin 'yan matan da na ga su na rububinsa. Na dade ina mamaki yadda har ya kasa boye son nawa ma.
Kwatsam na ji labarin a bakin mahaifina wai Usman ya zo ya tambaye shi izinin akan yana so ya fara zuwa wajena da sunan soyayyar aure. Nan da nan na amince kamar ya san kuwa da tunanisa nake kwana nake tashi amma ban taba fadawa kowa ba. Sai dai na yi addu'a ba kadan ba tsakanina da mahalaccina akan Allah Ya bani Usman.
Ranar da na ga Usman a tare da ni a soron qofar gidanmu da sunan zance na kusa suma sai in ji 'Limmmm' kamar zan fadi saboda farin ciki da kuma tunanin ko dai mafarki nake.
Allahu akbar! Allah mai kyauta, sai dai na ga baqin