KISHIN BALBAL HAUSA NOVELS BY JAMILA UMAR TANKO.doc

Author :  Jamila Umar Tanko Category :  Romance

Chapter   10 / 13

27K to 30K   out of 36.9K words

ba ko da wasa, da ya fada mata ai da tuni ta fada min a dauki mataki da wuri gashi abu ya lalace.
Na tambaye ta "meye abin yi?"
Ta ce da ni " Maman Ahmad ki kwantar da hankalinki na san wannan ba wata matsala ba ce na san Usman zai kutsa a mayar da shi ko kuma ya sami wani aikin kawai."
Na yi shiru ina tunani sai ta tambaye "amma me kika gani, meye abin yi?"
Na ce "ina ganin kawai ku zo ke da stephanie mu je a karya asirin nan, Murjanatu Bibi ta zo ta taimake shi. In ya so sai a sake yin wani asirin a sake raba su bayan ta taimake shi."
Safiya ta zabura kamar na cake mata allura, ta ce " Fatiti kin kuwa san abinda kike cewa kuwa? A karya fa kika ce. Mun ci uwar wahalar nan mun sami kan mazanmu da kyar sannan ki ce a karya asiri. Haba ina tunaninka yake? Yanzu fa gidan nan babu fargaba babu Mufidah babu Murjanatu, mazanmu kamar zasu hadiye mu dan qauna sannan ki dawo da mu ruwa. Ni fa Dakta har a ofis 'yan mata gare shi, amma kakaf yanzu sun rabu da shi, ya rabu da su. Ma bincika na tabbatar sun rabu kuma shima ya fada min da bakinsa. Ban taba samun kwanciyar hankali a cikin aurena kamar a wannan lokacin ba."
Ta nuna ba ta goyon bayan yin haka ai soyayyar mazanmu tafi aikin kwanciyar hankali, zai sami wani.
Na ce ta kira stephanie a waya dai, ta zo a shawarta. A ka kira ta a waya, Stephanie ta so ta ce sai da yamma zata sami damar zuwa amma da ta ji muryoyinmu alamar akwai matsala sai ta garzayo ta taho kafin ma ta je wajen aiki.
Safiya ce ta tsara mata duk halinda ake ciki, nan da nan ta zabura ta shiga halin dimuwa.
Ta ce " ai kuwa bokan nan baa yi masa haka, bai taba yin gaba ya dawo baya ba. Ko haukata mutum ya yi baka isa ka koma ka ce a karya ba kamar yadda in ya kashe bai isa ya dawo da matacce rayayye ba."
Na tambaye su yanzu kenan haka zan zauna mijina babu aiki, babu kudi?
Su ka tabbatar min zai sake samun wani aiki kada in damu.
A haka dai muka rabu na hau sama na iske Usman da Haidar a zaune a falo sun yi jigum, ya jiyo kukan Haidar a dole ya taso ya dauke shi.
Ina shigowa ya harare ni ya ta tambaya "daga kike?"
Na yi wuqi-wuqi dan ban isa in ce daga gidan Safiya nake da sassafe nan ba, kuma zai yi zargin labari na kai mata na korarsa daga aiki alhali ya gargadi ni cewa baya son kowa ya sani.
Na ce "yara na raka makaranta tunda ka ce ba za ka kai su ba."
Ya bani amsa cikin gadara "eh na cire su daman ni na saka su kuma 'yayana ne. Dan me za ki kai su makaranta, ba tare da izinina ba?"
Na ji maganarsa banbarakwai kamar babu qauna a tare da ita, sai jin haushi.
Na tabe baki na ce " nima kuma 'ya'yana ne, tunda sun kusa gama term din nan ai sai a bari su gama."
Ya yi tsaki ya dauki mukullin mota ya fita, ina leqensa na ga ya shiga Mota ya fita. Ban san in da ya je ba kuma bai dawo ba sai bayan magruba. Ya dawo gaba daya a galabaice kayan jikinsa yamutse, da alama ya sha wuya. Na kawo masa abinci shinkafa da miya da salat amma babu nama.Ya ci da yawa kuwa da alama ya kwaso yunwa. Ina ta so in ja shi da hira amma da alama baya so, bashi da niyyar fada min komai.
Ya shiga wanka, nan da nan na dauki wayarsa na shige lungu na shiga dudubawa kamar yadda na saba.
Dialled calls dinsa na shiga, kakaf lambar Murjanatu ce yayi ta kira yana maimaitawa, da alama bata amsa ba. Na shiga massages gaba daya ita ya yi ta turawa yana magiya akan ta amsa shi amma babu amsar da maido masa da ita.
Sai na sake jin a raina ni fa gaskiya zan je in karya asirin nan, amma idan na tuna maganganun su Safiya sai in ga sun fi ni gaskiya. Gara mu zauna da shi ko a bukka ne cikin talaucin ni da shi kadai da ya sami kudi ya qaro aure.
Wasa-wasa an tafi mako guda Usman ko fita baya yi sai barci sai kallon talabijin amma kuma na lura gaba daya baya cikin hayyacinsa, babu abinda yake yi masa dadi, baya son yin magana baya so a cika yi masa hira, baya son kallona ma balle in sami kulawa da soyayyar da nake muradi.
Na yi kwalliyar, na turare gidan da turaren wuta masu qamshi amma ko yabawa baya yi balle ya ce na burge. Ya zauna shiru kamar kurma kamar wani mutum-mutumi.
Ina jin sa yana waya da Mamarsa tana so ya tura musu kudi, bikin qanwarsa ya kusa. Ya amsa mata da cewa zai aiko.
Na kalle shi cike da damuwa na ce "ai gara ka fada mu su gaskiya cewar yanzu baka aiki."
Tsawa ya yi min ya ce "kada in sake in fadawa kowa a gidansu ko a gidanmu cewar baya aiki yanzu. Baya so kowa ya sani, Allah ne Ya dora masa Shi ne kuma zai fitar da shi.
Kayan abincinmu yayi qasa, yara sun fara qorafi lunch box dinsu kwalam baa zuba musu soye-soye da alewoyi. Haka nake ta basu haquri ina musu wayo, a samu dai a qarasa term din.
Na kalli usman na langwabe kai na fara zayyano masa abubuwan da babu a gidan. Ya yi shiru kamar bai ji ni ba, sannan ya tashi ya shiga dakinsa ya dauko min naira dubu shida da wasu canji 'yan naira biyar-biyar da 'yan naira goma-goma basu kai dubu daya ba. Ya ce duk duniya abinda yake da shi kenan daga daki har banki dan haka in yi ta cancanawa.
Jikina ya mutu hankalina ya tashi har sai da ya gane kamar na fi shi shiga damuwa. Ua shiga yi min wa'azi cewa duk bawan da Allah Ya fi so shi aka fi jarabta, ya yarda da qaddara kuma ya tabbatar Allah Zai kawo masa mafita.
Ya bayyana min cewa shi babbar damuwarsa ma kudin nan da bai cikawa banki ba, gashi lokacin da aka bashi ya qure, zasu iya zuwa su kama shi su daure. Dan babu ruwan banki da halin da mutum yake ciki. Murjanatu Bibi ta qi yarda su hadu har yanzu.
NNa tambaya cike da fargaba " ina Mufidah? Ko ita za ka samu ka riqe ta, ta yi mata magana?"
Ina ambatar sunan Mufidah sai na ga ya hade girar sama da qasa kamar na watsa masa wuta.
Ya harare ni ya ce "ina ruwana da wannan kuma? Meye hadina da ita da zan bi ta wajenta? Kada ki sake yi min maganarta. Yaya zaa yi in san ma da take? Matar da sanadiyyar aka kusa kora ta daga aiki dan dai Allah Ya rubuto ba a lokacin zan bar aiki ba, da a lokacin an kore ni ita ce sila. Kuma har da wadannan laifukan da nata aka hada aka kore ni yanzu."
Dadi ya kama ni daman dan in ji matsayinta a wajensa ne na tambaya, Alhamdulullah tana nan a matsayin maqiyiyarsa har yanzu.
Na shafa gefen fuskarsa na ce " relax my dear ba haka nake nufi ba, ka yi hakuri."
Washe gari Usman ya tashi ya fita da sassafe ya ce min shi dai sai an gan shi zai fita, in kula da gida mu ci gaba da haquri. Asabar ce yara basa zuwa makarantar boko, tahfiz din ma ban kai su ba. Gidan Safiya muka sauka acan zamu yini ko Allah zai sa mu sami dan farfesun da muka dade ba mu ci ba da kwai da dankali. Na bararraje falonta na shaida mata yau ni da tawagar gidana kakaf mun zo mu yi mata wuni, mun zo mu ci dadi. Haka kuwa aka yi muka ci abinda muke so ga nama, ga kwai ga dankali, ga kayan marmari.
Ina ta sha'awar safiya firij din ta a cike nat da kayan dadi haka store dinta. Kudi mai yawa mijinta ya bata da zai fita.
Na roqe ta kudi ta dauko naira dubu daya kacal ta bani amma ban ji dadi ba a cikin dubu goma ta kasa bani dubu biyu ko uku ma. Ban yi magana ba dai na daure na san in bata bani da yawa yau ba gobe zata bani ai yanzu aka fara.
Sai da muka ci na dare tuwon shinkafa da miyar taushe ta sha nama da kifi, bayan mun qoshi ni da yarana har na debowa Usman, shima wanda zai ci idan ya dawo na huta yin girki yau kenan.
Safiya ta rako mu waje abin mamaki sai muka ga motar Mufidah bata nan an dauke ta. Mu ka hada ido cike da mamaki da alamar tambaya. Safiya bata yi niyyar hawa sama ba amma sai ta hawo saboda mu bincika mu ga ko ta dawo ne.
Mun dade a bakin qofarta muna ta leqe-leqe babu ita babu dalilinta. Sai muka tabbatar ba ta dawo ba wataqila direban Murjanatu ne ya zo ya dauki motar. Dadi ya kama mu haka muke so mu gani, muna kuma sauraren ranar da zata aiko a kwashe mata sauran kayan gidan ma gaba daya. Safiya ta sake tabbatar min kada in damu da rashin aikin Usman tunda mun gama da zuciyoyinsu magana ta qare komai nafila ne.
Usman ya dawo gida a galabaice ga yunwa, ya ji dadin matuqa da ganin tuwon nan dan yana son tuwo kowanne iri ne. Ya cinye tas qatuwar malmala yana ta santi, sai da ya shude hannu yake tambayata.
BIna na sami kudin sayen nama da kifi duk da ana cikin wani yana yi na qarma-qarma?
Na bashi labarin cewa gidan Safiya na je na yi mana girki da kayan abincinta tunda ita komai tana da su kamar banza.
Kamar na caka masa wuqa haka ya zabura ya miqe tsaye yana ta bambamin fada yana cewa kada in sake kai yaransa kwadayi, shima kada in sake kawo masa abincin wani gidan. wannan ai rashin hankali ne kuma in rubuta in ajiye nan gaba sai an yi min gori. Me yasa ba zan yi haquri da canjin rayuwar da muka tsinci kanmu na wani dan lokaci ba?
Sai da ya ga ina ta kuka sannan ya tsagaita da hayaniyar, ya koma ya zauna ya fara yi min magana mai dadi cikin nasiha ya ke bani shawara. Ya ce In daina tonawa kanmu asiri, halin da muka tsinci kanmu kaffara ce kuma jarabawa ce. Allah ba Ya son haka tamkar qarar Ubangiji muke kaiwa in har zamu je mu dinga cewa a taimaka mana bamu da komai yanzu.
Ya fadi haka saboda rashin sanin amintar da take tsakanina da Safiya ne, da ya san amintarmu ba zai fadi haka. Ban yarda da Safiya zata gaji da ni ba, kuma ba zata taba yi min gori ba.Nima ai na taimake ta lokacin da basu da shi.
Usman ya karkade aljihunsa ya harhado kudin da suke aljihunsa naira dubu daya da dari uku da hamsim ya miqo min. Na tambaye shi a ina ya samo? Bai bani amsa ba, da na takura masa da tambaya ya ce ba zai taba kawo min haram ba insha Allah, kawai in karbi duk abinda ya kawo min in cancana.
Tabbas mun shiga wani hali tunda har mun fara cin shinkafa da mai da yaji, taliya da manja da magi idan babu yajin ma.
Innalilahi wa inna ilaihi rajuun wata rana idan ya fita ma haka yake dawowa ya ce bai samo komai ba.
Na shiga cin bashi a wajen Safiya da stephanie dan babu yadda zan yi, bayan su ma har a wajen Hanne me kitso ma na ranto naira dubu uku. Dukka cefane na yi da abincin 'yan makaranta da kudin tasin kai yara makaranta da dauko su saboda motar Usman tana da shan mai kuma bashi da kudin zubawa da yawa.
Wani abu da ya gigita ni shine Safiya ta fara canja min da alama ta gaji da ni kuma ta fara raina ni. Idan mu ka shiga gidan ni da yarana sai in ga kamar bata so, ta hada rai ina magana tana amsawa dakyar, kai har ta kai ta kawo Safiya ta kulle firij da store dinta, dan kada in bude in dauki kayan dadi da kayan abinci. Ina yi mata magana tana basarwa da kyar take magana.
Ina zaune stephanie ta zo amma matar nan kamar bata sanni ba sai in yi magana ta yi kamar bata ji ba.Yarana kuwa su na kallon alewoyi a dakin Mus'ab amma ya hana su suka sha kuka amma Safiya ta qi yi masa magana.
Babu shiri na tattara yarana muka tafi ko rakiya Safiya bata yi min ba.
Da aka kwana biyu ma na aiko Ahmad na ce ta ranta min naira dubu daya. Ta ce ya ce min bata da shi. Na kira stephanie na ce ta ranta min dubu biyu, ta ce basu yi albashi ba ita ma bata da ko sisi. Na san sun gaji da ni ne kawai hanawa suka yi dan haka bani da sauran mafita ban da in koma wajen boka ya karya a sirin nan.
Murjanatu ta zo ta taimake mu. Ga mutanen da suka zuga ni nan yau su ne na farkon masu tsanata.
Babban tashin hankalin ma hayar mu ta qare Godwin ya kawo doguwar takarda har da qarin naira dubu hamsin aka qarawa gidan. Usman ya dafe kai kawai ya kasa magana.
Da sassafe na bi me tasi, da ya ajiye yara a makaranta na ce ya kai ni cikin gari gidan wata mata dillaliya. Daman na ciko ledoji da kayana na sakawa leshina da atamfofi super holland, na ce ta saya ta bani kudin.
Tayin wulaqanci ta dinga yi min, dakyar na roqe ta, ta yarda ta qara min wani abu dan na yi lissafi kudin da zai ishe ni in tafi garin su boka in dawo. Bani da abin da zan biya shi ma, sai dai komai ta fanjama-fanjam gara in je.
Na sake shirgawa Usman qaryar seminar da zaa yi ranar asabar mai zuwa, da farko ya ce ba zan je ba sai na sake tsara shi da kalamai masu zaqi.
Na ce " kai fa ka ce neman ilimi yana da kyau gashi sana'ar hannu zaa koya mana, zan koyi yadda ake yin kek sai in zo ina yin na siyarwa in samu mu rufawa kanmu asiri. Ya dade yana tunanin daga baya ya bar ni.
Ban fadawa Safiya zan je ba ta dai ga fitar mu ni da yara sanye da kayan makarantar tahfiz da qafa mu na tafe rabe-rabe, har ta daga min hannu, a tunaninta makaranta zan kai su in je in dawo. Ban wuce ko ina ba sai gidan Hanne da yaran gaba daya na ce kada su je makaranta ina gudun kada a tashi daga makaranta mai tasi ya kawo su gida, Usman ya ga dare yayi ya gaji da jirana ya yi ta kiran wata ya ji a kashe. Na lallaba yaran na ce ba zasu je makaranta ba su zauna da ita zance in dawo sun farin ciki kuwa da jin haka suka dinga murna.

10 / 13