KISHIN BALBAL HAUSA NOVELS BY JAMILA UMAR TANKO.doc

Author :  Jamila Umar Tanko Category :  Romance

Chapter   3 / 13

6K to 9K   out of 36.9K words

ciki da hassada a idanuwan 'yan matan unguwarmu har da qawayena na amana wadanda na yarda da su. Daga nan na yi amanna da cewa Usman kadara ce gara in riqe shi dam-qam.
Amma a cikin hira ya fayyace min dalilin da ya sa ya ji ya na sona. Da farko ya ce tun ban yi wayo ba ya ji na shiga ransa ina burge shi haka kawai. Ni yarinya ce mai surutu da tsiwa da wayon gaske. Sai dai ina da qoqari a islamiyya dan nan da nan idan an koya mana nake dauka. Sannan da na girma ya kula bana kula samari kowa yayi min wannan shaidar, saurayi ma idan ka zo wajena sai na caralle maka, ko in yi maka ihun barawo.
Ya yarda ina da gaskiya ko laifi aka yi a aji zan fadi gaskiya kuma in ce tare da ni aka yi . Kuma da wuya a yi laifi ko surutu a ajin nan a tarar ban da ni. Ni ce ma ja gaba. A yi dukan a yi nasihar amma fa gobe ma zan fadi gaskiya kuma ni ce shugabar laifin. Ya ce wadannan halayyar tawa tana burge shi matuqa.
Soyayyar shekara biyu mu ka yi ya gama bautar qasa ni kuma na gama sakandire. Shine ya taimaka min sosai a wajen karatuna na sakandire ya koya min karatu sosai kuma ya hana ni fita yawon unguwa har sai da na kammala Waec da Neco. Alhamdulullah na ci sosai kuma.
Aka saka mana ranar bikinmu, watanni shida. Kafin lokacin ya samu aikin banki amma baa kano ba a Bauchi. Tabbas wannan abu ya yi kyau komai na tafiya daidai.
Usman dan soyayya ne kai ka ce a turai ya taso nan kuwa ko jirgin sama bai taba hawa ba.
Hakan ya qara min tsananin qaunarsa da mugun kishinsa. Kai ko quda ne ya taba shi sai na ji kishi na tabbatar kudan nan mace take binsa. Tun ban aure shi ba nake jin kishinsa balle kuma bayan da na aure shi.
Usman nawa ne ni kadai ba na kowa ba ina fatan mu rayu tare mu mutu tare dan na tabbatar zan iya yin fatalwa idan na riga shi mutuwa don in hana shi auren wata.
Na hadu da wata qawata mai shegen wayo, ga wayewa mai suna Aziza tana tare da mijinta kamar zasu hadiye juna ta tabbatar min wannan soyayya da kulawa da take samu a sanadiyyar jajircewar ta ne, bata taba bari wata mace ta fuskance shi ko a gida ko a office ba. Dan haka ita kadai ce macen da ya ke kallo shiyasa koda yaushe son ke qaruwa. Amma daga lokacin da namiji ya saba leqe-leqe ya na haduwa da tsala-tsalan 'yan mata daga lokacin zai daina ganin kyawunki ko kyawun dabi'unki dan an raba masa hankali.
Na dauki karatun nan sosai dan haka na zage dantse dan yin yaqi da duk wata matar da za ta tunkaro maigidanna da sunan zumunci ko qawance balle ma da sunan soyayya.
Wallahi zan iya kawar da duk macen da ta yi yunqurin kwace Usman daga wajena. Duk da na yarda da kaina cewar Usman bai taba son wata 'ya mace ba kuma baya sha'awar ya kula wata amma ana yawan kai masa hari."
Tunda Mufidah ta yi ajiyar zuciya ta koma ta jinjina da kujera ta tsurawa talabijin idanu bata sake kallona ba sai yanzu.
Ta kalle ni a yatsune ta ce " yanzu wannan labarin meye ya shafe ni a ciki? Go straight to the point. Wanne saqo kike so ki isar min?"
Na gyara zama na ce " ina so ki san qarfin qaunar da take tsakaninmu sannan ki cire bakinki daga shiga fadana da shi. Na ji kina maganar za ki kai shi kotu ki tsaya min. Ki kai mijina kotu saboda me ? Sannan kin fado cikin gidanmu tamkar tsirara da sunan cetona, ko addini bai yarda wani namijin ya ganki a haka ba, wanda ba mijinki ba."
Wannan karon wani irin kallo na tara saura kwata ta tsaya ta na yi min, ta yi wani murmushi wanda bai kai zuci ba ta ce " na bude qofata na turo shara zan hada da bakin qofa in share daidai lokacin da kika bude masa qofa ya wanka miki mari sannan ya bi ki ciki zai qara, a gigice na shiga na riqe shi ba tare na damu da kayan da na saka ba."
Na ce "ba kowacce mace ce take burge Usman ba ma."
Ta ce " kamar yadda ba kowanne namiji ne yake burge Mufidah ba, musamman mijinki. Dukka wannan kyau da halayarsa da kika fada ni a idona ban gani ba, ban taba gani ba sai ma akasin haka. Usman bai taba burge ni ba, ba ya cikin layin mazan da zan yi lissafi da su."
Ta gwaba min magana, na ji haushi sosai amma na daure na miqe tsaye a tsanake na ce "na ga alama shiyasa ba a tashi yin sharar qofar falo da matattakala sai da safe daidai sanda zai fita ba a tashi sake maimaitawa sai daidai lokacin da zai dawo."
Ta kalli agogo ta ce " ya kamata ki tafi gida ki yi jinyar fuskarki, ciwon da masoyinki ya ji miki tunda duka ma ya na cikin jerin qaunar juna."
Ashe haka ta iya baqar magana zan bata amsa sai na ga ta bude qofar falonta warai ta nuna min hanyar fita da hannu. Ba tare da ta yi magana ba.
Takaici ya ishe ni na ce "zan fita daman ba sai kin kore ni ba amma dan Allah sharar nan ta safe da dare a daina tsallakowa qofar falona. Zo ki ga iyakar gidanki."
Da na fito ta biyo ni ta jingina da qofarta ta tsaya ta maqale hannu a qirji tana wasa da wannan fulawar da take jere a qirjinta. Tana kallona ina bayani na saka qafa na ja layin tiles din da ya kamata ya zama daidai da daidai.
Qofar falona aka bude Usman ne ya bayyana, sanye yake da gajeren wando sai singileti ga Mufidah sanye da tsigalalliyar rigar nan da har gara ta dazu ta fi ta kauri.
Hankalina ya tashi matuqa musamman kallon- kallon da suka hau yi a junansu. Innalilahi wa inna ilaihi rajuun me ya ke shirin faruwa haka ? Me na jawowa kaina ne haka?
Na tura Usman na ce mu je gida, sai ya qi tafiya, sai dai wasu dogaye tambayoyi da ya dinga jero min.Ni yake tambaya amma idanuwansa akan Mufidah.
Wani hadadden murmushi Mufidah take saki tana yi tana wasa da gashin kanta da kuma fulawoyin gaba qirjinta kamar da gayya take yi.
[7/22, 10:49 AM] Jamila Umar Tanko: 4

Mufidah ta ce "mijinki ya na tambayarki ki bashi amsa. Me ya fito da ke cikin dare kika shigo gidana? Shin kin zo wajen lauyarki ce dan ta qwatar miki haqqin marin da yayi miki ne?"
Wannan karon Usman kallona yayi a gigice har da bude baki da alamar mamaki.
Allah Ya sa nima ina da baki da wayo da Mufidah ta kashe min aure a cikin daren nan.
Na zabura na dafa Usman na ce " ko quda bana fatan ya taba min Usman dina, na zo ne in yi miki warning akan babu ruwanki da shiga tsakanina da mijina balle ki ce za ki kai shi kotu akaina. Mijina abin qaunata ya na da kyau da tsari, ba ya hulda da matan da suke ta kararanba a gari.
Mufidah ta yi murmushi irin na takaici ta ce "sai dai mijinki bai taba burge ni ba, kuma ba ya cikin lissafin irin mazan da su ke burge ni ma. Ban taba ganin mutumin da bai yi min ba a rayuwa irin mijinki Usman, ban taba ganin kyawun nan na sa da kullum kike yabawa ba."
Usman ya juya ya dubi Mufidah cike da tsananin tsana, ya sake juyawa ya kalle ni a fusace ya nuna Mufidah da hannu ya ce " kada ki sake shiga harkar wannan banzar. Ina ruwanki da ita da za ki shiga gidanta kina hana ta, ta kai ni kotu? Idan ta na shan giya ne ta je can gidan giyar ta yi shashancinta ba a gidana ba."
Dadi ya kama ni zuciyata ta yi wasai domin sun tsani juna muguwar tsana ma kuwa. Alhamdulullah na yi hamdala a zuciyata. Usman ya bude qofar falonmu ya nuna min da hannu ya ce wuce mu tafi.
Mufidah ta yi murmushi ta ce " matarka tana sonka sosai amma bata san yadda zata tafiyar da soyayyar daidai ba saboda tana da qarancin wayewa da rashin ilimi. Dan da ta waye ba zata kalar da ta hada a falonta ba. Ko za ka taimake ta ka mayar da ita makaranta? Ba ita kadai za ka taimaka ba har da kai kanka da mu maqwabtanku. Ka ji ?"
Ta juya baya tana Girgiza zata shiga gida. Innalillahi wa inna ilaihi rajuun, ni na san abinda na gani, Ina kallon idanuwan Usman ma ya na kallon abinda nake gani.
Na fusata na zabura zan fito in bata amsa Usman ya sa hannu ya tare ni ita kuwa har ta shige ta banko qofar falonta.Ya juyo ya galla min harara ya daka min tsawa rufe min baki.
Ya shigo falon a fusace ya ce "rufe min baki Mufidah ta fadi gaskiya. akwai rashin ilimi a tare da ke? Sau nawa ki ka zana jamb kin tsaya kin ci ? Wacce kika ci ma har admission na nemo miki kika ce ke ciki gare ki sai kin haihu. Bayan kin haihu na ce ki koma sai a samo yarinya mai aiki tana taya ki raino kika ce babu yarinyar da zaki dauka aiki saboda masifar kishi irin na ki. Mufidah ta yi gaskiya kuma ta fi ki gaskiya. Dan me kika shigar mata gida? Na san abinda ya kai ki gidanta, daman kina ta maganganun ta saka qaramar riga ta shigo mana gida? Har da sharri wai ki na kallon idanuwana ina ta kallonta. Ke me ya sa ba ki da tunani ne? An fada miki kowacce mace namiji yake gani yayi shaawa? Ya kamata ace zuwa yanzu kin san halina, ba wannan ne a gabana ba. Yanzu da tsakar daren nan, matar nan tana bacci kin fito da ita babu shiri rabin jikinta a tsirara, ni din da ba kya so in gani na ga abinda dazu ban gani ba, kin jefa idanuwana a halaka."
Na fusata na ce " Au fada min kake yi ma ka ganta? Me ya kai idanuwanka kanta? Ai daman na san sai ka kalla har ma ka haddace qirar jikinta. Tunda ta ganka ta hau girgiza da shafe-shafe sassan jikinta. Wallahi ba zan iya zama da karuwa a gida daya ba."
Ya daga hannu a fusace na zaci marina zai yi na saka hannu na kare fuskata. Ya fasa sai na ga ya sauke hannun. Ya na magana cikin fusata amma muryarsa ta yi qasa idanuwansa sun cika da hawaye sun jajawur.
Ya ce " na yi alqawari ba zan sake marinki a rayuwata ba insha Allah, wancan ma da na yi na yi nadama. Akwai banbancin tunani a tsakanin mutum da dabba, ba zan dinga dukanki ba tunda ke ba dabba ba ce. Ke mutum ce wacce ya kamata ace ki na tunani a kwakwalwarki, ki dinga tantance abu mai kyau da marar kyau. Ina son ki amma kina so qarfi da yaji ki sa a dole sai na yakice ki daga cikin zuciyata. Kishinki yayi yawa kin kasa zama lafiya da kowa nima kin kasa zama lafiya da ni kin hana ni in huta.
Ki duba agogo ki gani qarfe biyun dare ta wuce ban kwanta ba gobe qarfe bakwai zan fita aiki. Ta yaya kike tunanin zan iya aikin kirki. Duk sanda na kuskure lissafi zan iya jawo matsalar da zaa iya kora ta. Kin san yanayin aikinmu yana buqatar nutsuwa amms ni ba ni da nutsuwa.
Mufidah za ta je aikinta gobe kin shiga kin hana ta bacci, aikin lauya yana buqatar hutu a qwaqwalwa don ta yi tunani sosai wajen abubuwan da zata fada da wanda zata tambaya amma kin hana ta. Ke gobe ina za ki je bayan yara sun tafi makaranta? Yini kike kina bacci ko shara da wanke wanke ba kya yi, ashe har maqwabta sun fara ganewa ke baki waye ba. Tana yi mana gorin jan carpet da blue din labule da brown din kujeru sai da ta fada ma na lura. Kuma duk ke kika zabar mana hakan."
Na fusata na ce " ban gane ba, na ji kana ta kiran Mufidah! Mufidah ban bari ta kwanta da wuri ba zata je aiki gobe. Ka damu da ita ne kuma har ka ji haushin ban bari ta yi bacci da wuri ba?"
Ya fusata ya ce " eh ai mutum ce kuma musulma ce, sannan makwabciyarmu ce. Kina da ilimin addini ai kin san yadda Annabi Muhammad S.A.W ya umarci mu da mu kyautatawa makwabci, tana da haqqi akanmu."
Na fusata na zaburo kansa zan yi masifa.
Ya daga hannu ya dakatar da ni ya ce " daga nan har zuwa gobe da safe kika sake furta kalma daya wallahi sai na aikata wani abu wanda daga ni har ke zamu yi da-na-sani da nadama nan gaba."
Tunda nake da Usman bai taba furta min irin wannan kalaman ba. Na tabbatar abinda zai aikata bai wuce saki ba. Ni kuwa rabuwa da Usman daidai yake da rabuwa da rayuwata. Na bi shi da kallo har ya shige dakinsa ya datse ban sake cewa komai ba. Amma tsaki da qwafa na kwana ina yi, ina ta zagaye gida tsakanin falo da daki. Mufidah! Mufidah !! Mufidah!!! Tabbas ba ta isa ta ga bayana sai dai in ga bayanta. Na qudiri aniyyar sai na yi mata abinda zata tsani gidan nan ta tashi da kanta, sai na hada su fadan da sai sun sake tsanar junansu kamar mage da bera.
Washegari da sassafe na yi wanka da wuri na caba ado da wata hadaddiyar material voil, dinki doguwar riga, na shiga kicin na hadawa yarana da maigidana abinci.
Usman ya fito tsaf a cikin baqar Suit irin ta ma'aitan banki, wacce farar fatarsa take haskowa a ciki.
Na gaishe ya amsa amma ciki-ciki. Na nuna masa shayin kayan qamshin da yake iya sha da safe kullum kafin ya fita. Sai ya girgiza kai alamar ba zai sha ba, na koma gefe na yi abin tausayi da fuskata yadda nake bashi tausayi duk sanda na yi irin wannan yanayin. Sai ya dube ni sannan ya kawar da kai ya ajiye jakar laptop dinsa akan kujera ya qarasa kan dining ya zauna , na tafi a nutse na dauki kofi na zuba masa shayi mai zafi ya sha kaysn hadin qamshi, na koma gefensa na zauna ina ta qamshin turaren wuta da humra saboda na san shi da tsananin son qamshi.Sai baza hanci yake yana shaqa.
Ya tsurawa gefen fuskata ido yana kallo, wajen yayi jajawur shatin marin, sai na ga kamar bai ji dadi ba. Na sake yin kalar tausayi na dube shi yayin da idanuwana suka cika da qwalla.
Na ce "Usman na yarda da kai fiye da yadda na yarda da kaina. Ni na jawo komai har ka mare ni, na ga kamar ka damu da marin da ka yi min tun jiya."
Ya ajiye kofin shayin ya dafe kai yana jujjuyawa yayin da ya daga tafin hannu da ya mare ni ya kalla, sai yayi tsaki.
Ya dago ya dube ni ya ce " na ji na tsani wannan hannun nawa da ya aikata mari..."
Bai rufe bakinsa ba na saka hannu na toshe masa baki.
Nia ce "kada ka sake fadar haka."
Ya jawo ni jikinsa yana magana cike da nadama.
"Dan Allah maganar na taba marinki a rayuwata ki ja bakinki ki yi shiru bana so a sake daga maganar nan, ba

3 / 13