KISHIN BALBAL HAUSA NOVELS BY JAMILA UMAR TANKO.doc

Author :  Jamila Umar Tanko Category :  Romance

Chapter   11 / 13

30K to 33K   out of 36.9K words


Wai yau ni ce Hanne take yiwa fada tana cewa ta gaji da bani bashi, ga kudinta naira dubu uku daga cewa yanzu-yanzu zan biya amma shiru har yanzu, ga yara na kawo mata raino har guda hudu shima kudin rainon na ce bashi ne.
Na yi ta bata hakuri na lallaba yara na tafi. Sai da na kai Billiri ina qoqarin hawa wata motar zuwa garin Banganje sai ga kiran Safiya a gigice take magana.
Ta ce min "Fatiti kina ina ne?"
Na tambaya cikin fargabar ko wani abu ne ya faru a gidana na ce "me ya faru lafiya?"
Ta ce "ga ni na zo kitso gidan Hanne na ga yaranki anan an ce kin tafi ke kadai. Ina kika tafi haka?"
Na fada cikin gadara "eh na tafi wajen boka a karya asirin da aka yi mana gaba daya daga nawa har nasihar ma da na stephanie."
Safiya ta zabura ta fara magana cikin gigita tana lallaba ni wai in dawo in saboda kudi ne ita ta yi alqawari zamu dinga raba kudin cefanenta. Sai a wannan lokacin ne na sami damar cashe mata tas.
Na karanto mata dukkan wulaqancin da su ka yi min ita da stephanie dan haka babu maganar dawowa baya, aikin gama ma ya gama.
Na kashe wayata, ta dinga kira na qi dauka na sami motar garin Banganje na hau aka ci gaba da nausawa.
Babu jimawa na ga kiran stephanie, na dauka na yi shiru itama ta gama na ta tsarin tana lallaba ni gami da tsoratarwa cewa baa yi masa haka zai ji haushi ya haukata ni. Na ce mata ai ni na fi qarfin a haukata ni saboda ni musulma ce na riqe azkar. Na katse wayar, stephanie ta ci gaba da kira Safiya ma na ci gaba da kira na qi dauka daga qarshe ma na kashe wayata gaba gaba daya, na ci gaba da miqewa cikin dawa, ban qi kowa ya rasa ba duk mu hadu mu mutu.
Yau ma kamar wancan lokacin na sha wahalar hawa babur, na sha fadowa da gurjewa da karcewa har dai Allah Ya sa na isa garin. Sauqinta dai yau da shirina na fito dan sai da na ci abinci na qoshi sannan na saka wando da riga a cikin abaya, da gumu ta yi gumu na linke abayar na saka a jaka na fito a 'yar duniya sak riga da t. shirt da 'yar hula na saje da su daman bai kamata a ga masu hijabi a irin wadannan wajen ba.
Na isa da misalin qarfe biyu na rana, sai dai kash .....
Na iske baya nan ya shiga daji shi da yaransa yin wasu tsubbace-tsubbace. Aka ce mu zauna akan wata fata kamar ta zaki mu jira shi anan, sai na tsugunna na qi zama ina tsoron kada in zauna ina bace. Ba su dawo ba sai da la'asar liqis hankalina ya gama tashi.
Ya nufo mu ya na tafe yana tsalle ya na juyi ya na ta kirari, shima yaransa su na yi masa a cikin yaren da ban san me ake cewa ba.
Babbar fargabata yadda imanina yake walagigi ban sani ba ko ina da sauran imanin ko kuwa ya tafi gaba daya sai na sake sabuwar kalmar shahada? Menene matsayina a wajen Allah? Ina ta addua kada in fada aikin shirka. Idan kuwa na zama mushirikiya na gama tabawa na yi asara duniya da lahira.
Na dinga tuba ina yiwa Allah alqawari ba zan sake dawowa nan ba. Dan na ga alamar babu Allah a wajen matsafan nan. Na tuhumi zuciyata na ce me ya sa na biyewa ahlul katabu stephanie muka yarda muka biyo ta nan ? Ina imaninmu yake? Ina tauhidi? Ina saukar qur' aninda na yi tun ina yarinya? Ina hadisan manzon Allah S.A.W da aka koya mana a islamiyya?" Sai na fara hawayen nadama ina tsoron kamun da Ubangijina Zai yi min nan gaba.
Na sami mutane a gabana da yawa amma cikin hukuncin Ubangiji na ci saa sai na ji ya kwalla kiran sunana ya ce Musulma, Hausa ta shigo. Na daka tsalle na fada na cikin bukkar, na bi dokokinsa duk yadda ya ce in yi dai in yi, in zan zauna sai ya yi qara ya ce in matsa zan taka su, har dai na isa in da ya ce in zauna yayi dsidai. Ni dai bana iya zama sai dai in tsugunna, zan fara magana ya dakarta da ni da hannu ya ci gaba da kiraye-kirayensa sannan ya dube ni.
Ya ce "a karya ko?"
Na ce "eh da nawa da na Safiya da na stephanie dukkansu sun bani saqo sun ce a karya."
Na yi mamaki da ya dube ni ya bushe da dariya ya ce "muguwa, me qarya."
Daga nan bai qara cewa komai ba ya ci gaba da bubbuge-bubbugensa.
Sai gabana ya fadi na dafe kirji ina jiran hukuncin da zai dauka a kaina tunda ya gane cewar na yi masa qarya. Salatin Annabi S.A.W nake ta yi, ina neman tsari daga sharrinsa.
Ya daga wasu akushi guda 3 sai ga qananan kunkuru su na fitowa idan ya damqo daya sai ya bude bakin ya ciro wani abu sai ya saka kunkurun a cikin kwarya, ya sake damqo na biyu shima haka ya damqo na uku shima haka. Na tabbatar ya ji magana ta ya karya na mu ukun.
Na gyara tsugunnona dan qafata ta sage cikin fargaba da ladabi na ce "a karya na tsakanin Usman da Murjanatu amma kada a karya na tsakanin Usman da Mufidah."
Ya harare ni ya ce "daman na Mufidah bai ci ba na Murjanatu ne ya ci."
Na zazzare ido na ce "boka saboda me ita na Mufidah bai ci ba?"
Ya daka min tsawa ya ce "ki ajiye mana abinda kika kawo ki tafi gida ga mijinki can yanzu-yanzu haka yana tare da wata, tana sonsa da aure, ta hanyar bashi kudi, kudi,kudi, aure, aure, soyayya, soyayya, ciki, ciki, haihuwa, haihuwa."
Wani abu ya tsargo min tunda daga sama har qasa.
Na zazzare ido na dafe qirji na ce "Boka Mufidah ce ko wata ce?"
Boka ya sake zabura ya juya gefensa ya ce ga wata can ma, yanzu haka shi take jira in anjima zai je wajenta, tana sonsa sosai tana ta addua akansa.Ya sake juya bayansa ya ce akwai wata ma tana sha'awarsa amma ya qi yarda tana tsafi irin namu akansa."
Ai sai na yi zaman 'yan bori na baje akan fatar da bana zama, na fashe da kuka kai ka ce mutuwa aka fada min.
Na ce "boka a mayar da asirin na fasa karyawa."
Ya ce harare ni ya ce "daman asirin akan Murjanatu da Mufidah kika ce ayi tun darko ma na Mufida bai ci ba, Murjanatu kadai ya saboda bata addua, kuma na karya yanzu."
Na ce "toh matan da ka hango fa yanzu har guda uku, yaya zaa yi da su?"
Ya ce "da wuya asiri ya ci mijinki saboda yana addua, yana qona mu kullum."
Na ce "Mufidah tana cikin matan da ka zano masu sonsa?"
Ya girgiza kai ya ce "wasu ne daban su na nesa da ku, babu wacce take kusa da ku a cikinsu."
Yawun bakina ya bushe hawaye ya kasa tsayawa na ce "me yasa asirin bai ci Mufidah ba?"
Ya dade yana dube-dube sannan ya dago ya dube ni ya ce "ki bita a hankali ta fi mu hatsabibanci, ki rabu da matar nan."
Gabana ya fadi na na dafe qirji na ce " Boka! tana sonsa ne?"
Ya girgiza kai ya ce "bata sonsa ko kadan,tsana,tsana, haushi, haushi, mugunta, mugunta, qauna, qauna, fada, fada.
Na ji sanyi-sanyi a raina, tambayar da na yi ita "shi yana sonta ne?"
Boka ya gyada kai ya ce "shine yake sonta, sosai ma kuwa, amma ya boye, boyewa, boyewa,haushi, haushi, tsana,tsana, soyayya, soyayya."
Gashi shi ba cikakken nutsuwa da hankali irin na mutane gare shi ba baya yin magana sak irin ta mutane. Balle in tambaye shi abubuwan da yake nufi da wadannan maganganun na sa. Da yake ta fada yana ta maimaitawa, masu tayar da hankali. Na rikice na kasa gane in da ya nufa, ko ma dai menene maganganunsa babu alkhairi ko daya."
Na dora hannu akai na kurma ihu na ce "innalilahi wa'inna ilaihi raju'un. Wayyo Usman dina, na shiga uku. Yau yaya zan yi?"
Da na fadi haka sai boka ya rikice ya rufe ni da fada wai dan me zan yi masa addu'a anan gashi duk na rikita aljanunsa wasu sun fice da gudu. Baa yi musu addua a nan dan haka ba zai sake saurarena ba in tashi in tafi.
Karyayyun 'yan kunnayena ne na gwal na hado na d'aure a leda, da shi na je daman, dan na san dole ya caje ni kudi. Na fito na saka a cikin jakar da ake zubawa, na tafi jikina a sanyaye. Kuka nake ta gurzawa kamar raona zai fita, masu kwale-kwale suka dinga lallashina na qi na daina haka mai babur din da ya dauke ni yayi iya qoqarinsa wajen bani haquri da yi min nasiha, amma ban saurare shi ba, dan ba zasu taba gane halinda nake ciki ba ne.
Yau an bani baqin labarin da ban taba jin labari mafi muni irinsa ba. Na yi nadamar zuwana garin nan yau, dama na haqura na yi zamana ban zo ba.Ta ina zan fara yaqi da matan da ban sansu ba ban san illarsu ba? Ashe ma Mufidar da na tsana ita Usman baya gabanta amma kuma an ce shi a zuciyarsa yana sonta. Kenan wannan shigar da ya ga ta yi ne ya ji yana sonta da shawarta ko tun kafin nan ma? Ai dole ya so ta na tabbatar daman zai so ta dan ta hada duk wani abu da na san Usman yana so a jikin mace."
Na yi dare sosai dan sai qarfe goma na iso gidan Hanne, ni da me tasi yara gaba daya sun yi bacci.
Hanne na ganina ta rufe ni da fada wai na dade ban dawo ba daga cewa gani nan yanzu-yanzu, gashi na bar ta da yara ta sha wuya, basa jin magana, abincin da na bar musu a lunch box ya qare su na jin yunwa sai tuwon dumamenta ta basu dukka. Maana dai qarin kudi take so.
Ban ce mata komai ba, ta taya ni tashin yara da harhado lunch box dinsu muka duru a cikin mota. Bata daina yi min mita ba kuma ta ci gaba da jira in miqo mata kudi. Na cewa me tasi ya ja ya tafi, ina ji tana cewa ai dan tuwon gobe ake wanke tukunya . Oho! Goben komai ta fanjama-fanjam bani da shi. Babun zan bata?
Mu ka isa gida cike da fargaba da saqe-saqen qaryar da zan yiwa Usman, bani da hujjar da zan yi amfani da ita wajen kare kaina.
Na tabbatar zai tambaye ni ya ce daga ina na dauko yara da daddaren nan? A ina na bar su bayan an tashi daga makaranta? Zai gansu da kayan makaranta zai tabbatar ba mu dawo gida ba. Toh a ina na ajiye su? wacce irin seminar ce har qarfe gomar dare?
Cabdijam akwai matsala sosai kuwa. Ina shiga farfajiyar gidan na ga banga motar Usman ba sai na ji sanyi-sanyi a raina, na ci gaba da addua Allah Ya sa ba gidan radiyo ya tafi filin cigiya da sanarwa ba.
Safiya na hango tana ta leqe-leqe, daga ta ji motsi sai ta leqo ashe ni take jira. Na kalle ta na kawar da kai ina qoqarin hawa sama, yara har sun yi gaba.
Ta fito da sauri ta tari gabana, fatana ta cakume ni da fada ni kuwa in sauke yaron da yake hannuna in lillisata. Ta ga alamar haka dan haka ta sauko da muryarta qasa.
Ta ce 'Fatiti da gaske can kika je kuwa? Stephanie ta kira mai acabar da suke shiga da su ciki, akan ya saka ido ko zai ga wata musulma mai hijabi ko abaya ya fada mata. Amma wuni guda su na waya ya ce gashi yana ta jira bai ganki ba. Na san dai wasa kike ba can kika je ba ko?"
Na yi tsaki na kauce zan tafi, ta sake tarar gabana ta ce " haba Fatiti kin qi yin magana, kamar ba da ke nake magana ba."
Wannan karon dogon tsaki na ja na harare ta sama da qasa na ce "kada ki sake tarar gabana, ki bar ni in shiga gidana. Ina ruwanki da rayuwata? Tunda na zama talaka ai bai kamata ki dinga Kula talakawa ba. Ke da stephanie ne ya dace ku yi qawancenku me kudira me kudi."
Za ta sake yin magana na bangaje ta na haye sama, na bude gida muka shiga. Alhamdulullah! Usman baya nan sai dai ban san sanya ya fita ba. Bayan yara sun ciccire kayan makaranta sun saka na bacci sun tabbatar min da cewa a qoshe suke sun ci tuwo da yawa sai na ce su kwanta bani da qarfin da zan iya yi musu wanka duk da qurar da ke jikinsu badudu.
Da sauri na fita wajen Tanimu da kudin biredina a hannu amma biredin ne damuwata ba, dan kawai in ji labarin Usman ne. Tanimu ya ce ai tun safe oga Usman ya fita bai dawo ba.
Ya na rufe baki sai ga Usman ya turo hancin motarsa bakin get. Tanimu ya tafi da gudu ya wangale masa get ya shigo, na so in tsare dan kada ya ganni amma babu yadda zan yi ya riga ya gan ni.Ya yi ta kallona, kallo irin na tuhuma mai cike da alamar tambaya.
Kafin ya ce wani abu sai da ya kalli lokaci a jikin agogon wayarsa, qarfe goma sha daya na dare.
Sannan ya dube ni ya tambaya "daga ina zuwa ina?"
Na dan yi in-Ina na ce "yanzu na sauko, biredi zan aiki Tanimu ya siyo min yunwa nake ji."
Kallon tausayi yayi min ya ce "kada ki aike shi zo mu shiga ciki."
Ya wuce da motarsa waje da yake ajiye ta, na biyo shi da qafa. Ledoji a cike da kaya yayi ta miqo min, shima ya cika hannayensa biyu da manyan ledoji, da alama ya shiga super market daga nan yayi wadannan siyayyar. Fuskarsa cike da fara'a haka jikinsa babu alamar yaqunewa ko galabaice.
Sai na ji zuciyata ta harba, na dube shi cike da mamaki kafin in jero masa tambayoyi sai ya katse ni ya ce mu je sama tukunna.
Da Safiya muka hada ido tana ta leqe ta windon dakinta ta ga abinda ta dade bata gani ba, sai na canja tafiya ina karkade leda dan ta gasgata shopping ne mijina yayi min.
Na tabbatar hankalinta a tashe yake dan mijinta bai dawo gida ba har yanzu, da alama ya fara komawa gidan jiya sai ya kai tsakar dare tun safe ya ce tiyata yake yi. Amma daga lokacin da ta yi asirin nan, qarfe shida a gida take yi masa kuma baya sake fita sai washe gari.
Shine take so ta ji shin ko da gaske na je na karya ko qarya nake yi, ni dai ba zata ji mutuwar sarki a bakina ba.
Mu ka shiga falo muka baje ledoji, Usman ya ce in firfito da

11 / 13