Author : Jamila Umar Tanko Category : Romance
saka a tsakiya mu na ta jerowa tambayoyi. Ta dinga dariya ta ce yau shekara nawa da take bamu labarin mutumin amma muka qi zuwa? Da farko dan ta ja mana rai ma cewa ta yi wai ya mutu . Hankalinmu ya tashi ashe wasa take sai daga baya ta tsaya muka yi maganar gaskiya da gaskiya. A bakinta ma muka dinga jin labari Murjanatu Bibi dan mu ashe ma bamu san komai ba ma a kanta sai sama sama. Tabbas barin Murjanatu da Mufidah a gidan nan tamkar ajalinmu ne.
Ta qirgo mana ranakun da baya aiki a ciki har da litinin, sai ta bamu shawara mu je ranar lahadi kawai ita ce ranar da aikin ya fi ci kuma itama ta na gida ba ta zuwa aiki. Gashi garin da nisa sosai bayan an je Billiri zaa dauki hanya can ciki, bayan tafiyar mota ta qare sai a hau babura, bayan tafiyar babura ta qare zaa hau kwale-kwale.
Innalilahi wa inna ilaihi rajuun kawai nake karantowa, dan a iya ilimin addinin da nake da shi na tabbatar zaa bata anan tabbas akwai sabon Allah. Amma sai in tuna cewa za mu yi ne dan mu ceto mazanmu daga halaka, ba kisa, babu hauka ko saka ciwo, kawai a farraqa su, babu su babu su har abada.
Mu ka kwana muna shirya yadda za mu yiwa mazanmu qaryar da za su bari mu fita unguwa tun da sassafe har dare.
Yaya zan yi da yaran nan, ga shi lahadi ce babu makarantar boko? Sai na tuna ashe a makarantar islamiyya tahfiz suke wuni daga qarfe takwas har qarfe shida. Qaramin ne abin ji, mai shan mama na san Usman ba zai yarda in tafi in bar shi ba. Yaya zan yi da shi toh? Dan tafiyar nan mai nisa ba zata yiwu da yaro a bayana ba. Sai na tuno da gidan Hanne mai kitsona, tunda yana shan abincin gwangwani, ya na kuma cin kwai da dankali kawai in hada kayan abincin in kai shi, sai in biya ta kudi mai yawa na san idan ta ga kudi zata riqe min shi da gudu ma kuwa, ba tare da Usman ya sani ba.
Toh amma in tafi in bar Usman a gida shi kadai gashi ga Mufidah ga Murjanatu hankalina ba zai kwanta ba. Meye abin yi? Ina mafita?
Washegari na kebe ni da Safiya a gefe na fada mata abinda na ke ta hangowa. Safiya akwai kaifin hankali ta ce daman ba zata tafi da mus'ab ba zata je ta dauko qanwarta budurwa Halima a gidan yayarta dan ta kula da Mus'ab. Amma sai su hau sama su zauna a gidana saboda a ranar Dakta zai yi tafiya zuwa garinsu Misau daurin aure. Toh sai a cewa Usman zasu zauna a sama saboda ya fi tsaro, kada su zauna a qasa su kadai. Ita kuma Halima mu ce ta saka mana ido ta dinga ganin shige da ficen Murjanatu da Usman.
Sannan sai na tuna da cewa an ce fa aikinsa kafin ka zo gida ya ci. Meye ma abin damuwa tunda a ranar zaa farraqa su. Sai na daina damuwa na kwantar da hankalina.
Tabbas qaryar da muka shiryawa mazanmu ta tsaru kuma sun amince zamu je mu yini a unguwa. Amma fa unguwar anan cikin garin Bauchi ne muka ce, a radio muka ji sanarwa zaa yi seminar ta yini daya daga qarfe bakwai na safe zuwa shida na yamma, kyauta ne kuma mata zalla ne. Zaa yi lacca ne akan raino da tarbiyya a musulumci da kuma koyar da girki da tsaftar jiki da ta gida.
Nan da nan suka yarda har da murna, da alama sun ga kamar mun fara sanin darajar kanmu zamu nemi ilimi. Usman har wani lallaba ni yake, kin ga daga nan ma zaa fadakar da ku akan muhimmancin neman ilimi 'ya mace. Shekara mai zuwa kawai ki fara karatu. Na amsa masa da insha Allah admission dinma da kaina zan nema.
A tunaninsu ganin wayewar Murjanatu da Mufidah ne ya koya mana hankali, nan kuwa basu san dawan garin ba.
Ranar lahadi na tashi tunda asuba na shiga kicin na shiryawa yara abincin da zasu yini su na ci a tahfiz, na ware na Usman da zai yini yana ci dan na tabbatar jiya sun ci abincin Murjanatu na qarshe yau nawa zaa ci a hada da haquri, ma'ana a dawo gidan jiya abincin garau-garau.
Na goya dana 'dass' a bayana na rataya jakar raino na yi musu sallama. Na shaida masa Halima qanwar Safiya zata zo ta zauna da Mus'ab anan sama saboda kada a bar su a qasa su kadai. Usman dai kamar bai ji dadi da hakan ba, ya shiga tunanin dalilin yin hakan tunda ai ga Dakta a gida zai yini. Na fitar da shi daga kokonto na ce Dakta zai je garinsu Missau daurin aure.
Na yi sallama da yara na fito, Safiya ma da Halima da Mus'ab suka fito ta rufe gida su Halima suka hau sama. Gidan Hanne mai kitso muka nufa daman na fada mata komai a waya tun jiya. Babu bata lokaci na dire mata yaro daman an ci saa yana bacci muka kwasa muka yi gaba. Stephanie ta dade a bakin titi tana jiranmu, sai kawai muka hau mota tasi muka tafi tasha ba tare da bata lokaci sai muka nufi garin Billiri.
Daga nan fa tafiya ta fara wahalar da ban taba sha ba a ranar na sha ta, gashi ban iya hawa acaba sosai ba a dole na koya amma fa sai da na qone da salansa kuma sau biyu ina tiqowa daga kan babur duk na daddauje qafa da hannu. Abin tausayi har da kuka na sharba gami da tsinewa su Mufidah dan duk su ne suka jawo min.
A qarshe dai mun isa da misalin qarfe biyu da rabi na rana, babu ci, babu sha, a galabaice idanuwanmu cike da tsakin qasa. Ganin bokan ma ya isa abin tsoro balle ka ji muryarsa da abubuwan da yake yi na tsibbu. Shi ya bamu labari ba mu muka bashi ba. Ya kira sunan Murjanatu ya ce an gama da ita, amma da ya zo kan sunan Mufidah sai ya daka tsalle yayi gefe, ya dade ya na ta kiraye-kirayen sunayen abin bautarsa, ya dinga jinjina kai daga qarshe bai ce da mu komai ba. Mu ka dinga zayyano abinda muke so mazanmu su kasance ba ma so su qara ganin wata mace su ji su na sonta bayan haka a raba su da duk matan da suke binsu su na sonsu. Su ji su na sonmu mu kadai son da sai abinda muka ce musu zasu yi, kada su dinga yi mana musu. Ya ce da mu an gama mu tashi mu tafi.
Ya jehowa kowannenmu qullin magani baqi-qirin dan mitsitsi.
Ina da tambayoyi masu yawa amma babu halin tambaya, na fara jerowa ya daka min wata uwar tsawa sai da na ji kamar kunnuwa zasu kurmance, ya yi mana korar kare. A cikin wata jaka ta fatar damisa ake zuba kudin da ya umarta, mu bayar. Har da dalolin da Murjanatu ta bani na hada dukka na zuba saboda ya ce kowacce ta bada naira dubu sittin-sittin. Tattalin arzikinmu kakaf muka juye masa har sai da stephanie ma ta cikawa Safiya naira dubu goma sha biyar.
Mu ka fito zuciyoyinmu cike da kokonto. Kamar yaya zai ce mu tafi an gama babu komai? Sai wani dan qaramin baqin magani ya ce mu zuba a bakin get da matattakala da bakin qofofin shiga gidajenmu. Qullin maganin ma dan mitsitsi. Mu na ta qorafi dai da tsaki da harare-harare.
Stephanie ta ce wallahi mu rufe bankinmu dan yana jiyo mu idan mu na kokonto zai bata aikin. Mu ka tafi kowa cike da haushi da rashin yarda ni na fi zargin Stephenie ma, ina zarginta da hada baki da yi mana damfara.
Ba mu iso gidan Hanne ba sai qarfe takwas dai-dai na dare, na iske yarona lafiya ya ci ya qoshi yana wasansa da yara. A gaggauce na dauke shi muka isa gida. Tanimu mai gadi muka aika shago dan kawai ya matsa mu aiwatar da aikinmu. Kowacce ta barbada garin magani muka rage sauran da zamu barbara a bakin qofofinmu. Mu ka shiga gida kowacce cike da tunanin qaryar da zata sake shirgawa mijinta. Safiya ta cika da murna da ta iske babu motar Dakta bai dawo ba, sai ga Halima da Mus'ab sun sauko dan ya ga dare yayi bai ga uwa ba ya fara koke-koke, ta sauko dan ta lallashe shi, aka yi katari ma mun dawo. Safiya ta barbada ragowar maganin a qofar falonta. Na fara hawa sama ina barbadawa akan matattakalar.
Kamar daga sama na ga Mufidah a tsaye a bakin qofarta ta kama qugu, gabana ya yanke ya fadi, na zabura saura kadan in yi cilli da ledar maganin, na dai daure. Ta na yi min wannan kallon da ta yi min a falon Safiya, kallo ne wanda ba na lafiya ba. Idanuwanta ne ke kafewa ba ta qiftawa.
"Auzubillahi minal shaidanir rajim" na fada a bayyane. Hakan bai sa na fasa watsa ragowar maganin a bakin qofata ba, amma a boye ta cikin hijabina. Na yi sauri na afka cikin falona na ci saa qofar ba a kulle ba. Ina shiga na iske falon ba kowa sai na saka mukulli na datse na leqa ta jikin hudar qofa ina kallonta.
Wannan karon saitin qasan qofata ta qurawa ido in da na barbada maganin, take ta kallo. Abin mamaki sai ta dago ta qurawa hudar da nake leqata ido, caraf muka hada ido, yayin da na ji wani abu ya tsarga min tun daga sama har qasa. Na ja da baya da sauri ina mai karanto qulaquzai. Ma tambayi zuciyata "anya kuwa wannan ba maiya ba ce?
Bugun qofata ake yi da qarfi sai na sake razana na ja da baya, muryata na rawa na tambaya waye?
Ya ce "Tanimu ne, ga biredin na kawo."
Na yi ajiyar zuciya na je na bude a hankali. Qofar Mufidah na fara kallo, na ga bata nan ta shige ciki. Na karbi sakon na yi godiya. Abin mamaki maimakon ya sauka qasa sai ya juya qofar falon Mufidah zai buga, nan da na na kira sunansa na tambaya. Lafiya zai buga mata qofa? Sai ya sanar da ni labari mai dadin gaske cewa direban Murjanatu ne yana waje ya zo daukar Mufidah ne daman ita Murjanatu tunda rana ta kwashe kayanta da masu aikinta ta koma gida, yanzu Mufidah zaa dauka zata yi jinyar acan... Bai qarasa bani wannan labari mai dadi ba na ce ba damuwa buga mata qofar.
Na yi sauri na shige ciki na datse qofata. Ina shirin sauke goyo sai na ji wayata tana ta ruri a cikin jakata, ina dubawa na ga Safiya ce, cike take da murna ta fara bani albishir cewa Halima ta bata labarin duk abinda ya faru. Wato babu abinda aka yi Murjanatu ta dauki akwatuna da masu aikinta ta ce ba za ta kwana a gidan nan ba ita gidanta za ta koma. Ta ce In Mufidah bata shirya tafiya yanzu ba toh da daddare zata aiko direba ya kai ta. Usman ya na ta yi mata magana ko kallonsa bata yi ba ta kwasa ta tafi.
Mu ka dinga murna gami da hamdala da mamakin wannan irin aiki kamar yanka wuqa. Ban gama wayar ba Usman na hango ya fito daga daki. Na yi sauri na katse wayar. Maimakon ya yi fushi ko ya tutsiye ni da wadannan tambayoyin na sa, amma murmushi kawai yake yi min gami da rungume ni ya yi min sannu da zuwa.
Yara sai yanzu su ka jiyo muryarta dan haka da gudu suka firfito su na murna su na tsalle, sai a lokacin na tuna ana yin tsaraba ashe in an fita unguwa gashi ban siyo musu komai ba, amma na tuna ina da alewa a daki. Sai na yi musu dubara na ce su zazzauna zan dauko musu alewa idan na zazzage kayan jakata a daki.
Na shiga daki na kwantar da Haidar na debo alewa a durowata na fito na rarraba musu. Usman sai kallona yake duk in da na gifta, yana yi min murmushin so da qauna, irin kallon nan na kamar in hadiye ki din nan.
Dadi ya kama ni na yi hamdala ga Allah da Ya bani iko na qwato mijina daga hannun muyagun mata masu kidnapping zuciyoyin mazan mutane.
Bayan na yi wanka na yiwa yara wanka su ma sai na ce duk su je su kwanta gobe litinin akwai makaranta.
Na shiga kicin a gigice saboda tsananin yunwar da nake ji, na iske babu abinci duk sun cinye dukka. Na duba ko ina har cikin shara ban ga takarda mai kalli irin wacce Murjanatu take na do kaza ba wato (powl peper) ba, daga na tabbatar yau Murjanatu bata kawo abinci ba. Na yi murmushin jin dadi, a gaggauce na dafa indomie guda uku, na zuba kifin gwangwani na soya kwai. Dan na tabbatar Usman idan ya ga abincin nan sai ya ci.
Ashe kuwa yunwa yake ji bai ci abincin dare ba duk yara sun cinye, mu na ci muna hira da gangan sai in bata rai dan in gwada aikin nan da nan sai ya gigice yana lallashi. Duk motsin da na yi sannu yake yi min.
Ya tambaye ni ina littafin jotar da na rubuta abubuwan da aka koya mana? Sai na ji gabana ya yanke ya fadi, na yamutse fuska na ce su na jakar Safiya. Zai sake jeho wata tambayar sai na tsuke fuska nan da na ya yi kwana.
Na gyara zama na harare shi na ce " yau kuma baa kawo muku abincin professional chef Jimoh ba ne, na ga ka qare a indomie da kwai?"
Ya gyada kai ya ce " ina ga Murjanatu ta bar gidan nan, na ga kamar ranta a bace ta hada kayanta ta tafi, ina yi mata magana ma bata amsa ba. Kin san halinku na mata akwai qananan maganganu, gulma ba ta yi muku wuya. Ban sani ba ko fada suka yi da Mufidah oho. Amma na yi mamaki a iya sanina da Murjanatu bata taba yarda ayi fada da ita, kuma bata da saurin fushi. Ban dai gane ba kuma fa har ta leqo ta tsaya a bakin qofa muka yi hira, ta tambaye ina dakta isa? Na ce yayi tafiya yau baya nan."
Ta ce "kash! gashi yau mutuminsa zaa gasa wato Kifi."
Ta bar nan da misalin qarfe biyu da rabi ta shiga gidan Mufidah ba jimawa misalin qarfe uku, na ji ana ta karafkaraftu da akwatuna, ina leqawa na ganta a fusace tana tafiya akwatun na rinjayarta, akwatin ma ita take ja da kanta qatuwa ta yi mata nauyi ta hana su Jimoh su taya ta."
Fuskata cike da faraa na ce "toh a lokacin ina Mufidah take?"
Ya ce "da na leqa na ganta a tsaye a bakin qofa tana ta kallonsu kawai. Kin san ita miskila ce wani lokaci bata magana sai kallo sai harara. Na leqa ina magana da Murjanatu na ga Mufidah na ta harara ta, sai kawai ma na shigo ciki na rufe qofata, wannan dalili ne ma ya sa ban bi Murjanatu qasa ba, balle na ji dalilin tafiyarta haka babu shiri."
Na tsuke fuska na ce " na ga kamar ka damu da tafiyar da Murjanatu ta yi ko?"
Ya zabura ya girgiza kai ya ce "damuwar me? Na dai huta dan na ga alamar ba kya son hulda ta da ita, kuma in dai tana nan ba zata iya zama a waje daya ba, dole sai ta shiga harkarmu. Gara da ta tafi ki huta nima in huta. Ko mai love?"
Na lagwabe kai na ce " na zaci dadin abincinta kadai ya isa ka yi kewarta."
Ya ce " duk sanda na ci wani abincin da ba na ki ba bana jin daidai sai dai a bisa larura. "
Daga wadannan kalamai na tabbatar Usman ya shiga cikin kwalbata na rufe zuciyar 'bammmm' na jefa mukullin a teku. Daga ni sai shi, na huta zulumi da fargabar wata zata kwace min shi.
Da ya ga ciwukan da na