Author : Jamila Umar Tanko Category : Romance
komai. Sai ga kwai, ga dankali, ga danyun kaji, ga gasassun kaji, ga birdie, madara, milo corn flask, biskit, alewa, cincin, kori, maggi, Pampers, pad , saubulan wanka masu tsada irin namu na da , omo, turararruka na fesawa da roll on har da room fresheners.
Na kalle shi cike da mamaki zan yi magana, ya as hannu ya toshe bakina yana ta murmushi, naira dubu ashirin ya miqo min ya ce in ajiye na cefane.
Na gyara zama na yi tagumi ina jiran in ji labari. Ya ce in kai kicin in jera. Shi zai shiga wanka, nima in yi wanka in yi masa ado da rigar bacci mai kyau mu zo mu ci kaji sai mu yi hirar. Ya wuce zuwa dakinsa fuskarsa cike da nishadi.
Abinda ya fara zuwa zuciyata shine asiri ya karya sun hadu da Murjanatu Bibi ita ce ta bashi kudin nan. Sai na ji sanyi a raina na kinkimi kaya na je na jejjera a inda ya dace, na wuce na shiga wanka. Duk rigar baccin da na dauko sai in ga ta yi shige da wadanda Mufidah ta saka ba zan saka ba balle ya gani ya tuno da ita dan haka sai in ajiye. Daga qarshe dai riga da wando na saka dan Mufidah bata saka mai wando ba.
Da ya fito daga dakinsa dakina ya shigo, ya same ni ina fesa turaren da ya siyo mana.
Ya lumshe ido ya ce "na yi missing wannan qamshin."
Ya kamo hannuna muka fito falo, ni dai na yi sororo gani nan gani nan dai bana fara'a saboda labaran da boka ya bani masu daga hankali ne matuqa, na rasa ma ta in da zan fara.
Ya ce in dibarwa yara kajin in saka musu a firij gobe sai a dumama musu in zasu je tahfiz. Na ce na riga na dibar musu. Mu na cin kaji masu dadin gaske ga dumi, ga laushi, yana ta yi min labaru masu dadi da kalaman soyayya. Ya ga dai bana mayarwa.
Ya ce "na fuskanci kin qagu ki ji in da na samo kudi nan ko? Toh ki yi haquri zan baki labarin komai yanzu kuwa."
Na tabe baki na figi cinyar kaza na ce "na san bai wuce Murjanatu Bibi ba ce ta baka kudin nan. Wataqila ta yarda kun hadu a yammacin nan."
Ya tsuke fuska ya ce "haba dai Allah Ya sawake ai na yi alqawarin ni da Murjanatu har abada, ba zan sake nemanta ba. Na yarda matsalar ta kashe ni da in sake kallon in da take ai wulaqancin da ta yi min ya isa."
Na tsaya ina kallonsa cike da fargaba na ce "ka na nufin baku hadu ba?"
Ya ce "an ce ma bata qasar ta yi tafiya da dadewa shiyasa ashe bana iya samunta ma a waya."
"Bata qasar?" Na zabura na maimaita.
Ya gyada kai ya ce "ba ta qasar, idan ta yi irin wannan tafiyar kuwa sai ta shekara bata dawo ba. Kin san fa ita haifaffiyar Amerika ce tana da takardar qasar, ita 'yar qasarsu ce cikakkiya karatuna kaf acan ta yi sai dai ta shigo Nigeria hutu."
Na yi sororo ina kallonsa cike da takaici da nadama na ji a raina dama ban je wajen boka na karya asirin da na yi ba, dan bashi da amfani.
Na ce " kuma ko da wasa bata kira ka a waya ba yau?"
Ya ce "ai na saka lambobinta a irin tsarin da ta saka ni, ko ta kira ba zai shigo ba haka ko ta turo saqo ba zai zo ba."
Na yi shiru ina tunani, can na dago na dube shi na ce "toh in ba Murjanatu ba ce, waye ya baka kudin nan haka?"
Usman yayi ta ja min rai ya qi ya fada min labarin nan sai da muka gama ci muka kora da lemo da ruwa muka wanke hannu.
Ya sake cewa mu je daki hirar zata fi dadi akan gado. Na tsuke fuska na ce "ni fa na qagu in ji kanun labaran nan."
Na zauna a gefen gado yana daga kwance yayi-yayi in matso kusa da shi in kwanta mu yi labarin, na ce ya fada min kawai ido na ganin ido.
Ya tashi ya zauna a tsakiyar gado ya fara labari, toh tun a sentence din farko na gigice na fita daga hayyacina, maganar boka ta fara fitowa kenan.
Innalilahi wa inna ilaihi rajuun mafarki nake ko a ido biyu? A wannan duniyar nake ko kuwa a wata duniyar nake? Usman dina ne wannan ko kuwa na yi gamo ne?"
[7/22, 11:52 PM] Jamila Umar Tanko: 10
Ido da ido Usman yake kallona yana fada min wannan mummunan labari.
Ya ce min "wannan matar da ki ka zaga a waya kwanaki matar mataimakin gwamna ita ce ta aika min in je gidanta.
Da ya ga hankalina ya tashi na fara hada zufa sai ya so ya dakata da labarin. A dole na lalubo nutsuwa da murmushi dan ya ci gaba.
Na yi murmushi qarfin hali na ce "ikon Allah baiwar Allah Yaya aka yi ta san in da kake har ta san ka sami matsala da banki?"
Ya yi murmushi ya yi shiru ya sunkuyar da kai qasa zuwa wasu 'yan lokuta sannan ya dago ya dube ni ya ci gaba da cewa."
"Ta na da qanwa mai suna Jalilah toh a gaskiya dai ina ganinta a gidan a lokacin da nake zuwa maganar kudin nan da zasu kai ajiya bankinmu amma ni bana ma na kallonta kuma bana lura da ita ba zan ce ga yadda kamanninta ma suke ba, na ga dai tana yi min hidima ta kawo ruwa, ta koma ta kawo lemo, ta kawo nama. Wai ashe ta sha zuwa bankinmu nemana bata same ni ba, 'yan Ofis dinmu su na ce mata ban qaraso ba, daga baya dai ta nemi da su fada mata gaskiya ko an yi min transfer ne. Sai abokina Sulaiman ya ja ta gefe ya fada mata duk abinda ya faru da ni."
Yadda na dinga jero ajiyar zuciya a jejjere ita ta katse Usman daga ci gaba da labarin. Ya dube ni cike da fargaba amma abin mamaki sai ya ga ina murmushi hakan ya qara masa qarfin guiwar ci gaba da labarin.
Bai gane cewa labarin nan nasa ya fi komai muni a kunnuwana haka ya fi komai zafi a cikin zuciyata, tafasa take tana qonewa.
Ya yi wani lallausan murmushi ya ce " in takaice miki dai ta karbi lambar wayata daga wajen abokina ta kira ni sau biyu, ta dinga yi min bayani na nuna ban santa ba nace kawai ta daina kirana. Daga baya sai kawai na ga kiran wayar her excellency yayarta ita ina da lambarta, nan da nan na amsa. Abinda ta ce min shine kawai in zo gidanta tana da magana da ni. Sai mamaki ya kama ni saboda ko ta yarda ne zata bani ajiyar kudin ne amma ta makara yanzu ba zai amfani ni da komai ba sai dai in hada ta da abokaina."
Kafin Usman ya dire maganarsa zuciyata ta gama ci da wuta ta fado farfajiyar qirjina wani abu na ji ya diro a qahon qirjina, sai na zabura na miqe tsaye a gigice na ji kawai ba zan iya jure jin qarshen labarin ba amma kwakwalwata tana cewa ki daure don ki ji komai ki kama shi da hujja.
Ya daga ido da sauri yana tambaya "Fatiti lafiya kika zabura kika miqe tsaye?"
Cikin rawar murya na ce "zan shiga bandaki ina zuwa, sai mu ci gaba. Ina shiga bandaki na saka mukulli na kulle na qurawa kaina ido a mudubi ina kallon jajayen idanuwana, gumi ne ke keto min fuskata ta yi jajawur itama. Na wanke fuska na jima ina haki sannan na samu zuciyata ta dan daidaita sai na fito.
Na iske Usman yana karanta wasu sakonni a wayarsa fuskarsa cike da murmushi, kawai sai zuciyata ta yanke hukunci cewar Jalilah ce.
Ya na ganina ya ajiye waya da sauri hakan ya tabbatar min da rashin gaskiyarsa a bayyane.
Ya ci gaba da cewa "cike da fargaba na isa gidan aka yi min tarya ta musamman, amma na yi mamaki da na ji Her excellency ta san duk matsalar da nake ciki. Ta ce me yasa ban fada mata ko in fadawa mijinta ba? Ashe har da kora daga aikin da aka yi min an fada mata cewar akwai bashi banki da ake bina, kullum ana yi min barazanar zaa dauri ni.
Cikin jin nauyi na tambaya yaya aka yi su ka sani? sai ta ce min ai Jalilah ce ta je bankin nemana ta tarar bana nan. Ta nuna min ita sai a lokacin na dube ta na gane cewa ashe ita ce ta sha kirana tana bayani, har ta bi ni whasapp tana yi min magana na ga hotonta a DP sannan na gane ta."
'Hmmmm! Hmmmm!!" kawai nake ta jerowa. Ya takaice min labari sun tambayi yawan kudin ya fada musu kuma sun tura masa ta account dinsa a take kafin ya bar gidan a matsayin rance kuma har suka qara masa dubu dari biyu wannan kyauta ce dan ya dinga cefane. A ciki ma ya kashe mana naira dubu hamsin yayi mana cefane.
Daga nan ya ja bakinsa yayi shiru yana nufin a banza ma kenan suka bashi wadannan maqudan kudi bai san dalili ba.
Na ci gaba da sauraronsa gami da qura masa ido, bai sake cewa komai ba.
Na ce "ina sauraronka ka ci gaba mana."
Ya yi murmushi ya ce "shikenan ai, fatana Allah Ya hore min in biya su kawai, sun taimake ni sosai, kuma ba komai ba ne addu'a ce Allah Ya amsa. Dan kullum ina addua Allah Ya rufa min asiri ta in da ban zata ba, kada banki su wulaqanta ni a kama ni cikin ankwa, su buga ni a jarida kamar wani dan fashi."
Na tabe baki na girgiza kai na ce "a tunaninka ne shikenan amma ni na san da magana a qasa."
Ya yi min duba na rashin fahimta. Zai jero min tambayoyi sai na zabura na tashi na bar masa dakin na koma falo na kwanta akan doguwar kujera ina ta huci. Abinda zuciyata ta kitsa min shine babu maganar boka ko Malam kawai ni zan yi yaqi in kwato mijina. Na daina ragawa duk wata mace da za ta shiga gona ta. Na gano manufar Hajiyar nan shine ta yi qudirin sai ta aura masa qanwarta dan kawai ta rama zagin da na yi mata. Tunda ba zata iya aurensa ba shine zata aura masa qanwarta, suka yi amfani da dukiya da kuma halin da yake ciki suka siye shi da kudi.
Yadda yake bayar da labarin yana murmushi alamu sun nuna yana so shima, amma tabbas zai tafka babban kuskure idan har ya ce zai auri Jalilah.
Usman ne ya katse min tunani, na ji ana girgiza ni, na runtse ido kamar mai bacci na qi budewa. Daga nan ya tabbatar fushi na yi. Ya fara kame-kame irin na su na maza idan sun yi rashin gaskiya.
Ya daga kaina ya zauna ya dora kaina akan cinyarsa ya fara tambaya "Fatiti fushi kika yi ko? Daga baki labari sai ki yi fushi? Ki na so in fara boye miki halinda nake ciki kenan nan gaba?"
Maganar boka nake tunawa ya ce bayan wannan ma akwai wata mai sonsa tana ta taface- tsaface akansa kuma itama a jiya sun hadu.
Na zabura na tashi na zauna na kalle shi cike da takaici na ce "bayan itama ai jiya ka je wajen wata itama sonka take."
Ya yi shiru yana kallona cike da mamaki can ya ce "wata wa? Ban je wajen wata ba, kamar yadda kika sani wannan baya cikin tsarina."
Na tabe baki na ce "wallahi ka na da wata da take sonka kuma kun hadu jiya."
Ya dade yana tunani sai can ya ce "Minat? Na dai hadu da wata abokiyar aikina a wajen siyan gasassun kajin nan."
Gabana ya yanke ya fadi na tambaye shi a rikice "wacece Minat? Kuma meye alaqarka da ita?"
Ya dan yi jugum sannan ya ci gaba da cewa "ta na aiki da mu ne a matsayin 'yar bautar qasa shikenan."
Na ce "tana sonka amma, kuma da aure."
Ya ce "wataqila zai iya yiwuwa amma a zuciyarta dan ni ban san tana yi ba. Na san dai mu na mutunci a ofis. Ta sha gayyatarmu cin abinci gidansu ni da abokan aikina gidansu, gaskiya ban taba zuwa ba.Ta yi birthday party ma ta gayyace mu a wani Restaurant gaskiya gaba daya ban sami zuwa ba amma abokan aiki wasu sun je. Aka ce min Minat tana fushi da ni fa dan ban taba amsa gayyatarta ba, kuma saboda ni take gayyatar. Ban damu da in binciki dalili ba dan kawai bana so ma wata alaqa a tsakaninmu ta yi qarrfi, kawai sai na bata haquri.
Jiya kuma ban ganta ba ma bayan na je na yi placing order kaji na dawo na zauna a mota ina jira saboda akwai layi sai na ga an bude gaban motata an shigo ina dubawa na ga Minat ce itama ta zo siya tana zaune a motarta ta hango ni. Mun dade mu na hira dai tana ta jajanta min akan abin da ya same ni, kuma ta ce tana qoqari ta ga wani abokin Babanta yayi Regional manager a bankin ko zai iya taimaka min. Na ce mata na gode kawai."
Zuciyata ta dinga bugun uku-uku na harare shi " na ce amma ka gane akwai soyayya ko?"
Ya girgiza kai ya ce "ke ni fa matsalar da take gabana ita ta dame ni, ban damu da maganar 'yan mata ba. Ta ina zan iya qirga mata masu son namiji, wasu customers ne, wasu kuma a meeting zamu hada, ko seminar kawai sai su sami lambar mutum su yi ta kira. Na fada miki ki daina damun kanki mu ci gaba da addu'a in da alkhairi kawai Allah Ya dawo min da aikina."
Zuciyata ta dinga tafasa kaina yayi min nauyi abubuwa sun yi min yawa, na rasa ma me zance masa. Gashi dai bai yi min qarya ba kuma bai nuna alamar ya razana ba, dan haka iyakacin gaskiyarsa kenan .
Ya ce in zo mu je mu kwanta na ce yau a falo nake son in kwanta, ya dade yana jirana da ya ga da gaske ba zan taso ba ya tashi ya shiga cikin dakina ya je ya kwanta. Can da jimawa na ji kukan Haidar sai ya dauko shi ya kawo min shi na yi kamar ina bacci, yayi ta tashina dakyar na bude ido na karbe shi na sake gyara kwanciyata.
Daga gani babu tambaya ya san fushi nake, ya tafi daki ya kwanta ban sani ba ko ya samu yayi baccin, ni dai yadda na ga rana haka na ga dare ga gajiya ga tashin hankali dole ma in yi ciwon kai.
*** *** ***
Washe gari ma haka muka yini babu dadi ya rasa kaina, kayan abinci da kayan dadi gasu na kala-kala amma na kasa ci sai yara ke ta murna su na hidimarsu. Ya ce su zauna a gida su huta. Su ka wuni su na wasa da mahaifinsu a gida. In an tambaye ni meye matsalata ba zan iya fada ba, ba komai ba ne haushin Jalila da Minat kawai, dama zan gansu tabbas da na koya musu