Author : Jamila Umar Tanko Category : Romance
waje ya hargitse da hayaniya su dukka ukun baa jin abinda wani ke cewa, fadan dai da turanci ne don Godwin baya jin Hausa.
Ba na gane abinda kowa yake cewa amma naga ana magana ana nuna juna da yatsu, Godwin na qoqarin shiga tsakiyarsu.
Daga baya na hango Mufidah a fusace tana tafiya a tsakiyar titi zata tsallaka ba tare da ta duba motocin da suke rarakar gudu ba, wata qatuwar mota ce ta tako da gudu qirar tirela tun daga nesa take sakin wasu mugayen horn, direban dannawa yake yana sake dannawa da alama da Mufidah yake dan lokaci ya qure ga motoci a bayansa ba zai iya taka burki ya tsaya ba. Da alama bacin rai ya yiwa Mufidah yawa bata cikin hayyacinta a lokacin bata qi duniya ta kife da ita a ciki ba, ba ta qi sama da qasa ta hade da ita a tsakiya ba. Ba ta qi ayi girgizar qasa ta afka ba.
Innalilahi wa inna ilaihi rajuun Allah kada ka nuna min abinda na gani a ranar. Usman da Mufidah na gani a rungume da juna a kwance su na ta murmurginawa a gefen titi. Da gudu ya tafi ya finciko ta ta fado jikinsa suka fadi a gefen titi sannan ya sake murginawa da ita don su bar kan titi domin saura kadan motar ta murtsike ta.
Hankalina ya tashi wannan karon abin nan da na gani ya fi komai muni a rayuwata yadda Usman ya zabi ya ceto ta, shi kuma ya rasa na sa ran, yadda yake da kyamar taba hannun matar da ba tasa ba a yau gashi ya rungume wata mace a kwance a qasa su na murgine murgine. Akan idona ina raye muraran na ga mijina da wata a haka duk da ma ba haduwar kwanciyar hankali ba ce, a cikin tashin hankali ne. Amma ni na jawo masa na jawowa kaina, da ace na bar shi yayi baccinsa da bai fito sun ga juna ba har ya kai su ga runguma.
Godwin tunda ya dora hannu aka har yanzu bai sauke ba ya ga masifa, daga baya suka taru akansu har da su Dr.Musa da Isa na hango, Safiya da Umma duk sun fito saboda ihun Godwin da masu gadi. Na sanqare a tsaye cike da fargaba gami da takaici, sai can na zabura na sanya hijabina na fito da gudu, na iske abu fa ya yi muni gaba daya sun guggurje hannaye da qafafuwa. Mufidah ta suma bata farka ba. Usman kuwa farar rigarsa ta farfashe ta baci da jini. Wasu na cewa a je asibiti wasu na cewa tunda ga su doctor a yi musu Dressing anan. Usman da qarfin hali duk jikinsa ciwo amma bata kansa yake ba ta Mufidah yake. Na riqe shi qam na ce ya zauna kada ya fadi, sai ya fisge ya tafi ya dago Mufida Dr. Isa ya taya shi suka cicciba aka shaga da ita falon Safiya kan doguwar kujerarta aka kwantar.
Ni ce na tsinto wayarsa da wayarta duk sun kwankwase da mukullin motarsa a yashe a qasa. Direbobin da abinda ya faru akan idanuwansu suka tsatstsaya sai suka yi fatan Allah ya kiyaye gaba suka shiga motocinsu suka tafi.
Ni da Safiya da Umma da Godwin ne muka nufi cikin gida muna ta tattaunawa. Ina dukan cikin Godwin in ji abinda Mufidah take fada masa. Ya yi bayani ya ce matar ta yi fushi sosai kuma shi a iya sanin da yayi mace ce da bata da fushi, tana da hankali da hakuri bai san abin da yayi zafi haka ba har ta ce ba zata sake yin sati daya a gidan nan ba sai ta tashi in samo mata wani gidan. Kudin shekara biyu ta biya bata cika shekara ba ma amma ta ce ta yafe ta bar kudin in samo mata wani gidan.
Godwin ya ci gaba da cewa "ni nake ta lallashinta har ta fara daukowa, fitowar oga Usman ne ya sake taso da tarzoma shima ya ce gara ya tashi da ya ci gaba da zama da ita a gidan. Sai fada ya hargitse. Ta fashe da kuka ta nufi titi zata tsallaka ba mu san ma in da zata je ba, wannan abu ya faru. Gaskiya yau Usman ya nuna shi namiji ne kuma mai imani da tausayi don ya jefa rayuwarsa a halaka dan ya ceto abokiyar fadansa. Wato dai fadan na su bai kai shi ga ya ji ya tsane ta ba tunda gashi har gara ma shi ya rasa ransa akan ita ta mutu. In nine muka yi fada da mutum ai bari zan yi ya je ya kwankwatse ma in huta."
Na ji haushin Godwin ya kama ni da yake ta yabon wannan alaqar dake tsakaninsu mai sarqaqiya.
Safiya ta kalle ni na kalle ta muka dan yi gefe dan ba ma so Umma ta ji balle ta yi mana waazi. Uwar tausayi Umma sai kuka take tana ta jerawa Godwin tambayoyi suka wuce suka shiga falon Safiya.
Na ce " Safiya ina cikin wani hali matar nan ta na ta shiga cikin rayuwar Usman, duk sanda na yi yunqurin hada wani hargitsi a tsakaninsu sai in ga kamar hanya nake basu su hade."
Safiya ta ce " kin ga yadda Usman da Dotor suke wadaqa a jikin matar nan da sunan ceto rai, kai gaskiya da sake. Ta fi mu komai da komai, musamman wannan kayan da ta saka matsatstsu ai kinga abinda na gani dai. Ga shi can dai ya samu dama da sunan ceton rai Allah ne kadai ya san in da zai shiga ya auna. Toh amma shi Usman da suka fada me yasa ya fi kowa gigicewa? Ai da ya bar ta motar ta yi ciki da ita duk mu huta."
Na girgiza kai na ce "na san halinsa da tausayi musamman ga mata da yara wallahi ya yarda ya mutu dan ya ceto Mufidah ba dan yana son ta ba, a'a haka dai imaninsa yake. Amma wallahi akwai matsala zaman Mufidah a gidan nan."
Sai muka jiyo Muryar Usman ya fara karatun qur'ani irin na ruqiyya. Nan da na muka bude baki mu na ta kallon-kallo ni da Safiya cike da mamaki.
Ta jawo hannuna muka shiga cikin falon da gudu. Umma ce ta zauna akan kujerar ta dora kan Mufidah akan cinyarta amma an sakawa Mufidah hijab din Safiya. Usman ya jawo qaramin tebur ya matso kusa da kunne Mufida yana karatu yana tofa mata.
"Rukiyya kuma, ta meye?" Na tambaya, babu wanda ya bani amsa.
Safiya ta jawo hannun mijinta ta ce " me ya faru kuma na ga an bar maganar likitanci an koma ta malamai?
Ya gyada kai ya ce "ba suma tayi ba na auna komai na ta normal ne, Usman ya ce ya ga alamar kamar bugun aljanu ne. Ranta ya baci da yawa wataqila tana da su, zaa yi karatun dai a gani ko za ta farka."
Na kalli Safiya ta kalle ni muka ci gaba da kallon ikon Allah. Sai can Mufidah ta yi ajiyar zuciya ta fara miqa. In ma aljanin ne toh 'yan iska ne, ta yaya ga Umma nan a kusa da ita ta rasa wanda zata jawo ta rungume sai Malam mai Rukiyya? Ta fashe da kuka ta jawo Usman ta qanqame shi tsam. Mu ka yi ta damben banbarewa abu ya gagara, Umma na jan Mufidah ina jan Usman shi kuma ya rasa inda zai ture a jikinta, ya san halina zance ya taba ta.
Ya ci gaba da karatu a kunnenta sai miqa take tana sake damqe shi. Ni dai hankalina bai dauka ba, ana rada a kunne an rungume juna sannan kuma duk ace baa ji komai ba. Na daka tsawa na ce a ina aka taba yin ruqiyya da lallashi? In sun qi sauka ka sakar musu duka mana, ka tunkude su kawai ta bar jikinka."
Ina kallon su dakta suna son yin dariya. Godwin kuwa ya dora hannu aka yana ta kiran abin bautarsa.
Umma dai tsakani da Allah tausayi take sai kuka ta tana sake jawo Mufidah jikjnta. Abu ya ci tura su Dakta suka saka hannu su na ta jan Usman nima na cire hijab na yi dammara ni da Safiya haka muka dinga Jan Mufidah muka hada gumi bayana kamar zai rabe sabo da tsugunno da kyar muka banbare su.
Ta koma ta kwanta akan cinyar Umma, hawaye ke ta zuba daga idanuwanta amma idanuwanta a rufe.
Na fada cikin bacin rai "Usman ka ja mata ayoyi masu zafi a qona su kawai kowa ma ya huta."
Wannan karon bude idanuwanta tayi dara-dara a tsatstsaye ta na kallona, kallon nan ba na lafiya ba ne. Na yi sauri na canja waje, sai ta sake waiwayowa ta ci gaba da kallona tun daga kaina har qafata na ji wani ya tsarga min kamar an yi min shocking da wayar lantarki. Daga nan na san akwai magana ko aljanu ko 'yar kungiyar matsafa ce. Gabana ya yanke ya fadi na shiga tofa mata lahaula da qulaquzai na fada a baya ne Auzubillahi minal shaidanir rajim na fi karfin duk wani mugu. Ba ta daina kallona ba sai da na fita daga cikin falon.
Ta juya daya bayan daya ta kalli kowa sai ta zabura ta tashi zaune da alama ta dawo hayyacinta. Kallo irin na mamaki ta ta yi, sai yuqura da sauri zata miqe tsaye sai ta koma ta zauna saboda raunikan da ke jikinta. Ta kalli hijabin da yake jikinta ta juya ta kalli Umma da Usman.
Sai Godwin ya matso ya yi mata magana ya ce ta kwantar da hankalinta ba komai ba ne hatsari ne ya kusa afkuwa Allah Ya kare.
Ta yi shiru tana tunani da alama kwakwalwarta tana boothing har ta tunano abubuwan da suka faru, sai ta qurawa Usman ido kamar tana yi masa kallon mamaki kamar kuma harara.
Usman ya tashi daga kusa da ita shima ya fito inda nake a tsaye muka hau kallon-kallo, kowannenmu cike da takaici.
Ta yi magana a fusace ta ce " Godwin ka kaini gidana ka fita da ni daga kusa da wadannan mutanen.Ta miqa masa hannu ya dago ta tsaye abinka da ahlul katabu babu ruwansa da maganar muharma, kwakusarta yayi da yake qato ne qosasshe cimak ya daga ta. Na ce a raina daman akwai wannan mutumin har su Usman suka taru su biyu su na wani cali-cali? Ga wanda zai taba jikinta a wajensa babu haramci.
Dr. Isa ya zabura ya ce " Godwin ban gama yi mata Dressing din ba fa."
Godwin zai juyo sai ta yi tsawa ta ce "ba na so kada ka mayar da ni. Kuma na fada maka ka samo min wani gida ba zan iya zama a cikin wadannan ba sun tsane ni." Ta fashe da kuka mai tayar da hankalin masu tausayi irin su Usman.
Godwin na bada hakuri yana daukar alqawarin zai yi abinda ta ce su ka wuce sama.
Umma ta ce "Allah sarki bai kamata a bar ta ita kadai a cikin wannan halin ba, gara in je in zauna da ita kafin ta kira 'yan uwanta."
Mijinta ya sakar mata harara sai ta koma gefe.
Usman ne a zaune Dr.isa ya na yi masa dressing din manyan raunikan da ya ji a hannu da baya da guiwoyin qafarsa. Abin tausayi ko ina ya kwaile. Da aka gama ya rubuta magununa ya bani takardar, muka dunguma muka hau sama da kyar Usman yake takawa ina tallabe shi.
Qofar Mufida a bude ta yi wurgi da Hijabin jikinta ta tsugunna a qasa ta qanqame kanta a cikin quiwoyinta tana ta rusa kuka. Godwin na ta fama da ita daga ya matso kusa da ita sai ta bankade shi. Laifina shine wai me ya sa aka ceto ta, ai da an bari mota ta danne ta. Daga nan na tabbatar ba qaramar gaba na hada ba, har na fara nadama don sun bani tausayi. Allah sarki nima ba yi na ba ne, kawai saboda tsaro ne.
Na kira sunan Godwin na miqa masa fasasshiyar wayarta na ce ya bata na ja Usman na shige dashi falo dan na ga alamar ya shiga wani hali ya tsaya kawai yana kallon Mufida cike da tausayi.
Ruwan zafi na dora na dauko tawul na cire masa wannan rigar na zuba a shara, na goge masa jikinsa na daddana masa ko ina dan duk jikinsa ciwo yake. Na hada masa shayi mai kauri ya sha da yake yana qaunar kwai na soya masa waina dan na tabbatar zai iya ci.
Na dauko kudi na fita na bawa mai gadi takardar magani na ce ya siyo min. Ina tsaye a bakin get ina jiran Tanimu mai gadi ya dawo sai ga Murjanatu Bibi ta shigo cikin wata tsadadiyar motarta golden color, motar nan ta hadu ba na jin a garin nan na Bauchi kaf akwai mai irinta. Lambar motocinta ma sunanta ne M. BIBI 7.
Ta fito da sauri da alama itama daga wajen motsa jiki take aka kira ta aka sanar mata aminiya ba lafiya, ta taho a sukwane. Wando ne 3 qauter da rigarsa shimi, gaban rigar ne kawai a rufe bayan babu komai kuma ladies tired ne. Gashin doki har tsakar bayanta. Babu yadda zaa dauka Hausa zata fito daga bakinta balle kalmar shahada. Ta hau sama da sauri, na bi ta da harara na ce can ta matse muku ni dai na kwato mijina. Tanimu ya jima bai dawo ba sai can ya dawo ya na lissafin shagunan da ya je babu har sai da ya hau acaba amma dai an samu. Ya miqo min canjin naira dari biyu, na ce ya riqe.
Na hau sama da sauri sai na ga qofar Mufida a bude warai kamar yadda tawa qofar take a bude warai, na cika da mamaki dan ni na san na jawo qofata na rufe. Toh Usman ne ya bude ya shiga gidan Mufidah ko ita ce ta shigo mana? Na tambayi zuciyata.
Na qarasa cikin falona da sauri. Innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Me zan gani? Murjanatu Bibi na gani ta naniqi Usman zama daf da daf gashi ko riga babu a jikinsa, da sunan wai dubiya ta zo tana mai tausaya masa tana yi masa sannu tana tallafo shi tana gyara masa zama, ta na masa tausa a hannu.
Na tsaya cak ina kallo yayin da jinin da yake zagayawa a cikin zuciyata ya rage gudu ina qoqarin shidewa in sume, ledar maganin ta fado daga hannuna qasa, Usman ya gane sai ya farfado daga langwabe-langwaben da yake yi. Ya gyara zama ya matsa daga kusa da ita. Na taho a fusace na cire hijabina na lullube masa jiki, na jawo shi jikana na maqale shi. Na galla mata uwar harara na murguda baki.
Allah Ya tsinewa wayewa irin ta nasara da yahudu wacce Murjanatu take kwaikwayarsu. Matar nan ko a jikinta maimakon ma ta razana ko ta ji haushi sai ta ce "yauwa madam gara da kika lullube shi dan na ji jikinsa da zafi kamar yana jin sanyi ma dan na ga duk tsikar jikinsa ta tashi, na ji bugun zuciyarsa ma da sauri da sauri, sannan numfashinsa sama-sama kamar hancinsa a toshe. Na ga cikinsa yayi kwalab yana buqatar ya ci wani abu. Ina ganin ruwa mai sanyi-sanyi za ki samu da tawul ki shafa masa a duk jikinsa, sannan ya sha magani ya kwanta ya huta.
Zuciyata ta sake hargitsa ta ina ta auna duk wadannan abubuwan a jikin mijina wajen da ni kadai ya kamata in shiga ita har ta zo ta gama lalube shi ina qasa.Wannan wacce irin masifa ce ta fado a cikin gidana haka?
Na fusata na ce "dukka aikina na ne kula da shi ba sai wani ya fada min ba."
Matar nan fa har yanzu bata san baqar magana nake fada mata ba sai ta miqe tsaye, ta tsaya akanmu, Allah Ya sani ko ni mace bai kamata in ganta a wannan shigar ba, balle namiji. Na yi sauri na jawo fuskar Usman na kawar daga saitinta.
Ta ce " Alhamdulullah tunda duk kin gane yadda na ce ki yi