Author : Jamila Umar Tanko Category : Romance
Usman ya juya a fusace ya harare ta, sai suka hada ido wannan karon mamaki ne ya lullube fuskokinsu.
Ta ce "Usman Aliyu daman kai ne?"
Ya ce "Murjanatu Bibi ke ce a gidan nan?"
Innalilahi wa inna ilaihi rajuun me zan gani? Hira ta barke suka dunguma suka fice dan ma Mufidah a fusace ta fisge hannunta daga hannun Murjanatu ta fice waje da sauri ta barsu a baya su na ta magana, su na tuntsira dariya. Ban san sanda na ajiye lap-top din a qasa ba, na biyo bayansu. Murjanatu ta shiga mota zsuna Usman na tsaye a gefenta, su na magana.
Mufidah ta tabe baki ta ce "Murjanatu za mu yi magana a waya na shiga gida ni kam."
Ina ? Murjanatu ba ta ji ba tana can ta sami farin saurayi kyakyawa.
A bakin get muka yi kicibus da Mufidah aka hau kallon- kallo da ni amma yanzu ba ita ce a gabana ba waccan Murjanatu ce dan na ga alama ta fi gobara barna, sai dai in kira ta da 'Valcano erection' wato dutse mai aman wuta.
Sai gani na diro a bakin mota, Usman na ganina ban ga alamar razana ba, sai ya dafa ni ya ce yauwa ga madam din ma ta fito ku gaisa."
Ta miqo min wasu dogayen yatsu masu dogayen farata kamar na mayu, mu ka gaisa sai dai laushinsu da qanshinsu ya isa.
Ta maqale murya ta ce "Madam yaya yara?"
Ban amsa mata ba ina tsaye ina girgiza kamar 'yar tauri. Zufa kawai nake yi, dukka cikin rigata ya jiqe.
Dallar dari biyu ta miqo min ta ce a siyawa yara alewa. Na yi godiya galala, Usman ma ya yi godiya.
"Sai na zo kawai Usman, zamu qarasa maganar." In ji Murjanatu.
Ya amsa da "ok yaushe?" Ta ce "ranar monday zan shigo Insha Allah."
Ya kamata Usman ya jiyo bugun uku-ukun da zuciya ke bugawa. Ya juyo ya dube ni ya ce "shiga gida bari na yi alwalla har ma an tayar da iqama."
Ya tafi da sauri ya dauki buta ya koma gefe yana alwallah.
Tafiya nake tamkar kwai ya fashe min a ciki na wuce cikin gida. Yara na hayaniya na ji kamar su na zazzago da kwakwalwata, na sakar musu asharai kwarara guda uku sai su ka baje a guje suka shige daki har da Haidar mai rarrafe shima yayi ta kansa. Na cire dankwalina na wurgar saboda yayi min nauyi, na watsar da dalolin qasa na zauna.
Can sai ga Usman ya shigo a fusace yana magana " me yake damunki ne? Yaya aka yi kika bar min laptop dina a qasa? Da mota ta taka min fa?"
Sai a lokacin na tuna ashe na yasar da ita a qasa.
Na rasa masar da zan bashi, ya ci gaba da kallon yanayin da nake ciki.
Har zai wuce zuwa daki sai ya juyo ya dawo ya ce "Fatiti kamar a qofar gida na ganki babu gyale, ke ce kuwa ko surutu ya dauke min tunani ba ke ba ce? Sai ya juya ya kalli dallar dari biyun da Murjanatu ta bayar, ya sake gasgatawa ni din ce. Sai ya sauke laptop ya finciko ni, ni da nake zaune sai gani a tsaye ya nuna gidan Mufidah da hannu ya ce " kada da fa a ce kin fara kwaikwayen makwabciyar nan ta ki da qawayenta? Ka da ki ce min ke ma kin fara fita titi babu gyale? Wai in tambaye ki ma, yaya aka yi kika san ina wajen mota har kika fito ki ka zo inda nake?"
Amsa daya tak ta gagari bakina. Ya tsare ni da ido yana kallo ya fara gane dalilin da yasa na shiga cikin wannan hali.
Ya girgiza kai ya ce "Allah Ya baki lafiya toh. Murjanatu Bibi customer mu ce babba, da take da account din dallars a bankinmu kuma nine manager da nake kula da account dinta. 'Yar canji ce tana da kamfanin canja dallar. Da kika ji ta ce zata shigo mu hadu, ba ko ina za ta shigo ba sai banki kuma maganar kudi ne. Shikenan ko ki na da wata tambaya kuma?"
Na girgiza kai alamar babu komai.Ya wuce abin sa zuwa cikin dakinsa yayi wanka ya fito. Da alama yunwa yake masifar ji, ya ci saa kuma na dafa abinda ya fi so wato tuwo da miyar kuka da manshanu. Ya ci da yawa ya na ta faraa yana ta ja na da hira. Amma hakan bai burge ni ba na fi zaton saboda ya hadu da Murjanatu ne yasa yake nishadi, amma kuma dole sai na binciko tsakaninsu a wayarsa, duk abinda bincike na ya nuna toh zan dauki mataki, ya san sauran.
Na maqale murya na ce " tunda yamma suka shigo tare da Mufidah su ka shiga falo suka saki wani uban kida qarar har qasa ana ji. Gaskiya wannan ba su da tarbiyya wataqila ma daga club su ka dawo ko ma sun yi shaye- shayensu."
Ya girgiza kai ya ce "ba kida ba ne, karatun qur'ani ne yanzu da na wuce ma na ji. Kuma ki daina yankewa mutum hukunci saboda shigarsa da yake yi a zahiri, ba ki san menene halinsa a badini ba. Murjanatu tana da kirki, ga kyauta ga fara'a, ba ta da wulaqanci an ce ta na yawan ginin masallatai da islamiyoyi da rijiyoyi sadaka ce aikinta kuma bata wasa da yin sallah da azumi ni shaida ne, in lokacin sallah yayi a office sai ta yi.
Shigarta ce kawai illa saboda girma a turai da ta yi amma ana yi mata wa'azi dan ta fara gyarawa ma ba kamar da ba, tunda har kika ga ta saka atamfa riga da siket dogo, in da ne sai dai gajeren wando da singileti."
Tun daga nan na san ashe ma aikin banza na yi, har na je ina zagin dattijan mata wadanda basu ji basu gani ba. Ashe ga abin zagi irin su Murjanatu. Yaya zan yi? Ta ina zan fara wannan yaqin? Ba zai yiwu ba wallahi dole in raba su.
Wato Mufidah makira ce ashe, sai ta gama jin disko daidai sanda Mijjna zai dawo sai ta saka karatun qur'ani kenan. Lallai akwai aiki babba a gabana, ai kuwa zan tunkare su ko ni ko su, babu gudu babu ja da baya.
Bayan watanni biyu watarana da daddare Usman ya dawo daga wajen aiki a fusace. Ina ganin yadda neck tire da farar shirt dinsa suka cukuikuye na san a fusace yake, fuskarsa babu annuri. Ya na shigowa na ja da baya da sauri dan kada in ji saukar mari, na shiga tunanin yau kuma me na yi masa? Na san dai ban kira kowa na zaga ba, rabona da daukar wayarsa in dauki lambar wata in kira in zaga tun wancan watan da na kira Murjanatu Bibi na ja mata kunne akan ta fita harkar mijina.Shegiyar sai ta zamar da ni mahaukaciya ta nuna halin ko in kula ta ce mijin nawa waye shi a cikin sanatoci da gwamnoni Nigeria dan tana da su bila-adadin? Na yi wuqi- wuqi ta ci gaba da cewa please in kin san mijinki talaka ne to ki dauka dan dakona ne bai isa in kula shi ba. Tunda ta juya harshe ta fara turanci na saddaqar na hakura, na tabbatar da gaske take Usman a matsayin yaronta yake. Kuma sabon layi na siya na kira ta balle in ce ta gane nice na kira ta fada masa.
Usman ya dube ni a fusace ya nuna gidan Mufidah da hannu ya ce " ko da wasa babu ke babu wannan matar, ko a bakin matattakala ban yarda ku hadu ba balle yarana su Shiga gidanta. Kin ji abinda na ce miki ko?"
Dadi ya kama ni na gyada kai na ce ' insha Allah sweet yadda ka ce haka zaa yi."
Ya wuce dakinsa a fusace, dadi da murna ya rufe ni, na hau rawa yara su na taya ni sai da na ji motsin fitowarsa na wayence. Na hada masa abincinsa a kan dining, da yayi wanka sai yayi kyan gani ya warware. Sanye yake da farar jallabiya fara qal marar nauyi ya zo ya zauna ya fara cin abinci. Na jawo kujera ta nima na zuba. Ya dube ni ya ce "ke ma baki ci abincin ba kenan, har takwas ta wuce fa?"
Na ce ta yaya zan iya cin abinci abin qaunata na can na fama da aiki?"
Sai na ga yayi min wani irin duba, na gane me yake nufi wato sau nawa ma kike ci bana nan din. Bai ce komai ba dai. Ina ta tsokano hira kala-kala ina so in tambaye shi abinda ya hada shi da Mufidah amma na kasa, saboda na san halinsa wani lokaci ko yayi niyyar fada idan aka dame shi da tambaya sai ya fasa. Da kansa ya fara bani labari.
Ya ce " Murjanatu Bibi ce ta zo office dina tare da qawarta wai itama tana so a bude mata dallar account, don duk wata yayanta da yake aiki a America yana turo mata kudi tana so ya dinga shiga accout dinta kai tsaye. Bayan Murjanatu ta gama yi min bayani na ce ba damuwa ina qawarta din? Sai ta kwalla mata kira ta Taso amma wani suna ta kira bai yi kama da sunan hausawa ba. Ta na qarasowa ta gaishe ni kaina a sunkuye, na dago muka gaisa kawai sai na ga Mufidah ce. Ta kalle ni ta hada girar sama da qasa ta juya ta kalli Murjanatu ta ce daman wajen wannan mutumin kika kawo ni? wanda bai san darajar mata ba? Toh ko zan rasa dallars duk wata gara in rasa da ace dai a hannun wannan zan bude dallar account. A cikin mutane fa abokan aiki da abokan kasuwanci ta kira ni da wanda bai san darajar mata ba."
Na gyara zama fuskata ta nuna alamar damuwa amma fa farin ciki ne fal a cikina. Na zuba uban tagumi ina girgiza kai alamar tausayi.
Cikin jimami ya ci gaba da cewa " na ce mata da in bude miki account da hannuna gara in rasa aikin nan da nake yi. Wacce bata san darajar maza ba baki san darajar kanki ba."
Wai wannan maganar tawa ita ce ta yi zafi har area manager ya fito daga office aka bani quiry wai na yi fada da customers na kori customers.
Aka taru akan Mufidah ana bata haquri dan ta iya munafunci ta dinga kuka kamar idanuwanta zasu zazzago. Ga shegen taurin kai babu roqon da baa yi mata ba, ta ce ba zata bude account da mu ba.
Murjanatu ta yi ta kokarin bata baki amma ta qi. Area manager yayi rantsuwa in har Mufidah bata yarda ya bude accout din nan ba sai ya kai ni qara babban office din mu na Lagos ya fadi abinda na yi na kore babbar customer. Dan haka wai in je in bata hakuri an bani kwanaki biyu. Da in bata hakuri gara in rasa aikina wallahi. Amma Murjanatu ta yi alqawari zata shawo kanta. Kinga da gayya kenan ta je ofis din dan mun yi fada dan ta bata min suna, ta sa a kore ni daga aiki amma ta Allah ba tata ba. Zan kai qararta wajen Ubangiji."
Na zabura na dafe qirji na fashe da kuka na ce " au haka ta bullo mana, tuggu da ta hada mana kenan? Sweety na fada maka ni kadai na san abinda matar nan take yi min a cikin gidan nan. Gashinan yanzu asirinmu a rufe zata tona mana. In an kore ka daga aiki Kano fa za mu koma, yara basu saba rayuwar Geto area ba. Ko gida bamu da shi acan, dariya zaa yi mana wallahi."
Usman ya dafe kai yana jujjuyawa ya ce "maganar gaskiya dole mu tashi mu bar mata gidan nan bana so in sake ganinta balle wata mu'amula maqwabtaka ta hadamu. Ki na kiranta da 'yar iska tana kawo maza ban taba yarda ba, amma yanzu da zan hawo sama a jikin wata mota na ganta wani qato ya rungume ta yana share mata hawaye tana kuka. Ina ga fadan da muka yi dazu ne take bashi labari dan na ji tana ambaton sunan bankinmu shine har yanzu bata daina kukan ba. Toh me yayi zafi dole ne sai mun zauna tare?"
Na zabura na miqe tsaye hankalina a tashe har ga Allah na damu da barazanar rasa aikinsa amma na ji dadi yadda kyakykywar tsana ta darsu a tsakaninsu.
Na dinga safa da Marwa ina tunano mana mafita, shi kuwa duk inda na yi sai ya bi ni da kallo, ya tabbatar zan nemo mafita don ya yarda da kaifin kwakwalwata.
Ya taso daga kan dining ya kama hannuna muka zauna akan kujeru ya gyara zama ya ce " ki kwantar da hankalinki addua ita ce mafita, na san ki da yawan addua ki yi min saukar qur'ani sannan mu daina bacci cikin dare mu tashi mu yi ta sallah, Allah zai kare mu daga sharrinta.
Washegari da yake asabar ce gidan shiru kowa na baccin safe, misalin qarfe takwas da rabi na ji na gaji da kwanciyar na tashi na leqa windo da yake ina ta jiyo muryar mace da namiji ana magana. Ina leqawa na ga Mufidah ce a tsaye tare da Godwin lauyan me gidajen da muke haya. Duk wanda zai shiga gidan shi yake sakawa yake rubuta resit. Sanye take da wasu damammun riga da wando da kanbas da alama ta dawo daga jim ne. kamar yadda ta sama zuwa kusan kullum da sassafe ko kuma ta yi gudu ta kai qarshen titi ta dawo, ko ta hau keke ta zagaya titunan unguwa, wai duk a cikin gayu ne baa so a yi tumbi a rasa shape mai kyau.
Sai magana da bayani take ta na nuna gidanmu. Na saka hannu na dan daddaki Usman na ce ya leqo ya ga wani abu. Ya tashin gigice ya leqa ya ga abinda na gani sai yayi tsaki ya koma ya kwanta. Na fara yi masa bayani akan abinda nake hange, na ce gara ya sauka don za ta iya shirya masa tugun da mai gidan nan zai iya korarmu neman wani gidan hayar ma aiki ne kuma da wuya mu sake samun sabon gida mai kyau irin wannan, kuma yadda kudin hayar nan ta mu ya kusa qarewa saura watanni biyu in a gidan nan muke sai mu qara watanni shida ba mu biya ba kuma baya daga mana hankali. Kai yanzu ka na da wani kudin da zaka biya sabuwar haya? Sannan matar nan mu ta zo ta samu ita ya kamata a tasa daman ita ce bare bai kamata ta zo ta shiga tsakiyar masu aure ba. Ka tashi ka je ka fadawa lauyan nan Illar zaman matar nan a gidan nan. Ga ta can tana ta hada mana tuggu, gara ka je tun tana nan a tutsiye mai qarya."
Yayi shiru kamar mai bacci yana ta nazarin maganata, ya qi tashi sai can da jimawa ya tashi ya shiga bandaki ina jin sa yana brush ya wanke fuska ya fito ya goge da qaramin tawul.Ya dauki wayarsa da mukullin mota ya fice ba tare da ya ce min komai ba.
Zuciyata fari tas na san yau zaa yi ta, ta qare in har zasu hada kai shi da su Dr. Musa da isa su ce ba sa sonta a gidan a tashe ta ko su bar gidan lauyan nan mai shegen son kudi zai ga gara ya tashi mutum daya da ya tashi mutane uku. Amma na san yadda zan bullowa Safiya da Umma zuga su zan yi su kuma su zuga mazansu, kowa ya yi tawaye su ce baa son zaman Mufidah a gidan.
Ina ta murmushi ina leqe ta wundona a lokacin Bar.Godwn da Bar.Mufidah sun fita wajen get tana ta bayani tana ta nuna gidajenmu. Usman ya sauko ya duba ko ina bai gansu ba a cikin farfajiyar gidan yayi kamar zai juyo ya dawo sai na bude windo na leqo na ce Abban Ahamd ga su can a wajen get can ka bi bayansu.
Ya na isa nan da nan