Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BAƘAR MASARAUTA A Cikin Duhu PART 1 by Umar Faruq D

Author :  Umar Faruq D Category :  African Stories & Novels

Chapter   5 / 43

12K to 15K   out of 128.4K words

tashin hankaki Gimbiya Tasmir ta samu kanta aciki irin wanda tunda tazo duniya bata taɓa riskar kanta aciki ba.
Ɗaga ƙafafuwan ta ta farayi tana mai zaga tanƙashe-shen falon da yakasan ce tsit da shi, kanta asama tana kallon rufin falon, so take ta gano inda zantukan mahaifin ta suka dosa da kuma abun da suke nufi amma gaba ɗaya ta kasa, ko kaɗan bata fahimci inda tsauraran kalaman sa suka dosa ba, abu ɗaya kawai da ta sani shine ransa yayi matuƙar ɓaci irin ɓacin da bata taɓa ganin sa acikin sa ba, tun da take da shi bai taɓa yi mata ko da tsawa ba, sabo da irin mugun ƙaunar da yake mata, amma sai gashi yau har ihu ya mata acikin kunnuwan ta akan wani ƙas-ƙantaccen bawa mara galihu.

Dunƙule tafin hannun ta tayi da ƙarfi bayan ta rumtse idanuwan ta, sabo da yarce sautin muryar mahaifin nata take ta mata amsa kuwwa acikin kunnuwa yana faɗin.
_"Na baki daƙiƙa daga ɗaya zuwa biyar, karki kuskura sukai shida balle har su tsallaka goma ba tare da kin kwance sa ba!"_

"Inaaaa!! Tayaya ma!! Shin me hakan ke nufi kenan?" Ta faɗa da mugun ƙaraji idanuwan ta na furfutowa waje, yayin da jijiyoyin kanta suka futo sukai raɗa raɗa akan goshin ta, tukun daga bisani ta fara ɗaga ƙafafuwan ta cikin sauri tana mai dosar hanyar da zata sada ta da waje takobin ta damƙe acikin tafin hannun ta, har kuma lokacin kalaman mahaifin na basu dena mata amsa kuwwa acikin kunnan ta ba.

Tana futa gaba ɗaya bayi da dakarun da suke acikin harabar wurin suka zube wanwar aƙasa suna masuyin ribda ciki, amma sai dai ko inda suke bata kalla ba balle har ta tsaya cak kamar yacce ta saba, tai shigewar ta gaba cikin sauri kamar ta kifa ƙasa.

Cikin tsantsar sauri dakarun nan nata suka mimmiƙe tsaye, sabo da ganin da sukayi ta shige ba tare da tsaya sun gama gaishe ta ba, balle har ta bawa mariƙi takobin ta suyi gaba.
Dasauri suka fara ɗaga ƙafafuwan su suna masu dosar inda tayi, sai dai tun kafin su ƙaraso wurin da take tayi saurin ɗaga musu tafin hannun ta sama tana mai dakatar da su ba tare da tace ƙala ba, tukun ta cigaba da ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar inda wani garken dokuna suke.

Bata dakata ba har sai da taccima gaban wani ɗirkeken baƙin doki da yake atsaye yana cin ciyawa.

Wani irin mugun tsalle ta buga tana mai ɗanewa kansa, tukun tasanya hannun ta na hagu tana mai damƙar linzamin dake rataye awuyan sa da shi, kana tasa dunduniyar ƙafar ta tana mai dukan cikin sa da matuƙar ƙarfi da ita.

Wata irin haniniya dokin ya saki da matuƙar ƙarfi, tukun ya zabura da mugun gudu yana mai dosar yamma.
Gudu yake ba gudun wasa ba, yayin da ita kuma Gimbiya Tasmir ta kasance zaune asaman sa jajayen idanuwan ta kafe akan hanya, yayin da iska ke kaɗa mayawaicin baƙin gashin dake kanta yana tashi sama, ga kuma jibgegiyar rigar ta da ƴammatan bayi keta aikin riƙewa ɗazu da take ta faman tashi sama itama, sabo da irin tsantsar gudun da dokin yake yi.

Cikin lokacin da bai huce daƙiƙa ukku ba duka suka bayyana adai-dai bakin ƙofar ɗakin azaba.
Cak dokin ya tsaya awurin sabo da yarce ta matse linzamin dake jikin sa da hannu.
Sakin linzamin dokin tayi, sannan ta durko daga kansa zuwa ƙasa.
Kana ta miƙar da takobin dake ɗauke ahannun ta tana mai nuna ƙofar nan da ita, sannan ta buɗe baki cikin tsantsar sauti tana mai faɗin. "Gargabiluuuuuuu!"

Take awurin ko ƙofar nan ta fara ɗagawa sama har ta buɗe duka.
Wani irin baƙin hayaƙi ne ke futo daga cikin ta da matuƙar gudu.
Sauke takobin tata ƙasa tayi tana mai cake tsinin ta acikin ƙasa, tukun ta sake rumtse idanuwan ta tana mai yin wasu irin surutai, sannan daga bisani ta buɗe su tana mai buɗe tafin hannun nata ta watsa abubuwan da suka bayyana acikin sa zuwa cikin ɗakin.

Take haske ya bayyana acikin sa, sai dai kuma duk da haka hayaƙin nan dake futowa bai fasa futowa ba da matuƙar tururi.
Ɗaga ƙafafuwan ta ta farayi tana mai matsawa jikin ƙofar. Sake rumtse idanuwan ta tayi tana mai dunƙule tafin hannun ta, sannan ta sake buɗe baki tana mai faɗin. "Rai Rai Rai Buuu Hooo Reeee!!!" Da tsantsar ƙarfi.

Take awurin hayaƙin nan duka ya ɓace ɓat, tukun ta juya baya tana mai zuwa ta funciki takobin ta daga jikin ƙasar da ta cake ta, sannan ta juya tana mai sake nufar cikin ɗakin gadan-gadan.

Tsaye yake ajikin ƙarafan nan da yake ɗaure jikin sa nata faman kar-karwa, yayin da gumi ya jiƙa sa yay masa sharkaf yarce kasan wanda aka tsamo daga cikin ruwa, banda layi da girgiza kai babu abun da yake iya yi, sai kuma buɗe baki da yake ta aikin yi gaba ɗaya leɓun kasa sun bushe sun yi baƙiƙƙirin dasu! Kallo ɗaya zaka masa ka fahimci ba ƙaramun jigatuwa yayi ba, sabo da yarce duka yana yin hallitar sa ta sauya.

Cigaba da taka ƙafafuwan ta tayi tana mai dosar wurin da yake.
Sai da taje har gab da shi tukun taja ta tsaya tana mai ƙare masa kallo, yayin da shi kuma har lokacin kansa ke ɗage asama yana ta faman aikin girgiza sa.

Shiru tai ba tare da tace komai ba, sai kawai idanuwa da take binsa da su tana mai jin tamkar ta shaƙe masa huya ya faɗi ya mutu, ko taji sassaucin baƙin cikin da take ji acikin ranta ta sanadin sa.

Sauke kansa ya farayi ƙasa -ƙasa har ya sauke idanuwan sa duka acikin nata.
Wani irin murmushi ya ƙaƙalo yana mai jifan ta da shi duk da irin wahalar da yake ciki, kana daga bisani ya buɗe baki cikin muryar sa da take tsantsar rawa, sabo da azabar dake sauka ajikin sa yana mai faɗin. "Gimbiyar mu Gimbiyar BAƘAR MASARAUTA... Ya da dawowa yanzu kuma?" Ya ƙarashe maganar yana mai sake jifan ta da murmushi, yayin da har lokacin kuma gumi ke cigaba da tsats-tsafowa ta kowace kafar gashi dake jikin sa.

"Kai ɗin wane ne? Wane ubanka? Wace kuma uwarka acikin BAƘAR MASARAUTA da har kake ja da iko na?" Ta faɗa cikin ƙaraji tana mai sanya idanuwan ta acikin nasa ita ma.

Murmushi ya sake yi yana kallon ta, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Abun da na daɗe ina son sani kenan tsahon shekara da shekaru acikin baƙar masarauta, amma ba damuwa, tunda har kema kin buƙaci ki sani yanzu, shikenan na barki da aikin neman, in yaso duk randa kika gano ko suwaye sai inzo ki faɗamun su nima!" Ya ƙarashe maganar yana mai zaro harshe ya lashi busassun laɓɓan sa, har kuma lokacin bai fasa jifan ta da murmushin da yake aikin yi ba.

"Wat...!
_"Na baki daƙiƙa daga ɗaya zuwa biyar, karki kuskura sukai shida balle har su tsallaka goma ba tare da kin kwance sa ba!"
Muryar mahaifin ta ta sake dukan kunnen ta da matuƙar ƙarfi, tayarce har tai sanadin tsinkewar maganar da take kanyi ba tare da ta kai ba.

Danna lips ɗin ta na ƙasa tayi cikin baki tana mai taune sa da mugun ƙarfi tare da kafe Beer da jajayen idanuwan ta da suke sake rikiɗewa, tukun daga bisani ta ɗaga takobin ta sama tana mai nuna ƙarafan da yake ɗaure ajikin su da ita, sannan ta buɗe baki da matuƙar ƙarfi tana mai yin wasu irin surutai.
Ko rufe baki bata kaiga yi ba ƙarafan nan suka fara buɗewa wani irin sauti na tashi.

Timm! Kake jin ƙarar faɗuwar Bir ƙasa alokacin da ƙarafan suka gama sakin jikin sa.
Wani irin nishi yake saki yana daga kife aƙasa, yayin da ita kuma ta juya tana mai dosar hanyar waje cikin tsantsar sauri, banda sautin ƙarar sarƙoƙin gwal ɗin da suke sanye aƙafar ta babu sautin dake tashi awurin.

Dasauri shima Bir ya fara jan jiki yana mai bin bayan ta gudun karta sake rufe sa acikin ɗakin.

Tana fucewa bata tsaya wata wata ba ta daka tsalle tana mai hayewa saman dokin nan, tukun ta ɗaga takon dake riƙe ahannun ta tana mai nuna ƙofar da ita, akuma dai dai lokacin shima Bir ya futo waje da jan jikin da yake yana ta faman sakin nishi da ƙarfi.
Sosai farar fatar sa tayi wani irin dabbara dabbaran baƙi awurare daban -daban, yayin da jajayen laɓɓan sa kuma sukai wani iri duk ta sanadin wahalar da ta basa da huta.
Dogo ne sosai mai ƙirar ƙarafa, yana da faffaɗan ƙirji wanda yake cike da kwantacce gashi mai matuƙar taushi akan sa. Yana da dara daran idanuwa tare da dogon hanci dashe akan fuskar sa, sai ɗan ƙaramin bakin sa kuma da ya kasance ɗauke da jajayen laɓɓa da suke matuƙar ƙara masa kyau suma, yayin da sumar kansa kuma ta kasance mayalwaciya mai matuƙar taushi da santsi.


"Gargabiluuuu!" Ta faɗa da ƙarfi tana mai nuna ƙofar da takobin. Take kuwa ta koma ta rufe gam, tukun tasanya hannun hagun ta tana mai jan linzamin dokin, tare dasa dunduniyar ƙafar ta ta daki cikin sa da ita.

Haniniya dokin ya ƙara saki, tukun ya fara ɗaga ƙafafuwan sa yana mai ƙara danna kansa gaba.

Bata tsayar da shi ba har sai da suka ɓulla wani wuri da yake da dogayen bishiyu tare da duwar-watsu tako ina, agefe kuma ga wani tafkeken ruwa da yake ta faman tawowa daga saman wani dutse yana sauka acikin wani ƙaton rami.

Durowa tayi akan dokin, tukun ta samu wani wuri da yake da yashi tana mai cake takobin ta agun, kana ta fara dosar inda wani dutse yake gadan gadan, jajayen idanuwan ta kafe akan sa.

Sai da taje gab da shi, tukun taja ta tsaya cak, kana ta rumtse idanuwan ta da ƙarfi tana mai dunƙule duka tafukan hannayen ta.

"Kai!! Inaaa!! Bazai yuwu ba wallahi!" Ta faɗa da matuƙar ƙaraji tana mai girgiza kanta, tukun daga bisani ta buɗe idanuwan ta da suka sake rikiɗewa suna masu ƙarayin jajajir, sannan ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai komawa wurin da ta cake takobin ta.

Funcikar ta tayi da ƙarfi adai dai lokacin da taje wurin, tukun ta sake ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar gaban ruwan nan idanuwan ta ƙur akan sa.

"Yau kimanin shekaru Ashirin da biyu, da wata biyu, da kwana biyu da zuwa na duniya mahaifina bai taɓa yimun koda kallon banza ba balle harya yimun tsawa sai yau.
Shin wai shi ɗin wane ne ma? Me gare shi, wane kalar tarihi ne da har zai hana hukunci na yin aiki akan sa? Inaaa! Hakan bazai taɓa yiwu ba wallahi." Ta faɗa tana mai tsayawa agaban ruwan idanuwan ta ƙur akan sa.
Tukun daga bisani ta ɗaga takobin ta tana mai nuna ruwan nan da shi, sannan ta buɗe murya cikin sauti tana mai faɗin. "Shairama!!!"

Take wata wata tamfatse-tsiyar macijiya ta bayanna acikin ruwan kanta fashe tana mai karkaɗa harshe!

"Shairama!!" Ta sake faɗe da ƙarfi tana mai nuna gefen ruwan daga waje da takobin.
Wani irin tsalle macijiyar nan ta daka, sai gata ta dira adai dai wurin data nuna da takobin tana mai karkaɗa harshen ta.
Yayin da ita kuma ta sake neman wuri ta cake takobin, kana ta fara ɗaga ƙafar ta tana mai dosar inda macijiyar take gadan -gadan.
Hannu tasa ta damƙi kanta da matuƙar ƙarfi, tana mai zaro idanuwan ta bayan ta durƙusa agaban ta!


*ƘASAR HAUSA JAHAR WASAI*

ASADULLAH PALACE

Babban wuri ne mai matuƙar girma da yalwa, gaba ɗayan sa wurin shimfiɗe yake da wata haɗaɗɗiyar ciyawar roba koriya shar da ita, yayin akabi aka ƙawata ko ina da furanni kala kala masu matuƙar kyau da suka yi matuƙar ƙara haska ka wurin.
Agefe guda kuma wani haɗaɗɗen building ne mai kimanin hawa biyu, wanda cikin sa yake jera da ɗakuna, sai daga ɓangare ɗaya kuma wani tafkeken swimming pool ne ɗauke da wasu tayoyin roba tare da bluen ruwa acikin sa, yayin da bakin swimming pool ɗin kuma aka bi aka zagaye sa da wasu haɗaɗɗun kujeru masu kama da gadaje, bayan kujerun kuma wasu irin haɗaɗɗun furanni ne adashe, sai daga can cikin wurin kuma wasu kujeru ne na roba kakkefe da mutane suka kasan ce zazzaune akan su, wasu na cin abinci, yayin da wasu kuma suke shan drinks.
Kusan duk wanda zaka kalla awurin zaka gansa ne tare da budurwar sa suna zaune.

Anan cikin swimming pool ɗin ma wasu ƴammata ne da samari suke ta faman wanka suna watsawa juna ruwa.

Sanye mazan suke da boxer kawai wanda jikin sa aka rubuta Asadullah palace, yayin da su kuma matan suka kasan ce sanye da wasu ƴan ƙana-nan riguna, tare da gajerun wandina waƴan da suma duka jikin su yake zane da Asadullah palace.
Daga kan kujerun da suke abakin ruwan nan ma wasu ƴammata da samarin ne ɗaure da towel aƙugunan su, kishingiɗe suke kowan ne hannun sa riƙe da cup ɗin lemo.
Duk wanda ka kalla acikin wurin nan basai an faɗa maka ba zaka san yayi matuƙar tarawa, ko kuma an tara masa, duba da kalar motocin da suke ajiye a parking space da kuma yarce skin ɗin jikin su take.


Ahankali ya cigaba da taka motar yarce kasan bazai tafi ba, tunda ya shigo gaba ɗaya jama'ar dake cikin wurin hankulan su ya dawo kansa, yayin da ƴammatan da suka kasance acikin wurin waƴan da mafi yawan su tare da samarin su suke suka fara mimmiƙewa tsaye suna masu gyara jikin su, kana suka fara tattakawa suna masu dosar inda motar sa take.

Wani haɗɗaɗen get da yake daga can cikin wurin ya tunkara da motar tasa gadan gadan.

Kallon yarce haɗaɗɗun ƴammata keta zuwa suna giftawa Al'amin yayi, tukun ya buɗe baki yana mai faɗin. "Ɗan iskan banza kawai, wato kai da ka zauna ayi hawa da kai ka gwammace ka tawo wurin da zaka lodarwa kan ka zunubi ko?"

Murmushi Yarima Asad yayi adai dai lokacin da suka ƙarasa bakin get ɗin nan, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Hausawa dai kance Abokin ɗan iska ɗan iska ne, kaga kenan daga ni har kai duk samma kar, kuma idan ka isa har mu shiga wurin nan mu futa karka kuskura ka ɗaga kai kakalli wata yarinyar."

"Dallacan malam rufemun baki tunda ni ba dutse bane dan uwarka!"
Al'amin ya faɗa yana mai sakin ƙwafa da ƙarfi, domin shi har yanzu haushin Asad yake ji, sabo da yayi matuƙar tama ranar yau ɗin amma gashi lokaci ɗaya duk ya rushe masa ita.

"Malam ni sauke ni anan na ƙaraso daga baya, domin ko ga zafafan ciks nan suna buƙatar ataya."
Al'amin ya faɗa yana mai kallon yarce haɗaɗɗun ƴammata keta kai kawo asaitin inda motar su take ta cikin glass ɗin daya kasan ce ɗauke da baƙin tinteck ajikin sa.

Taɓe baki Yarima Asad yayi ba tare da yace komai ba, haka kuma bai buɗe masa murfin motar ba, saima danna hancin ta da yayi zuwa cikin haɗaɗɗen wurin da aka wangale masa get ɗin sa.

Plat building ne mai tsananin kyau da ɗaukar hankali agefe guda na cikin wurin. Yayin da gefen sa kuma wani tafkeken swimming pool wanda gefen sa yake zagaye da ƴan gadaje ya kasan ce.
Sosai wurin yayi matuƙar haɗuwa fiye da na farkon, sai dai shi wannan bai kai wancan girma ba, kuma babu ko mutum ɗaya acikin sa sai su da suka shigo yanzu kawai.
Daga can ƙarshen wurin kuma daga jikin bango wasu danƙara danƙara kosassun dokuna ne fari da maroon ɗaure ajikin garken su suna cin dusa.

Direct yayi parkin space da motar sa.
Ɗan gajeren tsaki ya saki yana mai lumshe idanuwan sa, sabo da yarce Al'amin ya fara takura masa da masifar sa.
Ahankali yasa hannu ya buɗe murfin motar, tukun ya zura ƙafafuwan sa daga waje bayan ya ɗauki wayar sa ba tare da ya tankawa Al'amin ba, kana ya fuce duka yana mai juyawa ya doshi bakin ruwan nan kai tsaye.

Budewa shima Al'amin yay ya futo yana mai juyawa ya doshi get din da suka shigo, danmiyar yaje ya dubo wata cikin yammatan da suka huce awaje tukun su dawo.

"Banza kawai ballagaji mara aji." Yarima Asad ya faɗa alokacin da ya zauna kan ɗan gadon da yake bakin swimming ɗin yana mai kallon Al'amin, tukum daga bisani ya mai da idanuwan sa kan wayar sa yana mai fara shafata.

Wata irin azababbiyar mota ce sabuwa gadagal ta danno kanta cikin wurin.
Direct ta huce inda aka tana da dan ajiye motoci, parking mamallakin motar yayi, tukun daga bisani aka buɗe murfin ta.

Fararen ƙafafuwan ta da suke sanye da wani mugun hill shoe ta fara zurowa waje, tukun daga bisani ta futo duka tana mai sa hannu ta rufe murfin, sannan ta juya tana mai kai idanuwan ta bakin ruwan nan.
Murmushi ta saki sabo da yarce ta hango sa zaune cikin shigar sa da take mugun tafiya da ita, wacce akullum idan ta gansa acikin ta sai ta ƙarajin ta tsundum acikin kogin ƙaunar sa.

Farace doguwa siririya, tana da dogon hanci tare da ƴan madai daitan idanuwa akan fuskar ta, sai bakin ta da ya kasance shi baza ace masa ƙarami ba haka kuma baza'a kira sa da tafkeke ba, wato ataƙaice dai tana da kyanta dai dai misali.

Sanye take da blue crazy jeans da yayi matuƙar kama jikin ta, sai red t shirt mai gajeran hannu wacce take ɗauke da kwalliyar flawoyi akan ta, yayin da kanta kuma ya kasance abuɗe ko darajar ɗankwali bai samu ba, sai uban jan gashin atach da yake zube agadon bayan ta yana reto.
Riƙe take da ƴar ƙaramar jakar ta wacce ta kanace kala ɗaya da takalmin dake sanye aƙafar ta mai matuƙar tsini da sirantaka, yayin da ɗayan hannun nata kuma ya kasan ce riƙe da wayar ta ƙirar iphon 13 pro max itama. BILKISU ABUBAKAR SARDAUNA kenan, wacce ƙawayen ta suke kiran ta da Billy Baby. Ƴa ga gwamnan Jahar Wasai mai ci ayanzu, sun haɗu da Yarima Asad ne a oxford university dake ingla, alokacin shi yana mastering degree ɗin sa, yayin da ita kuma take degree,

5 / 43