Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BAƘAR MASARAUTA A Cikin Duhu PART 1 by Umar Faruq D

Author :  Umar Faruq D Category :  African Stories & Novels

Chapter   10 / 43

27K to 30K   out of 128.4K words

ba zai san yayi nisa cikin kogin ƙaunar ta.

Cak ta tsaya a'inda take daga ɗan nesa da shi ba tare da ta cigaba da takowa ba.
Tsaye suma ƴammatan bayin nan sukayi abayan ta cak, tukun daga bisani ta ɗaga musu hannu ta sama ta baya ba tare da ta juya ta kalle su ba.

"Afuto lafiya Gimbiya." Suka faɗa suna masu juyawa suka doshi hanyar da suka biyo.
Ba ita ta cigaba da tafiya ba har sai da ta tabbatar da tabar jin motsin su tas, alamun sun bar cikin wurin, tukun ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar kan shimfiɗar da Yariman Yamma yake kishingiɗe akai, idanuwan ta kafe ƙur akan fuskar sa kamar yacce shima ya kafe ta da nasa, sai dai ita kuma ba irin kallon da yake mata ba take masa, tana masa kallo ne na tsantsar -tsanar sa da take ji aranta tare da ƙin sa, ahaka har ta ƙarasa bakin shimfiɗar da yake kai.

Lumshe idanuwan sa yayi yana mai sake gyara kishingiɗar sa yayi balance ransa face, domin kuwa sai yanzu data matso wurin sa ya ƙara tabbatarwa da kansa lallai ba ƙaramun dace yayi ba, muddin ya mallaki wannan babbar kadarar aduniya amatsayin abokiyar rayuwar sa. Tukun daga bisani ya sake wara idanuwan sa akan fuskar ta da take cunkushe tsaye agaban sa, kana ya buɗe baki cikin yin ƙasa da murya yana mai faɗin.

"Barka da isowa Gimbiyar Jauron Yamma, Sarauniya kuma ga tsuntsaye da shanu na Masarautar Fulɗe."
Ya faɗa fuskar sa ɗauke da annuri.
Yayin da ita kuma taji saukar furucin sa na Gimbiyar Jauron Yamma da wani irin azabar raɗaɗi acikin ranta, tayarce har sai da ta rumtse idanuwan ta da ƙarfi tare da taune lower lips ɗin ta.
Tukun daga bisani ta warasu akan fuskar sa kamar yacce shima yake kallon ta gaba ɗaya har sun fara canza launi suna yin ja.

Sannan ta tuɓe takalman da suke sanye aƙafar ta tana mai dosar kan shimfiɗar da yake kishingiɗe akai, zuciyar ta na tsantsar turiri.
Tsaye tayi agaban sa tana mai aika masa da wani irin matsiyacin kallo, tukun daga bisani ta ɗaga laɓɓan ta cikin kaushi, tana mai faɗin. "Shin wa...............✍




*HAK'IK'A INA GAB DA DAKATAWA GABA D'AYA MUDDIN BAZAKU DINGA YIN COMMENT BA.*

🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎
👑👑
🦋
🦅🕊🦆
🐍🎠🐄🏹



_*NA*_




UMAR FARUQ*D*



*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*




*PAGE 07*



"Shin waya sanar da kai wannan tatsuniyar da har kake shelantawa duniya cewar ni ɗin takace?" Ta faɗa cikin kaushi tana mai kafesa da dara-daran idanuwan ta, tukun daga bisani ta ɗora da faɗin. "To idan ma mafarki kake ina son kayi gaggawar farkwa, domin kuwa ni ɗin nan daka gani an hallice ni ne domin mutum ɗaya, haka kuma na daɗe da zamtowa mallakin sa, dan haka ina mai shawartar ka akan kayi gaggawar komawa wurin waƴan da suka aiko ka zuwa gare ni kasanar musu da cewar banyi ba, domin ko bazan taɓa yi maka ba har abada, kamar yacce kaima bakai mun ba, kuma baka da abubuwan da zanyi tinanin zakayi mun ko agaba!" Ta ƙarsahe maganar ƙasa-ƙasa tana mai jifan sa da wani irin matsayacin kallo, tukun daga bisani ta juya tana mai sauka daga kan shmfiɗar, sannan ta sanya takalmam ta, tukun ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar hanyar da ta biyo ba tare da ta tsaya jin ta bakin sa ba.
Yayin da shi kuma Yariman Yamma lokaci ɗaya yana yin sa ya sauya, kana gaba ɗaya annurin dake kan fuskar sa ya ɓace ɓat, idanuwan sa kuma suka kaɗa sukai jajajir yana mai kallon ta, kafin daga bisani kuma ya buɗe baki cikin kaushi yana mai faɗin. "Shin waya baki izinin tafiya ne da har kika juya kika tafi?"

Cak Gimbiya Haddiyal ta tsaya daga inda take, sabo da furucin sa da taji ya daki dodon kunenn ta da ƙarfi, rumtse idanuwan ta tayi daga inda take ba tare da ta juyo ba, haka kuma bata cigaba da tafiya ba, sai zallar turiri kawai da take jin ranta na mata, tana mai tinanin kalar amsar da zata basa idan ta juyo.
Yayin da shi kuma ya miƙe daga kishingiɗen da yake yana mai zuwa ya sanya takalman sa, tukun ya fara ɗaga ƙafa cikin takun sa na isa yana mai dosar inda take.

Direct ya huce bayan ta yana mai zagayawa ya tsaya daga gaban ta gab da ita, tukun ya ranƙwafo da kansa yana mai rage tsayin sa ya zamto fuskar sa ta dawo saitin tata fuskar, tayarce har suke jin dirar numfashin junan su.

Kallon-kallo suka fara aikawa junan su da shi ba tare da wani daga cikin su yace tak ba, tukun daga bisani shi Yariman Yamma ya buɗe baki cikin kakkausar muryar sa yana mai faɗin. "Ke atinanin ki har akwai wani jarumin ne bayan ni aduk faɗin jahar nan da ƙetaren ta, ko ko azaton ki akwai wani mutum wanda zai iya jure raɗaɗin tsumagiya ta? Shin shi ɗin ɗan wace masarauta ne ma da farko?" Ya faɗa ƙasa-ƙasa tayarce ita kaɗai ce zata ji yana mai kafeta da idanuwan sa, kamar yacce itama ta kafesa da nata, tukun daga bisani ya saki wani shu'umin murmushin da yayi ai'nahin futo da kyawun sa, sannan ya ɗora da cewar. "Agaskiya nayi matuƙar jin daɗin sauraron wannan labarin daga bakin ki, domin ko ada ina tinanin bani da abokin karawa wanda zamu gwada ƙwanji tsakanin ni da shi wurin neman ki, amma sai gashi yau naji cewar akwai sa daga bakin ki, hakan kuwa ki sani ba ƙaramun farin ciki ya sanya ni ba, sai dai kuma ina son ki shaida masa cewar ni Yariman Yamma, tun farkon kafuwar ahalin mu ba'a taɓa yin wani wanda yay bugun shaɗi ba tare da yayi nasara ba, dan haka sai shima ya ƙara shiri akan wanda yake yi, domin kuwa ke ɗin tawace ni kaɗai, kuma an halkice kine domin n... "Dakata Malam!"
Ta faɗa da ƙarfi tana mai ɗaga masa hannu sama, tukun ta buɗe baki tana mai sakin wani irin wuci tare da faɗin. "Kar ka kuskura ka ƙara gigin furta kalmar cewar ni ɗin takace muddin baso kake na datse harshen ka ba kafun kabar wurin nan, domin kuwa wannan kalmar mutum ɗaya ne kawai ya halatta ya faɗe ta aduk faɗin duniya, kuma wallahi wallahi ni ɗin tasa ce kamar yacce shi ɗin yake nawa, bayan shi kuma babu wani agefen sa." Ta ƙarasa maganar tana mai juyawa daniyyar tafiya.

Caraf taji Yarima ya cafki yatsun hannuwan ta adai dai lokacin da ta ɗaga ƙafa danniyar yin gaba.
Cak ta tsaya ai'nda take ba tare data juyo ba ranta na tsantsar ƙuna, yayin da shi kuma ya saki yatsun hannun nata yana mai sake komawa daga gaban ta.
Ɗauke kai tayi daga kansa tana mai kallon gefe tare da sakin huci, domin kuwa aduk lokacin da zata kalli fuskar sa ji take tamkar ta shaƙesa ya mutu dan baƙin ciki.

"Ya da jin haushi haka kuma Gimbiya ta, ko kuwa har kin sare ne tun yanzu sabo da kin san nine dana sara?" Ya faɗa yana mai jifan ta da murmushi, tukun ya sake ranƙwafawa dai dai saitin fuskar ta yana mai yin ƙasa-ƙasa da murya tare da faɗin. "Ki sani ina sonki, kuma akan sonki babu abun da bazan iya ai'katawa ba dan ganin na mallakeki, dan haka ina mai sake sanar miki da ki shaidawa shi wancan ɗin ya fara shiryawa, domin ko haɗuwa ta da tasa bazata taɓa yin kyau ba, nima kuma da zarar na koma gida zan sanarwa da Lamiɗon mu cewa na samu abokin karawa."
Ya ƙarasa maganar yana mai matsawa gefe ya bata hanya.
Sai lokacin ta ɗago kai tana mai jifan sa da wani irin matsiyacin kallo. Wata irin tsanar sa take ji aranta irin wacce bata taɓa yiwa wani mahaluki ita ba aduniya, sabo da ganin sa da take amatsayin barazana gare ta akan soyayyar ra da Giɗaɗon ta, tukun daga bisani ta janye idanuwan ta tana mai ɗaga ƙafafuwan ta tayi gaba ba tare da ta sake tanka masa ba.
Amai-makon tayi hanyar da zata sadata da gida sai kawai ta doshi hanyar wurin da tsuntsayen ta suke ranta atsantsar ɓace.
Yayin da shi kuma Yariman Yamma ya juya yana mai komawa kan shimfiɗar nan ya zauna zuciyar sa na tsantsar tururi, sabo da ganin irin tarbar da tayi masa amatsayin sa na wanda zai zamto miji gare ta.
Taune lips ɗin sa na ƙasa yayi da ƙarfi yana mai girgiza kansa tare da rumtse idanuwan sa, tukun daga bisani ya buɗe su yana mai buɗe baki yace. "Tabbas ko kai wane ne sai na sanya ka kayi nadamar soyayyar da ka fara da wacce nake muradin aure, sai nasa kayi dana sanin-sanin ta amatsayin ƴa mace balle har kasota, domin ko wallahi wallahi Haddiyal tawace ni kaɗai!"
Ya faɗa cikin kaushi yana mai sake rumtse idanuwan sa, zuciyar sa na tsantsar tururi da ƙuna.



*ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ, CIKIN BAƘAR MASARAUTA.*

Sosai shirye shiryen bikin godiya ga abun bauta Gargabilu da za'ayi ajibi ya kan-kama da gasken gaske acikin baƙar masarauta.
Gaba ɗaya an sake sabon fenti akowane wuri tare da sabon tambari acikin masarautar, yayin da ko wane bawa da baiwa suka kasance suna ta shiri kuma har yau suna kan shirywa.

Acan filin biki ma bayi ne suke ta aikin share share da jera kujeru acikin sa.
Yayin da wasu kuma suke ta faman wucewa da wasu mahaukatan iccina ɗauke akafaɗun su suna masu kai su wani fili su aje.

Acan wurin su Bir kuwa zaune yake agaban Iyar Bayi ya tanƙwashe ƙafafuwan sa suna tattaunawa.
Sake matsawa kusa da Bir Iyar Bayi tayi tana mai miƙa yatsun hannun ta ta riƙo nasa da su.
Ɗago idanuwan sa yayi ya kalleta kamar yacce ita ɗin ma take kallon sa, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Al'farma nake roƙo awurin ka Jarumi na, ina son gobe ka zamto yaro nitsats-tse kamar yacce sauran yara suke, kayi abun da yake agaban ka karka kuskura ka kalli ko inda Gimbiya take balle har kaje wurin ta kajawa kanka bala'i kaji."

Uhm! "Iya ta kenan, to ni dama ai bawai ina zuwa wurin ta bane, itace dai take biyowa hanyar data kasance hanyar mu, ni kuma abu ɗaya dana sani shine banga abun da yake tattare da itaba wanda har zai firgita dan tazo wuri in gudu in ɓuya, wannan dalilin ne yasan ya aduk lokacin da tazo giftawa nake ƙara matsawa inda take domin naga ƙarshen ikon ta." Bir ya faɗa yana mai sakin murmushi idanuwan sa akan fuskar Iyar Bayi, yayin da ƙwaƙwalwar sa kuma ke hasko masa kyawun fuskar Gimbiya Tasmir tare da kyawun surar jikin ta.

"To wa gari ya waya kuma, wane yake wahala bayan kai Jarumi?" Iyar Bayi ta faɗa tana mai cigaba da kallon sa, tukun ta daga bisani ta ɗora da faɗin. "Tun kafuwar tarihin BAƘAR MASARAUTA ba ataɓa yin zamanin da ɗan sarki ko sarki yake zuwa giftawa ta wuri ba, asamu wata hallita da ke kasancewa awurin ba tare da sun gudu ba bayan ƴan rakiyar su kawai sai akan ka Jarumi, shin kai ɗin me zai hana kazamto kamar sauran ƴan uwanka bayi ko domin lafiyar ka Jarumi, domin ko kasan akan wannan abun da kake ai'katawa tsaf har ranka kana iya rasawa acikin BAƘAR MASARAUTA."

"Iya ta kenan, bazaki fahimci yarce nake ji bane kwata-kwata, sai dai kuma abun da zan faɗa miki shine, wallahi bazan iya nisantar ta ba, bazan iya jurewa jin sautin taba ba tare da na ɗaga ido na kalle ta ba." Bir ya faɗa yana mai kallon Iya, yayin da ita kuma Iya ta saki baki cikin firgici tana mai zaro idanuwa waje, tukun daga bisani ta fara ɗaga laɓɓa bakin ta na tsantsar rawa tana mai faɗin. "Shin kasan abun da kake faɗe kuwa Jarumi? Shin wai anya ma kana cikin hankalin kane Jarumi, to wai ma mekake nufi da bazaka iya jure jin sautin taba ba tare da ka ɗaga ido ka kalle ta ba?" Iyar bayi ta watso masa tambaya amatuƙar ruɗe tana mai futo da idanuwa waje.

"Shiyasa tun farko nace miki bazaki fahimta ba Iya, amma ba komai kawai ki kwantar da hankalin ki akwai lokacin da bake kaɗai ba hatta da sauran mutanen dake cikin masarautar nan zaku fahimta." Ya faɗa yana mai lumshe idanuwan sa, tukun daga bisani ya wara su yana mai zame ƴan yatsun hannuwan sa daga cikin na Iyar Bayi da ta saki baki take aikin kallon sa, kana ya miƙe tsaye yana mai juyawa zai tafi.

"Jarumi!" Iyar Bayi ta faɗa tana mai miƙewa tsaye itama.
Cak Bir ya tsaya a'inda yake ba tare da ya juyo ba, yayin da ita kuma Iya ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai nufar inda yake.

Gaban sa ta ƙarasa ta tsaya tana mai kallon fuskar sa.
Lumshe idanuwan sa yayi agaban Iya ba tare da yace komai ba, domin ko yasan duk abun da zata faɗa masa ayanzu bama fahimta zai ba.

"Na roƙe ka Jarumi badan ni ba, na roƙe da abun bauta Gargabilu ka futa daga harkar Gimbiya Tasmir, domin ko tsaf ana iya fille kanka muddin irin wannan furucin da kayi ayanzu zai cigaba da futa daga cikin bakin ka acikin BAƘAR MASARAUTA."

Hmmmm! "Ki kwantar da hankalin ki Iya ta, ni da kaina na faɗa miki babu damuwa, sannan kuma babu abun da zai faru."

"To idan har hakane da gaske ina son yanzu kamun al'ƙwarin babu abun da zai haɗaka da Gimbiya Tasmir gobe." Iya ta faɗa tana kallon sa.

"To ai dama Iya ba daga ni bane matsalar, tambaya ce kawai take mun akan rayuwar ta ni kuma nake yarce naso da ita ta hakan, wannan fa shine kawai abun da ke faruwa."

"To amma mai zai hana ka bata amsar tambayar da taimakan idan ka sani ko domin hutun ka?"

"Iya kenan, shiyasa tun farko nace miki bazaki fahimta ba, amma ba komai yanzu dai na miki al'ƙwarin bazan ko kalli inda take ba gobe balle har wani abu ya shiga tsakanin mu Iya ta." Ya faɗa yana mai juayawa ya cigaba da tafiyar sa hankali kwance, yayin da ita kuma Iya ta juya tana mai komawa ta zauna tare da buga uban tagumi da hannu bibbiyu.


Acan ɓangaren Gimbiya Tasmir kuwa sosai ake shirya ta tun yau, wani irin gyara ake yiwa gashin kanta, yayin da ƙafafuwam ta da hannuwan ta kuma aka ƙunshe su da ƙunshi irin na jan lalle da yay tsananin yi mata kyau.
Zaune take akan wata kujerar ƙarfe mai azabar kyau ana mata gyaran gashi.
Sosai ta ƙagara ranar gobe tazo, domin kuwa gobe ne take ganin ranar da zata wuce duk baƙin cikin da wancan ƙas-ƙantaccen bawan ya ƙunsa mata cikin sauƙi!



*ƘASAR HAUSA JAHAR WASAI, CIKIN MASARAUTAR WASAI.*

Misalin ƙarfe goma na safe dai dai Babban yaya ya tura kansa cikin ɗakin Asad bakin sa ɗauke da sallama.

Kwance ya hange sa akan gado gaba ɗaya ya ƙudun dune jikin sa da eskimo, sai fuskar sa kawai da ya bari awaje yana shara-rar bacci.

Kallon haɗaɗɗen agogon bangon da yake manne ajikin bangon ɗakin Babban yaya yayi, sabo da ganin da yay har yanzu Asad bai tashi ba.
Girgiza kai yayi bayan ya janye idanuwan sa daga kan agogon, tukun ya cigaba da takawa yana mai dosar bakin bed ɗin.

Wuri ya samu daga gefen gadon ya zauna, tukun yakai tafin hannun sa zuwa jikin Yarima Asad yana mai ɗan bubbugasa, bakin sa na furta kalmar. "Kai Asad! Asad!! Asa..." "Wai kai dallacan me yasa mugun jarababben mutum ne kai!" Yarima Asad ya faɗa aharzuƙe yana mai buɗe idanuwan sa tare da miƙewa zaune.

Ƙam ya tsaya ayarce yake yana mai zaro idanuwa tare da buɗe baki, sabo da fuskar da yay araba da ita wacce ko kaɗan bai kawo cewar itan zai gani ba, kafin daga bisani kuma ya fara ɗan sosa ƙeya yana mai sakin yaƙe tare da faɗin. "Ashe Babban yaya nane ban sani ba."

Uhm! Babban yaya ya sauke ɗan gajeren numfashi yana mai kafesa da idanuwa.
Sake sosa ƙeya yayi, sabo da yarce yaga yaƙi ya ɗauke ido daga kan sa, tukun daga bisani yace. "Kayi haƙuri Yaya na wallah na zata wancan masifaffen al'amin ɗin ne yazo, shiyasa kaji na faɗi haka."

Taɓe baki babbayn yaya yayi ba tare da yace komai ba, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Ina fatan dai kayi sallah, ba wai sai yanzu ka tashi ba ko?"

"Haba dai ai acikin masallaci nai sallah ma Babban Yaya." Asad ya faɗa yana mai gyara zaman sa, tukun daga bisani ya ɗora da faɗin. "Ina kwana Yaya na."

"Alhamdulillah." Babban Yaya ya faɗa yana mai miƙewa tsaye, tukun ya sake fuskantar ƙanin nasa yana mai faɗin. "Dama zuwa nai na sanar maka ka kasance cikin shiri, gobe misalin ƙarfe tara na safe zakamun rakiya zuwa MASARAUTAR FULƊE ta cikin JAHAR KAGUL."

"Amma Yaya masarautar fulɗe?" Yarima Asad ya faɗa yana mai sosa kai, kana far'ar kan fuskar sa na gushewa, tukun daga bisani ya ɗora da faɗin. "Da kuma akawai wani wuri da zamuje gobe ni da Al'amin fa Yaya."

"Sai ku ɗaga taku tafiyar zuwa jibi idan mun dawo, domin kuwa wannan tare na shirya mana ita ku duka biyun, kuma har mai martaba ma yasan da shirin."

"Kuma shima Abban ya yadda atafi dani?" Yarima Asad ya faɗa yana mai ɗan zaro idanuwa, sabo da sanin mahaifin nasa da yay baya taɓa yanke masa hukunci sai ya fara tambayar sa yaji yana son abun ko ko, badan komai ba kuwa sai dan kawai tsananin ƙaunar da yake mai, wanda hakan yana

10 / 43