Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BAƘAR MASARAUTA A Cikin Duhu PART 1 by Umar Faruq D

Author :  Umar Faruq D Category :  African Stories & Novels

Chapter   11 / 43

30K to 33K   out of 128.4K words

ɗaya daga cikin abubuwan da sukayi sanadin ƙara lalata sa.

"Kai Asad wannan fa umarni ne nake baka ba shawara ba da har kake shirin cika ni da tambayoyi, dan haka katabbatar gobe kun shirya da wuri daga kai har Al'amin ɗin tun kafin na futo." Babban Yaya ya faɗa yana mai ɗan ɗaure fuska, sabo da ganin da yay sakin fuskar tasa na shirin sanyawa yace bazai bisa ba, domin ko ya riga daya sani muddin yaje ya samu mai martaba ya faɗa masa baya son zuwa to shikenan fa zuwan ya fasaya sa shi.

"Tom shikenan Allah ya kaimu Yaya na." Yarima Asad ya faɗa badan ransa yaso ba.
Yayin da shi kuma Babban Yaya ya juya yana mai dosar waje bakin sa na furta cewar. Katabbatar kuma ka futo kayi break, sannan kaje ka nagaisar da Mamy yanzu."

"Oh shirt!" Yarima Asad ya faɗa yana mai dukan fillow alokacin da ya tabbatar da Yayan nasa ya futa, tukun daga bisani ya ɗora da faɗin. "Aiko wallahi babu wanda ya isa yasan ya ni nasa blanket ajiki sai dai afasa zuwan dani." Tukun yasa hannu yana mai yaye eskimon dake jikin sa zuwa gefe, sannan ya zuro dogayen fararen ƙafafuwan sa da suke lulluɓe da kwantaccen baƙin gashi akan su zuwa ƙasa.
Babu komai a jikin sa sai ɗan ƙaramin boxer da ya tsaya masa asaman guiwoyin sa.
Janyo takalman dake ajiye agafen gadon yayi yana mai zura kafafuwan sa acikin su, tukun ya miƙe tsaye duka yana mai dosar hanyar toilet cikin takun sa wanda shi kaɗai ke zautar da Ƴammatan dake binsa.


*GIDAN GWAMNAN JAHAR WASAI.*

Tunda Billy ta baro Asadullah palace har kawo yau bata bar ƙunci ba tare da jin takaicin abun da Yarima Asad yayi mata.
Sanye take cikin engilsh wear na black ɗin wando jeans da yayi matuƙar kama jikin ta ƙam-ƙam, sai ƴar ƙaramar jar riga mai ɗan guntun hannu da take sanye ajikin ta wacce ta zamto kusan da ita da babu duk ɗaya, domin kuwa bata hana komai bayyana ba na daga surar jikin ta.
Yayin da kanta kuma yake ɗauke da farin gashin atarch ta tufkesa, sai wani uban hill shoe da yake sanye aƙafar ta tana mai sakkowa daga kan stairs.
Direct ta doshi dining area ɗin da mahaifin ta da kuma mahaifiyar ta suke zaune akan kujeru, da alamun ita ɗin suke jira ta ƙaraso dama.

"Morning Dad! Morning Mom!" Ta faɗa tana mai jan kujera ɗaya sannan ta zauna akai.

"Morning daughter, fatan kin tashi lafiya." Mom ɗin tata ta faɗa tana mai bubbuɗe kulolin da suke agaban ta waƴan da suke ɗauke da kala-kalan abinci cikin su danniyar tayi serving ɗin su.
Yayin da shi kuma Dad ɗin nata ya bita da idanuwa kawai ba tare da ya amsa gaisuwar da ta masa ba.
Mai da idanuwan ta tayi kan wayar ta dake riƙe ahannun ta tana mai fara shafata.

"Dear meke damun daughter ne, gaba ɗaya tun jiya naga duka yanayin ta ya sauya, kwata-kwata bata walwala kamar yacce ta saba, shin meke faruwa ne mara daɗi da bansan da shi ba?" Mahaifin nata ya faɗa yana mai kallon mahaifiyar tata alamun ita ɗin yake tambaya ba ƴar ba.

Uhm!
Ta sauke ɗan gajeren numfashi, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "To gatanan dai, sai dai yanzu kaima ka ɗora daga inda na tsaya, domin kuwa tun jiya data fuce daga gidan nan ita kaɗai ba tare da guard's ba ta dawo gaba ɗaya abirkice, kuma babu kalar tambayar da ban mata ba akan ta faɗamun abun da ke faruwa amma tace mun wai babu, shi yasa na rabu da ita da zummar yau idan kai ka tambaye ta ta faɗa maka muji." Mom ɗin tata ta faɗa tana mai kallon sa.

"Subhanallahi, wai dama ba na hanaki futa bane ke kaɗai daughter, shin mene ne ma yafaru ajiyan, wane ya taɓaki kuma mai yay miki, sannan waye ubansa afaɗin Jahar Wasai?" Dad ɗin nata ya faɗa ahargitse yana mai kallon ta.

Ajiye wayar dake ɗauke ahannun ta tayi akan table ɗin dake gaban ta tana mai shash-shake fuska ba tare da tace komai ba."

"Kwantar da hankalin ki daughter ki yimun bayanin damuwar ki, ni kuma na miki al'ƙawarin muddin bata ƙarfi na ba zan yaye miki ita ayau yau ɗin nan." Ya faɗa yana mai miƙa hannu ya riƙo tafukan hannayen ta cikin nasa.

"Yarima Asad ne Dady!"

"Yayi miki me? Ba dai ya sake wulaƙanta ki bane kamar yarce kika faɗamun ya miki a kwanaki ba ko?"

"Ai da Dady da kalar na kwanaki ne ma dako sani ba zakuyi ba, domin ko shi ba komai bane akan wanda yamun jiya."

"Dukan ki yay ko ko zagin ki yay ne?" Mahaifin nata ya faɗa da ƙarfi yana mai miƙewa tsaye jijiyoyin kansa na futowa raɗa-raɗa akan goshin sa.

"Kusan hakan Dad, domin kuwa har hankaɗe ni yay na faɗa cikin swimming pool, dan bada ban Allah yasa na iya ruwa ba da shikenan sai dai akawo muku gawata!" Ta faɗa tana mai matso ƙwalla daga cikin idanuwan ta.

"Ina!!! Ai ko wallahi sai yayi nadamar abun da ya ai'kata, zanje in samu uban sa ayau yau basai gobe ba domin ajasa masa kunn...

"A'a Dad ba haka nake so ayi ba." Ta katse baban nata da faɗin haka ba tare da ta bari yakai ƙarshen maganar saba.

"Kamar ya ba haka kike so ayi ba daughter, ko ko kina nufin kice mun na barsa ne awannan karan nan gaba kuma ya illatamun ke yacuce ni, shin shi agidan ubanwa aka faɗa masa haka ake soyayya, ko kuwa haka yaga ubansa nawa uwarsa tsawa da duka, to wallahi daga yau anyi an gama kema, dan ke kanki bazan saurare ki ba ballan tana har ki sanyani na yafe masa."

"Nima bawai ina nufin ayafe masa bane Dad." Ta faɗa tana mai kallon mahaifin nata.

"To ya kike so amasa ne daughter?" Ya faɗa shima yana mai komawa ya zauan akan kujerar da ya tashi, yayin da ita kuma mahaifiyar tata tai shiru ba tare da tace komai ba, sai abincin ta da take ci kawai tana kallon su.

"Wani shegen murmushi Billy ta saki tana mai ɗan tane lower lips ɗin ta, tukun daga bisani ta buɗe baki bayan ta miƙa hannu ta riƙo hannun mahaifin nata cikin nata tana mai faɗin. "S................✍

🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎
👑👑
🦋
🦅🕊🦆
🐍🎠🐄🏹



_*NA*_




UMAR FARUQ*D*



*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*



*FREE PAGE 08*



"So nake abi masa ta hanyar da bai taɓa zato ba Dad, ma'ana kawai ka samu iyayen sa kayi musu magana akan auren mu, nasan idan akayi hakan dole ya dena mun hulaƙacin da yake yi mun, kamar yacce nasan babu tayarce za'ai mahaifin sa yaƙi yin komai kace yayi." Ta faɗa tana mai kallin baban nata, yayin da shi kuma yayi shiru ba tare da yace komai ba, sai kansa da ya ɗaga sama yana mai kallon haɗaɗɗen rufun dake cikin ɗakin, tukun daga bisani ya sauke kan nasa ƙasa yana mai watsa ƙwayar idanuwan sa akan fuskar ƴar tasa, sannan ya buɗe baki yana mai faɗin. "Tabbas na gamsu da zancen ki ɗari bisa ɗari my Daughter, Dan haka ayau yau ɗin nan zan turawa mahafin nasa da saƙon zuwa na gare sa, domin kuwa agobe-goben nan nake son ayi duk mai yuhuwa, sannan kuma aƙarshe in faɗawa mahaifin sa aja masa kunne, sabo da ya kiyaye kar bayan anyi aure ya cigaba da abun da yake yi yanzu." Ya faɗa still idanuwan sa akan fuskar ƴar tasa.
Yayin da ita kuma tayi wata irin miƙewa tana mai matawa kusa da shi, tukun tayi hugging ɗin sa daga zaunen da yake da matuƙar ƙarfi tana mai faɗin. "Yess my Dad, that's why akullum nake ƙara son ka, sabo da kaima kana son abun da nake so." Ta ƙarasa maganar da sakar masa kiss akan goshin sa, tukun ta juya aguje tana mai kama hanyar stair's cikin tsantsar farin ciki.
Yayin da shi kuma mahaifin nata ya bita da idanuwa fuskar sa ɗauke da yalwataccen murmushi shima.


*WASHEGARI*

ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.

Tun daga bakin tafkeken ruwan da yayiwa jahar karfuz ƙawanya mutum zai fahimci yau ɗin ana wani gagarumin taro ne acikin sa basai an faɗa masa ba, sabo da yarce jama'a na garuruwa daban- daban suke ta shigowa suna wucewa, wasu akan dokuna, yayin da wasu kuma suke akan ƙafafuwan su, ga kuma yarce akabi aka zagye gefen ruwan da yake abakin garin, wanda dole sai mutum ya tsallake sa kafin ya shiga jahar karfuz da wuta acikin kaskwaye tanaci bal-bal-bal!

Acan cikin Baƙar Masarauta kuwa ban da sautin kiɗa babu abun da akeji yana tashi, domin kuwa tun cikin dare aka gama shirya filin biki tas, sannan kuma aka zageye sa da kayan kiɗa masu matuƙar sauti, tare da kaskwayen Huta waƴan da suke ɗauke da iccina suna ci acikin su.
Yayin da daga can gefen filin kuma wani tamfatsetsen farin ruwa mai wucewa yake.

Sosai aka ƙawata wurin da ado kala-kala, yayin da tambarin masarautar tasu kuma ya kasance manne akowane wuri, acan ƙarshen filin kuwa daga jikin bango wata irin haɗaɗɗiyar ƙatuwar kujerar ƙarfe ce aka jere awurin, yayin da gefe da gefen ta kuma aka aje wasu ƙananan kujerun masu azababben kyau suma na ƙarfe masu dauke da tambarin baƙar masarauta ajikin su, yayin da tsakiyar filin kuwa aka ƙawata sa fiye da yarce aka ƙawata ko wane wuri.

Wani tafkeken daɓe (floor) ne akayi awuri mai matuƙar tudu da tsairs ajikin sa, gaba ɗayan sa zage yake da randinan da suke ɗauke da Huta acikin su suna matuƙar ci sosai, yayin da saman daɓen kuma aka ajiye wani danƙareran gunkin da akayi sa da taɓo da basa da kyan gani ko kaɗan, yayin da gefe da gefen sa kuma ya kasance ɗauke da fulawoyi zube aƙasa zageye da shi masu matuƙar yawa da wal-wali, sai kuma tambarin baƙar masarauta da aka bi aka manna sa aduka ƙasan daɓen.

Acan ɓangaren bayi kuwa ko wanne shiryawa yake cikin kalar shigar sa.
Yayin da ɓangaren Gimbiya Tasmir kuwa ta kasance zaune akan wata ar'niyar kujerar ƙarfe mai azabar kyau da sheƙi acikin ɗakin ta, yayin da wasu ƴammata da suke ɗaure da ɗan guntun baƙin ƙyalle iya guiwar su tare da ƙatuwar farar rigar yadi ajikin su mai ɗauke zanen tambarin masarautar tasu suke aikin tsan-tsara mata wata irin azababbiyar kwalliya mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, kallo ɗaya zaka musu katabbatar da amatuƙar tsorace suke, sannan kuma ko kaɗan basa cikin nutsuwar su, sabo da yarce suke aikin wasu sassa na jikin su na kar-karwa.
Yayin da ita kuma ta kasance lumshe da idanuwan ta tana mai ɗan taune leɓen ta na ƙasa ahankali, tare da ɗan sakin murmushi lokaci bayan lokaci, wanda yayi matuƙar bawa ƴammatan da suke yi mata kwalliya mamaki, domin kuwa zasu iya cewa tunda suke da ita basu taɓa ganin ta tana murmushi irin haka ba sai yau, duk da dai dama bawai suna iya kallon fuskar ta bane ba ada, yanzun ma dan suna mata kwalliya ne shiyasa har suka samu wannan damar kallon ta, amma sai dai tun da suke basu taɓa jin ko alabari ba ance tayi murmushi sai yau da suka gani azahiri .

Afannin ta kuwa ba komai ne ke sata murmushi ba sai tunawa da take yi yauce ranar da zata koyawa ƙasƙantaccen ƙazamin bawan can Bir da yake ganinta tamkar tsaran sa hankali, domin kuwa ta tanadi azabobi kala kala waƴan da zata yi masa su ayau fiye da duk sauran da ta masa abaya muddin bai bata amsar tambayar ta ba.

Sanye take da wata doguwar riga mara kafaɗa wacce ta kasance ruwan ƙasa mai duhu sosai, yayin da kanta kuma ya kasance ɗaure da abun ɗaurin ɗan kwali kalar ruwan zuma da aka mata ɗauri irin mai hawa hawa da shi, sai sarƙar goshi mai azababben kyau ta goal da take zagaye akan ta. Yayin da ƙafafuwan ta da hannuwan ta harma da wuyan ta suka kasance ɗauke da sarƙoƙin goal masu matuƙar kyau da tsada suna ƙyalli.

Sosai tayi matuƙar kyau tana ta faman sheƙi ta ko ina.

Acan ɓangaren su Bir kuwa tun cikin dare Iyar Bayi ta sake zaunar da shi tana mai sake roƙon sa akan karya ko kalli fuskar Gimbiya Tasmir, balle har tai masa wani abun.
Da tom ya amsa mata shima yana mai ƙudurtawa ransa cewar zaiyi yarce Iyar tasa ta roƙe sa yayi ko domin farin cikin ta, amma bawai dan yana tsoron wani abu da Gimbiya Tasmir zata masa ba, asalima yasan sai yayi tsantsar kai zuciyar sa nesa, tukun zai iya haƙura ya kasa ɗaga kai ya kalle ta muddin sukai kusanci da juna, gashi kuma yasan wajibine suyi kusancin, tunda akwai gaisuwa ta daban da Bayi suke kaiwa ahalin Sarki aduk irin wannan ranar.


*ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN BAƘAR MASARAUTA.*

Tun misalin ƙarfe takwas da minti arba'in Yarima Asad ya gama shirin sa tsaf kamar yacce Babban yaya ya umarce sa akan ya shirya da wuri.
Sai dai kuma irin shigar da yay ta yau tafi ta kusan koda yaushe muni, domin ko sanye yake da wani farin wando three quarter wanda yake akekkece daga saitin cinyoyin sa, tayarce har ake hangen farin net boxer ɗin dake sanye jikin sa, wato crazy, sai wata baƙar t shirt mai ɗan guntun hannu da take sanye ajikin sa da tayi matuƙar kama jikin sa, tayarce har ta bayyana gaba ɗaya murɗaɗɗiyar surar sa.
Yayin da sumar dake ɗauke akansa sa mai tsananin yawa kuma ta kasance atsage gida biyu, banda wal-wali da sheƙi babu abun da take yi, sabo da ruwan mayukan da ya mulketa dasu har zuwa ƙasumbar sa, sai wuyan sa kuma da yake ɗauke da wani silin sarƙar goal mai matuƙar ƙyalli, yayin da hannun sa ɗaya kuma ya kasance ɗaure da wani azababben baƙin agogo yayi matuƙar ƙara haskaka fatar hannun, sai kuma ɗayan hannun da ya bisa da wasu abun hannuwa na roba suma baƙaƙe. Banda faman ciccin magani yana kumbura babu abun da yake aikin yi, donin ko koda Al'amin yazo yana masa magana ma ko kai bai ɗaga ya kalle sa ba balle ya tanka masa, hakan da Al'amin ya gani ne, sannan kuma ya fahimci dalilin fushin nasa ya sanya yake ta faman tsokanar sa yana sheƙar uwar dariya, domin ko shi sanye yake da manyan kaya ɗinkin riga da wando na shadda.

Ƙarasawa yayi zuwa inda takalman sa suke yana mai sa hannu ya ɗauko wani sabon baƙin boot yana mai sanya ƙafafuwan sa acikin su, tukun ya janyo wayar sa ya riƙe ahannun sa yana mai komawa gefen bed ɗin sa ya zauna tare da mai da idanuwan sa kanta.
Ko minti biyu baiyi ba da zama sautin ringing ya fara tashi daga cikin wayar tasa.
Yamutsa fuska yayi yana mai sake ɗaure fuska, sabo da sunan da yaga yana yawo akan screen ɗin wayar tasa, wato Yaya na. Tukun daga bisani yayi picking yana mai kai wayar kan kunnen sa.

Lumshe idanuwan sa yayi yana mai ɗan taune lower lips ɗin sa da haƙora ba tare da yace komai ba, da alamun dai yana sauraran abun da ake faɗe ne daga can, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Tom shikenan gamunan." Daga can ƙasan makoshin sa, kana ya janye wayar daga kan kunnen sa yana mai miƙewa tsaye.

"Ka taso Malam ana jiran mu." Ya faɗi haka yana mai yin gaba.

Murmushi Al'amin yayi ba tare da yace komai ba shima, tukun shima ya miƙe yana mai bin bayan sa.

Acan ɓangaren Babban yaya kuwa sanye yake da manyan kaya harda alkyabba ajikin sa.
Tsaye suke agaban wasu arnayen motoci da suke ta faman ɗaukar ido, tare da dogaran sa da suke sanye da uniform da zura zuran bulalai riƙe ahannun su, suna masu kallon hanyar da su Yarima Asad zasu ɓullo, alamun su ɗin kawai suke jira kenan.

Al'amin ne ya fara ɓullowa tukun Yarima Asad ya biyo bayan sa, tun daga nesa Babban yaya ya saki baki tare da zuba idanuwa akan ƙanin nasa saboda shigar da ya hango sanye ajikin sa, yayin da suma dakarun nan gaba ɗaya suka bisa da kallo, duk da dai hakan ba sabon abu bane awurin su, sai dai amma gaba ɗaya cikin su babu wanda yay zaton ganin sa ahaka yau, duba da wurin da suka san zasuje.

Tafe suke babu mai cewa wani ƙala daga shi har Al'amin, dan shi Yarima Asad ma kansa sunkuye yake aƙasa, ahaka har suka ƙaraso bakin motocin nan.

"Ina kwana Yaya." Al'amin da Yarima Asad suka faɗa adai dai lokacin da suka ƙaraso gaban Ciroma.

"Da alamu ka manta sunan wurin dana faɗa maka zamuje ne, ko kuma ka kurmance alokacin da nake faɗa maka jiya, shiyasa har ka sanyo waƴan nan ƴan iskan kayan ajikin ka ko?" Babban yaya ya faɗi haka ransa aɓace ba tare da ya amsa gaisuwar da suka masa ba, sai idanuwa kawai da ya kafe yarima Asad dasu yana kallon sa.
Yayin da shi kuma ya sake gyara tsayuwar sa awurin da yake yana mai ɗaure fuska tare da ɗaukar yastun hannuwan sa ya kai kan ƙeyar sa yana sosawa ba tare da yace komai ba.

"Wai ba magana nake maka bane da kamun shiru kana bina da idanuwa?" Babban Yaya ya faɗa da ƙarfi ransa na ƙara tafar fasa.
Yayin da shi kuma Yarima Asad ya rumtse idanuwan sa da ƙarfi yana mai danna lower lips ɗin sa cikin baki ya cije su, sabo da tsawar da yayan nasa yamasa ransa na ɓaci shima, tukun daga bisani ya buɗe baki still yana sosa ƙeya tare da faɗin. "Am dama

11 / 43