Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BAƘAR MASARAUTA A Cikin Duhu PART 1 by Umar Faruq D

Author :  Umar Faruq D Category :  African Stories & Novels

Chapter   39 / 43

114K to 117K   out of 128.4K words

kafe sa da idanuwan ta da suka canza launi.
Yayin da dakarun nan nata kuwa gaba d'ayan su suma sukayi tsaye cirko-cirko suna masu jiran ta basu umarni su far masa.

A hankali Bir ya d'an jujjuya kansa, kana daga bisani ya lumshe idanuwansa, sannan ya sake bud'e su akan fuskar Gimbiya Tasmir da yake ganin yau ta k'arayi masa kyau fiye da yadda ya ganta a baya.
Kana ya d'an zaro harshen sa yana mai lasar busassun lab'b'an sa da yajisu sun bushen take yanzu, sannan ya d'an jujjuya k'wayoyin idanuwansa.
Kana wani irin murmushin farin ciki ya sub'uce masa, yana mai cigaba da kallon fuskar ta, yayin da yake jin zuciyar sa na wani irn sanyi.
Tukun daga bisani ya d'an d'aga lab'b'an sa a hankali bayan ya langwab'ar da kansa gefe, idanuwan sa akan ta, yana mai fad'in.

"Tabbas nine d'in dai kuwa Gimbiya, kinga yau ma mun sake had'uwa ko.
Amma fa kin san me?"

Ya fad'a yana mai cigaba da jifan ta da kyakkyawan murmushin sa, wanda ita kuma take jin sa tamkar futar wuta daga cikin bakin sa zuwa zuciyar ta, tsabar yadda take sake tafar-fasa.
Kana ya sake lumshe idanuwan sa, sannan ya d'ora da cewa.
"Hak'ik'a ke d'in kin kasance ta daban acikin duka matan duniya, domin kuwa kyawun ki ya zarc...."
"Dakata! Dakata mun haka k'ask'antacen Bawa mara galihu!"
Gimbiya Tasmir ta katse sa da fadin haka cikin wani irin lafazi mai matuk'ar kaushi da sauti, ta yadda har sai da hurin gaba d'aya ya amsa a lokacin da tayi furucin.
Yayin da jijiyoyin kanta kuma suka futo sukai rud'u-rud'u akan goshin ta, ga wani irin gumi da ya cigaba da tsats-tsafo mata, ta yadda zuwa yanzu har ya fara d'iga, kana idanuwanta sukayi wani irin jajahur tamkar gauta.

Bud'e idanuwanta data rumtse su a lokacin da take furucin tayi akan fuskar sa.
Kana daga bisani ta fara d'aga k'afafuwanta da suke futar da sautin sarak'aunan gwal tana mai dosar wurin da yake, cikin wani irin taku wanda shi kad'ai ya isa ya kad'a hanjin cikin matsoraci, amma shi kuwa Bir wani irin farin ciki ne yaji ya sake ziyartar sa a lokacin da ta doso wurin da yaken.
Yayin da yake ganin fuskar tasa ta na sake yi masa kyau acikin idanuwansa fiye da baya, ta yadda har yake ganin tamkar canzawa take aduk bayan wasu lokutan.
Lumshe idanuwansa yayi adai-dai lokacin da yaji ta iso dab da shi.
Kana ya d'ago tafin hannun sa yana mai d'orasa adai-dai saitin zuciyar sa ya dafe ta.
Sannan ya bud'e idanuwan nasa wanda hakan kuma yayi dai-dai da tsayuwar ta cak a gaban sa.

Cikin muryar ta mai futar da amon b'acin rai ta bud'e baki tana mai fad'in.
"Hak'ik'a yau zan tabbatar maka da kayi gangancin shiga gona ta, zan tabbatar maka da ni d'in ko wacece, zan sanya ka ka bambance tazarar da take a tsakanin ni da kai matsiyacin Bawa, domin kuwa nayi rantsuwa da Ubangiji Gargabilu akan sai nasa an maka ninkin ba ninkin abun da akai maka waccan ranar."

Ta k'arasa maganar tana mai sakin wani irin huci, ta yadda hucin ke dukan fuskar Bir.

Amai-makon taga tsoro ya bayyana akan fuskar Bir sai kawai taga ya sakar mata kyakkyawan murmushin sa yana kallon ta, tukun daga bisani ya bud'e baki yana mai fad'in.
"Dama har akwai azaba wacce za'a fad'e ta da har zata firgita Bawan da ya tashi cikin BAK'AR MASARAUTA Gimbiya?
Shin wai kin san ma me kuwa iyata take kirana da shi?
To bara kiji in fad'a miki.
Jarumi shine sunan da iyata ta mun lak'abi da shi tun ina cikin tsumma na.
Shi kuma Jarumi kin san ako da yaushe ba raggo bane shi d'in, dan haka ina mai farin cikin sanar miki da cewar Jarumi yana mai maraba da duk wata wahala da zata b'ullo muddin daga gareki ne, domin kuwa ta kan juyawa ta koma dad'i ne, tare da farin ciki a cikin zuciyar Bir."

Ya k'arasa maganar da busa mata sauran iskar bakin sa akan fuskar ta, yana mai sakin murmushi mai sauti.
Take kuwa a wurin ta lumshe idanuwan ta tana mai sakin ajiyar zuciya.
Sosai Bir ya k'yalk'yale da dariya, yana mai d'aga yatsar sa ya nuna ta da ita.
Yayin da ita kuma ta bud'e idanuwanta tana mai jin tamkar ta kashe kanta dan bak'in ciki.
Cikin wani irin yanayi ta mik'ar da hannunta gefe, tana mai bud'e tafin hannun ta da yake wata irin karkarwa ba tare da tace komai ba.
Da sauri badakaran da ke rik'e da takobin tsafinta ta gado ya fara tawowa da baya da baya, yana mai yowa wurin da take.

Zube gwuiwoyinsa yayi a k'asa yana mai durk'usar da kai k'asa, tukun daga bisani ya d'ora mata zureriyar takobin nan akan tafin hannun ta.

Damk'eta tayi da matuk'ar k'arfi, tare da rumtse idanuwan ta, kana daga bisani kuma ta bud'e su akan fuskar Bir dan taga yadda yanayin sa ya koma.
Amma amai-makon taga ya tsorata yanzu sai taga dai still yana cigaba da jefo mata murmushin sa ne.
Hakan yasa tayi wani irin ja baya daga wurin da take tana mai nuna sa da takobin nan.
Kana ta bud'e baki cikin muryar ta mai matuk'ar amo tana mai fad'in.
"Rai Rai Rai Buuuu Hoooo Reeee!"
Sannan tayi wani irin kautar da takobin daga kansa tana mai matsar da ita jikin wata bishiya da take a gefen su.

Fittt!
Kakajein k'arar wucewar Bir asama, yadda kasan wanda iska ta d'auke sa yana mai zuwa ya manne a jikin bishiyar nan.
Kana wasu irin igiyoyi suka futo suna masu d'ad'd'aure sa a jikin bishiyar.

Sosai gaba d'aya dakarun nan sukayi matuk'ar firgita da abun da suka gani, yayin da su kuma 'yammatan bayin nan jikin su ya kama wata irin karkarwa tsabar tsoro.

"Shairamaaa!"
Gimbiya Tasmir ta fad'a da k'arfi tana mai nuna gefen bishiyar nan.
Take kuwa dank'areriyar macijiya ta bayyana a wurin, tana mai kad'a harshenta.

Sake d'aga takobin tayi ta nuna jikin Bir da ita, tana mai fadin.
"So nake ki bambance masa tsakani na da shi Shairama."

Ai kuwa take wannan macijiyar tayi kansa gadan-gadan.

Da matukar k'arfi Bir ya rumtse idanuwansa yana mai jin bugun zuciyar sa na k'aruwa.
Yayin da ita kuma wannan macijiyar ta cigaba da tunkarar sa.

Tana dab da zuwa gare sa Gimbiya Tasmir ta sake kiran sunan ta da matuk'ar k'arfi, tana mai nuna can gefe wurin da ta baro.
Yayin da take sakin wani irin nishi, tamkar wadda taga zaki ko kuma aka biyota za'a kasheta ta samu ta tsira.

Ita kuwa wannan macijiyar da wani irin sauri ta juya tana mai komawa wurin ta na farko.
Kana daga bisani kuma ta b'ace-b'at, yadda kasan bata tab'a bayyana a wurin ba.

Hakan da Gimbiya Tasmir ta gani ne ya sanya ta juyawa b'arin da dakarun ta suke, sannan ta bud'e baki cikin wani irin sauti tana mai fad'in.
"Kutsamamamun jikin sa, ta yadda zaiji ina ma baizo duniya ba yanzu-yanzu."

Aiko da wani irin sauri suka tunkare sa gaba d'ayan su, suna masu zare bulalan su.
Yayin da ita ma ta fara d'aga k'afafuwan ta tana mai nufar bakin bishiyar nan.

Su kuwa dakarun nan suna k'arasawa gaban bishiyar suka fara dukan Bir ta ko ina, tamkar suna dukan bishiyar.
Yayin da ita kuma Gimbiya Tasmir tayi tsaye a gaban sa tana mai sakin wani irin murmushi aduk lokacin da taji ya saki ihu, sabo da wani irin farin ciki da take jin yana lullub'e zuciya da ruhin ta da ganin sa a hakan da tayi.

Su kuwa 'yamnatan bayin nan wata irin karkarwa jikin su yake daga wurin da suke a tsaye.
Sosai suka toshe kunnuwan su suna masu durk'usar da kawunan su k'asa, sabo da kar kallon Bir da kuma jin sautin ihun su ya sanya su zubda hawaye, daga nan suma kuma su had'u da nasu hukuncin wurin Gimbiya Tasmir.

Basu suka dakata da dukan sa ba har sai da sukaga gaba d'aya ya dena numfashi, a lokacin kuma tini suka huce awa guda da fara dukan sa.
Ganin da Gimbiya Tasmir tayi kansa ya tuntsire yayi gefe ne, ga kuma jinin dake tsiyayowa ta ko ina daga jikin sa, tun daga tsakar kansa har zuwa tafukan k'afafuwan sa ne, ya sanya ta dakatar da su.
Kana kuma taji bugun zuciyar ta ya sake sauyawa fiye da baya, ga wani irin tsoro da bata san kona mene ne ba da taji ya lullub'e ta, sai dai kuma duk maitar mutum bai isa ya gano halin da take ciki ba dan ya kalle ta.

Da wani irin sauri ta d'aga takobin ta tana mai nuna sa da ita, kana ta furta kalmar.
"Gargabilu!"
Take kuwa igiyoyin nan suka tsits-tsinke gaba d'ayan su, Bir na fad'owa k'asa jikake Tim.
Sannan ta juya tana mai nufar hanyar da zata mayar da ita gida ba tare da ta kula wa'yan nan dakarun nata ba.

Da sauri suma suka take mata baya suna masu bin ta.

Suna b'acewa daga wurin sai ga dan dazon bayi nan hankulan su atsantsar tashe sun yi kan Bir gadan-gadan.
Yayin da Iyar Bayi kuma da wasu daga cikin Bayin suke wani irin kuka na tausayin halin da suka samu Bir a ciki.

Da k'arfi Mazum ya shek'awa Bir ruwan da yake d'auke a hannun sa a gaba d'aya jikin sa.
Take kuwa a wurin yaja wata irin doguwa ajiyar zuciya, yana mai bud'e idanuwansa da sukayi matuk'ar kumbura a hankali.
Yayin da bakin sa kuma ke furta kalmar.

"Gimbiyata!!!"

Ganin jama'ar da yayi zagaye da shi ta ko ina ne ga Iyar Bayi da ta durk'uso gare sa tana rusar kuka ne ya sanya sa yin shiru, yana mai mayar da idanuwan sa ya sake lumshe su.

Cikin sauri Iya ta fara basa taimakon gaggawa take a wurin.
Har lokacin kuma bata bar kukan tausayin sa ba tana aikin nanata kalmar.
"Jarumi! Jarumi!! Jarumi!!!"


*ENGLAND*
Tun bayan rabuwar su da Yarima Asad a waccan ranar har yau da akayi sati d'aya dai-dai basu k'ara had'uwa ba.
Hakan kuma ya faru ne sabo da rashin neman san da ba tayi ba.
Amma kuma babu ranar da tazo ta huce a cikin ranakun da bata tura masa da sak'on fatan Alkhairi ba.
Sai dai kuma tun da take yin har zuwa yau bai tab'a yo mata replay ba, duk da sunan tan da take rubuta masa aduk lokacin da zata tura masa sak'on.

Haka kuma har kiran sa tana yi a kowace rana sau d'aya, amma shima baita yin picking ba.

Wannan dalilin ne ya sanya yau ta k'udiri aniyar komawa wurin sa, domin ayi komai a huce wurin.

Sosai kuwa taci ado na gani na fad'a cikin shigar k'ana nan kaya.

Bluen wando jeans ne da tsayin sa ya tsaya a iyakar k'aurin ta sanye a jikin ta, sai kuma wata farar t shirt mai d'an fad'i tare da kwalliyar duwatsu a gaban ta da take sanye a jikin ta.
Kana kuma sai wani blue d'in d'an k'aramin mayafi da ta d'orasa asaman kanta, tare da hulla jelolin sa baya, yayin da k'afafuwan ta kuma suka kasance cikin wani farin toms da yay matuk'ar had'uwa.
Sai farin agogon fata da yake d'aure akan tsintsiyar hannun ta da yayi bala'in yi mata kyau.
Sosai tayi matuk'ar yin kyau cikin shigar tata.
'Daukar hand bag d'in ta tayi tana mai yiwa Zee sallama, sannan ta fuce daga cikin room d'in su.


Acan wurin Yarima Asad kuwa misalin k'arfe hud'u da kwata dai-dai ya futo wurin nasa ya zauna.
Sanye yake da wandon jeans nevy blue a jikin sa da yayi matuk'ar yi masa kyau.
Yayin da rigar sa kuma ta kasance bak'a mai d'an fad'i.

Sai tsitsiyar hannun sa kuma da take d'aure da bak'in agogon fata.
K'afafuwan sa kuwa sanye suke da bak'in cover shoe da yayi bala'in had'uwa.

Ya d'ora k'afa d'aya akan d'aya yana sipping d'in kofi d'in sa hankali kwance, yayin da d'ayan hannun sa kuma yake aikin shafa wayar sa da shi tamkar koda yaushe.

A kullum yana ganin sak'wannin Billy da take turo masa, amma kuma tun da ya karanta na farko har yau bai k'ara karanta wani ba.
Sabo da dama shi d'in haka yake, sannan kuma duk bala'in yarinya baki isa ya tura miki da sak'on gaisuwa ba, sai dai idan yana buk'atar ki tukun zai neme ki, shima kuma kawai I'm waiting, zakiga ya turo, domin kuwa shi ababen hutu kawai ya d'auki mata a wurin sa.

Zaman sa baifi da minti Ashirin a wurin ba Billy ta k'araso da irin salon ta na wancan satin.

"Hello Prince."

Ta fad'a k'asa-k'asa a dai-dai lokacin da ta k'araso gaban kujerar da yake, tana mai tsayawa daga gefen sa.

Lumshe idanuwa Yarima Asad yayi yana mai shak'ar daddad'an k'amsin turaren da yake sanye a jikin ta ba tare da ya d'ago ya kalle ta ba.

Tsaf ya gane ko wacece ta sanadin muryar ta da yaji, wacce ya shaidata tun a waccan ranar da suka fara had'uwa.

"Can I sit Please?"

Billy ta fad'a cikin wata irin murya mai matuk'ar shiga jiki, kana tana mai d'an had'awa da sakin murmushi a k'arshen maganar tata.

Wani irin abu Yarima Asad yaji ya tsarga masa tun daga 'yantsun k'afafuwan sa har zuwa k'wak'walwar sa, ta sanadin muryar da tayi amfani da ita wurin yin maganar, ga kuma k'amshin turaren da yake sanye a jikin ta da suke fara shirin canza masa yanayi.

A hankali ya d'ago kansa yana nai watsa yan madai-daitan fararen idanuwan sa akan fuskar ta.

Wani irin murmushi Billy ta sakar masa tana mai d'an jujjuya idanuwan ta.

Yayin da shi kuma Yarima Asad yayi wani irin lumshe idanuwan sa, yana mai jin wani irin azababben filing na taso masa, sabo da shigar dake sanye a jikin ta da ya sake yin arba da ita.
Kana daga bisani kuma ya janye idanuwan sa daga kan ta yana mai fad'in.
"Uhm!"
Sannan ya juya yana mai kallon gefen sa, tukun ya mayar da idanuwan sa kan wayar sa yana mai cigaba da shafata.

Hakan da Billy taga yayi ne ya sanya ta fahimtar yana nufin ta zauna kenan.
Ai kuwa cikin tsantsar farin ciki irin wanda ba zai misaltu ta tsinci knata a ciki.
"Alhamdulillah."
Ta furta acikin ranta tana mai matsawa kusa da shi ta zauna.
Ta yadda har k'ugun sa da nata suka a jone wuri d'aya, kana cinyar ta na gugar tasa cinyar.
Wanda hakan da tayi kuma ya sake hulla Yarima Asad ciki wani yanayi, sai dai kuma girman kansa yak'i ya bari ya nuna hakan a gare ta kwata-kwata.

Cikin wata iriyar murya wacce take tattare da shagwab'a a cikin ta Billy ta bud'e baki, bayan ta d'ora tafin hannun ta akan kafad'ar Yarima Asad, tana mai fad'in.
"Tun ranar da na ganka a wurin nan nazo wucewa da nazo wurin ka nayi maka magana, kana kuma nayi maka introducing d'in kai na, amma kai har yau kak'i kace mun komai.
Sunan ka ma sai a jikin katin ka kawai na gani, kana daga baya naji labarin ka a wurin k'awata."
Ta k'arasa maganar cikin wata irin murya tamkar zata fashe da kuka, kana tana d'an murza kafad'ar sa cikin wani irin salo.

Rumtse idanuwa Yarima Asad yayi yana mai d'an sauke wata 'yar gajerar ajiyar zuciya.
Tukun daga bisani ya bud'e su gaba d'ayan su har sun fara sauya launi, kana ya juya gefen ta yana mai watsa idanuwan nasa da suka fara canza launi akan fuskar Billy.
Tukun ya d'an zaro mata su yana mai d'aukar yatsat hannun sa d'aya ya d'ora ta akan lips d'in sa.
Wato dai yayi mata irin yadda ake yiwa yara idan ba aso suyi magana.
Kana daga bisani ya janye idanuwan sa daga kanta yana nai d'an fesar da wata zazzafar iska daga cikin bakin sa.

Hakan da Billy ta gani ne ya sanya ta sake fad'awa jikin sa tana mai kife tafukan hannayen ta a k'irjin sa, tukun ta fara wani irin shafasa tana mai bud'e baki cikin shagwab'a tace.

"Allah yau nima sai kayi mun magana, na gano ka so kake kayi mun rowar muryar ka."
Ta k'arasa maganar tana mai d'an diddira k'afafuwan ta a k'asa.
Yayin da rabin jikin ta kuma ya kasance akan na Yarima Asad.

Ai kuwa take yaji gaba d'ayan da ya sake fad'awa cikin wata duniyar.
Hakan ne yasa sa sanya hannuwan sa yana mai d'ago kanta da ta kwantar da shi akan k'irjin ta cikin wani irin yanayi, sannan ya bud'e baki cikin muryar sa da take a matuk'ar shak'e.
Yana mai fad'in.
"Ke ki mun shiru fa ko kuwa yanzu na mammakeki."
Ya k'arasa maganar da zaro mata idanuwan sa.

Hakan da Billy ta gani ne ya sanya ta sake b'are baki tana mai cigaba da sakin kukan, tare da mai-maita kalmar sai ka yimun magana ni dai wallahi.

Ai kuwa take a wurin Yarima Asad yayi wani irin lumshe idanuwan sa, tukun ya fara yin k'asa da kansa a hankali-ahakali, harya dan gana fuskar sa da tata fuskar, ta yadda har tsinin hanicin su suke tokarar juna.
Kafin daga bisani kuma ya d'ora lips d'in sa akan nata.

Wasu irin tagwayen ajiyar zuciya Billy sauke tana mai lumshe idanuwan ta.
Tukun daga bisani suka fara kissing d'in junan su cikin wani irin yanayi na zak'uwa gaba d'ayan su, ko tinanin cewar a waje suke ma ba suyi ba.

Sun d'auki tsayin mintina goma suna abu d'aya a wurin.
Kafin daga bisani kuma Yarima Asad ya mik'e tsaye d'auke da Billy a hannun sa tamkar jaririya.
Sannan ya juya yana mai dosar hanyar da zata kaisa room d'in sa hannun sa d'auke da Billy.
Yayin da ita kuma Billy taji wani irin farin ciki mara misaltuwa na lullub'e zuciya da ruhin ta.
Ji take ina ma ace da jama'a a wurin sosai, domin su gani su tabbatar da ita d'in mai sa'a ce, kana kuma ta daban ce, tun da gashi nan tayi abun da dubban mata suka kasa yi, wato sace zuciyar Yarima Asad.

Ba shi ya sauke ta ba har sai da ya sadata da had'ad'd'iyar doguwar kujerar da take a cikin falon nasa.
Tukun ya dire ta akai yana mai bin ta suka cigaba da aikata masha'ar su, cikin tsantsar nishad'i da jin dad'i................✍


*MUNA GAB DA DAWOWA CIKIN LABARIN MU, SAURA KIRIS YA RAGE KAWAI .👌
DAN HAKA ASAKE WANKE IDANUWA, DOMIN KUWA ANAN NE WASAN ZAI FARA. 😅



*BAK'AR MASARAUTA*



*NA*



UMAR FARUQ*D*



*PAGE 29*



Wani irin farin ciki mara misaltuwa Billy take jin kanta a cikinsa, domin kuwa tun daga lokacin data fara soyayyar minti da saurayin ta da yake a k'asar Hausa bata tab'a jin irin abun da take ji

39 / 43