Author : Umar Faruq D Category : African Stories & Novels
zai faru agaba, da kuma wanda zai faru yanzu ta hanyar duban sa da yake, wanda aduk lokacin da yake aikin duban nasa suke faɗin yana saduwa ne da abun bautar su, amatsayin sa na waliyin sa.
Shi kuwa wannan bokan ba kowa bane face BOKA MAI HUTAR KASKO!
Tsoho ne tukuf mai kimanin shekaru tamanin da tara aduniya, shima kuma ya gaji bokancin ne awurin mahaifin sa, wanda ya mutu yana da shekaru ɗari da ashirin da biyu aduniya shi, sabo da shi kansa bokancin gado ne a Baƙar Masarauta, domin kuwa acewar su jinin waliyin abun Bauta ne kawai ke iya sake zama waliyin sa, kamar yacce ɗan Sarki ne kawai ke sake zamtowa sarki, kuma gaba ɗayan su suna amfani ne da Huta tare da Ƙasa wurin duban nasu, hakan yasa ake kiran duk wanda yake kan karagar ta bokancin da suna BOKA MAI HUTAR KASKO, sabo da ita wannan hutar dake ci acikin kasko itace mai haska masa gaban sa, kuma itace take fara isar masa da duk wani saƙon Gargabilu ga jama'a, hakan yasa ba'a taɓa barin ta ta mutu, ko da yaushe ake cikin ƙara izata a kowane lokaci.
Sarki Barbaru shine sarki na talatin alokacin, yayin da Boka mai hutar Kasko kuma ya zamto Boka na goma shabiyar awannnan lokacin.
Ko kaɗan ba aɗauki rai abakin komai ba acikin Baƙar Masauta, dan ko ataƙaice ma babu satin dake zuwa ya huce ba tare da an kashe rai sama da ukku ba acikin masarautar, kuma idan an tashi kisan anayin sane acikin bainar jama'a, gaban kowa da kowa, dan kuwa sai anyi sanarwa ma tukun ake ai'watarwa, kuma mafi akasarin kisan da akeyi bawai anayin sa bane kan an ai'kata wani Babban laifi ne ba, asalima ko Sarki ne yazo giftawa ko kuma ɗan sarki muddin bawa ya kuskura ya biyo hanyar, to hukuncin kisa ne akansa, hakan shine dalilin da ya sanya Bayi ke mugun tsoron Ƴaƴan Sarkin tare da shi kansa Sarkin, ga kuma tsafi da suke da shi na masifa, wanda ake basu shi tun aranar da suka zo duniya.
Sarki Barbaru yana da mata biyu ne tare da Ƴaƴa biyu maza awancan lokacin.
Gimbya Haiwa itace matar sa ta farko, kuma uwar Ƴaƴan sa maza biyu.
Yarima Sauman shine ɗan sa na farko, kamar su ɗaya da uban sa sak, basu da bam-banci ko kaɗan, domin kuwa har halayyar sa ma irin ta ubansa ce tun yana ƙarami.
Sai kuma Yarima Sairan wanda ya kasance na biyu kuma ƙaramin su, kasancewar ita amaryar Sarki Barbaru mai suna Gimbiya Salwa bata haihu ba, ita kuma Gimbiya Haiwa Ƴaƴa biyu kawai ta haifa duk maza.
Gaba ɗaya matan nasa biyu suma ƴaƴan sarakai ne na wasu masarautun, waƴan da al'adun su suka kasance kusan duk iri ɗaya ne.
Sosai Gimbiya Salwa take da sauƙin kai fiye da Gimbiya Haiwa, domin kuwa ita Gimbiya Salwa har ta hanyar Bayi tana iyabi idan ta futo zagaya gida, kuma koda ta haɗu da Bawa ko Baiwa akan hanya bata sanyawa akashe su, sai dai kawai tayi gaba abun ta, saɓanin Gimbiya Haiwa da ko hanyar su bata iya bi, ballan tana har ta iyayi musu gafara idan sun haɗu.
Wannan kenan.
ƘASAR HAUSA, MASARAUTAR WASAI.
Sarki Abdallah shine ya zamto sarki na Ashirin acikin sarakan da suka mulki Jahar Wasai.
Kamar yadda aka sani mafi akasarin gidajen Sarauta ana samun rikici, hassada, baƙin ciki, tare da munafurci acikin sa, to hakan ma ya kasance acikin Masarautar Wasai, domin kuwa Sarki Abdallah ya taso ne tare da Ƴan uba, wato yayye da ƙanne waƴan da suke uba ɗaya, amma uwa kowa da tasa, kasancewar Margayi Sarki Ahmadu ya auri mata har kimanin huɗu ne.
To hakan yasa koda aka fara shirye shiryen naɗa Sarki Abdallah kan karagar mulki abayan mutuwar Sarki Ahmdu aka sha rikici, tare da ƙulalla-ƙullata ta kowace hanya wurin ganin bai hau kan karagar mulki ba, duk da kasancewar sa babban Ɗa namiji kuwa acikin Ƴaƴan Sarki Ahmadu, amma da yake shi ɗin Allah yace zaiyi, haka sukayi duk mugun abun da zasuyi suka gama, kuma yazo ya hau kan karagar mulki.
Yayin da awancan lokacin Galadima da Waziri kuma suka kasance ƙannen baban sa duka biyun, sai bayan sun rasu kuma abayan mutuwar sarki Ahmadu, sannan aka naɗa mutum biyu daga cikin ƙannen Sarki Abdallah, waƴan da suka haɗa uba ɗaya akan muƙaman, wato Alhaji Kabir Galadima, sai kuma Alhaji Nuhu aka basa Waziri, yayin da sauran ƴan uwan nasu suma duka suka zamto suna da tasu sarautar.
Sarki Abdallah ya kasance yana da mata Ukku ne cif.
Gimbiya Huwaila itace matar sa ta farko, ƴar sarki itama awata masarautar, sai kuma Gimbiya Amina matar sa ta biyu, itama ɗin ɗiyar Sarkin wata masarautar ne, sai amaryar sa kuma Gimbiya Khadija wacce akewa lakabi da Fulani, kasancewar ta bafullatana wacce kallo ɗaya mutum zai mata ya fahimci hakan, sabo da tsantsar kyanta tare da hasken fatar ta, duk da dai shima Sarki Abdallah'n Fulani ne na sali suma.
Tun kafin ya hau kan karagar mulki suke tare da Gimbiya Huwaila tsawon shekaru goma shabiyar, ƴayan su huɗu suka haifa, sai dai kuma cikin su duka huɗun mata ne babu namiji ko ɗaya.
Yarsu ta farko itace Gimbiya Rahama, sai ta biyu kuma mai suna Hafsat, sai kuma Fatima, daga ita kuma sai ƙaramar su mai suna Suwaiba.
Sosai jama'ar gidan suka sanyawa Sarki Abdallah ido tare da yin farinci, sabo da ganin da sukai bai taɓa haihuwar Ɗa namiji ba, wanda hakan yasa kowanne suke ta mafarkin wataran Sarautar tana iya juyewa ta koma ɗakin su.
Watan Sarki Abdallah ukku da hawa mulki ya sake yo sabon aure, inda ya auro Gimbiya Amina. Sosai hankalin Gimbiya Huwaila yayi matuƙar tashi alokacin da akai auren, domin kuwa tsoron ta ɗaya, shine kar Gimbiya Amina tazo ta haifi magajin Sarki Abdallah ba tare da ita ta ta haifo ba, amatsayin ta na matar farko, yayin da suma duka dangi suka zuba idanuwa suna jiran sukaga da abun da zata fara ita.
Sai dai kuma har tayi haihuwa biyu itama Allah bai bata ɗa namiji ba, duka biyun suka zamto mata, Wato Gimbiya Sumayya da Kuma Gimbiya Hafsat.
Sosai hankalin jama'ar gidan nasu masu jiran mulki ya sake kwanciya, sabo da ganin haka da sukayi, yayin da masu yin asiri akan hakan suke ganin aikin su naci sosai.
Itama Gimbiya Huwaila sosai taji daɗi, sannan kuma hankalin ta ya kwanta, sabo da ganin yarce Gimbiya Amina ta jero mata duka kamar ita, hakan yasa ta cigaba da fatan ta zamto uwar magajin masarauta.
Afannin Sarki Abdallah shima sosai abun ya dame sa, ba kuma wai dan baya son su ƴaƴan nasa mata da ake haifar masa ba, sai dai kuma ko banza shima yan son ace ɗan sane zai ɗora daga inda ya tsaya, kamar yacce ya zamto shima ya ɗora daga wurin da mahaifin sa ya tsaya, sannan kuma ko badan mulki bama, yana son ace ya haɗa ko wanne jinsi daga mazan har matan cikin ƴaƴan sa, domin kuwa ko wanne daga cikin su yana da daɗi tare da amfanin sa.
Hakan yasa ko shekara biyar ba'a rufa da auren su da Gimbiya Amina ba ya sake yo wani auren. Wato Gimbiya Khadija wacce ake kira da Fulani.
Sosai hankalin jama'ar gidan dana kishiyoyin ta ya sake tashi a lokacin da aka kawo ta gidan, ba dan komai ba kuwa sai dan kar suje ita ta haifo ɗa namiji, hakan yasa kusan duk suka duƙufa wurin ganin ba asamu ɗa nimiji ba, itama ta haifo mace kamar yacce sauran sukai, sai dai kuma suna nasu Allah na tashi, haka kuma muddin Allah yace ga yarce yake to babu wanda ya isa ya canza sa, domin kuwa watan Gimbiya Fulani goma shaɗaya dai dai acikin Masarautar Wasai, ta haifo ɗan ta namiji ƙatoto da shi, sannan kuma kyakkyawa mai tsananin kama da ita.
Subahanallah, zo kuga yarce aka nuna baƙin ciki ƙarara tare da hassada, haka jama'ar gidan da basu so hakan ta faru ba suka nuna, domin kuwa cikin su harda waƴan da suka kasa zuwa barka da baƙin ciki, dan ko hatta Gimbiya Huwaila da Gimbiya Amina sai bayan anyi Sallah isha suka iya zuwa ganin Ɗa, bayan kuma haihuwar anyi ta ne tun asubar fari, sosai suke jin baƙin ciki yarce kasan su mutu, dan ko ita kanta bayan ishar ma sunje gudun kar mai Martaba yaji labarin basuje ba ya zargi wani abun aransa.
Yayin da ta fannin mai Martaba kuma tare da masoyan sa na cikin gidan suka kasance cikin tsantsar farin ciki mara misaltuwa da samuwar ɗa namijin da sukai
Koda ranar suna tazo sosai akai shagali irin wanda ba ataɓa makamancin sa ba aduk sauran haihuwar da matan mai martaba sukayi, domin kuwa ko kilisar da akayi anyi tane ta bugawa ajarida, dan kuwa hatta da mai martaba sai da yayi wasa da doki irin wasan da bai taɓa yin makamancin saba tunda ya yake duniya, wanda hakan kuwa ba ƙaramun sosa ran mutane da yawa yayi ba acikin masarautar, haka akasha shagali aka watasar da kuɗaɗe kamar ba neman su ake ba, bayan jinjiri yaci suna. USMAN. Yayin da masoyan sa kuma masoyan mai martaba waƴan da sukai marhabun da zuwan sa da gasken-gaske suka yi masa laƙabi da BABBAN YAYA tun aranar da aka haife sa.
Tunda Gimbiya Fulani ta gano akwai masu ƙin dan nata sosai acikin masarautar ta dage dayi masa addu'a ba dare ba rana, sosai ta dage wurin yi masa azikarai irin waƴan da addini ya koyar har da ita kanta, kasancewar ta mace mai matuƙar ililimi da kuma aiki da shi.
Yayin da magauta kuma suka dage wurin ganin sun kassara rayuwar sa.
Bayan haihuwar Babban yaya da shekara biyu da rabi Gimbiya Fulani ta sake haihuwa, sai dai kuma wannan karan ƴa mace ta haifa, yarinya taci suna Sumayya, bayan ita kuma da shekara wata biyu da rabin ta sake haihuwar wata ƴar, still mace dai ita kuma taci suna Nafisat.
Hakan da magautan ta suka gani ne na bata ƙara haihuwar wani ɗa namijin ba yasan ya hankalin su yayi matuƙar kwanciya, domin kuwa ganin su tunda itama bata sakeyo wani namijin ba to abun yazo musu da sauƙi, tunda da zarar sun ɓarar da rayuwar Babban Yaya, ko kuma suka illatasa shikenan ya zamto babu ko ɗaya.
Yayin da ita kuma Gimbiya Fulani ta cigaba da dagewa da yiwa ƴaƴan ta addu'a gaba ɗayan su, sannan ta koyawa Babban Yaya su tun baifi shekara ukku ba, kasancewar yanzu shekarun sa sun kai kimanin biyar aduniya kenan.
Bayan haihuwar Gimbiya Nafisat kuma Gimbiya Fulani bata sake haihuwa ba, sai sauran matan Gimbiya Huwaila da kuma Gimbiya Amina da suka haifi wasu ƴaƴa matan, kowacce ɗaya har shekaru suka ja sosai.
BABBAN ZAURE LOCUS.
Azamanin baya Iyayen sheikh Ahmad ba acikin unguwar Babban Zaure locus suke zaune ba, suna cikin wata unguwace wacce ta kasance geto area, da take anan cikin garin Wasai, wato unguwar Ɗan Tanki.
Mahaifin sa mai suna Ishak haifaffan cikin garin Wasai ne.
Yayin da mahaifiyar sa Aishatu kuma ta kasance bafullatanar daji, makiyaya da suke yada zango awuri kafun su sake yin gaba kuma.
Sun haɗu da Ishak ne a watarana cikin wata kasuwa da take akusa da rugar su Aisha da suka yada zango awurin, ita sunzo siyen takalma silifas ita da ƙanin ta mai suna Aliyu, yayin da shi kuma ya raka wani abokin sa siyo kaji, kasancewar kasuwar irin kasuwannin nan da suke ci sau ɗaya arana, hakan yasa idan kaje a ranar kasuwar kusan zaka samu komai, hatta da akuyoyi masu su suna zuwa siyarwa, kuma suna yin sauƙi fiye da yarce ake samun su acikin gari.
Shigar su kasuwar kenan sukaci karo dasu har sun siya takalman suna shirin juyawa ita da ƙanin ta.
Aikuwa Ishaƙ na ƙyalle ido ya gansu gaba ɗayan sa ya ruɗe, ataƙaice dai haka ya sanya abokin sa suka bisu abaya, bai bari koda wasa sun ɓace musu ba, kuma basu bari sun fahimci su suke bi ba har suka ƙarasa rugar su.
Tun daga nesa su Ishak suka hange ta ita da ƙanin nata sun durƙusa gaban wasu mutane guda biyu da suke zaune akan tabarma ƙarƙashin inuwar darbejiya, tare da kur'anai buɗe agaban su, da alamun karatu sukeyi dai, tukun daga bisani sukaga sun miƙe suna masu shigewa cikin wani gida da aka masa shinge da karare, wanda yake ɗauke da bukkoki acikin sa.
Hakan yasa su Ishak suka ƙarasa zuwa wurin mutanen nan da suke zaune suna karatu bakunan su ɗauke da Sallama.
Gaba ɗayan su rufe kur'anan su sukayi suna sauraran su, tukun abokin Ishak ya koro musu bayanin abun da ya kawo su.
Take ko awurin yanayin mahaifin Aishatu malam Audu ya sauya, sabo da jin da yay sunce wurin ƴarsa sukazo, gashi kuma yaga ko kaɗan basuyi masa kama da mutanne rigar tasu ba.
Malam Sammani shi ya biye musu suka tattauna sosai, sannana aƙarshe yace suje su dawo bayan kwana biyu, alokacin sun gama yin tunani. Aikuwa ba tare da gardama ba suka tashi suka tafi, tukun shi kuma ya juya ga malam Audu yana mai yi masa nasihohi tare da nuna masa bam-bancin al'adu ko kuma yare bashi ke nufin babu aure tsakanin mutane ba, domin kuwa duk musulmi ɗan uwan musulmi ne. Haka dai yay ta masa nasihohi tare da kawo masa misalai, kasancewar sa malamin sa da yake ɗaukar karatu awurin sa tun da suka sauka agarin, tukun aƙarshe yace masa bincike akeyi shine ke nuni da ko mutum wanene, ba hakanan kawai kai tsaye ake yanke hukunci ba alamarin aure.
Ai kuwa tini ya fahimce sa, da yake dama ya riga ya gama amunta dashi, yasan bazai taɓa cutar dashi ba ko kuma wani nasa amatsayin sa na malami.
Bayan kwana biyu nayi sai ga Ishak da Abokin sa nan sun dawo kuwa, ai kuwa aranar dai basu tafi ba har sai da suka gana da Aishatu, kuma Alhamdulilah sun samu fahimtar juna cikin sauƙi, sannan kuma sunga canji sosai awurin mahaifin ta malam Audu, domin kuwa shi da kansa ya kawo musu fura da tabarma ya shimfiɗa musu, sannan kuma aƙarshe ya jasu sukaje wurin malam Sammani aka musu duk tambayoyin da za'ayi musu.
Ataƙaice dai duka baifi wata biyu sukai da haɗuwa ba aka ɗaura musu aure, aka tafi da Aishatu cikin garin wasai unguwar Ɗan tanki.
Gida ɗaya suke da mahaifan sa, sai dai kuma su nasu part ɗin daban yake, wato dai akwai katanga tsakanin su. Sosai suke zaman lafiya da junan su, sannan kuma mahaifan Ishak suke matuƙar ƙaunar Aishatu yarce kasan ƴar cikin su, barin ma mahaifiyar sa Baba Zulai, wanda hakan ko ba ƙaramun daɗi yayiwa mahaifan Aishatu ba alokacin da sukaji labari daga gare ta, tukun bayan bikin Aisha da shekara ɗaya da rabi kuma iyayen ta suka bar rugar su, suna masu sake yin gaba zuwa sosai, domin kuwa gaba ɗaya Ƙasar Hausa ma suka bari da su da shanayen su zuwa Ƙasar Malin, can wani yanki mai suna Jahar RUMAN, alokacin kuma Aisha ta haifi ɗan ta na farko ita da Ishak da suka sanya masa suna AHMAD, suna masa inkiya da mu'allim.
Sosai Aishatu tayi kuka, tayi kuka kamar ranta zai futa alokacin da suka yiwa iyayen ta rakiya zuwa bakin ruwa, kasancewar azamanin ana tafiya mai nisa ne ta cikin ruwa ga mutumin da yake neman sauƙi.
Bayan haihuwar Ahmad Allah ya sake azurata su da samun wasu ƴaƴan har guda ukku, amma su kuma duk mata ne. Bilkisu, Maimuna sai kuma ƙaramar su Ruƙayya. Dukan su suna da tazarar shekara bibbiyu har da rabi-rabi ne tsakanin junan su.
Afannin iyayen Aishatu kuwa tunda suka koma Kasar Malin yankin Jahar Ruman basu kara canza wuri ba, kasancewar nan ɗin sun same sa da tsantsar ni'ima ga kuma wadatar abincin dabbobi acikin sa, sannan kuma mutanen garin mafi akasarin su Musulamai ne masu san ƴan uwan su musulmai, ba kamar yankin Jahar Karfuz ba.
Sau ukku Aishatu da Ishak suna zuwa garin abayan komawar su, domin kuwa zuwa na ƙarshe ma har da ɗan su mu'allim da yake da shekara bakwai da rabi yanzu suka je.
JAHAR KAGUL, MASARAUTAR FULƊE.
Lamiɗo Sulaiman mahaifin Gimbiya Haddiyal shine sarki na goma acikin Masarautar Fulɗe, yana da mata biyu tare da Ƴaƴa biyar.
Matar sa ta farko itace Gimbiya Kaɓel, tana da ƴaƴa ukku, na farko shine Ummaru wanda sukewa laƙabi da Jauron Fulɗe, daga nan kuma bayan shi da shekara huɗu ta sake haifo wani ɗan namiji yaci suna Halilu, amma suna kiran sa da Bammi, bayan shi kuma sai Abubakar wanda suke kira da Buba.
Yayin da ita kuma matar sa ta biyu take da suna Gimbiya Maraimu, ita kuma tana da ƴaƴa biyu ne duk maza suma, Habibu shine ɗan ta na fari wanda suke sa'nni da Jauro Ummaru, bayan shi kuma ta sake haihuwar wani yaron mai suna Harisu wanda suke sa'anni da Buba, domin kuwa duka tsiran su baifi tazarar wata ukku ba.
Sosai Lamiɗo yake matuƙar son samun ƴa mace, hakama kuma afannin matan nasa da ƴaƴan sa suma duk suna son sugan su da yarin ƴa mace, amma sai dai Allah bai basu ba duka yaran maza ne.
Ita dai Masarautar Fulɗe ta kasance masarauta ce wacce ko kaɗan mutanne cikin ta basu da ilimin addini, duk da suna ikirarin su ɗin musulmai ne ako da yaushe, sai dai kuma ko kaɗan basa amfani da faɗar Allah, ataƙaice ma ko tauhidi basu sani ba, dan kuwa sun mayar da tsafi ba komai ba awurin su, domin kuwa babu wani Ɗa dake tasowa acikin gidan sarautar harya girma ba tare da ya iya tsafi kala-kala ba, a cewar su wannan itace kaɗai hanya wacce zasu iya kare kansu daga kowanne irin mugun mutum cikin sauƙi.
Basu damu da sai sunyi karatun boko ba, domin kuwa ada kwata-kwata ma basu yarda da ita bokon ba, sai daga baya ne abayan haihuwar Buba da Harisu aka samu wasu turawa tare da haɗin goyon bayan gwamnati sukazo har cikin Masarautar suka ƙarayi musu bayani akan boko tare da muhimmancin sa, kuma Alhamdulillahi alokacin sunyi sa'a, Lamiɗo ya aminta da zancen su duk da kasancewar sa mutum mai kafiya da tsayawa