Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BAƘAR MASARAUTA A Cikin Duhu PART 1 by Umar Faruq D

Author :  Umar Faruq D Category :  African Stories & Novels

Chapter   14 / 43

39K to 42K   out of 128.4K words

cike maƙil da kayan ciya-ciye, irin su ruwa, fruits, naman kaji, dana rago wanda aka sarrafa sa kala-kala jere akan wani ƙaton tray.

Basu jima da zama awurin ba sai ga Waziri da Galadima nan sun futo ta wata ƙofa da take acikin fallon bakunan su ɗauke da sallama.
Ƙarasawa sukayi zuwa kan kujerar da take facing ɗin wacce su mai girma gwamna suke akai, tukun suka zauna suna masu fara gaisawa cikin mutunta juna da girmamawa.
Zaman su baifi da minti biyar ba sai ga mai martaba Sarki Abdallah nan ya futo ta cikin ƙofar dasu galadima suka futo bakin sa ɗauke da sallama shima.

"Wa'alaikumu salam." Gaba ɗayan su suka amsa masa suna masu kai idanuwan su kansa.
Sanye yake da shigar sa irin ta koda yaushe, wato manyan kaya tare da alkyabba mai azabar kyau da rawani ɗauke akan sa.

Ƙarasawa yayi zuwa gaban kujerar da su mai girma gwamna suke yana mai miƙa musu hannu sukayi musabaha cikin mutunci da girmamawa, kana ya juya yana mai komawa kan kujerar da take agefen wacce su Waziri suke akai ya zauna, sannan ya buɗe baki yana mai faɗin. "Bismillah ga abinci nan ku taɓa mana." Ya ƙarasa maganar yana mai musu nuni da tray'n dake cike da kayan abinci kala kala akan sa da yatsar sa manuniya.

"Alhamdulillah! Alhamdulillah wallahi!!" Suka haɗa baki wurin fadɗe suma fuskar su ɗauke da murmushi.

Shiru ne ya biyo baya ba tare da wani ya ƙara cewa komai ba acikin su. Tukun daga bisani aminin mai girma gwamna mai suna Alhaji Saleh yayi gyaran murya yana mai ɗago kai ya fuskanci su mai martaba, tukun daga bisani ya fara ɗaga laɓɓan sa yana mai faɗin. "To ataƙaice dai ba komai ne yasan ya mu muka buƙaci zama daku ba sai akan wani muhimmin abu da yake atsakanin yaran mu duka, wanda afannin mu mu muke masa kallon abun alkhairi tare da alfahari garemu gaba ɗaya idan har muka samu ya tabbata." Ya faɗa yana mai gyara zaman sa akan kujera, yayin da su kuma su mai martaba suka zuba masa ido suna masu kallon su tare da sauraran sa fuskar su ɗauke da murmushi, ba tare da sunce komai ba.
Tukun shi kuma ya ɗora da faɗin. "Ba komai bane ba kuwa face soyayyar dake atsakanin yarinyar wurin mu, wato bilkisu ƴar wurin mai girma Gwamna, da kuma yaron wurin ku Yarima Asad."

"Asad kuma!" Suka haɗa baki su duka ukkun suna masu faɗin haka fuskar su cike da tsantsar mamaki, domin kuwa cikin su duka babu wanda bai san halin Asad ba na rashin son aure, dan kuwa babu yarce ba'ayi ba da shi akan su futar da matan aure amma shi yaƙi sai Al'amin ne kawai ya futar da tasa.

"Tabbas kuwa Asad naku da Bilkisu, dan kuwa ataƙaice sun ɗauki tsawon shekaru kusan huɗu suna atare, hakan yasa mukaga amai-makon su zauna suna ta abu ɗaya gwanda ace kawai anyi mai duka kowa ya huta, wannan shine dalilin da yasa muka buƙaci zama daku." Yaƙarasa maganar yana mai sakin murmushi.

"Masha Allah! Masha Allah!!" Galadima da Waziri suka faɗa gaba ɗayan su fuskar su ɗauke da murmushi, tukun daga bisani suka sake buɗe baki atare suna masu faɗin. "Haƙiƙa munyi matuƙar jin daɗin wannan labari daga bakin ku, kuma insha Allah abun bazai ɗauke mu ga dogon lokaci ba ba tare da anyi sa ba, tunda har su yaran sun samu fahimtar juna." Suka sake faɗe fuskar su ɗauke da murmushi.
Yayin da shi kuma mai martaba ya sake gyara zaman sa akan kujera, kana daga bisani yayi gyaran murya, tukun ya buɗe baki cikin yanayin sa wanda baka isa kace fariciki yake ba ko kuwa akasin sa, yana mai faɗin. "Masha Allah, naji duk abun da aka tattauna akai, kuma nayi farin ciki da jin hakan, dan haka yanzu sai muyi fatan Allah ya tabbatar mana da alkhairi." Ya ƙarasa maganar da sakin murmushin yaƙe, domin kuwa haka kawai yaji bai wani amunta da zancen su mai girma Gwamna ba, na cewar Yarima Asad na san Bilkisu, gashi shi kuma aransa yana mai jin bazai taɓa iya yiwa ɗan nasa mafi soyuwa acikin ransa auren dole ba, sai dai kuma yasan tunda abun ya zamto ahaka to koda tinanin sa ya zamto gaskiya na Asad baya son yarinyar babu yarce zasuyi daga shi har Asad ɗin dole suyi haƙuri ayi, domin ko shi dai bazai iya buɗar baki yace bazai haɗa jini da mai girma Gwamna ba, hakan shine ya sanya gaba ɗaya yaji yana yin sa ya sauya, sannan kuma ya ƙudiri aniyar samun Asad da maganar dan yaji ta bakin sa ayau yau ba sai gobe ba.

Ta fannin Alhaji Saleh kuwa cikin farin ciki ya buɗe baki yana mai faɗin. "Amin Amin."
Yayin da shi kuma mai girma Gwamna yake ta sakin murmushi ba tare da yace komai ba, duk da yarce yake son tun ɗazu ya buɗe baki yayi wa mai martaba bayanin abun da Yarima Asad yake yiwa Bilkisu tare da kashedin ajamasa kunne, sabo da jin da yay Alhaji saleh baiyi magana akan hakan ba, sai dai kuma da zarar ya kalli mai martaba danniyar ya buɗe baki yay masa magana akan hakan sai yaga ya masa wani irin kwarjini acikin idanuwa, hakan yasa yake ta ruƙon maganar acikin sa tun ɗazu duk da yarce yake son ya furta ta ba tare da yayin ba.

Sun ɗauki kimanin mintina talatin zuwa arba'in suna tattaunawa, tukun daga ƙarshe suka yiwa juna sallama su mai girma Gwamna suna masu miƙewa suka doshi hanyar waje.


*JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FULƊE.*

Cikin sauri Gimbiya Haddiyal ta ƙarasa cikin ɗakin ta, direct ta doshi ƙofar ɗakin da kayan tsafin ta na gado suke aciki, tana mai zuwa ta buɗesa, tukun ta mayar da sandar nan tata awurin data ɗauke ta tana mai ɗaukar farin ƙyallan da ake rufe ta da shi ta lulluɓe ta, sannan ta sake juyawa cikin sayri tana mai fucewa daga cikin ɗakin, kana ta doshi hanyar da zata sadata da fallo dan taje ta sanya atatso madara.

"Barka da futowa yake kyakkyawar Gimbiya." Wata matashiyar Baiwa da take share cikin tafkeken falon ta faɗa tana mai ajiye tsintsiyar hannun ta ƙasa tare da zube giuwoyin ta aƙasa alokacin da Gimbiya Haddiya ta futo daga cikin ɗaki.

"Am, kiyi maza yanzu-yanzu ki tashi ki tafi wurin majiaɗin shanu, ki sanar da shi cewar ina buƙatar sabuwar madara cikin ƙwarya ukku kafun nan da giftawar da ƙiƙa talatin gaba." Gimbiya Haddiyal ta faɗa tana mai kallon Baiwar dake durƙushe agaban ta ba tare data amsa gaisuwar da tai mata ba.
Yayin da ita kuma baiwar ta miƙe da sauri tana mai nufar hanyar da zata sadata da waje.
Tukun ita kuma Gimbiya Haddiyal ta juya tana mai komawa cikin ɗakin ta.

Tana shiga ta huce gaban wata wadrobe ta ƙarfe mai azabar kyau ruwan zuma da take ajikin bangon ɗakin.
Hannu tasa ta buɗe ta tana mai zaro wani farin towel mai ɗauke da lallausan gashi jikin sa, tukun ta maida murfin ta rufe sa, kana ta juya tana mai dosar hanyar da zata sadata da bathroom ɗin da yake acikin bedroom ɗin nata ba tare da ta tsaya cire kayan jikin ta ba, gaba ɗaya tana komai ne cikin sauri duk da yarce ranta yake amatuƙar cunkushe da baƙin ciki.


*****
Misalin ƙarfe shaɗaya da rabi na safe motocin su Babban Yaya suka shigo cikin Masarautar Fulɗe, kasancewar gudu sukayi bana wasa ba, domin kuwa tafiyar kusan awa biyar ce har da rabi, amma su sukayi ta acikin awa biyu da ƴan mintinu.

Tunda suka shigo garin Yarima Asad yake aikin yamutsa fuska tare da wurga kallon ƙasƙanci acikin sa, domin kuwa gaba ɗaya ji yay bazai taɓa iya rayuwa acikin wannan bagidajen garin ba, wanda ya kasance babu wasu wayayyun mutane acikin sa.
Banda aikin yamutsa fuska da taɓe baki babu abun da yake yi, yayin da shi kuma Al'amin yake ta sakin zuba yana mai faɗin. "Agaskiya garin nan yayi, domin kuwa ba ƙaramar ni'ima Allah ya wadata su da ita ba, kaga fa yarce suke da wata irin daddaɗar iska, ga ruwaye da suke ta faman gudu, tabbas mutum na garin nan dole ma fatar jikin sa tai ta ƙare kyau akoda yaushe, domin kuwa daga gani su basu san mece rana bama." Ya faɗa idanuwan sa akan hanyar da suke wucewa yana mai kallon ta ta cikin glass.
Yayin da shi kuma Yarima Asad ya rumtse idanuwa yana mai jin tamkar ya mammake Al'amin dan takaicin furucin sa, sabo da shi kwata kwata baiga wani abu da ya birge sa acikin garin ba, sai zallar haushi da ya basa ma, domin kuwa ya fuskanci hatta da mutanen cikin sa kusan dukan su duk ƙauyawa ne.
Aƙarshe ma da ya gaji da jin surutun Al'amin earpiece ya zaro acikin aljihun sa yana mai sanya ta cikin kunnuwan sa ya doɗe su da ita.
Ahaka har suka ƙarasa cikin Masarautar Fulɗe wacce take cike da abubuwan burgewa da kyan gani acikin ta, sai dai ta fannin Asad kuma har yanzu bai ga abun da ya burge saba acikin Masarautar.

Tun daga bakin ƙofa wasu dogarawa suka tarbe su cikin tsantsar girmamawa, sanye suke da kayan fulani, hannuwan su kuma riƙe da sandina, daga nan kuma suka yi musu jagora zuwa fadar Lamiɗon Masarautar Fulɗe.
Kallo ɗaya Yarima Asad yayiwa mutanen nan da suka zo tarbar su, daga nan kuma ya ɗauke idanuwan sa akan su ba tare da ya sake kallon wani daga cikin suba, dan ko gaba ɗaya ƙyanƙyamin su ma yaji shi, sabo da suturar dake sanye ajikin su, wacce yayiwa laƙabi da ta mahaukata ayanzu daga kallo ɗaya da yayi musu acikin zuciyar sa.

Dasauri Babban Yayan su Gimbiya Haddiyal wanda ake kira da Jauron masarautar Fulɗe yazo ya tarbe su cikin tsantsar mutun tawa, tukun daga nan ya shige gaba suna masu dosar cikin fada da take ɗauke da kayan ado na fulani tako ina gadan gadan.

Sosai Masarautar tayi matuƙar birge Al'amin, tayarce har yake jin ina ma ace sai sun kwana biyu tukun zasu barta, yayin da shi kuma Yarima Asad yaji gaba ɗaya wurin ya gundure sa, kana ko kaɗan bai ga wani abun burgewa ba acikin sa sai zallar ƙauyanci da yake gani.

Iso akayi musu har gaban Lamiɗo da yake zaune akan wata irin kujerar Al'farma ta ƙarfe mai azabar kyau, sanye yake da kaya irin na fulani, amma na sarauta tare da Alkyabba wacce ta kasance ta fulani ɗauke ajikin sa, sai farin rawani da yake ɗaure akansa, farine tas da shi yarce kasan ataɓasa jini ya ɓullo, kamar yacce duka ƴaƴan sa suka kasance suma.
Yayin da gefe da gefen sa kuna da gaban sa mutanen fada suka kasance zaune awurin.

Zama su Babban yaya sukayi akan shimfiɗar kafet ɗin da take agaban su suna masu kwasar gaisuwa awurin Lamiɗo.
Cikin mutun taka da far'a ya amsa musu fuskar sa ɗauke da tsantsar annuri, sannan daga ƙarshe suka sake gabatar da abun da yake tafe da su.

Gyaran murya mai martaba Lamiɗo yayi, tukun ya furta munji komai kamar yacce kuka faɗa arubuce, dan haka yanzu kai Jauro ka tashi ka kai su wurin cin abinci, inyaso idan sun gama sun huta sai su dawo ayi ciniki." Ya faɗa yana mai kallon Babban ɗan sa wanda zai kai kusan shekaru arba'in aduniya.
Amsa masa yayi da tom shima, tukun ya miƙe suma su Babban Yaya da su Yarima Asad da yake ta faman yamutsa har lokacin suka take masa baya.

Suna futa waje Jauron Masarautar Fulɗe ya hangi ƙanin sa mai suna Habu, mai kimanin shekaru talatin aduniya, wato sa'an su Yarima Asad dai.
Ƙwalla masa kira yayi da ƙarfi, cikin sauri Habu ya ƙaraso wurin da suke yana mai faɗin. "Barkan ku da zuwa baƙi." Fuskar sa ɗauke da murmushi yana mai kallon su Yarima Asad.
Idan ka gansa kai bazaka taɓacewa ɗan nan cikin Masarautar bane, domin kuwa sosai yake awaye shima, kasancewa yayi karatun boko har matakin degree shi.

"Yawwa."
Babban yaya da Al'amin suka faɗa cikin far'ah, yayin da shi kuma Yarima Asad ya faɗa ƙasa ƙasa ba tare da ya kalle sa ba.

"Yawwa Habu ga abokai nan kaja su ku tafi cikin lambu, sannan ka tabbatar an samar musu abinci da madara yanzu yanzu"

"Tom shikenan Hamma." Habu ya faɗa yana mai sake miƙa musu hannu suka sake yin musabaha, tukun yace ku tawo muje ko.

Jerawa sukai suka tafi suna tafiya suna hira da shi da Al'amin cikin raha, yarce kasan sun san juna dama. Yayin da shi kuma Yarima Asad yayi shiru yana sauraran su kawai ba tare da yace komai ba, ahaka har suka ƙarasa cikin wani ni'imtaccen lamubu mai ɗauke da korayen ciyayi tare da sanyi acikin sa.
Direct sukayi kan wata shimfiɗar Al'farma ta fata da take ɗauke da tum-tum akan ta daga can nesa.
Tunda suka shigo masarautar Fulɗe Yarima Asad baiga wurin da ya burge saba sai wannan kaɗai, hakan yasa ya jujjuya yana mai kai idanuwan sa ko wane sashe dake cikin wurin, tukun ya maida idanuwan sa kan shimfiɗar da suka ƙarasa gaban ta yana mai cire takalman dake sanye aƙafar sa ya hau ya zauna, kamar yacce Al'amin da suke uwar hira da Habu suka zauna.
Kishingiɗa yayi jikin tum-tum ɗin dake gaban sa yana mai lumshe idanuwan sa ba tare da yace komai ba.
Kallon sa Habu yayi fuskar sa ɗauke da murmushi, tukun daga bisani ya buɗe bakin sa yana mai faɗin. "Shin wai kai ɗin Bebe ne amma ko?" Ya ƙarasa maganar cikin raha.

Wara idanuwa Yarima Asad yayi akansa yana mai sakar masa murmushin yaƙe, still ba tare da yace komai ba, yayin da shi kuma Al'amin ya buɗe baki yana mai faɗin. "Bebe ko kuma miskili ba."
Ya faɗa yana mai hullawa Yarima Asad da ya zaro wayar sa yana shafawa harara.
Yayin da shi kuma Habu ya saki dariya yana mai faɗin. "Any way, ga dai abinci nan yanzu kuci tukun sai acigaba da hirar."
Ya faɗa yana mai fara buɗe haɗaɗɗun kwanukan da suke jere akan tray.
Farfesun naman ciki ne dana kaji da suka gaji da haɗuwa suna ta faman tashin turiri da ƙamshi acikin kwanika biyu da suke daga farko, sai kuma wani haɗaɗɗen kwandon kaba da yake ɗauke da Tufa, Inibi, Ayaba, Lemo, acikin sa da matuƙar yawa.

Bubbuɗe kwanukan duka yayi yaga babu madara kwata- kwata awurin.
Hakan ne yasa sa miƙewa yana mai kallon su tare da faɗin. "So sorry dan Allah fa, ashe wai basu kawo madaraba, but please ku ɗan jirani yanzu bara naje naji dalilin da yasa ba akawo ba." Ya faɗa yana mai miƙewa ya juya ya tafi ba tare da ya tsaya jin ta bakin su ba.

Bai tsaya ako ina ba sai acikin ɗakin Haddiyal da take zaune agaban madubi tana mutsikka mai afatar ta.
Da sauri ta juyo bayan ta tana mai kai idanuwan ta bakin ƙofa sabo da motsin da taji.

"Mai ya hana kisa akaiwa baƙi madara amatsayin ki na shugabar shanu, bayan kuma nasan an sanar miki da zuwan su tun kafin yau?" Ya faɗa yana mai kafeta da idanuwan sa.

"Kayi hakuri dan Allah Hamma, wallahi na sha'afa ne, amma nasa atatso ta tun ɗazu, kuma yanzu haka nasan an gama ma ƙila ma sun shigo da ita, dan haka bara na sanya kaya sai naje nasa akai madarar." Ta faɗa tana mai miƙewa ta doshi gaban wadrobe ɗin ta.

"A'a kawai ke yanzu abun da za'ayi shine, idan kin sa kayan kije ki ɗauki madarar ki kaita lambun gaban sa, ni kuma yanzu bara naje na ɗauka na kai lambun yamma inda su Hamma Jauro suke, domin kuwa har baƙin sunzo tun ɗazu gashi ba akai musu madara ba." Ya faɗa yana mai juyawa.

"Tom shikenan Hamma Habu." Gimbiya Haddiyal ta faɗa tana mai sanya hannun ta acikin wadrobe ɗin ta.

"Ki fa yi sauri, sabo da sun riga sunzo harma sun zauna." Ya faɗa yana mai ƙarasa fucewa daga cikin ɗakin.
Yayin da ita kuma ta fara sanya kayan da ta zaro farare na fulani, amma bawai na sarauta ba cikin sauri.
Tukun ta ƙarasa gaban mudubi tana mai kama uban gashin kanta da yake baƙiƙƙirin atsafe ta tufke sa wuri ɗaya, sannan ta ɗauki man leɓe kaɗai ta goga akan pink lips ɗin ta.
Sosai tayi matuƙar kyau yarce kasan sarauniyar kyawu ta duniya, duk dama ba wata kwalliya ce ke ɗauke afuskar ta ba, yayin da gashin kanta da ta tufke sa kuma ya zubo har gadon bayan ta ya kwanta.
Cikin sauri ta juya tana mai kama hanyar da zata sadata da waje, bayan tasanya wani plat shoe aƙafar ta ba tare data ɗaura ɗankwali ba.


*ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.*

Ahaka suka cigaba da shigowa cikin filin kafaɗun su ɗauke da iccina masu matuƙar yawa, suna masu dosar wurin da abun bauta Gargabilu yake.
Ahaka har akazo kan Bir da ya shigo shima kafaɗar da ɗauke da nasa iccinan da baya da baya, yana mai faman ɗirkar rawa daga shi sai farin ƙyalle ɗaure aƙugun sa.

Wani irin murmushi Gimbiya Tasmir ta saki alokacin da taga shigowar Bir cikin filin, tana mai cije leɓen ta na ƙasa.
Yayin da su kuma bayin nan daga mazan su har matan su suka cigaba da nufar wurin da abun bauta Gargabilu yake suna masu faɗin. "Gargabilu! Gargabilu!! Gargabilu!!!" Da matuƙar ƙarfi.

Duk wanda yaje gaban daɓen da abun bauta Gargabilu yake akai durƙusawa yake kansa sun kuye aƙasa yana mai faɗin. "Godiya ta tabbata gareka ubangjin mu daka nuna mana wannan rana." Sanna su sake yin juyi agaban sa suyi rawa iyakar rawa, tukun su huce zuwa cikin filin nan suna masu dosar inda Sarki da Iyalan sa suke, domin su kai gaisuwa, har lokacin kuma hannuwan su suna riƙe da kaskwayen hutar nan ne.

Dasari Gimbiya Tasmir ta miƙe tsaye daga kan kujerar da take alokacin da taga bayin nan sun fara doso hurin da suke, kamar yacce yayin ta biyu maza suma suka miƙe.
Tukun suka doshi wurin da wasu irin zura-zuran bulalai suke masu matuƙar tsayi da kauri cikin wani ruwa, suna masu sa hannu suka ɗauke su, sannan suka juyo suna masu dawowa tsakiyar filin nan ta ɓarin da bayi maza suke tawowa suka tsaya cirki cirko.
Ahaka har bayin

14 / 43