Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BAƘAR MASARAUTA A Cikin Duhu PART 1 by Umar Faruq D

Author :  Umar Faruq D Category :  African Stories & Novels

Chapter   27 / 43

78K to 81K   out of 128.4K words

ta saki kawai.

Da sauri duka mutanen dake a cikin ɗakin suka kai idanuwan su gare ta, yayin da wasu daga cikin su kuma suka buɗe baki suna masu faɗin. "Ke ko lafiya kika faɗowa mutane cikin ɗaki a haka?"

Bata iya basu amsa ba, sai gaba da ta cigaba dayi zuwa wurin da Gimbiya Fulani take cikin tsantsar ruɗu da tashin hankali.

"Yay...Yarima...ne ya faɗo...daga saman doki afil..."

"Me kike son kice mun ne haka, shin wane Yariman ne ma ya faɗo daga saman doki?" Gimbiya fulani ta faɗa a haukace bayan ta diro daga kan gadon da take hannun ta riƙe da ƴar jinjirar ta.
Yayin da sauran mutanen dake a cikin ɗakin ma duk suka miƙe tsaye hankula su a bal'in tashe.

Da sauri Gimbiya Fulani ta ratsa ta cikin mutanen nan da suke a cikin ɗakin ta tana mai kama hanyar waje, ba tare data ɗau ko da mayafi ba, tsabar ruɗun da take a ciki, domin kuwa hankalin ta idan yayi dubu sai da duka ya tashi.

Ganin hakan da sauran matan cikin ɗakin sukayi ne ya sanya su mara mata baya, suma duk hankulan su a matuƙar tashe.

Ƙarasawar ta bakin ƙofar futa daga cikin fallon nata yayi dai-dai da lokacin da Babban Yaya ya danno kansa cikin falon, rungume da Asad a ƙirjin sa yana mai sakin wani irin kuka a matuƙar haukace.

Take a wurin kuwa jikin Gimbiya Fulani ya ɗauki wata irin karkarwa, kana ta kasa yin gaba ta kasa yin baya, sai mamewa da tayi a wurin da take idanuwan ta ƙur akan Ƴaƴan nata guda biyu, yayin da zuciyar ta kuma ke wani irin gudu fiye da misali, fargaba da tashin hankalin abun da zata gani ta kuma ji sukayi matuƙar lulluɓe ta.

"Mamy na dan Allah kicewa Asad kar yatafi ya barni, mamy kice masa ya tashi, dama ni sai da nace masa kar yahau doki bazai iyaba, amma yace ya iya kuma yana hawa ai dama, gashi kuma yanzu ya faɗo dokin ya taka ƙirjin sa."
Babban yaya ya faɗa a wani irin haukace yana mai durƙushewa a gaban mamay'n tasu da ya ƙaraso, tare da sakin wani irin gigitacce kuka.
Girgiza kai Gimbiya Fulani ta farayi tana mai zube guiwoyin ta a ƙasa
Da sauri Hadima Larai ta ƙaraso wurin da take tana mai amshe baby'n hannun ta, sabo da yadda taga tana shirin yadda ta ba tare data sani bama.

Cikin sauri ta miƙa hannuwan ta da suke bal'in rawa, tana mai janyo Asad daga jikin Babban Yaya ta dawo da shi kan cinyar ta.
Kana ta ɗaga tafin hannun ta ɗaya tana mai ɗan marin fuskar sa, bakin ta na furta kalmar.
"Zaki! Zaki!! Zaki!!!"
Amma taji shiru ko alamun motsi babu tattare da shi.
Hakan ne yasa ta janye tafin hannun nata daga kan fuskar sa tana mai matsar da shi zuwa wurin rawanin da yake sanye a kansa ta tunɓuke sa ƙasa, tana mai cusa ƴan yatsun hannuwan ta a cikin lallausar sumar kansa.

Da sauri ta rumtse idanuwan ta tana mai janye ƴan yatsun nata daga cikin sumar sa, sabo da wani irin tururi da taji ya dake su mai tsantsar azabar zafi.

"Ku bani ruwa! Ku bani ruwa!! Sun ƙone mun kan yaro da huta!"" Ta faɗa a wani irn haukace tana mai juyawa ta kalli dandazon jama'ar da suke zagaye da su.

Cikin ƴan sakanni sai ga wasu mata nan har guda biyu sun miƙo mata ruwayen a cikin jarkokin su kamar yacce ta buƙata

Da mtuƙar hanzari ta buɗe murfin jarkar bayan ta warce ta a hannun matar, tukun daga bisani ta ɗaga ta tana mai tsiyaya ruwan a tsakiyar kan Asad, tare da kai yatsun hannuwan ta cikin sumar tasa ta fara cuɗa ta hankali a bala'in tashe.
A kuma dai-dai wannan lokacin Mai Martaba Sarki Abdallah ya faɗo cikin falon a matuƙar hargitse, ba tare da yayi ko sallama ba.


*JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FULƊE.*

Yau take ranar sunan jinjirar da Gimbiya Kaɓel ta haifa, hakan ne yasa ko ina ka kalla a cikin Masarautar kake ganin jama'a iri-iri, tun daga kan Sarakai na wasu masarautun maƙotan su har zuwa hadiman gidan suna ta giftawa, yayin da gaba ɗaya fuskokin su suke ɗauke da tsantsar farin ciki da annashuwa.
Tun bayan Sallah asuba aka yanka shanu har kimanin guda takwas narka-narka lafiyayyu a gidan, kana yarinya taci sunan Kakar ta, wato mahaifiyar Lamiɗo, amma za'ana kiran ta da HADDIYAL.

Sosai akai shagali irin shagalin da ba ataɓa yin kamar sa ba a cikin gidan, kana aka baiwa jinjirar tsafuka kala-kala, a cewar su hakan shine ƙarshen gatan da zasu yi mata a duniya.


*ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI MASARAUTAR WASAI.*

Cikin tsantsar ruɗu da tashin hankali mai martaba ya ƙaraso wurin da Gimbiya Fulani take riƙe da Asad, yana mai zube guiwoyin sa a ƙasa, yayin da sauran jama'ar dake wurin kuma suka bubbuɗa fili suna masu matsawa gefe.

Janyo Asad yayi daga jikin Gimbiya Fulani yana mai rungume sa a jikin sa, tukun daga bisani ya buɗe baki cikin tsantsar tashin hankali yana mai faɗin.
"Baba na! Baba na!! Baba na!!! Asad! Asad!! Asad!!!"
Ya faɗa cikin ruɗu da firgici yana mai girgiza sa, gaba ɗayan sa shima ya ruɗe ya firgice yadda kasan ba namiji ba, namijin ma kuma Sarki.
Amma sai dai Asad ko motsi baiyi ba, sai ma wata irin sandarewa da jikin sa yake sakeyi tamkar gawa, domin kuwa su kansu banda sunga zuciyar sa na bugawa da babu abun da zai hana suce ya mutu, sai dai kuma ga zuciyar tasa nan tana bugu da sauri da sauri kowa na gani, kasancewar babu kaya a jikin sa sai boxer kaɗai da yayi ragowa, domin kuwa duka sauran kayan Gimbiya Fulani ce ta cire masa su.

Cicciɓar sa mai martaba yayi yana mai miƙewa tsaye da shi, kana ya mannasa a ƙirjin sa yana mai masa wata irin runguma, tukun ya juya baya cikin sauri tamkar ya kifa a ƙasa, yana mai fucewa daga cikin falon gaba ɗaya.

Direct yayi part ɗin sa da shi yana mai zuwa ya kwantar da shi a kan tamfatse-tsen gadon sa na al'farma.

Baifi mintina biyar ya ɗauka da shigowar sa ɗakin ba, sai ga Babban lilkitan su da yake duba su sun shigo cikin bedroom ɗin, tare da su Galadima da Waziri da kuma duk sauran ƴan uwan mai martaba manyan maza.

"Yawwa likita matso-matso ka gaggauta dan Allah kayi sauri ka duba sa, bana son na rasa rayuwar Ɗana."
Mai Martaba Sarki Abdallah ya faɗa cikin tsantsar ruɗu, yana mai ƙarasawa wurin da Doctor'n yake ya kamo hannun sa.

Bai sakar masa hannun nasa ba har sai da ya kawosa gaban gadon da yarima Asad yake yashe akansa, tukun ya cika masa hannun yana mai komawa ɗayan ɓarin ya riƙo tafin hannun Asad ɗaya yana murza sa.
Yayin da shi kuma doctor nan ya buɗe box ɗin sa cikin sauri, kana ya fara zaro abubuwan gwaje-gwaje yana mai fara yin abun da ya kamata yayi.

Su kuwa su Galadima da sauran jama'ar gaba ɗayan su jugum-jugum sukai suna kallon Asad da yake kwance sheme akan gado yadda kasan gawa, zuciyoyin su cike da al'hinin wannan abu da ya faru lokaci guda, kana ko wanne daga cikin su da akwai abun da yake saƙawa a cikin zuciyar sa.

Sai da likitan ya ɗauki kimanin mintina arba'in yana faman bincikar yaron.
Kana daga bisani ya miƙe tsaye yana mai sharce gumin dake akan goshin sa, idanuwan sa akan fuskar mai martaba da shima yake kallon sa yana gumin, duk da sanyin A'C'n dake ratsa cikin ɗakin, amma hakan bai hana doctor'n haɗa zufa ba kamar yacce bata hana mai martana yin zufar fa shima.

"Ya ake ciki ne doctor? Mene yake damun Asad ɗina?
Shin dokin yay masa illa ne?"
Mai Martaba ya watsowa likitan tambayoyi a jere a kuma tsantsar ruɗe duk a lokaci ɗaya.
Yayin da shi kuma ya sake gyara tsayuwar sa a wurin da yake yana mai yin gyaran murya, tukun daga bisani ya buɗe baki cikin sanyi yana mai faɗin.
"Ina ganin wannan abun bazai yuwu anan cikin gida ba, dole sai mun dangana da Asibiti, sabo da acan ne muke da kayan aiki tare da kayan gwaje-gwaje waƴan da zasu taimaka mana wurin gano abun da ke damun sa, sabo da ni dai a yanzu gaba ɗaya ban fahimci komai ba dan gane da ciwon nasa, abu ɗaya kawai dana sani shine yana rayuwa har yanzu a doron duniya, but kuyi hakuri ku kwantar da hankalin ku, insha Allah hakan ba wata matsala bace Babba."
Ya ƙarasa maganar cikin sanyi.

Gaba ɗayan su suma shiru sukayi babu wanda aka iya samu ya furta komai, domin kuwa ba ƙaramun sanyi jikin su yayi ba duka.

Sun ɗauki tsawon minti na biyar a haka, tukun can mai martaba ya miƙe a wani irin zabure yana mai sake ɗaukar Asad, kana ya juya ya kama hanyar waje cikin sauri tamkar ya kifa a ƙasa, ba tare da yace musu komai ba.
Hakan da suka ganine ya sanya suma gaba ɗayan su mara masa baya har likitan, suna masu fucewa daga cikin ɗakin.

Cikin ƙanƙanin lokaci suka ƙarasa cikin tamfatsetsen private hospital ɗin da yayi bala'in gajiya hurin haɗuwa, domin kuwa tsayawa faɗar kyawun asibitin shi kansa ɓata lokaci ne, amma sai dai kallo ɗaya mutum zai masa ya fahimci cewa ba wurin zuwan ko wane irin mutum bane ba, domin kuwa cikin masu kuɗin ma sai waƴan da suka amasa sunan su na masu kuɗi, wayan da futa ƙasar waje ma ba tai musu huya.

Cikin tsantsar hanzari mai martana dake riƙe da Yarima Asad har lokacin a jikin sa ya furo daga cikin motar da wani Bafade ya buɗe masa ita.

Ba tare da ya tsaya ɗora sa akan gadon marasa lafiyan da wasu nurses suka kawo wurin ba ya huce gaba rungume da abun sa, ganin hakan da doctor'n yayi ne ya sanya sa bin bayan sa cikin sauri shima.

Ko da aka zo shiga da Asad da ya zamto tamkar gawa ɗakin da za'ayi masa gwa-gwajen, dagewa mai martaba yayi yace sai ya shiga shima, amma likitan yay ta basa haƙuri yana mai basa tabbacin zai tashi insha Allah, har ya samu ya shawo kansa ya haƙura da shigar, ta sanadin bakin da ƴan uwan sa suka sanya akan yayi haƙurin.
Tukun ya juya yana mai zuwa ya zauna akan kujerar da take a bakin ƙofar ɗakin, tare da ɗaga kansa sama ya lumshe idanuwan sa, yana mai jin zuciyar sa na tsantsar tafasa da ƙuna.
Yayin da su kuma likitocin suka shige cikin ɗakin dukan su, domin su fara ai'watar da abun da ya kamata suyi.


Acan cikin masarauta kuwa, ɓangaren Gimbiya Fulani, gaba ɗaya mutanen da suke a cikin falon jugum-jugum sukayi a lokacin da Mai Martaba ya fuce da Yarima Asad, yayin da Gimbiya Fulani kuma take wani irin kuka tana mai yiwa ɗan nata addu'oi, domin kuwa ba ƙaramun firgita tayi ba da halin da tagan sa a ciki, barin ma kuma da taji wannan azababben zafin da yake futa daga cikin jikin sa.
Shima Babban yaya gefe ya koma ya zauna yana mai aikin rusar kuka, domin kuwa shi duk a tinanin sa ƙanin nasa ya riga da ya mutu.
Suna cikin wannan halin sai ga Jakadiya nan ta afko cikin falon a matuƙar ruɗe, tana mai yowa wurin da suke.

"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, yau nayi mummunan ji, naji labarin da ya hargitsa ƙwa-ƙwalwa ta, shin ina ma shi shelelen yake ne yanzu?" Jakadiya ta faɗi haka a hargitse, hannun ta dafe da kanta.

Shiru gaba ɗaya mutanen dake wurin sukayi ba tare da wani ya tanka mata ba, jin hakan da tayi ne ya sanya ta sake buɗe baki cikin muryar ta da take tsantsar rawa, alamun kuka na shirin ƙwace mata tace.
"Dan Allah kuyi mun magana mana, ku faɗumun inda Shalelen Mai Martaba yake tun kafin zuciyata tai bundiga."

"Kiyi haƙuri Jakadiya, Mai Martaba ya ɗauke sa sun tafi asibiti ance."

Ɗaya daga cikin matan da suke zaune a wurin jugum-jugum ta faɗa, tana mai dafa kafaɗar Jakadiya da tashin hankali ƙarara ya bayyana akan fuskar ta.


Acan Asibiti kuwa sai da har likitocin suka ɗauki tsawon awa ɗaya suna binciken abun da ke damun Asad, amma basu gano komai ba da zasu iya cewa shi yayi sanadin sa-sa sumar, domin kuwa ko ƙirjin nasa da akace doki yabi takai su ba suga wani abun da ya same saba kwata-kwata, wato dai normal ƙirjin nasa yake kamar na kowa, sai dai kuma zuwa yanzu sun samu numfashin sa na futa dai-dai, ta sanadin oxygen da suka sanya masa, kana kuma bugun zuciyar tasa shima ya koma ya saitu kamar yacce yake a baya, sai dai kuma zafin jikin nasa ne har yanzu babu abun da ya ragu a kan na baya, sai ma sake ƙaruwa da yake yi fiye da da.

Jiki a tsantsar saɓule Doctor Muhammad ya juya yana mai kama hanyar futa daga cikin room ɗin.
Yayin da sauran Nurses ɗin kuma suka samu wuri suna masu zama akan kujeru, kamar yacce tsarin Asibitin yake, wato su da kansu suke jinyar patiant ɗin su ba wai ahalin mutum bane zasu zauna masa, sai dai kuma idan mutum ya takura akan shi zai zauna suna barin sa, tun da dai su baza a fasa basu kuɗin su ba cas, kamar yacce kowa ke bayarwa.

Doctor Muhammad na tura kai waje Mai Martaba da yake zaune akan wata haɗaɗɗiyar kujera da take abakin ƙofa anyi-anyi ya shiga office amma yaƙi, ya miƙe tsaye zumbur yana mai faɗin.
"Ya jikin nasa doctor, ina fatan dai yaro na yaki sauƙi yanzu ko?"
Ya watso masa tambayoyin a jera, sannan kuma a matuƙar ruɗe.

"Kayi haƙuri mu ƙarasa zuwa cikin office ranka ya daɗe."
Cewar Doctor Muhammad yana mai ɗan durƙusawa ya rage tsayin sa a gaban Mai Martaba, kamar yacce ya saba a koda yaushe.
Yayin da shi kuma Mai Martaba ya rumtse idanuwan sa yana mai fesar da wata zazzafar iska daga cikin bakin sa, tukun daga bisani ya buɗe su akan fuskar doctor ba tare a yace komai ba.
Ganin hakan da Doctor Muhammad yayi ne ya sanya sa yin gaba yana mai faɗin.
"Bismillah'n ku to."

Gaba ɗayan su miƙewa sukayi suna masu bin bayan sa, ko wanne a cikin su zuciyar sa cike da son jin abun da ke faruwa, yayin da wasu daga cikin su kuma suke murna da jin daɗi, tare da fatan Allah yasa mutuwa yaron yayi, idan kuma bai ba zaiyi, wato magautan su kenan, munafukai masu fuska biyu, su kuwa masoyan su cike suke da fargabar jin abun da Doctor zai ce.

Tamfatse-tsen office ne mai matuƙar girma da kyan tsari.
Jere yake da wasu haɗaɗɗun kejeru masu tsanin kyau da taushi acikin sa, yayin da daga can gefe ɗaya na cikin office ɗin kuma wani haɗaɗɗen table yake kafe a wurin, sai daga bayan table ɗin kuma kujera ce mai tsantsar kyau irin wacce ke juyawa da mutum idan yana kai, yayin da saman teburin kuma yake ɗauke da takaddu tare da system akan sa.

Direct doctor muhammad ya huce zuwa kan table ɗin, yayin da su kuma su Mai Martaba suka zazzauna akan kujerun nan suna masu fuskantar sa.

Gyaran murya yayi yana mai sa yatsun hannun sa ya cire maɓalli ɗaya daga cikin maɓallayan dake jikin gaban rigar sa.
Kana daga bisani ya buɗe baki cikin sanyi yana mai faɗin.
"Haƙiƙanin gaskiya dai shi ne, munyi iyakar yin mu, sannan kuma munyi amfani da duk abun a ya kamata muyi, domin mugano abun da ke damun sa, amma sai dai kuma gaba ɗaya binciken da mukayi babu wanda yay mana nuni da wata matsala da take tattare da shi, asalima duka result ɗin suna nuna negative ne na duka tests ɗin da mukayi masa, sai dai kuma munyi nasarar dai-dai ta numfashin sa tare da bugun zuciyar sa, but yanayin zafin jikin nasa ne har yanzu babu abun da ya ragu, sannan kuma shima ɗin bai farfaɗo ba."
Doctor Muhammad ya ƙarasa maganar cikin sanyi, domin kuwa ya yi iyakar yin sa amatsayin sa na cikakken Medical Doctor, amma bai gano komai na dan gane da abun da ke damun yaron ba, kuma baya tinanin ko sun bar nan sunje wani wurin za adace ɗin, domin kuwa gaba ɗaya kayan ai'yukan da yake amfanni da su a cikin asibitin nasa duk irin na ƙasashen turawa ne, wato irin waƴan da ake amfanni dasu acan ɗin ma idan an kai mutum, kasancewar sa mutum wanda yake da kuɗi, sannan kuma ya taso cikin ruwan kuɗi a gidan su, domin kuwa shi kansa duka karatun nasa ba a Ƙasar Hausa yayi sa ba, hatta da primary kuwa.

Wani irin zazzafan numfashi Mai Martaba ya fesar, yana mai jin kansa na sara masa, ga kuma idanuwan sa da sukayi jajajir, alamun ba ƙaramun tashin hankali yake ciki ba.

Galadima ne ya buɗe baki cikin sanyi yana mai faɗin.
"To yanzu mene abunyi kuma a gaba Doctor, bi ma'ana me kake ganin zaku iya sake yi masa, ko kuma wane wurin kake tinanin zamuje bayan nan wanda suke da kayan aikin da sukafi naku?"

Girgiza kai Doctor Muhammad yayi yana mau ɗan yin shiru, tukun daga bisani ya buɗe baki bayan ya ɗago ya kalle su, yana mai faɗin.

"Haƙiƙa bazance kuma ga wurin dana sani ba wanda nake da tabbacin yafi nan, domin kuwa a duk faɗin Jahar Wasai babu wani Asibiti da ya kai namu, sabo da mu kaɗai ne muke amfani da kayan aiki irin waƴan da ake afanni da su a Asibitocin mu na ƙasashen waje, amma sai dai kuma ni atawa shawarar sai nake ganin mai zai hana a gwada na Islamic chemist, wato na musulunci ko Allah zai sa adace."
Ya faɗa yana mai kallon su.
Yayin da su kuma dukan su sukayi shiru ba tare da wani ya iya furta komai ba.

Sun ɗauki tsayin mintina biyar a hakan, tukun daga bisani mai martaba ya buɗe bakin sa bayan yasa yatsun hannuwan sa ya sharce gumin dake tsats-tsafowa akan goshin sa, yana mai faɗin.
"Ina ganin shawarar taka ita zamubi Doctor, dan haka tun yanzu nake tinanin zamu shirya tafiyar, domin kuwa akwai wani Babban malami na da yake zaune a London, malami ne masanin Al'qur'ani tare da litattafai,

27 / 43
Connection failed: SQLSTATE[HY000] [2002] Operation not permitted