Author : Umar Faruq D Category : African Stories & Novels
zauna a cikin sa.
Kasancewar shekara d'aya kawai su kai da komawa gidan shima yayi aure, inda ya auri d'aya daga cikin d'aliban sa na makarantar islamiyyar sa.
A yanzu haka 'ya'yan su biyu shi da ita mace da namiji.
Ishak' mai sunan baban sa shine babba, yayin da suke kiran sa da Dady, sai kuma Aishatu mai sunan maman sa da tazo ata biyu, bayan haihuwar Dady da shekara biyu da rabi, ita kuma suna kiran ta da Amira.
Sosai sunan Sheikh Ahmad yayi matuk'ar shahara a cikin garin Wasai, domin kuwa a yanzu haka shine limamin juma'a na babban masallacin da yake a cikin garin wasai, idan aka cire na gidan sarki.
Sosai girman sa da kwarjinin sa tare da haibar sa harma da kyawun sa suka k'ara futowa, kasancewar a yanzu haka yana da shekaru kusan arba'in ne a duniya.
Yana da motocin hawa har guda biyu 'yan madai-daita masu kyau.
Yayin da Mahaifin sa Ishak' ma yake da ita, wadda shine ya siya masa da kansa.
A yanzu haka matsalar su d'aya ce kawai a gidan duniya, wacce kuma take matuk'ar nuk'ur-k'usar zuciya da ruhikan su, wato Aishatu, domin kuwa har kawo yau bata bar sanya damuwa a ranta ba, ta yadda har ta kamu da ciwon hawan jini mai tsanani, wanda aduk lokacin da ya tashi baya mata da sauk'i ko kad'an.
Ako da yaushe sai tayi kamar ta dena tinane-tinanen, kwatsam rana d'aya kuma sai suga ta koma gidan jiya.
Wannan damuwar da take ciki itace kawai take hana su sukuni gaba d'ayan su, domin kuwa hatta da kaka da d'akin ta yake anan k'asan bene ba k'aramun damuwa take da yanayin Aishatu ba, haka zata zauna wataran tai ta masifa tana fad'in, ta kasa d'aukar dangana sai kace ba musulma ba, kafin daga k'arshe kuma ta koma tai-ta rarrashin ta, wani lokacin ma har k'walla zakaga tana zubarwa.
A fannin fad'an su da Sheikh Ahmad kuwa babu ranar banza da zata zo ta k'are ba tare da sunyi ba, barin ma da aka aurar da k'annen sa mata gaba d'ayan su, ya zamto su biyu ne kawai sukai ragowa shi da autan su mai shekar kusan ashirin da d'aya yanzu take gani, to kullum sai ta takali sheikk Ahmad sunyi ta, domin kuwa shi Auta tasu tazo d'aya da shi sosai, hakan yasa da wuya aji ta fad'i ai'bun sa.
Yayin da Sheikh Ahmad kuma abun ya shafi har matar sa, domin kuwa kullum sai ta ai'bata ta tana kushe hallitar jikin ta, duk da kasancewar ta kyakkyawa sosai kuwa tamkar shi.
Yanzu haka gaba d'aya Ishak' da Aishatu sun aurar da 'ya'yan su mata.
Haka kuma bata sake haihuwa ba tun bayan haihuwar Auta.
*ENGLAND*
Da matuƙar ƙarfi Billy ta rumtse idanuwan ta sabo da abun da ta gani, jikin ta na wata irin karkarwa!
Yayin da ita kuma wannan baturiyar ta k'ara bud'a tafukan hanneyan ta tana mai tallabo k'eyar Yarima Asad da su.
Kana ta farasa harshen ta tana mai lasar saman jajayen lips d'in sa da suke matuk'ar birge ta da shi, kafin daga bisani kuma ta fara k'ok'arin tura harshen nata cikin bakin sa.
A hankali ya d'ago tafukan hannayen sa duka biyu shima, yana mai dire su akan jan gashin dake kanta, kana ya tallabo k'eyar ta, yana mai zaro tongue d'in sa ya hard'o nata da shi, tukun sukayi wani irin had'e bakunan su wuri d'aya suna masu fara kissing d'in junan su da sauri da sauri.
A kuma dai-dai lokacin Billy ta sake bud'e idanuwan ta akan su.
Da matuk'ar sauri ta durk'ushe k'asa tana mai sa tafin hannun ta-ta toshe bakin ta da shi, sabo da wani irin azabbaben kuka mai cin rai da taji ya k'wace mata.
Wani irin k'una take jin ranta da zuciyar ta suna yi mata.
Lokaci d'aya idanuwan ta suka kad'a sukai jajajir yadda kasan gauta, yayin da jikin ta kuma ke wata irin karkarwa tamkar wacce aka sanya acikin ruwa.
Cikin zafin rai tayi hurgi da jakar dake rik'e a hannun ta zuwa gefe, tukun ta fara dukan kanta da hannu bibbiyu, tana mai jin tamkar ta tashi taje ta shak'e wuyan baturiyar nan har sai taga ta dena numfashi, sabo da masifar kishin da yake caccakar zuciyar ta.
Kana kuma ta k'udirtarwa ranta waji bine itama taje ta same sa daga yau, da ta tsaya tana kallon wasu matan banzan na mu'ama da shi akan idanuwan ta, sai dai kome zai yi mata yayi mata.
A fannain su Yarima Asad kuwa cikin tsantsar shauk'i'n da suka tsinci kansu a ciki suka cigaba da abun da suke yi.
Kafin daga bisani kuma ya janye tafukan hannayen sa daga saman gashin baturiyar yana mai mayar da su zuwa kan k'ugun ta.
Kana ya fara zamar da jikin sa daga kan kujerar da yake yana mai d'an ture ta daga kan cinyar sa, tukun daga k'arshe ya jirkitar da ita ta koma k'asa, yayin da shi kuma ya d'ago zuwa saman ta yana mai yi mata rumfa da faffad'an k'irjin sa, suka cigaba da aikata abun su yadda kasan ba afili suke ba, domin kuwa ko kad'an babuwa ta kunyar tattare da su balle haf suji tsoron kar wani yazo ya gansu a haka.
Zumbur Billy ta mik'e tsaye tana mai jujjuya kai, sabo da abun da idanuwan ta suka hango mata Yarima Asad yayi, kafin daga bisani kuma ta fara d'aga k'afafuwan ta cikin tsantsar zafin rai da k'unar zuciya, tana mai futa daga cikin wurin da ta lab'e ta doshi gun da suke gadan-gadan.
Tana dab da zuwa wurin taja ta tsaya k'am a wuri d'aya, sabo da yadda taga Yarima Asad ya mik'e daga jikin baturiyar nan zumbur, yana mai yin wani irin jifa da ita a k'asa.
Tukun ya fara sakin huci yana mai aika mata wani mugun kallo, da idanuwan sa da gaba d'aya suka riga suka canza launi.
Kafin daga bisani kuma ya bud'e baki cikin cunkusassar muryar sa yana mai nuna baturiyar nan da yatsa, tare da fad'in.
"How many time did i wand you akan karki k'ara kuskuren kai k'azamin hannun ki jiki na, ko kuwa na fad'a miki dan ina d'an tab'a jikin ki shine yake nufin zamu iyayin komai da ke?
To bari kiji in fad'a miki, idan ma kina wannan tinanin, ina mai baki shawarar ki gaggauta kawar da shi a cikin zuciyar ki, because of jiki na ba irin jikin da kike tinanin zai iya kusantar ko wace kalar mace bane, kai impact ma babu ita, kuma ba ayi taba a duniya.
Dan haka daga yau babu ni babu ke, ko a hanya kika ganni kikai gangancin nuna kin sanni sai na hulak'antaki. Stupid bitch kawai."
Ya k'arasa maganar yana mai sakin nishi tamkar wanda ya futo daga filin dambe, ko kuma na tseren gudu, domin kuwa bai saba yin irin wannan doguwar maganar ba ko acikin sanyi, balle kuma yanzu da yayi ta a cikin zafin rai, hakan ne kuwa ya sanya sa yayi bala'in gajiya.
Gaba d'aya yayi furucin nasa ne cikin harshen turanci.
Kafin daga bisani kuma ya juya cikin tsantsar b'acinrai bayan yaja wani dogon tsaki, yana mai kama hanyar da zata sada sa da d'akin sa na cikin hotel d'in nan.
Yayinda ita kuma baturiyar nan ta fashe da wani irin kuka cikin tsantsar tashin hankali, tana mai tsantsar nadamar abun da ta aikata masa, duk da dama tasan baya so, amma sai dai kuma ko kad'an batayi tinanin zai yanke hukuncin rabuwa da ita ba gaba d'aya a lokaci guda, dama ta gwada sa'ar tane ko Allah zai sa ta dace ayau ya yayada yayi mu'amala da ita, amma sai gashi nan kuma gaba d'aya ta kwafsawa kanta lokaci guda, ta yadda har garin neman gira ta rasa ido.
Cikin tsantsar tashin hankali ta bud'e baki a lokacin da taga ya juya zai tafi tana mai fad'in.
"Please Please Please Prince don't live me, don't live me, don't do this to me, i promise i will never do that again."
Ta k'arasa maganar cikin matsanan cin kuka, tana mai rarrafawa da matuk'ar sauri ta kamo k'afar sa da hannun ta.
Cak ya tsaya a wurin da yake zuciyar sa na tsantsar tafasa da k'una, tukun daga bisani ya funcike k'afar sa da k'arfi yana mai juyawa ya kwad'a mata wani irin mugun kallon da ya sanya cikin ta kad'awa, ta yadda har sai da taja baya da sauri, tukun daga bisani kuma ya juya yana mai cigaba da tafiyar sa ba tare da yace mata komai ba.
Wani irin gigitaccen kuka ta saki tana mai nadamar abun da ta ai'kata masa a ranta.
Abun da ya faru kuwa shine, a lokacin da Asad ya dawo saman ta, sosai ya fara aika mata da salon sa wanda yake matuk'ar gigita duk matan da yake mu'amala da su.
Lokaci d'aya gaba d'aya taji ta rud'e ta gigice afagen buk'atar sa, sai dai kuma sanin halin sa da tayi ne na baya tab'a wuce hakan shi ya sanya ta biye masa suka cigaba da kssing d'in junan su, yayin da take jin notikan kanta na sake kwancewa, hakan ne yasa tace bara ta gwada sa'ar ta yau ko Allah zai sa ta dace, tunda taga shima d'in yayi nisa sosai a fagen.
Hakan ne yasa ta janye tafin hannun ta d'aya a hankali daga gadon bayan sa, tana mai cusa sa k'ark'ashin ta, wato tsakanin jikin su.
Tukun a hankali ta kife sa akan k'irjin sa tana mai fara shafawa, kana ta fara matsar da shi k'asa a hankali tana mai masa wani irin wai-waye da shi, a haka har ta kai ga zuwa kan cikin sa.
Cikin tsantsar k'warewa a salon iskanci ta cigaba da yin k'asa da hannun ta har ta k'arasar da shi zuwa kan mararsa dai-dai wurin robar wandon dake jikin sa, kana daga bisani kuma ta fara k'ok'arin tura hannun ta ciki.
A kuma dai-dai locin Yarima Asad yaji abun da take shirin yi masa, hakan ne yasa yayi saurin janyewa daga jikin ta yana mai hurgar da ita a k'asa.
Tukun ya fara aika mata da ruwan masifar sa cikin tsantsar zafin rai, domin kuwa babu abun da ya tsana sama da yaga yarinya na shirin haike masa, to fa daga wannan ranar ko wacece ke yake rabuwa dake, dan ko acewar sa wai har yau baiga macen da takai matsayin da zaiyi irin wannan mu'amalar da ita ba.
Yayinda su kuma su Al'amin da suke yi yake musu kallon shasha-shu marasa aji, inda su kuma suke ce masa daga su har shi d'in basu da bam-banci ko a wurin Allah, tun da dai duk kalar abu d'aya suke ji idan sunyi, dan haka idan zai warema ya cire girman kai ya mori rayuwar sa yayi, idan kuma bazai ba to karya k'ara sanya musu ido, domin kuwa sunfi k'arfin su tsaya a iyakar jagwal-gwalo.
Gaba d'aya sun manta da kalar girman zunubin da suke aikatawa.
Wata irin mahaukaciyar dariya Billy ta kwashe da ita daga wurin da take, tana mai kallon baturiyar nan da take aikin rusar kuka zaune a k'asa.
Tukun daga bisani kuma ta fara d'aga k'afafuwan ta cikin tsantsar farin ciki, tana mai dosar wurin da baturiyar nan take.
Tsaye tayi a kanta tana mai aika mata da wani irin matsiyacin kallo, kafin daga bisani kuma ta buga wata irin k'wafa da matuk'ar k'arfi, tana mai juyawa ta tafi, zuciyar ta cike da k'udirin tunkarar Yarima Asad a gobe da nata salon ba gudu baja da baya, babu kuma sauran wani b'oye-b'oye.
Yayin da ita kuma wannan baturiyar ta bita da kallo tana mai mamakin abun da yasa tazo gaban ta tsaya, kana kuma tayi mata tsaki da zata tafi, sai dai kuma damuwar da take ciki a yanzu ta rabuwa da Asad tafi bak'in ciki akan abun da Billy tayi mata, shi yasa ma bata bita taji dalilin ta nayin hakan ba, sabo da ba itace a gaban ta ba yanzu.
A b'angaren Yarima Asad kuwa cikin tsantsar zafin rai da tafasar zuciya ya murd'a handle d'in k'ofar d'akin yana mai tura kansa ciki, tukun ya mayar da ita ya rufe gam.
'Dan madaidacin falo ne mai matsakacin girma da ya gaji da had'uwa. Duk da dai ba cike yake da kayan tarkace a cikin sa ba.
Wasu irin itallian chair's ne masu azabar kyau zagaye a cikin d'akin.
Sai wani d'an farin mini freg da yake kafe a wuri d'aya, yayin da k'asan d'akin kuma ya kasance shimfid'e da wani irin lallausan capet kalar yadin kujerun, daga saman capet d'in kuma wani glass center table ne a jiye a wurin.
Tun daga bakin k'ofar ya fara cire guntayen kayan jikin sa yana mai fatali da su akan hanya, a haka har ya k'arasa cikin bathroom d'in da ya gaji da had'uwa, a lokacin kawai d'an guntun farin short-nika ne ya rage a jikin sa.
Direct ya huce wurin da shower take yana mai zuwa ya kunna ta, tukun daga bisani ya matsa k'ark'ashin ta yana mai lumshe idanuwan sa ruwan ya fara sauka atsakiyar kansa, ba tare da ya cire short-nikan da ya rage a jikin sa ba.
Lokaci d'aya ya fara sauke wasu irin tagwayen ajiyar zuciya, sabo da sanyin ruwan da yake sauka akan sa yana harbawa har cikin k'wak'walwar sa, wanda hakan yasa yaji zuciyar sa ta farayin sanyi.
Sai da ya d'auki tsayin mintina goma shabiyar ak'ar-k'ashin showar, kana daga bisani ya kauce daga wurin yana mai k'arasa cire sauran sitirar da tayi ragowa a jikin sa, ya koma cikin jakuzie'n da yake cike da ruwan kumfan da ya had'a yayi zaman sa a cikin sa.
*K'ASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAK'AR MASARAUTA.*
Suna k'arasawa gaban ruwan wannan badakaran ya kamo k'afafuwan Bir duka biyun da hannun sa, tukun ya d ago su sama yana mai mayar da kansa k'asa, sannan ya d'aga sa daga tsayen da yake yana mai danna kansa a cikin ruwan nan.
Take kuwa Bir ya fara wani irn shure-shure, yana mai hahaura k'afafuwan sa da matuk'ar k'arfi, tare da motsa jikin sa, amma sai dai kuma ko alamun k'wacewa baiyi ba daga hannun dank'are-ren mutumin nan mai sufa da samudawa.
Sai da suka d'auki kimanin minti goma, tukun wannan badakaran ya zaro Bir daga cikin ruwan, yana mai yadda shi a gefe.
Yayin da idanuwan Bir kuma sukayi wani irin kakkafewa, ga cikin sa kuma da yayi matuk'ar girma, alamum ba k'aramun ruwa yasha ba kenan.
Da sauri wani badakare yayi kansa gadan-gadan, a lokacin da wancan d'in yayi cilli da shi a gefe.
Yana mai k'arasawa wurin da yake, kana ya d'aga damb'areriyar k'afar sa d'aya, yana mai taka cikin Bir da ita.
Take kuwa yayi wata irin d'agowa sama, bakin sa na futar da uban ruwa da matuk'ar yawa.
'Daga k'afa badakaran nan ya sake yi da matuk'ar k'arfi, yana mai direta akan cikin Bir.
Wata irin k'ara Bir ya saki k'asa-k'asa, bayan wani ruwan ya sake futa daga cikin bakin sa da matuk'ar yawa, yana mai bud'e idanuwan sa tare da kifewa rufda ciki a k'asa.
Da sauri d'ayan badakaran ya sake matsawa wurin da yake yana mai d'aga k'afar sa d'aya yayi wani irin k'wallo da Bir.
Ai kuwa yadda kasan iska ta d'aga leda haka Bir yayi gefe yana mai zuwa ya gwaru da wata bishiya, tukun ya fad'i a k'asa.
Wani irin jini ne mai matuk'ar gudu ya b'alle daga cikin gashin Bir yana mai tsiyayowa akan fuskar sa.
Yayin da shi kuma yake ta sakin nishi da k'yar, yana mai juya juyi a wurin da yake cikin tsantsar azabar da take ratsa jikin sa, ga kuma idanuwan sa da suka furfuto waje tsabar wahala.
A tare gaba d'aya dakarun nan suka sake d'aga k'afafuwan su suna masu nufar inda yake.
Suna k'arasawa wurin da yake gaba d'ayan su suka zare mahaukatan bulalan su suna masu fara dukan sa da su ta ko ina, yadda kasan sun samu jaki, kai ko jaki ma bai can-canci amasa irin dukan nan ba kasancewar sa abu mai rai, sai dai ace gini ko dutse.
Sai da suka yi masa jina-jina, ta yadda har ya zamto sai da k'yar yake iya motsi a wurin da yake, tukun babban cikin su ya kalli k'aramin su yana mai fad'in.
"Kayi maza kaje ka sanarwa da Gimbiya cewar anyi tamkar yadda tace, umarnin ta na gaba kawai muke jira."
Ya k'arasa maganar yana mai sa k'afa ya shuri Bir da ita.
Yayin da shi kuma wannan badakaran da ya aika ya juya da matuk'ar sauri yana mai nufar hanyar da zata sadasa da wurin da Gimbiya Tasmir take.
A b'angaren Gimbiya Tasmir kuwa cikin tsantsar zafin rai da k'unar, zuciya ta cigaba da tafiya da matuk'ar sauri tana mai dosar hanyar da zara sadata da b'angaren su.
Sosai takejin zuciyar ta na wani rin k'una da tafar fasa idan ta tuna yadda Bir yayi mata k'uri da ido, har da su busa mata iskar bakin sa akan fuska.
Wata irin tafar-fasa take jin zuciyar ta nayi mata tsabar b'acin rai, lokaci d'aya taji bata da wanda ta tsana sama da shi.
Babu abun da ke k'ara k'ona mata rai sai yadda zuciyar ta ta dinga wani irin bugu a gaban sa, babban abun takaicin kuma shine tana barin wurin da yake d'i taji ta dawo gudu dai-dai, hakan ne yasa taji aranta tana mai son sanin dalilin da yasanya taji haka dan ta tsaya a gaban sa, tana son sanin me ya taka, wana kalar sihiri gare sa da har kallon sa ya sanya ta fad'uwar gaba.
Har ta kusa k'arasawa b'angare nasu taja ta tsaya a wuri d'aya, ba tare da ta cigaba da tafiyar ba, tana mai rumtse idanuwan ta da matuk'ar k'arfi, sabo da tinanin da ya fad'o mata aranta, na sanin muddin ta shiga cikin gidan nasu a wannan yanayin na b'acin ran da take dole ne tasan sai wani daga cikin a halin ta ya tambaye ta dalili, wanda idan hakan ta faru take ganin bata da amsar da zata bayar, domin kuwa ba zata tab'a iya bud'e baki tace wani k'ask'antaccen Bawa ne ya b'ata mata rai, sabo da hakan zai zamto babban abun kunya mai muni ne gare ta, wato a matsayin ta na d'iyar Sarki Barbaru yar lelen sa, kuma ace Bawa ya b'ata mata rai, harya sanya bak'in ciki a ckin ranta ta yadda har ya bayyana akan fuskar ta kowa ya gani.
Da matukar sauri ta juya baya zuciyar ta na cigaba da