Author : Umar Faruq D Category : African Stories & Novels
domin ko hatta mai martaba idan ya ganka acikin wannan shigar arana irin tayau wacce sarakunan garuruwa da dama suka halarci gidan nan kasan ransa ba ƙaramun ɓaci zai yi ba ko, ina ma laifin ace kasanya iyakar manyan kayan basai kasa alkyabbar ba, in yaso bayan an gama shagali sai kazo kacire su ka maida irin wanda kake so ko."
Al'amin ya ƙarashe maganar cikin sanyi kamar bashi ne ya fara ta cikin fushi ba, domin ko yasan har dai bata lallami yabi Abokin nasa ba to ko kallo ma bai ishesa ba balle har yayi amfani da abun da yake faɗe .
Kallon sa Yarin Asad ya cigaba dayi har sai da ya bari ya kai ƙarshen maganar sa, tukun ya ɗan taɓe baki yana mai juyawa ya doshi bakin bed ba tare da ya tanka masa ba.
Nannauyar ajiyar zuciya Al'amin ya sauke yana mai sakin murmushi, sabo da yarce yaga Yarima Asad ya nufi inda waƴan can kayan suke, amma sai dai ko gama murmushin nasa bai ba ya koma ya ɗinke fuska yana mai bin Asad da ido, sabo da yarce yaga ya huce ta gaban kayan ko kallon su baiyi ba balle ya dauka ya sanya.
Direct yayi saitin inda pillow'n sa yaka yana mai zuwa ya ɗauki makullin motar sa tare da wayar sa ƙirar iphone 13 pro max ya riƙe, tukun daga bisani ya juya yana mai dosar ƙofar da zata sadasa da waje ba tare da ya sake kallon inda Al'amin yake ba, yayin da shi kuma Al'amin har lokacin yake binsa da kallo yana mai jin-jina girman rainin hankalin Asad acikin ransa.
Sai da yaje har bakin ƙofa tukun ya tsaya yana mai juyowa ya sake jifan kayan nan da kallon ƙas-ƙanci, tukun daga bisani ya janye ƙwayoyin idanuwan sa daga kansu yana mai -mai dasu kan kujerar da Al'amin yake zaune yana kallon sa baki sake shima.
"Katabbatar ka kwashe waƴannan shirgin banzan naka kafun na dawo, and then idan ka gama abun da kake kana iya rufe mun ɗaki ka ƙara gaba." Ya faɗa yana mai juyawa ya sanya kai ya fuce ba tare da ya tsaya jin abun da Al'amin zai ce ba.
"Kuttt, Amma wallahi sai kaci ubanka Asad, yanzu duk awannin dana ɓata ina jiran ka kagama shiryawa mutafi tare shine har zaka huce ka barni, to dan uwarka baza a kwashe kayan ba kayi duk abun da zakayi." Al'amin ya faɗa da ƙarfi yarce Asad ɗin zai jiyo sa yana mai miƙewa cikin jin haushin sa yabi bayan sa.
"Barka da futowa yaya." Wasu kyawawan ƴammata da suke zaune akan haɗaɗɗun kujerun da suke jere acikin tamfatse-tsen fallon suka faɗa, suna masu kallon Yarima Asad da ya futo daga ɓarin sa.
"Ina mamy take ne?" Ya faɗa idanuwan sa akan waya ba tare da ya amsa gaisuwar da sukai masa ba.
Da sauri ɗaya daga cikin su ta buɗe baki tana mai cewa. "Mamy na part ɗin ta, amma bari baby taje ta kira maka ita." Ta ƙarashe maganar cikin wani irin salo wanda yake nuni da tayi hakan ne domin ya ɗago ya kalle ta, amma sai dai ko motsi bai canza ba daga kalar wanda yake yi balle har ya kallo tan, yayin da ita kuma wacce aka kira da baby ta miƙe tsaye da sauri tana mai faɗin. "Ok bara nayi sauri."
"To yaya ga wuri kazauna mana, kafin mamy'n ta ƙaraso ko." Ta faɗa tana mai far-fara idanuwa tare da ɗan buɗa space akusa da inda take idanuwan ta akan fuskar sa.
Taune lips ɗin sa na ƙasa yayi yana mai yamutsa fuska ba tare da yace tak ba, domin kuwa ita bata sani ba ba ƙaramun takura masa tayi ba da surutun da take tayi ma.
Ba tare da ya ɗaga kai ya kalli ko kujerar da take zaune akai ba duk da yarce take ta faman gyara zama tana kwar-kwasa kala kala ya juya yana shirin fucewa daga cikin falon, akuma lokacin ne Al'amin ya ƙaraso falon yana ta faman masifa.
Baice ƙala ba duk da yaji abun da Al'amin ke faɗa, sai ma taɓe baki da yayi yana mai cigaba da tafiyar sa hankali kwance.
Yana fucewa daga cikin part ɗin nasu ya tsaya cak abakin ƙofa, yana mai kallon yarce jama'a keta hucewa cikin irin banzar shigar da Al'amin ya aje masa da sunan yasa ta shima.
Tsaye yay awurin yana mai ƙan-ƙantar da idanuwan sa tare da kar-katar da kai yana mai bin duk masu hucewa da kallo, yi yake yana taɓe baki tare da yamutsa fuska, ji yay gaba ɗaya bazai iya zama acikin gidan ba idan har baza'a dena waƴan nan kaɗaɗen ƙauyen cin da ake yi ba, domin ko shi ba ƙaramun takura masa sukayi ba, gaba ɗaya bai ɗauki irin waƴan nan bushe bushen ba amatsayin abubuwan nishaɗi, sai zallar gida danci da rashin waye wa kawai yake gani.
"Kai yanzu dan Allah mutanen nan da suke hucewa cikin shigar nan basu burge kaba?" Al'amin ya faɗa alokacin da ya ƙaraso wurin yana kallon sa.
Uhm! Yace kawai yana mai yin parkin space.
Da sauri zagagen da suke tsai-tsaye a area wurin suka taso suna masuyo kan su. Tun daga nesa suka fara faɗin. "Barka da futowa ɗan sarki jikan sarki, takawar ka lafiya bujimin maza, takawar ka lafiya jinin mulki, gaba salamun baya salamun Asadullahi ikon Allah, ɗa ga sarki Abdallah, shalele wurin sarauniya kuma gimbiyar matan hausa, jika ga sarki Ahmadu ƙani ga ciroma uban....
Cak suka tsaya a'inda suke suna masuyin shiru dukan su, sabo da yarce ya ɗaga musu hannu sama yana mai dakatar dasu, ba tare da ya waigo ya kalli ko mutum ɗaya daga cikin su ba.
Juyawa suka farayi suna masu komawa wuraren da suke, yayin da shi kuma ya cigaba da takawa cikin takusan sa da shi kaɗai ke hautsina ƙwaƙwalen ƴan mata su muto akan sa, yana mai dosar inda wata azababbar farar mota take, wacce take ɗauke da number mai suna YARIMA ASAD 08 sabuwa fidigil da ita.
Tun daga nesa ya sanye remote ya buɗe ta, shi yasa yana ƙarasawa wurin ya sanya hannu ya buɗe murfin yana mai shigewa ciki ya zauna akujerar direba.
Da sauri shima Al'amin ya ƙaraso wurin yana mai buɗe murfin ya shiga.
Lumshe ido Yarima Asad yayi yana mai ɗora tafukan hannayen sa akan stiyarin motar bayan yayi mata key.
"Wai yana ga kayo nan ne Asad, bayan kuma kasan fada zamuje ko?" Al'amin ya faɗa yana kallon fuskar sa.
Ƙala bai ce masa ba sai ma buɗe idanuwan sa da yayi yana mai janyo wayar sa ƙirar iphone 13 pro max ya fara shafawa.
"Da kai fa nake Asad kamun banza."
"To kai ɗin ubane ne da bazan ma banza ba, ko kuwa na maka dole ne akan sai ka biyo ni inda zani." Ya faɗa ƙasa ƙasa yana mai cigaba da danna wayar sa ba tare da ya ɗago ya kalle sa ba.
"Me kake nufi da hakan? Idan na fahimta kamar kana so kace ba fada mukai daga nan ba ko?"
"Kai ka juyo kuma."
Yarima Asad ya faɗa yana mai danna giyar motar bayan ya rufe motar gam.
Da wani irin mahaukacin ƙarfi ya take ta yana mai lailaya kanta atsakan-kanin wurin da suke ya juya ta.
Tukun ya ɗebe ta atamanin yana mai ɗauke hanyar da zata sada sa da main get, ko mutanen da suke faman kai kawo aharabar gidan nasu bai lura dasu ba.
"Wai dallacan Asad me kake shirin yi haka ne?" Al'amin ya faɗa cikin ƙaraji yana mai dukan kujerar motar ransa amatuƙar ɓace.
Inda yake Asad bai ɗago ya kalla ba balle ya tanka masa, saima sake take motar da yayi ahaukace yana cigaba da dosar get ɗin da zai sada su da wajen gidan sarautar.
"Kaga malam dallacan samu wuri ka sauke ni anan." Al'amin ya sake faɗa cikin fushi yana mai jin kamar ya mammake fuskar Yarima Asad tsabar takaici.
"Ai kana iya buɗewa ka futa yanzu ma tunda ba ɗaure ka nayi ba, kuma da kake cewa na tsaya na sauke ka ai ina ce da ɗin bani na ɗora ka aciki ba ko?" Yarima Asad ya faɗa adai dai lokacin da ya shilla kan motar sa titi aguje.
Gaba ɗaya mutanen dake abakin titi harma da waƴan da suke acikin motocin su bin motar Yarima Asad sukayi da idanu, manya banda zagin sa da shegan tasa babu abun da suke yi, yayin da matasa kuma keta faman kambaba sa suna faɗin guy ɗin na burge su, sabo da yarce yayi matuƙar iya hannun sa.
Acan cikin mota kuwa Al'amin ne ya kalli Yarima Asad yana mai faɗin. "Amma Asad kai atinanin ka hakan da kayi ka kyautawa babban yaya kuwa?"
Murmushi Yarima Asad yayi wanda yayi matuƙar ƙara masa kyau, tukun daga bisani ya lumshe idanuwan sa ko damuwa bai ba da cewar kan titi yake duk da uban gudun da yake kwara-rawa, kana ya wara su daga baya yana mai buɗe baki yace. "Shin wai dan Allah ni nace ka biyo ni ne guy, koka na buɗe baki nace Al'amin kar kaje fada kallon naɗi ne?" Ya faɗa yana mai sake sakin murmushi hankali kwance.
Yayin da shi kuma Al'amin yayi matuƙar ƙulewa, sabo da yarce yaga shi ko ajikin sa bai damu bama.
"Amma dai ai kasan ban san nan kayo ba da babu abun da zai sa inbar hawan da zamuyi in biyo ka ko?"
Uhm! "To ai yanzu ma bata baci ba idan naje inda zani na tsaya sai ka futo kasamu mota ka juya, domin kuwa kasan ni dai bazan tsaya akan hanya ba, kuma kasan bazan iya zama acikin gidan can ba ana waƴan can kaɗaɗe da bushe -bushen banzan can na gidadanci."
"To karka tsaya ɗin mana ɗan iskan banza kawai." Al'amin ya faɗa cikin zafi yana mai buga ƙwafa, yayin da shi kuma yarima Asad yay shiru yana mai mai da hankali akan tuƙin haukar da yake hankali kwance.
*ASADULLAH PALACE*
Shi ne sunan da aka rubuta daga saman azababben building ɗin daya tunkara da motar tasa wanda get ɗin wurin kaɗai abun kallo ne bama ginin ba.
Tun daga nesa ya danna horn ɗaya daga nan kuma bai sake yin wani ba.
Da sauri wani matashin saurayi ya wangale tamfatse-tsen get ɗin yana mai kauce wa.
A hankali ya fara taka motar yarce kasan ba zai tafi ba yana tunkarar cikin wurin, kai idan har ba sani kayi ba ka gansa akan titi yanzu kuma akace maka shine yake irin wannan tafiyar sai ka rantse da Allah kace ƙarya ne, domin kuwa ko mutum dake tafe aƙafa sai ya hucewa sa sosai a'irin yarce yake taka ta yanzu!
*JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FULƊE*
Da gudu ƴar ƙaramar yarinyar mai kimanin shekaru bakwai aduniya ta afka cikin ɗakin tana ta faman numfar-fashi, alamun ba ƙaramun gudu tayi ba kenan.
Durƙushewa tayi akan guiwoyin ta tana ta faman zare ido tare da sakin numfar-fashi.
Ahankali kyakkyawar budurwar da take zaune agefen wani azababben gadon ƙarfe mai matuƙar kyau, wasu matasan ƴammata guda biyu da suke sanye da kayan fulani na tufke mata uban gashin da yake ɗauke akan ta mai tsananin yawa, tsayi da baƙi ta ɗago dara-daran fararen idanuwan ta tana mai watsa su akan ƴar yarin yar data shigo aguje.
Kallon yarin yar tafarayi tun daga sama har ƙasa ba tare da tace komai ba. Yayin da ita kuma ƴar yarinyar har lokacin take durƙushe aƙasa tana sakin nishi.
Ɗaya daga cikin ƴammatan da suke gyarawa budurwar nan gashi ne ta ɗago kai tana kallon yarinyar fuskar ta ɗauke da murmushi, tukun daga bisani ta buɗe baki cikin harshen fulatanci tana mai faɗin. "Shin me ya faru ne uwar gijiya ta beldo?"
Ɗago kai yarinyar tayi tana mai kallon ta, tukun tace. "Ba hulin ki nazo ba." Kana ta mai da idanuwan ta kan fuskar budurwar da ake gyarawa gashi tana mai cewa. "Adda ta gote ki duka sun tashi sun gudu, yanzu naje ansho fulata wani ya kal-kaɗamun jelar sa afuska ta ya tashi sama, kinga kenan gwalo yayi mun ko?" Yarinyar ta faɗa tana mai kallon budurwar bayan tazaro manya manyan idanuwan ta waje, alamun dai abun ba ƙaramun firgita ta yayi ba.
Yayin da waƴan nan ƴammatan bayin guda biyu suka tuntsire da dariya suna kallon ta. Ita ko uwar gayyar wacce aka kawowa labarin taɓe baki tayi tana kallon ƴar yarinyar, kana daga bisani ta ɗaga laɓɓan ta cikin zazzaƙar muryar ta mai matuƙar daɗi tana mai faɗin. "To uwar shirme ni wuce ki bani wuri." Ta faɗa tana ɗauke kai daga kan yarinyar, yayin da ita kuma yarin yar ta ɗaure fuska tana mai miƙewa tsaye ranta aɓace ta juya ta tafi, sai da taje bakin ƙofar futa daga ɗakin, tukun ta juyo tana mai kallon yayar tata, sannan daga bisani ta buɗe baki tana cewa. "Bama zan ƙala baki labari na ba, kuma Allah yasha kalsu dawo ma." Ta ƙarashe maganar da murguɗa baki, tukun ta juya tana mai fucewa daga cikin ɗakin.
Murmushi dukan su su ukkun sukayi har ita ba tare da sunce komai ba.
Sun ɗauki dogon lokaci suna gyaran gashin tukun suka kammala.
Gefe guda suka koma suka tsaya kawunan su durƙushe aƙasa, ko wacce hannun ta riƙe da cumb.
Gyara zaman ta tayi akan gadon da take, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Kuna iya tafiya sai na sake neman ku kuma." Ta faɗa tana mai miƙewa daga kan gadon.
"Tom ranki shi daɗe Allah ya ƙara lafiya." Suka haɗa baki wurin faɗin haka, tukun suka juya suna masu fucewa daga cikin ɗakin.
Tafiya tayi zuwa bakin mudubin da yake maƙale ajikin bangon ɗakin, wanda gefe da gefen sa yake ɗauke da ƙarafa masu adon flawoyi kalar ruwan zuma, kamar yacce duka kayan ɗakin suke.
Tsaye tayi agaban sa tana mai kallon kanta acikin madubin.
Sanye take da kayan fulani irin na sarauta, riga da zani ne farare masu ɗauke da adon ja da koren zare ajikin su, sai ƙafar ta kuma da take sanye da plat farin half cover shoe na fata mai ɗauke da adon gashi ajikin sa mai tsananin kyau, yayin da kanta kuma ya kasan ce abuɗe ba ɗankwali akai, sai uban gashin da aka gama gyarawa da aka rabasa gida biyu, aka kikkitse jelolin suka zubo har kan cikin ta baƙiƙƙirin dasu gwanin ban sha'awa.
Farace tas kamar ataɓa ta jini ya ɓullo, tana da tsayi tare da ƴar ƙiba dai dai misali, irin waƴan da ake so mace ta kasan ce dasu, tana da dara daran idanuwa masu ɗauke da blue black ɗin ƙwaya acikin su, sai siririn hancin ta da yake zaune daram akan fuskar ta wanda baza'a kira sa da dogo can ba kuma baza ace nasa ɗan guntu ba, yayin da bakin ta kuma ya kasan ce ɗan tsukut dashi ɗauke da pink lips akan sa suna ta faman ƙyalli.
Ba wata kwalliya ce ɗauke afuskar ta ba sai kawai zallar powder data shafa, daga nan kuma bata ƙara komai akai ba sai suturar dake sanye ajikin ta da sukayi matuƙar zama das da su. GIMABIYYA HADDIYAL kenan. Ƴa mace ta farko ga Lamiɗon masarautar fulɗe, gimbiya ƴar gata wacce ake tsananin ji da ita, gimbiyar da take da matuƙar izza da kwarjini irin na ƴaƴan sarauta.
Gimbiyar da ta maida tsun-tsaye da shanaye abokan rayuwar ta fiye da komai acikin masarautar tasu, hakan ya sanya har mahaifin ta Lamiɗo ya bata sarautar tsun-tsaye ta duka masarautar.
Lumshe idanuwan ta tayi agaban madubin fuskar ta ɗauke da sassanyan murmushi, babu abun da take hange acikin idanuwan ta sai kyakkyawar fuskar sa yana aiko mata da sassanyan murmushin sa kamar yacce take ganin sa aduk lokacin da taso ganin sa muddin ta kulle idanuwa ko kuma ta kwanta bacci.
Ta ɗauki tsayin mintina biyar rufe da idanuwan tana sakin murmushi, tukun daga bisani ta buɗe su tana mai sake duban kanta ajikin madubin, kana ta juya tana mai dosar ƙofar da zata sadata da waje cikin takun ta wanda yake nuni da ita ɗin wata ce basai anfaɗa ba.
Wani danƙareren fallow ne mai tsananin kyau, wanda aka ƙawa tasa da kujerun ƙarafa masu ruwan zuma ta ɓulla cikin sa.
Gaba ɗaya bangon fallow'n zagaye yake da adon ja da bluen stara masu tsananin kyau, yayin da daga saman starorin kuma aka kafe wasu haɗaɗɗun ƙwarare da luwade harma da faifayen kaba kala kala akan su. Kallo ɗaya mutum zaiwa wurin ko da bai san saba yasan tabbas ya shigo cikin babbar masarautar fulani waƴan da suke ji da Al'adun su, sabo da yarce aka ƙawata ko ina da kayan ado irin na fulani.
Kai tsaye ta tunkari inda wata farar dattijuwar mace mai kimanin shekaru hamsin da ƴan kai take, kishingiɗe take akan tabarmar kaba wacce saman ta take ɗauke da lallausar sarrafaffar fata akai, sai wasu tum-tum da suke ajiye agefe da gefen shimfiɗar, yayin da ita kuma matar take kishingiɗe akan tum-tum ɗin ta miƙe ƙafafuwan ta duka akan kafet ɗin. sanye take da kayan fulani farare kar da su, sai al'kyabba wacce itama take ta mahaɗin kayan fara mai adon baƙi sanye ajikin ta.
Kallo ɗaya zaka yiwa matar ka gane itace ta haifi Gimbiya Haddiyal, sabo da tsananin kamar da suke yi, riƙe take da wani haɗaɗɗen kofin silba ahannun ta, wanda cikin sa ya kasan ce cike danƙam da madarar shanu mai matuƙar dumi tana sha. Sai daga can wuraren ƙafafuwan ta kuma wata dattijiwar mata ce mai kimanin shekaru kusan hamsin da biyar aduniya take riƙe da ƙafafuwan ta tana ta aikin mammatsa su.
Tunda ta hango tawowar ƴarta ta take ta faman sakin murmushi tana kallon fuskar ta har ta ƙaraso wurin da suke.
Cire takalman dake sanye aƙafafuwan ta tayi, tukun ta hau kan kafet ɗin tana mai zama ta tanƙwashe ƙafafuwan ta akai.
Dasauri wannan dattijuwar matar dake aikin lallatsa ƙafafuwa ta buɗe baki har tana ɗan ranƙwafa jiki wurin faɗin. "Barka da futowa ranki ya daɗe."
"Yawwa barkan ki dai Iya." Gimbiya Haddiyal ta faɗa fuskarta ɗauke da murmushi, tukun ta juya ɓarin da mahaifiyar tata take tana mai buɗe baki cikin sanyi, bayan ta durƙusar da kanta ƙasa tace. "Barka da hutawa dadde na."
Janye kofin madarar da takai baki tayi bayan ta ɗan