Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BAƘAR MASARAUTA A Cikin Duhu PART 1 by Umar Faruq D

Author :  Umar Faruq D Category :  African Stories & Novels

Chapter   20 / 43

57K to 60K   out of 128.4K words

ko kaɗan.
Yayin da ita kuma Gimbiya Fulani ta ɗan saki gajeran murmushi, sabo da jin kalamin Jakadiya da tayi, bayan kuma tasan da zata futa daga nan ɗin ta tafi wurin wata itama hakan zatai mata, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "To Jakadiya abar dai zancen haka kawai, atafi na gaba kuma."

Murmushi Jakadiya tayi tana mai sake kai hannun ta baya tare da gyara zaman ta awurin, tayarce Gimbiya Fulani ba zata gane abun da take yi ba, tukun tace. "Dama mai Martaba ne ya turo ni gareki akan nazo na jiye masa lafiyar jaririn sa, domin kuwa akullum yana faɗin cewa mafarkin sa na nuna masa namiji ne ɗauke acikin ki wannan karan ma."

Murmushi itama Gimbiya Fulani tayi tana mai lumshe idanuwan ta, domin kuwa harga Allah ta gaji da surutun Jakadiya, gaba ɗaya ma ta ƙagara ta tashi ta futa ko taji da abun da take ji, tukun daga bisani ta buɗe idanuwan nata tana mai faɗin. "Hmmmm! Mai martaba kenan, to in kin koma sai kisanar dashi cewa, Baby na cikin ƙoshin lafiya."

"Tom shikenan ni zan huce, na barki lafiya Uwar Magaji." Ta ƙarasa maganar tana mai hulla layoyin nan ƙarƙashin gadon da sauri, sannan ta miƙe tsaye fuskar ta ɗauke da tsantsar murmushi, tana mai sake faɗin sai da anjima."

"Allah ya kaimu na gode." Gimbiya Fulani ta faɗa tana mai miƙar da ƙafafuwan ta akan kafet ɗin nan.
Yayin da Jakadiya kuma ta huce ranta fal farin ciki, sabo da ganin da tayi ta samu nasarar aiwatar da abu ɗaya daga cikin abubuwan da zatayi cikin salama.

Tana zuwa ƙofar ɗakin tayi sa'a kuwa babu ko mutum ɗaya dake cikin falon.
Ganin hakan da tayi ne ya sanya ta fara waige-waige, sai da ta tabbatar da babu ko ƙuda dake kallon ta acikin ɗakin, tukun ta sanya hannun ta jikin haɓar zanin ta tana mai ciro ƙullin maganin nan daga cikin sa.

Sake wawwaigawa tayi taga dai still babu kowa, sannan ta kwance sa cikin sauri tana mai zubasa abakin ƙofar ɗakin da matuƙar sauri, tukun ta juya tana mai yin gaba abun ta, bayan ta mayar da maganin cikin haɓar ta da zummar taje ta zuba abakin turakar mai martaba ma.


*ƘASAR MALIN, JAHAR RUMAN.*

Ƙarfe goma dai dai na safe jirgin su ya ɗaga ta cikin ruwa, yana mai ɗaukar hanyar da zata kaisa Ƙasar Hausa, bayan su Aishatu sun gama koke-koke ita da ƴan uwanta, kana suka mata fatan Allah ya sauke ta lafiya, tare da al'ƙawarin suna nan zuwa idan ta sauka.

Sosai zuciyar ta ke cigaba da tsinkewa, gaban ta na wani irin faɗuwa, alokacin da jirgin su ya fara nitsawa cikin hanya.

Jin ta take wani iri, gaba ɗaya jikin ta yayi matuƙar yin sanyi, ga kuma zuciyar ta dake cigaba da tsinkewa, yarce kasan ranar da aka sanar mata da mutuwar mahaifin ta.

Addu'oi ta fara karantowa acikin zuciyar ta ba tare da ta sanarwa Ishaƙ halin da take ciki ba.
Sai dai kuma shima ɗin duka yana lura da sauyawar tata, kasancewar akusa da shi take, amma sai bai kawo komai ba aransa, ya dangana hakan kawai da zafin rabuwa da ahalin tane ya sake sanyawa ta koma haka ba komai ba.


*ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.*

Ko da Jakadiya ta bar part ɗin Gimbiya fulani direct ta doshi turakar mai martaba, tayi sa'a kuwa babu wanda ta samu a wurin kamar yacce tai fata, hakan yasa ba tare da ta tsaya ɓata lokaci ba ta sake ciro ƙullin tsuman nan ta kwance sa, tana mai baɗasa abakin ƙofar, tukun tayi sauri ta koma baya cikin tsantsar farinciki.

Aɓangaren Gimbiya Fulani kuwa, sosai ciwon da take ji ya cigaba da ƙaruwa, barin ma bayan lokacin da aka idar da sallahr magariba amasallacin dake cikin masarautar, amma duk da haka tai shiru da bakin ta ba tare da ta sanarwa kowa ba, haka kuma koda dare yayi bata tafi turakar mai martaba ba, duk da kasancewar itace da shi ɗin yau.

Misalin ƙarfe goma ɗaya na dare ciwon naƙuda ya sake turnuƙe ta mai matuƙar tsanani, banda cizon leɓe tare da yarfa hannu babu abun da take ai'kin yi awannan lokacin.

Tana cikin wannan yanayin ta jiyo sautin muryar hadimar ta, wacce ta kasance tamkar Uwa ga Ƴaƴan ta, kuma ta zamto aminiya agare ta, tana mai kwaɗo sallama abakin ƙofar ɗakin ta, kasancewar aduk lokacin da take da ciki dama haka Hadimar tata mai suna Larai take ziyarta ta duk dare, dan taga halin da take ciki, domin kuwa wani lokacin ma idan ta shigo sai dai ta juya ba tare da ta same ta ba, idan har ranar ta kasance tana turakar mai Martaba kenan, sannan kuma da zarar ta haihu to kula da yaron da komai nasa yake komawa wurin ta, haka duk ta raini yaran tun daga kan Babban yaya har zuwa Nafisat auta.
Babu yarce magauta basuyi ba su janyo ta ajikin su, domin su samu damar kassara rayuwar Babban yaya cikin sauƙi, amma kwata-kwata taƙi, hakan ne yasa gaba ɗaya itama sukabi suka tsane ta, sannan kuma suke jin haushin ta, sai dai kuma babu yadda zasuyi da ita, domin kuwa Gimbiya Fulani ta daɗe da ƴanta ta.
Macece mai kimanin shekaru arba'in da ƴan kai aduniya, Ƴaƴa huɗu duka ta haifa, daga nan kuma mahaifin su ya rasu. Tun bayan rasuwar sa bata sake yin wani auren ba, ataƙaice ma tana zaune ne anan ɓangaren Gimbiya Fulani itama data bata ɗaki.

Da matuƙar sauri, sannan kuma cikin tsantsar tashin hankali ta ƙarasa wurin ta tana mai faɗin. "Subhanallahi haihuwar ce tazo kenan Mamy'n Yara." Ta ƙarasa maganar tana mai dafata, hankalin ta atsantsar tashe.
Yayin da ita kuma Gimbiya Fulani take ta cigaba da cizon yatsa, ba tare da tace mata komai ba.

Dasauri ta juya tana mai shirin tafiya, bakin ta na faɗin. "Bara naje na sanarwa Jakadiya ta sanarwa mai Martaba, in yaso ko asibiti ne sai ataf... Caraf taji Gimbiya Fulani ta riƙo yatsun hannun ta, hakan ne yasata juyowa ɓarin da take tana mai kai idanuwna ta kanta.
Ido huɗu sukai da junan su alokacin da ta juyo ɗin, tukun daga bisani Gimbiya Fulani ta buɗe baki cikin muryar ta da take nuni da halin da take ciki na tsantsar ciwo tana mai faɗin. "Kar kisanar masa, bana san wani mutum yaji labarin haihuwar nan ayanzu, domin kuwa kin san yarce wasu daga cikin mutanen gidan nan suke, dan haka ki barshi har zuwa nan da asuba muga yarce Allah zaiyi." Ta ƙarasa maganar da ƙyar tana mai cizon leɓe.

"Tom shikenan, amma bara naje ɗakina na ɗauko wasu magun-guna dana tanade su sabo ds zuwan wannan ranar."
Umma Larai ta faɗa ba tare data tsaya ja da maganar shugabar tata ba, domin kuwa sai dai ta bada labarin magautan cikin gidan nan, ba dai wani ya bata ba, tukun ta juya cikin sauri tana mai fucewa daga cikin ɗakin.


*ƘASAR MALIN, CIKIN JIRGIN RUWA.*

Dare ya tsala sosai, yayin da gari ya kasance baƙiƙƙirin da duhu, amma duk da haka jirgin nan bai tsaya ba, kasancewar ɗauke yake da futulu masu matuƙar haske tako ina ajikin sa, hakan yasa duk tsayin dare bai sanyawa direbobin su tsaya daga tuƙi, muddin ba abinci aka tsaya siya ba ko sallah.
Tini suka daɗe da futa daga cikin Jahar Ruman, dan har sun shiga Jahar Karfuz ma.

Tun da suka shigo jahar karfuz Aishatu taji jikin ta ya ƙara matuƙar yin sanyi, ga bugun zuciyar ta kuma da yayi matuƙar ƙaruwa, tayarce har take jin tamkar zata faso ƙirjin ta ta futo, tun tana addu'a acikin zuciyar ta har sai da ta dawo yin ta abayyane, sabo da yarce take jin yanayin na sake hau-hawa fiye da da, tayarce har Ɗan cikin ta shima keta motsi fiye da yarce ya saba yi.

Ta fannin Ishaƙ shima sosai yake jin zuciyar sa na cigaba da dukan tara-tara, ga wani irin tsoro da fargaba da suka lulluɓe zuciya da ruhin sa, irin wanda bai taɓa tsintar kansa a makamancin su ba.
Hakan ne yasa sa damƙe hannun Aishatu cikin nasa da matuƙar ƙarfi, yana mai karanto duk addu'ar da tazo zuciyar sa azuciyar sa shima.

Misalin ƙarfe huɗu da ar'ba'in dai-dai na dare jirgin su ya danna kansa zuwa yankin da ya ratso ta cikin BAƘAR MASARAUTA, wanda shigar tasa kuma tayi dai dai da bugawar da ƙirjin Aishatu yayi da matuƙar tsanani fiye da da, yayin da zuciyar ta kuma ta cigaba da tsinkewa da matuƙar sauri.

"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Rabi da kwatan mutanen dake cikin jirgin suka furta cikin tsantsar ruɗu da tashin hankali, sabo da yarce suka hango h.............✍

*BAƘAR MASARAUTA*



*NA*
UMAR FARUQ*D*



*PAGE 15*



Hasken futulu masu matuƙar ƙarfi an dallo idanuwan su tun daga can nesa da su.
Take a wurin Aishatu ta sake matuƙar rikicewa, jikin ta na tsanstsar rawa da karkarwa, hakan da Ishaƙ ya gani ne ya Sanya sa sake damƙar hannun ta da matuƙar ƙarfi, bakin sa na furta duk addu'oin da suka zo cikin zuciyar sa cikin tsantsar tashin hankali, kamar yadda sauran ɗaukacin mutanen da suke a cikin jirgin suke.
Yayinda tawagar mutanne Baƙar Masaruata kuma suka afka cikin jirgin ruwan su da matuƙar sauri, tukun suka doso inda suka hango jirgin su Aishatu, suna masu cigaba da dallewa direbobin tare da mutanen ciki idanuwa da hasken futulun su, bakin su kuma na aikin furta kalmar. "Gargabilu!" Da tsantsar ƙarfi.

Cikin daƙiƙun da basu zarta huɗu ba suka ƙaraso wurin da jirgin da su Aishatu suke ciki yake.
Ba tare da sun tsaya jan lokaci ba suka zare makaman su daga cikin jikin su, suna masu ɗaga su sama, tukun suka yiwa direbobin jirgin nuni da hanyar da zasu bi.

Cikin tsantsar ruɗu kuwa matuƙarn jirgin suka nufi wurin da suke nuna musu hankulan su abala'in tashe, domin kuwa ba iya makaman su bane abun tsoro, su kansu mutanen da suke a cikin jirgin abubuwan firgici ne ga mutumim da bai saba ganin su ba.
Yayin da jama'ar dake cikin jirgin kuma suka sanya ihu da matuƙar ƙarfi, suna masu faɗin sun shiga ukku cikin tsantsar tashin hankali.
Afannin Aishatu kuwa kallo ɗaya tayiwa mutanen taji cikin ta yayi wata irin murɗawa, sabo da firgita, tukun daga bisani Ɗan cikin nata ya fara wani irin hutsul-hutsul da matuƙar sauri, tayarce har na kusa da ita zai iya lura da motsin sa muddin ya kalli cikin nata.

Da matuƙar ƙarfi ta rumtse idanuwan ta, tana mai ɗaukar tafin hannun ta ta dafe cikin ta da shi, zuciyar ta na tsantsar bugawa, yayin da bakinta kuma ke ai'kin furta duk wasu addu'oi da sukazo cikin sa, ba tare da tasan tana yin suba ma.

Basu dakata ba har sai da suka turasu gefen ruwan nan, inda su sarki Barbaru da Boka mai hutar kasoko, tare da sauran jama'ar su suke.

Shimfiɗar fata ce ajiye daga gefen ruwan, wacce jikinta yake ɗauke da jini faca-faca, ɗauke take da kaskon wuta da yake matuƙar ci da wuta, yayin da gefen kaskon kuma aka aje wata irin kibiya mai matuƙar tsini, sai Boka mai wutar kasko da yake zaune daga gefen shimfiɗar, yayin da Sarki Barbaru kuma yake daga tsaye a bakin ruwan nan, gaba ɗayan sa a wani irin birkice, domin kuwa ko shigar da ke sanye jikin sa tun ta wancan satin ce, ranar da suka fara riskar tashin hankalin nan bai canza ta ba, asalima ko barin hurin kwata kwata baiyi ba har kawo yau, domin kuwa abinci ma a rana baifi sau ɗaya yake cinsa ba, shima sai yaji yunwa na shirin hanasa miƙewa tsaye.

Sosai mutanen cikin jirgin nan suka sake matuƙar firgita, suna masu sakin ihu da salati, sabo da irin mutanen da suke sake arba da su agafen ruwan da suka iso yanzu.

"Daƙiƙa ɗaya kawai na baku, ko wane mutum ya zamto ya kama bakin sa, muddin kuma kuka bari na sake jin ihun wani cikin kunnuwa na bayan giftawar daƙiƙun, to kusani sunan mutum gawa, ko waye ne shi kuwa."
Sarki Barbaru ya faɗa cikin muryar sa mai matuƙar amo, yana mai kallon mutanen cikin jirgin nan.

Take kuwa wurin ya ɗauki shiru gaba ɗaya, yarce kasan ba'a taɓa hallitar mutum ba, balle ayi zaton anan wurin ihun ya gama tashi.
Yayin da Aishatu kuma ta taune leɓen ta na ƙasa da ƙarfi, tana mai dafe cikin ta da hannu ɗaya, sabo da yadda taji marar ta tayi wani irin kartawa, ga kuma bayan ta da taji lokaci ɗaya ya riƙe gam!
Taune leɓenta ta cigaba dayi da ƙarfi, tana mai faman zare idanuwa tare da gumtse baki, gudun kar addu'ar da takeyi a zuciya ta suɓuce ta futo fili, Sarki Barbaru yaji, yayin da shi kuma Ishaƙ yake ta aikin shafa bayan ta a hankali, cikin tsantsar ruɗu shima.

"Ku shiga cikin jirgin nan yanzu, ku bincika mana ko ina da ina, lungu da saƙo, ku futo mana da duk wani jinjirin yaro namiji da kuka samu."
Sarki Barnaru ya faɗa cikin amo yana mai kallon wasu daga cikin dakarun nan nasu.
Yayin da su kuma mutanen cikin jirgin nan hankulan su ya sake bala'in tashi, barin ma matan da suka san suna ɗauke da jariran Ƴaƴa.

Dasauri wata mata da take ɗauke da jinjirin ta a hannunta, ta sake danna sa cikin hijabin ta jikin ta na tsantsar rawa, sabo da yadda taga mutanen nan sun tunkaro inda take gadan-gadan, kasancewar sun riga da sun hango ɗan nata tun farko, sabo riƙesan da tayi a hannun ta.

Girgiza kanta ta farayi tana mai ja da baya daga zaunen da take, cikin tsantsar tashin hankali da firgici, yayin da su kuma waƴan nan dakarun suka cigaba da doso ta gadan-gadan.

Ganin da tayi suna daf da isowa inda take ne, ya sanya ta miƙewa da sauri tana mai shirin rugawa baya, amma sai dai tana ɗaga ƙafarta ɗaya taji ta- ta kife kif a ƙasa, kanta na dukan katakon dake jikin jirgin da matuƙar ƙarfi, sabo da yadda ɗaya daga cikin dakarun ya sanya ƙafarsa ya tatsiye ta da ita.

Gadan-gadan ya ƙarasa zuwa wurin da take yana maj sa hannu da niyyar funcikar Ɗan, amma sai tayi sauri ta ƙara ruƙun-ƙume sa acikin jikin ta, tana mai fashewa da wani irin gigitaccen kuka mai ban tausayi, take kuwa shima jaririn ya tsanyare da kuka da matuƙar ƙarfi, sabo da zafin matsar da yaji, wacce uwar tasa tayi masa gudun kar aƙawace mata shi.

Tas! Tatas!! Tasss!!! Wasu irin ƙarar marika suka tashi a wurin da matuƙar ƙarfi, waƴan da suka sake sanya mutanen cikin jirgin ruɗewa da firgicewa, suna masu toshe bakunan su da hannu.

Badakaran nan ne ya ɗauke matar da wasu gigitattun marika, sabo da yadda yaga yana miƙa hannu zai karɓi Ɗan tana kuma sake ruƙun-ƙume sa, tukun daga bisani ya ɗago tsaye yana mai funciko wata doguwar takobi daga ƙugun sa yayi kan matar da ita.

Wata irin gigitattar ƙara matar ta saki, tana mai rumtse idanuwan ta da matuƙar ƙarfi.

Funcikar Ɗan ya sakeyi da matuƙar ƙarfi, yana mai mayar da takobin cikin jikin sa ba tare da ya kaita jikin ta ba, sabo da yadda yaga riƙon da tayiwa yaron yayi sakwa-sakwa ta dalilin ihun da ta saki, tukun ya juya jinjirin riƙe a hannun sa, da yake tsala uban kuka yana mai ɗaga kafafuwan sa sama yayi gaba.

Dasauri matar nan ta miƙe tsaye tana mai bin bayan sa cikin tsantsar ɗimaucewa.

Ƙafar sa ɗaya ya ɗaga yana mai harbin ta da ita ta baya, hakan yasa ta tafi taga taga tana mai kifewa a ƙasa kanta ya sake dukan wani icce, tayadda har sai da ya fashe jini ya futo, amna a haka ta sake miƙewa tana mai sakin kuka
Yayin da shi kuma wannan badakaran ya cigaba da tafiyar sa babu ko ɗigon imani tattare da shi, yana mai fucewa daga cikin jirgin.

Kai tsaye ya doshi kan shimfiɗar nan mai ɗauke da huta a kanta.

Miƙawa Boka mai hutar kasko jinjirin dake tsala uban kuka yayi, yayin da daga can bakin jirgin kuma wani badakaran ya tare wannan matar uwar jinjirin, da take shirin futowa yana mai sanyata ta duƙushe akan guiwoyin ta, tana hangen Ɗan nata daga nesa.

Matsawa Sarki Barbaru yayi zuwa gaban kaskon huta shima, yayin da Boka mai hutar kasko kuma ya tashi daga hurin da yake zaune, hannun sa riƙe da jinjirin, yana mai matsawa gaban kaskon nan, tukun ya durƙusa yana mai kwantar da shi a kusa da kaskon.

Hutsil-hutsil yaron ya farayi yana mai cigaba da tsanyarewa da kuka, sai dai kuma har bayan shuɗewar daƙiƙa goma ko kaɗan ƙafarsa bata taɓa jikin kaskon nan ba, balle harya tuntsirar da shi, hakan da suka ganine yasan ya Sarki Barbaru buɗe baki cikin muryar sa mai matuƙar amo da firgitarwa, yana mai faɗin. "Bashi bane wannan ma, dan haka matso ka caka nasa kibiyar shima." Ya ƙarasa maganar da kallon wani badakare da yake tsaye agefe.

Wata irin ƙara Uwar jinjirin nan ta saki, sabo da jin abun da Sarki Barbaru ya faɗa da tayi, ga kuma ganin da tayi badakaran yayi wurin jinirin gadan-gadan.

Da sauri wannan badakaran da yake tsaye a gaban ta ya damƙi tsintsiyar hannun ta, sabo da yadda yaga tana shirin fucewa daga cikin jirgin.
Yayin da shi kuma wancan da Sarki Barbaru yayiwa magana ya ƙarasa gaban Jinjirin nan, tukun ya durƙusa ƙasa yana mai sa hannu ya ɗauki kibiyar da take ajiye kusa da kaskon huta, sannan ya ɗago tsaye yana mai ɗaga ta sama, tukun yayi ƙasa da ita yana mai cakata a dai -dai ƙawon zuciyar jaririn!

Wata irin gigitattar ƙara Uwar jinjirin nan ta saki, tana mai zubewa a ƙasa sumamma, sabo da yadda taga an yiwa jinjirin nata da bai san hawa ba bare sauka, wanda bashi da haƙƙin kowa a kansa kisan gilla akan idon ta.
Yayinda Aishatu kuma ta saki wani irin salati da matuƙar ƙarfi, wanda ya janyo hankalin duka mutanen wurin, tunda ga kan su Sarki Barbaru har zuwa mutanen cikin jirgin nan da suke tare, tana mai rumtse idanuwan ta tare da yarfa hannun ta, sabo da wani irin mugun murɗawa da taji cikin ta yayi, ga kuma bayan ta daya riƙe gam, banda

20 / 43