KISHIN BALBAL BOOK 2 HAUSA READ NOVELS BY JAMILA UMAR TANKO.doc

Author :  Jamila Umar Tanko Category :  Romance

Chapter   9 / 11

24K to 27K   out of 31.6K words

Ya tsare da ido yana yi min kallon tuhuma.
Babu wacce ta fado min a rai sai Mufidah amma kuma.akwai gagarumar matsala idan na sanar masa da cewa ita ce dan tabbas tsanar da yayi mata zata koma qauna.
Na girgiza kai na ce "babu wacce na fadawa komai."
Kallon rashin yarda ya ci gaba da yi min.
Na zabura na ce "bai wuce Jalilah ba dan har gidan nan take zuwa nemanka."
Ya girgiza kai ya ce "ba Jalilah ba ce. Ta yaya zata san kudin hayata ya qare, ta ina zata san Godwin har ta tura masa kudi?"
Na sake zabura na ce "ka bincika ko Murjanatu Bibi ce ka san sun san Godwin, saboda kana fushi da ita zata iya biya ta ce kada a ce ita ce."
Nan da nan ya gamsu ya gyada kai ya ce " tabbas na san ita ce kadai matar da zata iya fitar da zunzurutun kudi har naira dubu dari hudu ta biya min haya, ba tare da ta damu da a san ita din ba ce.
Amma dan me zata biya kudin haya? Na ce mata ina neman taimakonta ne? Ko da kun hadu da ita kin fada mata ne? Ko kuma a waya kika kira ta kika fada?"
Na zunbura baki na ce "wai Usman me ka dauke ni ne? Ina da waya ne? Bayan ka fasa min wayata a ina zan sami lambar ta kuma? Ka yi ta dora min laifi da wanda na yi da wanda banyi ba saboda yanzu ka tsane ni."
Na fashe da kukan kissa, nan da nan na ga ya sauko ya fara magana ta nutsuwa.
Ya ce "ban ga amfanin biyan ba ma saboda tashi za mu yi mu koma kano, a cikin satin nan."
Gabana ya fadi na dafe qirji na ce "mu koma Kano gaba daya fa ka ce? A wanne gida zamu zauna?"
Ya linke resit ya mayar aljihu ya zauna a sanyaye akan kafet.
Ya ce "na sa an nemo min wani qaramin gida a qarshen layinmu, naira dubu sittin kudin hayar a shekara."
Na ji gaba daya hankalina ya tashi na sauke goyon Haidar na dire shi na ce "gidan hayar naira dubu sittin amma qarami ne, tsoho ginin gargajiya mai zaure da shadda masai ta rami ko?"
Ya gyada kai ya ce " eh sai mu yi maleji da shi ai ya fi babu, kin ce ba za ki zauna tare da facaloli ba nima ba zan so ku zauna din ba dan ke ba me son zaman lafiya ba ce gara ki na gefe."
Na tabbatar Usman fa da gaske yake sai na ji gaba daya na dimauce. Idan muka ci gaba da zama a Bauchi nan ma matsala ne ina tsakiyar kuraye guda biyu Mufidah da Jalilah.Kano kuma ba zan iya komawa rayuwar qasqanci ba ana ganinka kana shigowa garin tsaf kana turanci kana raba sababbin kudade, yanzu ka dawo tsakiyar 'yan camama ka zauna, akwai raini.
Na dinga kai kawo a falon ina fadin "Innalilahi wa inna ilaihi rajuun."
Ya harare ni ya ce "ke! Ki kawo min abinci in ci, ai ko ba ni da matsala a Bauchi ba za ki sake zama ba, na yanke shawara can za ki koma da zama."
Na juyo da sauri na dube shi, ya harare ni ya kawar da kai gefe gami da jeho min dan sirrin tsaki.
Na shiga kicin na kawo masa abinci ya fara ci da alama ya kwaso yunwa mai yawa.
Na zo na zauna a gefensa na marairaice murya na fara hawaye ina bashi haquri akan abinda ya faru a hanyar Kano. Bai ce min komai ba ya ci gaba da cin abincinsa.
Ina ta sharce-hawaye da majina dan ya tausaya min, dan ya jawo ni jikinsa ya lallashi ni amma bawan Allah nan ya daskare gaba daya, babu tausayin nan na sa.
Ya kalle ni a fusace ya ce "ki fara hada kayanki gaba daya na sakawa zan sami babbar mota zuwa jibi mu tashi, ki yiwa wannan dillaliyar magana ta zo ta sayi sauran kayan gadon dakinki da na yara. Ki adana kudin ki riqe in mun je kano zan cika miki ki sayi wani. Ba zan iya daukar hayar motar kaya daga nan ta kai mana Kano ba. Su labulaye da kayan kicin wadannan zamu tafi da su."
Na ji gaba daya garin yana ta juya min, na tambaya "da kai da mu gaba daya mun bar Bauchi kenan?"
Ya girgiza kai ya ce "A a ni ina Bauchi zan sami hayar daki daya in zauna in bazama neman kudi in biya su her excellency kudinsu naira miliyan daya, dan in sun ga na bar garin zasu dauka na gudu ne su je har Kano su kamo ni su yi min wulaqanci. Gara su na ganin nawa dai a garin ina basu haquri. Na samu wani aiki ma a wani Cafe ina yi musu typing sai dai kudin bai kai ya kawo ba, ba zan iya tara naira dubu hamsim ba ma balle miliyan daya."
Na zabura na dafe kirji na ce " kada fa ka kasa hada kudin dole ta sa ka yarda ka aure ta."
Harara ta yayi ya ce " ai sai dai su aura mata gawata dan basu biyo ta hanyar da zan aure ta ba ma, sun bata abin da suka saka dole a ciki da tsoratarwa da nuna isa."
Na yi ajiyar zuciyar jin dadi, na lankwashe kai na ce "gaskiya ba zan iya tafiya in barka ba tunda akwai sauran watanninmu da suka rage, mun samu an biya mana haya mu zauna kawai har ya qare sannan dole su bamu notice din watanni shida ka ga zamu iya qara shekara guda kenan."
Ya daka min tsawa ya ce "wai zaman Bauchin nan dole ne? Garinmu ne ko kuma wata tsiyar muka ajiye a garin ne? Aiki ne ya kawo mu kuma.babu aikin zaman me za mu yi? Yara ba sa zuwa makaranta, babu cin yau balle na gobe ga kudin haya mai tsada. Da me zan ji? Kin san halinda ake ciki ne a rayuwar nan kuwa? Ba ki sani ba, sai dai a nemo miki ki ci ki sha ki zargi waccan ki zagi waccan,ki yiwa waccan qazafin karuwanci, ki hana ni bacci saboda masifarki ta kishi.Ta kai ta kawo har kin fara fita titi babu riga kina fadawa cikin motata daga Bauchi har Kano saboda kina zargin na dauko karuwai. Wallahi kada ki zaci zan yafe miki wannan abinda kika yi min.Sai kin yi kuka da idanuwanki kamar yadda kika saka ni kuka, kika saka yaranki kuka kuma kika tagayyarasu kika tafi kika bar su. Kin wulaqanta ni kin cutar da ni, na ji duk qasqancin da kika yi min sai da kaka yi bara a kano sannan kika dawo gida. Danjuma ne ya taimaka ya dawo da ke gida har tsakar dare, yara su na ta walagigi daga wannan gida zuwa nan. Mufidah ta dauka, Umma ta dauka, qarshe Safiya ta dauka har kika dawo."
Na yi wuqi-wuqi da ido na kasa magana na cika da mamaki ta inda ya ji labaran abinda ya faru kakaf babu kuskure, babu qari babu ragi.
Ya tashi a fusace ya fice ya banko qofa da qarfi, na san masallaci zai je dan ga wayarsa da mukullin motarsa nan ya bari. Na sanqarae a zaune, na tabbatar qarshena ne ya zo. Sallar magaruba ake kira ya cewa yara su ajiye kekunan su zo su tafi masallaci. Su ka dunguma suka fice ina ta leqensu ta windo.
Basu shigo gida ba sai bayan sallar Isha'i, wannan karon a gigice ya shigo ya kira ni zuwa dakinsa.
Ya dube ni sosai sannan ya ce " na hadu da Godwin a qasa yanzu, na dame shi da magiya akan ya fada min wacce ta biya min haya."
Kafin ya rufe baki hantar cikina ta kada ina fargaba ya san cewa Mufidah ce.
Ya ci gaba da cewa "kin san wa ya ce min? Wai Mufida ce. Ta yaya haka ta faru? Yaya aka yi har matar nan marar mutunci zata tausaya ta biya mana haya? Matar da bata qi ta bude idanuwa ta ga bama gidan nan ba ko ma in ce ta ga bama duniyar. Abin ya daure min kai."
Na zabura na ce "anya Godwin bai yi kuskure ba ko dai Murjanatu Bibi zai ce?"
Ya gigiza kai ya ce "shi bai ma san Murjanatu Bibi ba. Ya ce yana ganinta jifa-jifa su gaisa."
Na sulale na zauna a gefen katifa cike da fargaba.
Usman ya katse min dogon tunanin da nake yi.
Ya ce " ki shirya ki zo mu shiga gidanta mu yi mata godiya. Duk da ma dai ya ce kada in nuna mata na sani amma bai kamata in yi shiru ba, mutumin da yayi maka wannan halascin."
Na zabura na miqe tsaye da sauri na kama hannun Usman 'gam' na ce "kada ma ka fara, kada ka je. Mufida mayya ce, matsafiya ta yi amfani da wannan damar ne dan ta jawo ka jikinta ta cutar da kai. Ta yi rantsuwa ta ce sai ta rama abinda ka yi mata."
Ya dube cike da mamaki da rashin fahimta.
Na fashe da kuka na qanqame shi ina fadin "wallahi mayya ce, kashe mu take so ta yi."
Ya bambare ni daga jikinsa ya ture, ya daka min tsawa ya ce "ba na son maganar banza ta jahilci. Kin kuwa san abinda kike fada? Kamar yaya mayya ce kuma matsafiya? Me yasa ba kya fadar alkhairi kullum akan mutune, musamman akan Mufidah? Me yasa kika tsane ta haka alhali tana bin ki da alkhairi? Lokacin da kika tafi kika bar yara, na kira Dr.Isa nace a duba gidana a dauko yara, ya ce min ya fita wayar Safiya ma da ita ya fita zai kai mata gyara, ya bar ta da wata qaramar waya amma bai riqe lambar glo din ta ba.
Umma da mijinta sun fita aiki, dan haka Mufidah ce a kusa da mu zata fi saurin kai musu agaji dan haka ya turo min lambar Mufidah na kira, a sanda na kira ma ta ce min har ta dauko yaran su na wajenta. Ta ce min sun yi futsari kayansu a jiqe har ta yi musu wanka babu kayan da zata saka musu. Na kwatanta mata dorowar dakinki na ce ta je ta dauko musu kayan. Ba ki san ita ta riqe su ba ma kenan? sai da yamma da za ta fita ta kaiwa Umma ?"
Na ji gabana ya sake faduwa na hau rawar murya amma na rasa lafazin da zan fada masa dan ya fahimce ni.
Sai fada yake yi yana gargasa min baqar magana, yabon Mufidah yake yi tun qarfi. Duk da ta ce kada in fadawa kowa abinda ya faru daga ni sai ita sai Allah amma ya zama dole in bashi wannan labarin dan in kwaci kaina, in ya so ta kashe ni."
Da na fara bashi labari tun a layin farko ya zabura ya fice daga dakin dan kwakwalwarsa ta kasa yarda da abinda nake cewa. Na biyo shi falo a guje ina yi masa rantsuwa akan ya yarda da abinda nake fada masa, sai ya saka hannu ya dakatar da ni ya ce in rufe masa baki baya son ji. Kawai in dauko mayafina in zo mu je gidan Mufidah umarni nake bashi.
Na fada cikin fitsara "ba zan je gidan mayyar da ta kusa hallaka ni ba."
Ya juyo a fusace ya harare ni ya e "ni nake cewa ki yi abu amma kike cewa ba za ki yi ba ido da ido?"
Na fashe da kuka na ce "shikenan in an kashe mu kai ka jawo min. Ni ba sai na saka mayafi ba mu je a haka ai dukka gidan ne."
Raina a bace mu ka nufi gidan Mufidah, shine yake ta kwankwasawa, ina daga baya-baya ina leqe, mun dade mu na bugawa sannan ta bude.
Mufidah ce ta bayyana cikin wata shiga mai dankaren kyau, party dress ta saka ruwan hoda (pink), an yi mata kwalliya (makeup) a fuska, an yi mata dauri da wani dankwali kalar rigar, Sarqarta da 'yan kunnayenta na tabbatar na lu'u-lu'u ne ko tantama bana yi, dan an fada min yadda za ka gane na gaskiyar. Ta yi kyau kyan da bata taba yin irinsa ba.
Ta na ganinmu sai aka hau kallon-kallo. Da alama bata yi maraba da zuwanmu ba, ta ja ta tsaya a bakin qofa ta babbake gami da maqale hannayenta biyu a hamata, Ta na sauraronmu.
Usman ya hau kame-kame kamar wanda ya manta abinda ya kawo mu ma. Sai can yayi qarfin hali ya yi mata sallama, sai ta amsa.
Aka yi jugum sannan ya ci gaba da cewa "mun zo dan mu yi miki godiya, duk da kin boye ba kya so mu sani, na bincika an ce ke ce kika biya mana kudin haya. Mun gode sosai Allah Ya saka da alkhairi. Haka ya kamata maqwabci ya kasance in yana da hali ya taimaki maqwabcinsa. Ya zo a cikin hadisan Manzon Allah S.A.W ya ce a kyautatawa maqwabci, sanda mala'ika Jibrilu ya saukar masa da ayar da tayi magana akan maqwabci ya yi zaton zaa ce maqwabci zai iya gadar maqwabcinsa"
Ta sa hannu ta dakatar da shi ta ce "ban gane abinda kake fada ba fa, na ji kana maganar kudin haya, da maganar maqwabci dukka ban gane ba. Waye ya ya biyawa wani kudin haya?"
Usman ya kalle ni na kalle shi sannan muka juya muka kalli mufidah.
Ta ce "ni Mufidah bani da business da kowa dan haka ban biyawa kowa kudin haya ba."
Na cika da mamaki na ce "amma ke kika gyara mana wuta da aka yanke."
Ta girgiza kai ta ce "bani da labarin ma an yanke muku wuta balle in mayar mu ku da ita, dan haka ba ni ba ce."
Usman ya ce " ina ga Godwin yayi kuskure ko Murjanatu Bibi ce ya manta ya ce ke ce."
Ta tabe baki ta ce "da kyar idan ita ce, dan bata qasar ma kuma bata san Godwin ba, bata taba sanin kudin hayarku ya qare ba, idan har zata biya tabbas zata fada min. Amma za ku iya sake bincikawa ku ji. Zan je wajen dinner ne ana jirana sai anjima."
Ta koma ciki ta datse qofarta.
Na ji dadi da ta yi.mana haka .Tunda ta musanta ta ce ba ita ta biya kudi aka gyara mana wuta ba alhali na ji da kunnena, na san ita din ce toh kudin hayar ma.ita ce kenan amma ta ce ba ita ba ce.
Cikin sanyin jiki mu ka.dawo cikin gida, da alama kan Usman ya daure sosai, mu na shiga ya dauko waya ya kira Godwin cikin saa sai ya dauka.
Wannan karon Usman magana ya ke cikin fusata ya ce "Godwin kada ka raina min hankali fa, yaya kake yi min boye-boye? Na ce ka fada min gaskiya magana wacece ko waye ya biya min kudin haya? Ka ce Mufidah ce, ita kuma ta tambabatar min ba ita ba ce. Kuma na fi yarda da ita fiye da kai. Wannan abin da ya shafi rayuwata ne ya kamata in sani. Ta yaya zan zauna a gidan da bansan ko waye ya biya min haya ba."
Godwin ya yi.rantsuwa da abinda yayi gaskiya da shi ya ce Mufidah ce ta biya kawai bata so dai a sani.
Tambayoyin da Usman yake jerowa Godwin shine ya rasa amsar da zai bashi. "Ta yaya matar nan zata biya min haya? Meye hadina da ita? A wanne dalili zata biya min haya? Na fada mata ina neman taimako da wajen irinsu ne? Ga shi yanzu ta ce ba ita ba ce, in ba ita ba ce toh wacece? An rasa, amma tsakanin kai da Mufidah zaa sami maqaryaci."
Ya kashe wayar a fusace, ba jimawa sai Godwin ya sake kira,

9 / 11