KISHIN BALBAL BOOK 2 HAUSA READ NOVELS BY JAMILA UMAR TANKO.doc

Author :  Jamila Umar Tanko Category :  Romance

Chapter   1 / 11

1 to 3K   out of 31.6K words

??????>?? ?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????[? ???#bjbj???? ;j????[B???????????MMM????aaa8??a(???????+++??????????????$????N??M+??^++???????????????+?^???8?????+??????5???????`?T^???a?x85??????0(???????????M???++??+++++??????+++(?++++?????????????????????????????????????????????????????????????????????+++++++++? ?: KISHIN BAL-BAL 2
NA

















JAMILA UMAR TANKO
(JUT)

Matashiya:
Assalamu alaikum wararahamatullah. Tsofaffi da sababbin masoyana masu bibiyar rubutuna. Ina yi muku Albishir da fitowar sabon labarina mai tafe da sabon salo , mai fadakarwa da nishadantarwa wato KISHIN BAL-BAL part 1 ,2 and 3.

Godiya:
Bismillahi Rahmanir Rahim
Na fara da sunan Allah mai rahama mai jin qai. Dukkan godiya ta tabbata ga ubangijin talikai mai kowa mai komai. Ina addua yadda Allah Ya bani ikon farawa Ya bani ikon kammalawa lafiya. Allah Ya dora alqalamina akan rubuta daidai ya kiyayeni da rubuta kuskure.Amin.

Sadaukarwa:
Ga dukka matan da suke yiwa mazansu uzuri, su ka iya danne da saita kansu wajen fito da mugun kishi.

An fara rubuta shi ranar 24/06/2022.
Qarfe 8:30am.






Hankalina gaba daya ya tashi na rasa me yake yi min dadi, na hau sama na ga qofar falon Mufidah a bude wanwar ma'aikata su na ta share-share da goge-goge. Masu sharar ma da alama daga kamfani aka dauko su mata da maza sun kai su biyar kowanne sanyi da t-shirt da sunan kamfani. Na shiga kokonto ita din ce zata dawo ko ta saki gidan wasu ne zasu dawo? Na ci gaba da addu'a Allah Ya sa a kawo tsofaffi ko gauraye dan in huta da zargi.
Na shiga falo na iske yara su na wasa, na tambaye su ina babansu sai suka ce ya fita har ya ce ma zai siyo musu ice cream. Sai kawai na ji a jikina wajen Jalila ya tafi dan na ga yayarta ta kira shi.
Na zabura na jawo wayata na kira shi bai dauka ba, na sake kira bai dauka ba, gumi ya keto min na miqe tsaye ina ta kai kawo a falona daga ni sai zuciyata ne suka san abinda yake damuna.
Na lalubo lambar Her excellency da niyyar in kira in zazzage ta in ya so duk wacce zaa yi ayi kawainsai na tuna irin illar da zagin zai haifar, kada in zo in sha dauri.
Na sake kiran Usman a fusace sai aka ci saa ya dauka.
Na tambaya cikin fushi "ka na ina?"
Ya amsa "ina qofar gida gani nan ma dab da get. Yaya aka yi, lafiya?"
Zuciyata ta fara kwanciya, na kashe waya ba tare da na san amsar da zan bashi ba. Shiru-shiru babu Usman babu motsinsa, sai na fusata na fito da niyyar zan leqa qofar gidan in gani, sai ga Mufidah a Mufidah akan kujera falonta tana kallona ina kallonta. Gaba na ya fadi, raina ya baci dan ban so ta dawo gidan ba, sai kawai na shiga gidan ba tare da na yi musu sallama ba, tana ta waya da alama vedio call take yi.
Wani babban mutum a zaune akan dining table dinta yana cin abinci. Ya bude baki yana kallona da ya ga dai ba zan gaishe shi ba sai ya gaishe ni, na amsa a shelaqe. Ita kuwa Gimbiyar kallo daya ta yi min ta watsar ta ci gaba da kallon wayarta tana hira.
A fusace na ce " malama wajenki na zo fa."
Ba ta kula ni ba sai da mutumin ya daka mata wata uwar tsawa, ba ita da aka yiwa tsawar ba ma ni kaina sai da na razana.
Ya ce " wanne irin abu ne haka, kin yi baquwa kin qi ki kulata? Ba ki bata wajen zama ba, babu sannu da zuwa. Ba na son irin haka fa."
Nan da nan ta nutsu ta gyara zama ta fada a ciki- ciki "ki zo ki zauna."
Ina tafe ina taqama na sami kujera na zauna na dora qafa daya kan daya.
Mutumin nan ya ci gaba da bani hakuri a madadinta. Ina kyautata zaton wataqila shi zai aure ta amma kuwa da na ji dadi in haka ne da na huta da zulumi. Kuma da alama zai gyara ta dan daga ganin fuskarsa ba shi da wasa kuma tana shakarsa dan na ga shigar da ta yi ma yau ta mutunci ce, riga da siket ta atamfa super holland mai kyan gaske pink color. Yau dai su Mufida har da yafa qaramin gyale a kai.
Ta kalle ni qasa-qasa shi ba harara ba shi ba farin ciki ba. Da alama tana so ta ji maqasudin zuwana.
Na yamutse fuska na ce "Lambar Murjanatu Bibi za ki bani, ina son yin magana da ita."
Sai ta sake dubana da alama tana mamaki, na zare mata ido na maimaita cikin gadara.
Bawan Allah nan ya sake hararo ta ya ce "ba ki ji abinda ta tambaya ba ne?"
Sai ta turo baki kawai ta dungura min wayarta akan cinyata. Ina dubawa sai mu ka yi ido hudu da Murjanatu Bibi a vedio call. Abinka da manyan wayoyi tar na ganta kamar a talabiji ya hadu da yanayin wajen da take ko baa fada ba qasar America ce a cikin wani qayataccen mall, a wani wajen cin abinci komai gashi nan a gabanta ita da wasu yara 'yan mata guda biyu.
Na daga wayar na dube ta dube ni sai ta yi wannan dariyar ta ta, ta ce " Ah fine girl ya kike? Ina mijinki? Kwana biyu ban ji ku ba."
Allah ya raba mu da 'yan bariki wato ma bata san ma abubuwan da suke faruwa ba.
Na qirqiri murmushi da kyar na ce "ya na nan mana aikin sani. Zan karbi lambar wayarki ne a wajen Mufidah ina so zamu kira ki mu yi magana."
Ta yi murmushi ta ce "ba damuwa na gode, ku kira ni fa dan in baku kira ba zan yi fushi."
Tab ana duniyanci wato ma matar nan tana nufin duk tsawon lokacin nan da yake bin ta tana guduwa ta manta.
Na miqawa Mufidah waya, wannan karon sai da ta harare ni sannan ta fusge, sai na ga ta yi sauri ta kalli kan dining table shi kuwa idanuwansa kyar akanmu yana so ta sake yi min wani wulaqancin ya yayyagata.
Ta yiwa Murjanatu magana cikin karshen nasara cewa ta kashe waya za ta kira ta. Ta dubo lambar Murjanatu maimakon ta karanto min sai ta sake dungurama min wayar akan cinyata.
Cikin murmushi da jin dadi na dauko kwarababbiyar wayata na dauki lambar amma da gangan na ke nunawa na yi mistake sai in goge sannan in sake dauka, tana so ta yi min magana amma sai ta daga ido ta hasko masun harar da yake soko mata sai ta kawar da kai gefe ya sha kunu. Lambar mijina na yi dialling in ga ko tana da shi sai naga sunansa bai fito ba, na yi sauri na goge lambarsa. Wani gallelen hotonta ne tare da wancan hakimin daya hakimce na kan dining table ya dafa ta su na murmushi, sun yi bala'in yin kyau kuwa a hoton. Tabbas sun dace Umma ta gaida Aisha ni dai a kyale nawa mijin dan talakana mu qarasa tare daga ni sai shi.
Na miqa mata wayarta, ta fusge gami da alakoron harara.
Ni kuwa dan in qara jawo mata fada, sai na miqe tsaye a nutse na dafa kafadarta na yi murmushi na ce "sannu da qoqari neirbour na nagode sosai sai anjima."
Na juya na kalle shi na yi murmushi na duqa na ce "sai an jima oga thank you so much. "
Ya yi murmushi ya ce "you are welcome madam. Sai anjima."
Ban gama ficewa ba daga falon ba na ji yayi kanta da fada akan bata yi min sallama ba, kuma bata raka ni ba, shi fa baya son irin wannan baqin halin, amma fa cikin karshen turanci irin na Amerika yake magana.
Ta zabura ta biyo bayana ina gabanta ina tafe ina ragwada har muka fito bakin bodar da ta raba mu.
Na juyo na dube ta a nutse na ce " ina godiya fa, ashe kuma dawowa kika yi na dauka kin bar gidan."
Ta maqale hannayenta biyu a hamata da alama zata gurza min rashin mutunci.Ta yi wani busasshen murmushi ta ce " oh Alah sarki ku na ta missing dina ko? Ai na san dole zaa yi hakan, a cikin uku zaa yi daya."
Na dube ta duba na rashin fahimta, ta yi dariyar jin dadi ta ce " ke ce za ki fi kowa missing dina, in baki yi missing din ba toh yaranki za su yi, in basu yi ba kuwa tabbas mijinki zai yi dole."
"Innalilahi wa inna ilaihi rajuun! Me kunnuwana suke jiye min ne haka? Gabana ya yanke ya fadi na waiwayo a fusace na kalle ta zan yi magana sai ga Usman a tsaye a gabanmu.
Ta yi dariya ta daga min hannu ta ce " ok bye na gode da ziyara my neirbour."
Ta shige falonta ta datse ta bar ni a tsaye ni da Usman mu na kallon-kallo, ya kalle ni ya juya ya kalli qofar Mufidah. Aka rasa wanda zai yi magana a cikinmu. Sai ya ja tsaki ya bangaje ni ya shige cikin gida.
Na rasa in da zan nufa shin in kwankwasa mata qofa ne in shiga gidan a yi ta ta qare ko kuwa in shiga gidana in sha takaicina ni kadai?"
Kiran sunana na ji ya qwalla a fusace, na shiga da sauri sai ya nuna min kan kafet yara sun yi min wasan madara da milo, gwangwanaye guda biyu kuma a cike an juye su akan kafet an kwaba, kowa bakinsa da hanyensa yayi dumu-dumu. Na yi kukan kura zan kai bugu, ya tare ni ya fada cikin fusata
" kada ma ki fara dukar min yara, ki na taba wani zan mare ki. Laifin waye? Ki na can kin tafi yawon gulma a maqwabta kin kasa zama ki tarbiyyyatar da yaranki. Babu abinda kika sani sai kishi da masifa da matan gari akan mijinki. An fada miki kowa ne ya damu da namiji? Mata masu aji wadanda suka san ciwon kansu su na can su na karatu, su na aiki, su na siyasa, su na rufawa kansu da mazansu asiri. Basu da lokacin bin mijinki? Talaka ma irina kina bata lokacinki akaina. Me kika je yi gidan Mufidah, neman fada? Me kike tunanin Mufidah za ta yi da ni? Ko a qafa aka daura mata ni za ta kwance ta yasar dan bana gabanta, ba ta qaunata bana qaunarta kuma ba irina take so ba. Ta fada miki ta sake fada miki ban yi mata ba ta ce duk a cikin maza bata taba ganin ma namijin da baya burge ta kamar ni.
Kin kuwa leqa qasa kin ga irin motar da take qofar gidanmu? Baqonta ne ya zo da motar kudin motar ko kakaf din zuri'armu tawa da ta ki aka siyar ba zamu iya yin kudin motar nan ba.
Shashancin banza tun jiya kike zage-zage akan Jalilah mutanen da suka taimaki mijin da kike so din suka kubutar da shi daga fadawa hannun hukuma, ba za ki gode mu su ba ma sai zagi. Wataqila kin fara duba ko kin fara bin 'yan tsubbu dan labaran da kike bani jiya da tambayar da kika yi min akan Minat na ga alamar kin fara duba, dan haka ki kiyaye kada kishi ya sa ki rasa imaninki. Na gane babu wata seminar da kuke zuwa bin bokayeku ka fara."
Ya ja tsaki ya wuce daki ya bar ni a tsaye kamar gunki.
Tabbas yau Usman ya yayyaga ni iya yagawa, na ji gaba daya na tsani kaina da kaina wai mutumin da na hana kaina sakat wajen kare martabar soyayyarmu da igiyoyin aurenmu yau shine yake cewa ma haukar banza nake. Cabdijam da sake wai anyi rabo an bawa mai rago kofato....."

*** *** ***
Gabar kwana biyu mu ka yi bama magana da shi yara ma tsakanina da su sai kwasala. Na qaura dakina shima ya na dakinsa, ko ya fita baya fada min nima bana sannu da zuwa bana a dawo lafiya. Da ya ga dai da gaske nake ba zan sauko ba kawai na zo wucewa na ji an jawo ni, ina waigawa na ga Usman ne.
Ya riqe ni qam na kasa fusgewa cikin lallausan murya da kalamai masu taushi yake magana
" iam very sorry my love, na san kina sona nima ina sonki, babu abinda zai raba ni da ke sai mutuwa. Na yi nadamar maganganun da na fada miki cikin bacin rai. Ni Mufidah na tsana da na ganku tare dai na ji gaba daya raina ya baci. Na so a ce ta tashi ma kada mu sake ganin juna."
Ai yana fadar haka na ji na yafe masa ma domin kalamansa sun faranta min rai.
Ya ja hannuna mu ka je muka zauna ya ci gaba da nuna min matuqar so da begena da yake ji a ransa da kuma irin halin damuwar da ya shiga a sandiyyar rashin kulawar da bana yi masa a kwanaki biyu. Sai da ya tabbatar na huce na yi dariya sannan hankalinsa ya kwanta.
Mu ka fara hira ta yaushe gamo kowa ya qunso labaransa ashe ya kasa fesarwa sai yau.
Ya fada min ya samu ya hada dubu dari biyu ya aikawa mahaifiyarsa zaa yi siyayyar kayan auren qanwarsa. Ya ce da kudin da Her excellency ta bashi dubu dari da hamsim, kuma aka biya shi wani tsohon bashin da yake bi naira dubu hamsim ya hada ya tura musu.
Na ji dadi sosai amma ban ji dadi ba, da ya tatike kudin cefanenmu tas ya zauna hannu babu komai.
Na gyara zama na bashi labarin da mijin Mufidah zata aura ne wannan mutumin da yadda yake yi mata tsawa nan da nan sai ta nutsu. Usman bai to magana ba amma daga dukkan alamu kamar baya son hirar.
Ya harare ni ya ce " me kuma ya kai ki gidanta?"
Na qirqiro katya na ce "Ahmad ne ya shiga gidan ya qi fitowa shine na bi shi na jawo shi dakyar, ya tafi can yana musu kwalama.
Na dauko wayata na danna lambar Murjanatu vedio call dan na ga haka 'yan gayun suke dan aga location dinka musamman idan aka fita qasar waje. Bugu daya sai ga Murjanatu ta bayyana tana ganina ta cika da murna.
Wannan karon a lambu suke komai kore sai fulawoyi masu launika daban-daban sun kewaye su.
Ta yi murmushi ta ce " fine girl yaya kike ina aminina?"
Usman yana jiyo wata murya da ta yi masa kama da irin wacce ya sani dan haka ya qagu da ya ga abinda nake kallo a tunanina ma fim ne.
Na dungura masa wayar sai ya karba ya qura ido yana kallo sai kuwa suka hada ido da Murjanatu Bibi. Daman ban fada masa na samo lambarta ba dan na yi masa bazata ne, na san zai yi mamaki, irin sai dai ya ganta kawai kamar a mafarki.
Na tabbatar zai yi murna da na nemo ta kuma zata karbe shi hannu bibbiyu, sannan ta yi masa abinda ya dade yana nema.
Ni kuma a bangarena na san zai qara sona ya gasgata ina yi masa son gaskiya sannan na damu da halinda yake ciki.
Murjanatu ta cika da murna ta fara dariya ta na daga masa hannu.
Ta ce "Ustaz ya kake? Ina nemanka fa."
Abin mamaki sai Usman ya murtuke fuska ya fusata ya yi wurgi da wayar, a take ta tarwatse. Ya yo kaina yana fada kamar kamar wani tsohon zaki irin mayunwacin nan ya ga nama zai hadiye ni.
Ya finciko ni kamar zai balla yana yi min gargadi akan babu ni babu Murjanatu, babu Mufidah har abada in fita harkarsu. Dan shi har

1 / 11