Author : Jamila Umar Tanko Category : Romance
Usman ya amsa a fusace ya ce "Godwin me zaka ce min kuma? Bayan ku na yi min wasa da hankali."
Godwin ya ce "kai dai ba an biya maka kudin haya ba, toh me yasa kake so sai ka san wacece dole?"
Usman ya sake fusata ya ce "ai ni ba sakarai ba ne da wata da ban sani ba zata biya min haya amma a boye min. Wa ya sani ma ko siyar da ni da iyalina ka yi ka karbi kudin."
Godwin ya kwashe da dariya ya ce "toh tunda ka ce haka zan nuna maka shaida, ka hau Whatsapp zan nuna maka alert din da sunan wacce ta biya maka."
Gabana ya fadi dan tabbas in an nuna alert zaa ga sunan Mufidah.
Usman ya ce "ni bani na yin whasapp kada ka wahalar da ni amma ka tabbata ba zan dauki wannan rainin hankalin ba."
Na karbi wayar na kashe na cewa Usman "kada ma ka sake sauraron wannan mutumin dan ma baka san wulaqancin da yayi min da baka nan ba."
Ya tattara hankalinsa gaba daya yana saurarona, na marairaice murya na bashi labarin yadda ya shigo min gida da maza ba tare da izinina ba. Sai dai ban fada masa cewar Mufidah ce ta kwace ni ba, na ce da kyar ya fita sai da suka gama bankade gidan suka leqa ko ina.
Tabbas ransa ya yi mummuna baci dan ina iya jiyo bugun da zuciyarsa ke yi.
Ya gyada kai ya ce "Godwin bai san ni ba ne, ya bar ganin dan shi lauya ne babu abinda ya dame ni, ba zan taba barin wannan maganar ba, za mu hadu da shi gobe ai.
Ya wuce dakinsa a fusace yayi wanka, ya kwanta ba tare da ya sake ce min komai ba, da alama Usman ya qaurace min dan idan ya shiga dakin ma sai ya datse daga ciki.
Na dade ban yi bacci ba bayan yara ma sun kwanta na dade ina ta zagaye a cikin gida har qarfe dayan dare. A lokacin na ji motsin Mufidah ta dawo daga wajen dinner, na daga labule a hankali ina ta leqensu. Ita da wata qawarta suka shigo a cikin motar Mufidah su ka hawo sama dauke da manya ledoji da alama a wajen bikin aka basu, bikin kuwa na masu hali ne daga dukkan alamu. Ashe wannan tsaleliyar rigar anko ce dan na ga qawarta ma sanye da irinta.
Na kalle su, su na ta dariya da shewa na tabbatar basu da matsalar rayuwa, har suka bani sha'awa na ji dama ni ce su don wani lokacin ma masu auren sun fi shiga jarabawa.
Kalli irin son da nake yiwa Usman amma bai hana ya juya min baya ba alhali ya san duk saboda sonsa na haukace gaba daya.
In ada ne da sai na fita na tari Mufidah in ji dalilin da ya sa take boye abinda ta yi mana. In ji menene manufarta? Sai dai kash yanzu ban isa ba, na tsoron kada ta hada ni da mucizai sannan a kaini bayan duniya.
Na ci gaba da tunanin yadda rayuwata zata kasance ni kadai a kano, Usman a Bauchi a kusa da wadannan kidnappers din Mufidah da Jalilah. Gaskiya ba zan iya ba sai dai ni da shi mu koma tare ko kuma mu ci gaba da zama a Bauchin tare.
*** *** **
Da gari ya waye Usman ya fito a shirye tsaf amma da qananan kaya ransa a bace, ya kalle ni na kalle shi dan ko na gaishe shi baya amsawa.
Ya miqa min kudin cefane ya ce "zan fita in kun ji shiru har dare ku rufe gida."
Na zabura na zazzare ido na tambaya "kamar yaya?"
Ya ce "Her excellency ta kira ni yanzu ta na ta wasu maganganu tana cewa na jefa qanwarta a damuwa ban san arziki ba, ban gaji arziki ba. Kawai na yanke hukuncin zan je ofis din his excellency mijinta ya san halin da ake ciki dan na ga alamar bai san komai ba akai mata ne zalla suke wannan shirmen. Kudinsu kuma a yanzu bani da shi amma zan biya, amma in sun kama ni sun daure shikenan.
Na bi bayansa sororo ina raka shi ba tare da na san abinda zan ce masa ba. Mu na bude qofa da Mufidah mu ka hada ido tana wannan shegiyar sharar ta, ta ta sassafe. Sanye take da wata qaramar rigar bacci launin shudaye, rigar babu hannu babu qirji rigar mama ce kawai shimi iya guiwa. Kanta babu dankwali balle mayafi sanye take da wani lallausan takalmi kalar rigar daga gani saiti ne da rigar.
Ta tsaya da sharar ta tana kallinmu, mu na kallonta.
Na rasa dalilin da ya sa idan Usman ya ga Mufidah baya iya dauke idanuwansa daga kallonta duk da wannan Ustazancin na sa da baya hada ido da mace mai hijab ma amma yana iya kallon Mufidah da take fitowa rabinta tsirara.
Itama haka take yi masa irin wannan kallon ido cikin ido duk sanda suka hadu.
Raina ya baci na riqe hannunsa na fisge shi muka yi qasa, abin mamaki sai na ga yana ta waiwayenta.
Mu na sauka na harare shi na ce "me kake kallo a jikin matar nan wai, har kana waiwaye?"
Budar bakinsa sai ya ce "mamaki take bani kawai."
Na tambaya "mamaki kamar yaya?"
Sai ya kasa amsa min ya shiga mota ya kunna yayi tagumi. Ina tsaye ina ta girgiza, zuciyata kamar zata fita dan haushi, ga Jalilah ga Mufida. Ina zan saka raina, da me zan ji?"
[8/1, 10:15 AM] Jamila Umar Tanko: 21
Na yi qasa-qasa da murya na ce "mamaki ma ai sai nan gaba za ka sha a kanta a lokacin da za ka san mayya ce, arniya, matsafiya kuma aljana ce."
Ya yi min kallo na takaici ya girgiza kai alamar yana tausaya min, ya ja mota ya tafi. Na bi shi da addu'ar neman tsari daga sharrin masu sharri a cikin zuciyata.
Safiya ce da Mus'ab da maigidanta suka fito gwanin sha'awa ta rako su. Mu ka gaisa da Dr.Isa sai washe min baki yake yana ja na da hira, bai san haushi yake bani ba tunda ya jone da ire-iren su Mufidah. Safiya ta yi min sigina alamar in tsaya akwai magana. Bayan ya ja mota sun tafi ta ja hannuna zuwa falonta. Tambayar da ta yi min ta bani mamaki ta ce "wai Mufidah ce ta gyara mu ku wutar gidanku da aka yanke?"
Na dube ta cike da mamaki ta yadda ta sami wannan labarin. Ta shaida min Dakta ne ya fito ya ga wasu akan falwaya ya tambaya sai su ka fada masa cewa Mufidah ce ta ce su mayar da wutar gidanku."
Na rasa amsar da zan bawa Safiya na sulale na zauna, ta zo ta zauna a kusa da ni da alama gulma ta ciyo ta ta sake cewa an ce ma ita ta biya muku kudin haya."
Na zabura na ce "in ji wanne shegen kuma?"
Safiya ta tabe baki ta ce "au baki da labari kenan? Usman ya boye miki toh dan su na tare da Dakta bayan sun fito daga masallaci Godwin ya fada mu su tare ya ce Mufida ce ta biya amma ta ce a boye sunanta."
Na yi shiru can na ce "haka na ji nima amma da mu ka tambaye ta, sai ta ce ba ita ba ce."
Safiya ta zabura ta ce "munafuka wallahi ita ce tana da wata manufa a qasa. Shawarar da zan baki ki yi ta addu'a kawai.
Hankalina ya sake tashi na yi tagumi can na dago na kalli Safiya na ce "cewa ta yi ba ita ba ce, har gyaran wutar ma. Amma ban yi mamaki ba kin san ba cikakkiyar mutum ba ce rabinta aljan rabbinta mutum, kuma mayya ce, sannan matsafiya ce, ba musulma ba ce kuma. Boka ya ce shu'uma ce asiri ma baya cinta. Ni dai kawai sai yadda Allah Ya yi da ni."
Safiya ta bude baki tana yi min kallo na rashin fahimta.
Ta ce "subhanallah! saboda kishi kike danganta da wadannan mugayen kalamai? Haba ai sun yi muni da yawa. Kar ki kafurta ta mana Fatiti."
Na yi shiru dan na san babu mai fahimta ta, amma ina fatan su ga abinda na gani, sannan za su fi gane ko wacece Mufidah.
Safiya ta ci gaba da cewa "yauwa yaya labarin Jalilah? Ashe kuma abu ya kai ga zasu maka Usman a kotu in bai biya su kudin nan ba, wai sun bashi zabi ko ya biya ko dole sai ya aure ta."
Na dago da sauri na kalli Safiya cike da takaici. Na ce "shima Daktan ne ya fada miki? Subhanallah! Haka gidana ya zama kuma a komai bani da sirri? Shi Dakta duk labarin da aka yi a waje sai ya juye miki?"
Safiya ta harare ni ta ce "lallai Fatiti, kin fara boye min matsalarki kenan? Meye ba ma fadawa juna? To shikenan tunda haka na zama yanzu a wajenki."
Safiya ta yi fushi ta zanbura baki.
Na fashe da kuka na dora kaina akan cinyarta, na ce " na shiga tsaka mai wuya Safiya, na rasa yadda zan yi da rayuwata. Kin ji wai kano zai kai ni shi ya dawo Bauchi ya zauna shi kadai. Usman baya kula ni, ba na gabansa yanzu saboda sun janye masa hankali, Jalilah da Mufidah."
Safiya ta dinga lallashin tana bani baki har ta samu na lafa da kukan ta ce "kada ki damu zan baki shawara a nutse, zaa samo mafita."
Ta rako ni har bakin matattakala na hau sama, ina hawa na hango falon Mufidah a bude wanwar sannan tawa qofar falon ma haka a bude. Yarana na hango har da mai rarrafe su na ta shawagi a cikin falonta.
Na zabura zan kwalla musu kira Mufida na gani a gabana ta fito ta tsaya a bakin qofar ta tsare ni da idanuwa.
Ta dube ni ta yi murmushi ta ce "za ki shigo ne? Zo ki wuce."
A zuciyata na ce "ni da shiga gidanki ai sai a qiyama."
Na girgiza kai na ce "ba shiga zan yi ba, amma a cewa yarana su fito."
Ta fada cikin gadara ta ce "ina so su taya ni hira ne, a madadinki."
Ta mayar da qofa ta rufe, nan da nan hankalina ya tashi na rasa abinda yake yi min dadi. Shin ihu zan saka mata ko sauka qasa zan yi in ari wayar Safiya in kira Usman in shaida masa cewar Mufidah ta kwashe min yara? Ai in na fada masa ma zai ga ba wani abu ba ne, mai son danka ai mai sonka ne. Ba zasu taba ganewa ko wacece matar nan ba.
Ina tsaye kamar gunki na ga an bude qofar sai ga yara a layi kowanne hannunsa cusu-cusu maqare da alewoyi da biskit.
Ta fada tana kallona ta ce "duk wacce ta kwace ta hana ku ci, ku kwalla kuka zan jiyo ku in zo, sai na hukunta mutum."
Ta na dauke da Haidar a hannunta ta na yi masa cakulkuli amma saqo take bani ta ce "qawaye, su na labarina ko Haidar? Gulma babu kyau fa. Zan hukunta mutum."
Nan fa qirjina ya fara dukan uku-uku, daga dukka alamu ta ji abinda nake fadawa Safiya.
"Na shiga uku." na fada a bayyane yayin da ta miqa min Haidar tana ta dariyarta. Da na samu na hada kan 'ya'yana sai na fada cikin gida da sauri na datse. Na rasa hukuncin da zan yiwa yaran nan, ga abinda ta ce kuma idan na hana su ci zata dauki mataki akaina. Ko baki ba su wannke ba suka tashi su ka tafi kwadayi.
*** *** ***
Usman ne ya dawo gida da misalin qarfe daya na rana da alama a gigice yake. Ina ganin yanayinsa sai hankalina ya tashi. Na tabbatar akwai matsala a gidan su Jalilah. Na tare shi ina tambayarsa ko lafiya? Maimakon ya fada min labarin Jalilah sai ya jeho min wata tambaya data bani tsoro.
Ya ce "Fatiti dazu a bakin mota me kike fada min akan Mufidah ma?"
Na harare shi na ce "ai kai kullum musu kake yi min, ka dauke ni ma mahaukaciya. Matar nan na fada maka mayya ce, kuma ba musulma ba ce, kuma ba cikakkiyar mutum ba ce, aljanna ce. Mucizai ne a gidanta, matsafiya ce."
Sai ya zazzare ido yana kallona, sannan ya gyada kai ya fara kai kawo a cikin falon.
Na tambaya "lafiya? Wani abu ka gani?"
Ya qyada kai ya ce "tabbas na ga wata alama, zo mu zauna ki bani labarin abinda ya sa kika ce haka akanta dan akwai qamshin gaskiya a maganarki."
Cike da fargaba na zauna shima ya zauna na fara bashi labari, tun daga farko har qarshe. Mamaki ya hana Usman sakat sai salati yake yana kiran Hasbunallahu wa ni'imal wakil. Lahaula walaquwwata illabillah.
Ya yi ajiyar zuciya ya ce "tabbas ba zan amince da wannan zalumci ba. Wato har kidnapping dinki ta yi kenan daga safe har dare? Ta raba ki da yaranki, toh ba zan amince ba, sai na dauki mataki. Na amince da maganarki shu'uma ce akwai dalilinta na biya mana kudin haya."
Na zabura na ce "au ita din ce ta biya? Yaya aka yi ka sani?"
Ya ce "Godwin ya nuna min alert din da ta yi masa da chating dinsu kuma, sannan sunan da kika fada haka ne sunanta a jikin alert din, Mufidah Hamza.Sannan maganar ko ba musulma ba ce tabbas haka ne, ya kira ta a waya ya sakata a hand's free. Yadda ta san littafinsu bata san qur'ani ba, duk in da Godwin ya ja sai ta qarasa masa. Haka ta dinga jawo ayoyinsu akan mutum mai qarya da bude asirrin wani, ta ce ai ta ce masa kada ya fada mana ita ta biya. Dan me zai fada kuma?
Dr. Isa ya tabbatar min kuma ita ta sa aka gyara mana wuta. Me take nufi da mu? Me take nema a wajenmu? Kin ce ta ce saura ni ko? Toh a shirye nake ina jira ta yi min kiranyen. Na fi qarfin aljanu, na fi qarfin matsafa, zan qona ta da ayar Allah."
Na bi Usman da kallo yana cika baki dan bai san irin na ta ba ne. Ya zaci irin qananan aljanun nan ne na 'yan makaranta da yake fatattakarsu. Ai ni na ga abinda na gani shiyasa bana iya yin wata magana kawai sai kallo.
Ya zabura ya shiga daki ya dauko qullin magani ya ce in hura masa gawayi a kasko.
Zan yi masa tambayoyi ya daga hannu ya dakatar da ni. Na cika da mamaki da fargaba abinda zai faru. Ya bude qofar gidanmu ya dauki garwashi ya kai bakin qofa a cikin kasko ya ajiye sannan ya dauki maganin ya zuba akai, kan ka ce kwabo sai hayaqi ya turnuqe koridon.
Ya dawo ciki ya zauna in zan yi magana sai ya dakatar da ni. Babu abinda muke ji sai qarar budewa da rufe qofofin 'bararam bam' daga gidan Mufidah,ta na ta shige da fice tana buga qofofi. Sai can ta fito sanye da wata riga T-shirt da zani, kanta babu dankwali da alama a gigice take ta fado cikin gidanmu da sauri, na yi tsalle na buya a bayan Usman.
Ta shigo falonmu ta dinga baza idanuwa tana kalle-kalle can ta ce a bata aron tsintsiya, Usman ya ce ga ta can ki dauka.
Sai ta girgiza kai ta fita, ya sake tashi ya qara maganin,sai hayaqi ya turnuqe, sai ta sake fitowa ta na muzurai.
Usman ya sake tambayar ta "lafiya?"
Ta ce muciya zaa bata aro. Ya shiga kicin ya dauko mata muciya ya miqa mata, sai ta qi karba ta fice