Author : Jamila Umar Tanko Category : Romance
da zata fita sai ta sa qafa ta yi cilli da da kaskon turaren wutar har sai da kaskon ya fashe, ta yi tsaki ya shige gidanta.
Usman ya yi dariya ya ce "tabbas biri yayi kama da mutum."
Na ce "Usman ka ga kada ka jawowa kanka ka rabu da ita fa, ba ruwana. Na ga tana harara ta zata ce ni na fada maka."
Ya ce "babu ruwanki, ku yi tafiyarku kano kawai ku rabu da ita."
Na ce "ni fa ba zan koma kano ba, qafata qafarka."
Ya harare ni ya ce "mahaifinki ma ba za ki dubo shi ba? Dan haka ki je ki hada kayanki da na yara, gobe Danjuma zai zo ya kai ku Kano."
Na tashi a fusace na shiga daki ina harhada kaya, zuciyata na karkarwa cike da kokonto "shin anya in tafi Kano kuwa in bar Usman a Bauchi? Kada in tafi kuma ya hana ni dawowa."
Ina so in yi masa qorafi amma ya qi bani fuska, ya na ta shan kunu yana bata fuska, yana ta tattaro min kayana.
Na shiga gidan Umma da Safiya da yamma na yi musu sallama na ce zan je Kano in duba Babana ba shi da lafiya amma ban sani ba ko na tafi ma kenan. Jikinsu yayi sanyi suka ce in Allah Ya yarda ma zan dawo.
Da daddare mu ka ga Godwin ya shiga gidan Mufidah da sauri, Usman ya kalle ni na kalle shi, kowa ya san abinda yake faruwa wataqila ce masa zata yi ba zata iya zama da mu ba ya nemo mata wani gidan.
Washe gari da asuba na ji Usman yana tashina ya ce mu yi wanka, dan da sassafe Danjuma zai zo. Na tashi a gigice na yi wanka na yiwa yara, muka karya kumallo. Gaba daya na rasa abinda Usman yake nufi, dan ban ga alamar da shi zaa yi wannan tafiyar ba.
Wayarsa ce ta yi qara ashe Danjuma ne ya iso bakin get, sai Usman ya ce ya hawo sama ya taya shi daukar kaya. Akwati daya na hada amma sai na ga Usman yana ta fito da manyan jakunkuna da manyan akwatuna su na ta sauka qasa da su dakyar Duke jansu saboda nauyi. Na shiga dakin yara da sauri na duba ashe kayan yara gaba daya ya hada bai rage komai ba, haka na duba durowata ya kwashe kayana tatas, na sa kayan ma kadan ya rage ya kwashe kayan gaba daya ya zuba a jakunkuna, sai na ji dan sauqi tunda shima ya hado da kayansa. Shikenan dai kenan da alama na tafi na bar Bauchi kenan? Tashina dai guda daya ne Mufidah da Jalilah.
Ya sallami Danjuma ya biya shi komai sannan ya dauki kudi naira dubu ashirin ya bani ya ce in riqe in cancana kafin ya zo.
Na fara jero masa tambayoyi "sai yaushe za ka zo? A ina zamu zauna mu ajiye wadannan himilin kayan?"
Ya ce "Ishaq zai nuna muku in da za ku ajiye kayan."
Da alama dai wannan kwarababben gidan hayar yake nufi zan sauka. Innalilahi wa inna ilaihi rajuun.
Na fusata na nuna in dai a wannan gidan da yake fada zan zauna ba zan tafi ba, na ja na tsaya a bakin mota. Wannan karon yaransa ya dauka ya zuba a cikin motar ya cewa Danjuma ya tafi da yaran da kayan ya ajiye su a gidansu.
Ya shige cikin get ya bar ni a tsaye, Danjuma yana ta bani baki. Kuka ne ya kece min, tashin hankali da fargaba. Na shiga motar a bisa larura dan babu yadda zan yi, muka tafi ba tare da na iya cewa komai ba.
Tunani na daya yadda zan bar Mufidah da Usman su kadai a gida daya. Duk da cewa yanzu komai ya bayyana bata sonsa baya sonta har ma da qarin tsanar juna bayan rashin son ma.
Yara su na ta murna abin haushi basu san haushi su ke bani ba. Na tsaya a hanya na sayi tsaraba, sai da na kashe naira dubu goma a cikin kudin dan ba zan shiga kano a bushe ba, alhali na saba kai musu tara ta arziki.
Ina jin Usman yana yawan kiran Danjuma yana tambayarsa a inda muke. Har sai da muka isa kano qofar gidanmu ya tabbatar mun isa lafiya sannan ya daina kira. Bai ce a bani waya ba nima ban ce a bani shi ba.
Abinka da gidan yawa yara da manya suka arto a guje ana murna da ganinmu dan na fi shekara rabona da zuwa Kano. Aka yi mamaki da aka ganni da himilin kaya amma an dauka duk a cikin dogon hutu ne kuma sun san ina zuwa da tsofaffin kayanmu in yi ta rabo.
Na je dakin Babana na gaishe shi sai ya fashe da kuka yana fada min halasci da karamcin da Usman ya yi masa, ya umarce ni da in yi masa biyayya har qarshen rayuwarmu, bai yarda in saba masa ba idan ban yi haka ba bai yafe min ba ko bayan ransa.
Fargaba mai yawa ta rufto min yadda mahaifana suka cure Usman har suke gindaya min irin wadannan dokoki. Su na nufin ko kishiya zai yi min in yi biyayya kenan? Ashe babu mai bin bayana kenan ya bani gaskiya, Usman ne kadai mai gaskiya?
Bayan zuwana da kwana biyu sai ga Ishaq qanin Usman ne tsakaninsu daya ya shigo gidanmu ya ce Usman ya ce ya kai ni in sayi gado da katifa in koma sabon gidan da ya kama min haya. A gaban Iyata aka yi maganar daman, zan yi musu sai ta dakatar da ni ashe duk sun san zancen har ma sun yi murna da hakan. Ya fada musu baya aiki zai dawo gida.
Haushi ya kamani na ce ba zan je siyo gadon ba, sai qanwata ce ta wakilce ni suka je suka siyo suka wuni acan gidan su na gyarawa.
Aka zo aka kwashi akwatunana aka kai suma suka jera kayan, na qi zuwa na gani dan takaici kwana da kwanaki.
A ka kawo min waya aka ce Usman ne zai yi magana da ni sai na qi karba.Ya sha kiran wayar 'yan gidanmu ya ce a bani zai yi min magana amma ba na amsawa. Daga qarshe ya bada saqo a fada min cewar in harhada in koma gidan nan, umarni yake bani ba shawara ba.
Nan dai a gida aka yi min caaa ana ta caccaka ta aka dauke ni aka kai ni. Sai na ga gidan ma ashe babu laifi ya na da kyau, dakuna uku ne falle-falle da tsakar gida da zaure sai kuma bandaki guda daya a tsakar gida, shadda ce ta tsugunno amma ta tangaran da tiles ba laifi.
Rayuwar da zan shiga ba irin rayuwar da na saba ba ce, tabbas na ci baya ba dan kadan ba.
Kuka na barke ina ta yi ba tare da na fada musu dalilin kukan nawa ba. Sai na ga kayan labulayen gidana na Bauchi kakaf da kayan kicin Usman ya hado min ya aiko.
Kamar wata amarya haka 'yan gidanmu da 'yan gidan su Usman su ka taru ana taya mu murna. Su na ta murna mun matso kusa da su zasu dinga ganinmu
akai-akai, masu tunanin dukka kudin Usman a wajena da yarana yake qarewa su na murna zasu ga komai akan idanuwansu.
KISHIN BALBAL 2
PAGE \* MERGEFORMAT 2
% & > ?
[? ?\ ,? J? K? ??????????vgYKYK=/h?E? h?D6 5?CJ OJ QJ h?E? h?nw 5?CJ OJ QJ h?E? h?nw 5?CJ OJ QJ h?D6 h?nw 5?CJ OJ QJ h?D6 h?D6 OJ QJ nHtH hci hci nHtH hci h?nw 5?CJ OJ QJ h?D6 h|D 5?CJ OJ QJ h?D6 h?D6 5?CJ OJ QJ h?D6 h|D 5?CJ, OJ QJ h?D6 h|D OJ QJ nHtH h?D6 h|D CJ OJ QJ h?D6 h|D CJ OJ QJ h?D6 h|D 5?CJ$ OJ QJ h?D6 h|D 5?CJD OJ QJ ! " # $ % & 8 > ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? $???d? ? ]???a$gdci ????Z ?L?d? ? ]???^?Z `?L?gd?E? $????Z ?L?d? ? ]???^?Z `?L?a$gd?E? ? J . / 8 S ]
^
j
?
?
?
? ?
T D n ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? d? ? gd?E? d? ? gdci $????Z ?L?d? ? ]???^?Z `?L?a$gd?E? n ? ` d ? ? ? E ? M ? W ? V ? > ? ? ? ] ? ^ ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? $????Z ?L?d? ? ]???^?Z `?L?a$gd?E? ? u! ?! J" !# ?# ?$ ?$ ?% `&