Author : Jamila Umar Tanko Category : Romance
da rayuwa a cikin aljanu. Mufidah ba ki da tausayi ne? Dan Allah ki bar ni in tafi cikin 'yan uwana bil-adama. Na ce na tuba, na daina damunki.
Ta yi dariya ta ce " ba ni na kawo ki ba fa ke kika shigo ko iso ban yi miki ba, babu sallama kika bangaje ni kika shigo.Wallahi mai fitar da ke daga gidan nan sai ya shirya ki ci gaba da addua kawai."
Na sake fitar da rai daga sake ci gaba da rayuwa, na fashe da kuka ina sharce majina da tulin tissue din da ta kawo min har katan daya.
Ta na cin abincinta a nutse tana yi min hira da alama tana cikin nishadi irin wanda ban taba ganinta a ciki ba.Tabbas na san yau ranar daukar fansa ce a wajenta ni kuma a wajena ranar da nake girbar abinda na shuka ne.
Ta kalle ni ta yi murmushi ta ce " na san kin tsane ni ada, a yau kin sake jin tsana ta amma ba komai daman bana buqatar soyayya daga wajen mutanen da basu san darajarta ba. Kuma ko mahaifiyata na soya na ba ki ba za ki so ni ba, kin cusawa mijinki hakan a ransa.
Gashi ba ni da niyyar tashi daga kusa da ku kamar yadda ba ku da niyyar tashi ku bar ni kenan mutu ka raba ni da ku.
Da farko har ga Allah gidan nan bai yi min ba saboda bana son zama ya wuce flats 2, na ga nan har mu hudu ke kika dinga roqata a dole na yarda musamman da na ganki da 'yan yara, gani da son yara na ce zasu dauke min kewa amma daga qarshe kika gudu kika bar ni kamar marainiya, ba ki bar ni da takaicin ma kadai ba, kika hada da tsana da sharri."
Na sunkuyar da kai dan na fara jin nauyin maganar da take fada, kuma na gasgata an yi.
Da na ga babu sarki sai Allah babu wata mafita banda in zauna mu yi hirar ko Allah zai sa idan ta gaji da surutun zata bar ni in tafi.
Sai na tambaye ta na ce "bani labarinki. Ina so in san ko ke wacece?"
Kallona ta yi ta yi murmushi ta ce "anya kwakwalwarki zata iya daukar labarin Mufidah? Akwai tsoro sosai da firgice a cikin labarina fa.
Ko da yake duk duniya ke kadai kika taba sanin wani abu daga cikin yadda rayuwata take dan haka ke ce babbar aminiyata bani da kamarki yanzu.
Ko Murjanatu Bibi bata taba sanin abinda kika sani ba dan ke ganau ce ba jiya ba."
Na gyada kai na ce "tabbas ni ganau ce ba jiyau ba ce, na ga abinda na gani, na ga abinda ban taba gani ba."
Sai ta kwashe da dariya tana tafa hannu amma fa dariyar ba irin ta hankali ba ce, kuma ba irin ta mutane ba ce.Tun ina ganin ba damuwa ba ce har ta fi qarfin tunanina.
Na razana na miqe tsaye zan nemo mafaka, sai ta damqo ni ta mayar da ni ta zaunar.
Wannan karon gumi ne ya keto min na tabbatar ba gumi ne na haka kawai ba saboda A.c a kunne take kuma ta dauki sanyi, na fi zaton gumin daukar rai ne ya tunkaro ni.
[7/24, 5:16 PM] Jamila Umar Tanko: 17
LABARIN MUFIDAH
Sunana Mufida Hamza, mahaifina dan asalin garin Bauchi, bahaushe ne. Sunan mahaifiyata Khadija 'yar qasar Habasha ce wato Ethiopia.
Wani aiki na shekaru biyu ya kai mahaifina qasar. Ya hadu da ita tana qarama, ya aure ta. Acan su ka fara zama, da zai dawo ya taho da ita a lokacin an haifi yayana Imam Malik.
Daman ashe yana da wata matar anan Nigeria amma ya boyewa mata da ita da danganta domin ya san idan ya fada ba zasu bashi aurenta ba kuma ba zasu yarda ya taho da ita ba.
Sunan matarsa Hafsat, sun dade tare har ma a lokacin su na da yara hudu dukka maza, yaran su na kiranta da Mummy.
A lokacin shi da iyalansa su na zama a Lagos anan yake aiki matarsa ma Mummy tana aiki anan tana koyarwa a jami'ar Lagos. Babbar mace ce mai ilimi dan a lokacin da suka yi aure ma ita da mahaifina sa'anni ne, kuma a shekara daya su ka gama karatu.
Gida daya ya kawo mahaifiyata ya hada su kasancewar babban gida ne mai bangarori daban-daban. Hakan bai hana Mummy neman rigima ba saboda baqin kishi wanda ya wuce misali.
Da farko ta fara fada akan ya boye mata auren da yayi ya ci amanarta, na biyu ya auro yarinya qarama 'yar cikinta, na uku kyakykyawa ce irin kyawun nan na gani na fada. Abin ya sake ninkuwa da ta ga yadda yake tsananin qaunar mahaifiyata fiye da kowa da komai.
Shi kuma bayanin da yake yi shine Khadija tana bashi tausayi ne saboda ya kawo ta qasar da bata san kowa ba sai shi mijinta kadai ta sani dole ya kula da ita. Ko Hausa ba ta iya ba sai dai turanci da yaren na 'yan Habasha.
Idan daddy ya fita wajen aiki, sai Mummy ta je bangaren Khadija ta yi ta masifa, bayan zagi har da duka, wataran ma har da yaranta suke haduwa su yi mata duka
Mahaifina yana daukar mataki amma fada kawai yake yi da gargadi, gobe ma zasu sake.
Mamana ta sake samun cikin yayana Umar sai ta ce a qasarsu take so ta je ta haihu. Shima ya san babu mai kula da ita anan, dan haka sai ya amince ya dauke ta ya kai ta gida. Ya bar mata komai da komai da zata buqata na haihuwa, ya dawo Nigeria.
Bayan ta haihu ta yi arba'in sai ya je zai dauko ta su dawo, nan fa ta ce ba zata bi shi ba. Sai a lokacin ta fadawa danginta cewa yana da wata matar har da yara guda shida, kullum duka take yi mata.
Su ma suka goyi da bayanta su ka ce ba zata dawo ba. Shekara da shekaru ya dinga sintirin zuwa yana ta magiya akan ayi haquri ta dawo zai canja mata gida ta zauna ita kadai, amma suka ce ba zata dawo ba.
A zuwan da yake yi ne tunda da akwai igiyoyin aure a tsaninsu, sai cikina ya bayyana dan haka aka harhado ta aka dawo Nigeria da ita dole.
A garin Lagos ne amma da sharadin zai canja mata gida. Bayan wasu watanni aka haife ni, ni ce kadai macen da aka fara haifa a cikin maza takwas. Mummy na da yara maza shida na mamana maza biyu. Masha Allah zo ka ga murna a wajen mahaifana.
Cikin ikon Allah gaba daya yaran gidan kakaf da mahaifinmu muka yi kama.Ya dauki son duniya ya dora min fiye da sauran 'ya'yansa, nan fa Mummy ta saka baqar lamba akaina duk duniya babu wacce ta tsana irina.
Gidan kowa daban amma sai ta taso ta zo neman rigima gidanmu, duk da an yi rubutu a tsakaninsu cewa kada ta sake takowa in da take balle ta doke ta amma fa sai ta zo din.
Da mamana za ta je garinsu ganin gida ya ce ba zata tafi ba, dan in ta tafi ba zata dawo ba.Ta ce sai ta tafi dan haka sai ya dauke ni ni da Yayana Imam Malik ya boye, its kuma ta tafi da Umar.
Ashe wannan tafiyar ta tafi kenan, qarshen auren ya zo. Shima ya yi fushi bai bi ta ba, su ma basu yi magana ba.
Tun ana waya aka daina, sai ya tura mata da takardar sakinta bayan wasu shekaru. Ina da shekaru uku a lokacin ya mayar da mu wajen matarsa, anan suka dinga gana mana azaba. Ya san da haka dan haka da aka tura shi wani aiki na shekaru garin Jalingo sai ya ga ba zai iya barina ba. Ya dauke ni ya tafi da ni ba tare da ya san yadda zai yi da ni ba amma ya bar Imam malik a gidan. Duk wata wahala da azaba ta duniyaan ganawa yaron nan, wato mummy da yaranta. Amma akwai Allah.
Mufidah ta yi shiru yayin da idanuwanta suka cika da hawaye.Ta dago ta dube ni na buga tagumi ina jinjina irin wannan badaqalar rayuwa.
Ta qura min ido tana kallo, kallo irin na su na mayu.
Ta ce "shiyasa gaba daya kike bani haushi saboda irin kishinki ya yi kama da na matar Ubana. Baqin kishi, baqin hali, baqin zargi, hayaniya, zage-zage. Kullum a haka take, mahaifina baya hutawa kamar yadda Usman dinki baya hutawa. Kun mayar da kanku kamar mahaukata, kun zubar da imaninku gaba daya, dan komai za ku iya yi akan mijinku."
Na sake nutsuwa don kada ta hada ni da baqin mijici. Na yi kalar tausayi da nuna alamar nadama. Amma na matsu na ji ci gaban labarin nan ta yadda ta rayu da uba da yadda ta koma rayuwa a cikin aljanu.
Mufida ta kurbi lemo ta dube ni ta yi murmushi ta ci gaba da cewa "rayuwa daga ni sai ubana a garin da babu dangi akwai wahala. Shi yake yi min wanka, ya dafa min abinci, ya yi wasa da ni. Ya saka ni a mota mu je wajen aiki tare.
Idan zai je Lagos wajen iyalansa sai ya taho da ni amma a garin Ibadan yake ajiye ni a gidan qanwarsa, ba ya yarda ya qaraso da ni gidan. Saboda tsabar tsanar da Mummy ta yi min, abin ya baci kuma ta koyawa yaranta irin wannan hali. Ko Imam Malik ma makarantar firamare da sakandire ce a hade amma ta kwana ya kai shi saboda zaman gidan ya gagare shi.
Mun fi shekara a haka, damarmaki da dama sun zo masa a wajen aiki, haka yake haqura da kudin da zai samu saboda ni ba zai iya yin tafiye-tafiye ba, kuma bai san in da zai kai ni ya ajiye ba.
Shekaruna biyar a lokacin, ina matuqar neman qawayen da zamu yi wasa tare dan haka kullum ina leqe ta windo ina kallon yara masu wucewa, su na ta bani sha'awa. Gidan da muke akwai bishiyoyin kwakwar manja da yawa har guda casa'in da shida, sun gazaye gidan gaba da baya.
Bishiyoyin cike suke da 'ya'yan itatuwan kwakwar manja bukuru-bukuru. Amma kuma mucizan da suke jikinsu sun linka yawan bishiyoyin sau dari, 'ya'yansu da jikokinsu.Tun ina tsoron miciji har na daina, kana tsaye a bandaki za ka ganshi ta windo, watarana ka ga wani a kicin, in baa rufe qofa ba har cikin falo. In yi ta ihu ada har na saba da su, su kalle ni in kalle su, su wuce.
Ba a raba gidanmu da yara 'yan makaranta masu tsintar kwakwar da suke faduwa musamman a ranar da aka yi ruwa da iska, sannan akwai himilin tsuntsayen da su ka qauro kan bishiyoyin su na ci su na zubarwa qasa. Reshen kwakwar kuwa shima su na dauka, su na ferewa su yi tsintsiyar kwakwa.
A haka na saba da yara da yawa, su na daga waje ina cikin gida ta jikin windo nake kwalla musu kira. Watarana ma in debo musu kwakwa ina basu don masu gadinmu su na tara min kwakwar su bani da yawa har in rasa yadda zan yi da su.
Na shaqu da wata irinta Janet duk da ta fi ni girma sosai shekarunta zai kai goma sha uku a lokacin amma tana da kirki. Janet mai aiki ce ko kuma in ce 'yar uwar maqawabtanmu ce da aka dauko daga qauye, tana yi musu bauta amma sun saka ta a makarantar boko.
Kullum ta so daga makaranta sai ta siyo min kayan dadi irin su alawar madara, kafi tsire, alewa da biskit sai ta miqo min ta windo sannan ta wuce gida. Mahaifina ya na yawan zama tare da ni a gida idan ta kama zai fita sai ya tafi da ni in da ba zai iya tafiya da ni ba kuma sai ya rufe ni ta baya ya ce yanzu zai dawo.
Daga baya kuma ya fara bari na a farfajiyar gidan tunda akwai mai gadi ya ce in yi wasa amma kada in tafi yawo. Daman kuma gidan baa katange shi ba a bude yake wanwar, sai dai akwai tazara tsakaninmu da maqwabta. A farfajiyar gidan nake wasa na musamman idan yana jin bacci na hana shi ko karatun jarida, sai ya ce in fita in yi wasa.
Idan Janet ta hango ni sai ta zo mu yi ta wasa, tana jin Hausa kadan-kadan bata jin turanci sai dai yarenta. Ni kuma turanci da Hausa kadai na iya a haka dai muke gane yaren junanmu, har na fara bin ta gidansu, tun tana boye ni har matar gidan ta ganni rannan.
Ta daka mana tsawa daga ni har Janet din, ta ce daga ina nake? Kuka na barke, yayin da Janet ta hau karkarwa tana bayani. Sai na ga ta yi dariya ta shafa min kai ta kira ni da yarinya mai kyau.
Mata mai kirki itama tana da kyauta, kullum tana bani manyan kyauta kamar su kek da alewa, da yake bata da qananan yara yaranta duk sun girma su na jami'a.
Sunanta madam Beatrice, babbar ma'aikaciya ce a kurkuku, ita ce babba a gaba daya kurkukun garin.
Watarana ta kamo hannu ta shigo gidanmu don ta gaisa da mahaifiyata, sai ta iske babu mata a gidan sai mahaifina ashe kuma ma sun san juna a sanadiyyar kamancecceniya ta aikinsu, ita a prison shi kuma lauya a kotu.
Ya fada mata gaskiyar lamari cewa daga shi sai ni dan haka ta qara tausaya min. Ta yarda in Janet ta dawo daga makaranta ta dinga zuwa tana daukana muna yini a gidanta. Ya ji dadi da hakan.
Sai in ji zaman kadaici ya ishe ni kafin Janet ta dawo sai in ji ina son kallon mucizai, dan haka gaba gadi nake tafiya matattararsu in saka su a gaba ina kallo. Wasu farare, wasu baqaqe wasu jajaye, wasu koraye. Na san inda suke taruwa da yawa a wasu lunguna ne a cikin dawa a nesa da gidan, dan haka da sassafe nake sulalewa in kai musu ziyara wasu a cikin ruwa wasu sun kanannade bishiya. Tun ina kallonsu daga nesa-nesa har na fara daukar sanda ina shuna musu, sai su kai cafka koma su kanannade sandar. Ina son 'yan yaransu qanana abin sha'awa.
Har ta kai ta kawo idan ina bacci ina mafarkinsu muna wasa, haka zan yi ta qyaqyata dariya a cikin bacci, sai dai kawai in ji mahaifina yana ta girgiza ni yana tambaya ta dariyar me nake yi? Ban fada masa komai ba, ni dai daga gari ya waye sai in tafi da gudu wajensu. Mun yi shaquwar da na fara jin yarensu su ka fara jin nawa.
Madam Beatrice ta fara saka ni a mota ta na tafiya da ni cikin prison anan ofishinta yake, daga ofishinsa sai in shaga bangaren daurarru maza. Nan ma na yi abokai da dama, ina zama mu yi hira da su kuma in saurari hirarsu. Babban abokina a cikin daurarrrun sunansa Cindo, ya na da kirki kullum sai ya daga ni sama ya cilla ni. Ni kuma sai in yi masa alqawarin zan kawo masa kwakwar manja da yawa.
Ba na fitowa daga tsakar gidansu, sai Madam ta tashi daga aiki sannan ta sa a nemo ni mu tafi. Abincinsu ma na koyi ci tare da su har nake taya su kashe kwarkwata. Nake tambayarsu me yasa suke yin kwarkwata? Su ka ce basu da omon wanki da sabulu dan haka idan na tashi zuwa nake kwaso musu na gidanmu in kawo musu.
Ina jin dadin sauraren hirarsu sannan hirar ta yin tasiri a cikin zuciyata. Maganar dai ita ce fada, caka wuqa, kai sara da adda, duka ,sata, rashin tausayi