KISHIN BALBAL BOOK 2 HAUSA READ NOVELS BY JAMILA UMAR TANKO.doc

Author :  Jamila Umar Tanko Category :  Romance

Chapter   7 / 11

18K to 21K   out of 31.6K words

da rashin adalci. Ba da ni suke yi ba amma ina nade duk abinda suka ce dan haka na tashi da wata irin zuciya mai tauri bana tsoro bana tausayi.
Su Cindo su na yawan zuwa gidan Madam akai-akai su na yi mata aiki kamar noma da wanki. Anan ma tare nake yini fa su, sai su qaraso har gidanmu su na tsinci kwakwa tare da ma'aikacin da yake kula da su, ake zuwa da yake ga gida ga gida ne babu ko katangar da ta raba mu.
Babban tashin hankali da na fara gani shine ranar da Cindo ya hau bishiyar kwakwa zai tsinko sai da ya kai qarshe sannan ya ga qaton miciji ya fasa kai zai sare shi, anan ya fado ya kakkarye.
Na ga masifa, qato yana kuka yana ihu nima ina kuka ina ihu, sauran firsinoni su na kuka. Aka kira madam ta zo a gigice aka garzaya da shi asibiti daga nan ban sake ganinsa ba sai bayan shekaru masu yawa. Ya zo takanas saboda ya ganni, ya zama gurgu da sanduna biyu, muka sha murna da ganin juna har wa'adinsa ya qare na gidan yari a kwanciyar da yayi a asibiti dan haka garinsu ya zarce. Na yi kawar mutumin da yake wasa da ni yake cilla ni sama.
Babban rashin da na sake yi shine Janet mai sona wacce a kullum sai ta siyo min kayan dadi itama ashe sata take yiwa madam, dukka kudin nan da take yi min sayayya ba bata ake yi ba dauka take yi. Ranar da asirinta ya tonu aka yi mata dukan kawo wuqa aka sakata a mota zaa mayar da ita garinsu. Ina tsaye ina kallonta, tana kallona tana hawaye ina hawaye na ji gaba daya duniyar ta yi min zafi rashin ta a wajena babbar asara ce.
"Da wa zan yi hira? Da wa zan wasa? wacece za ta bani kayan dadi?" Tambayar da na yiwa zuciyata kenan.
Na dade ina kukan rashinsu sai na ji garin ya fita a raina. Hankalina ya kama gaba daya wajen wasa da mucizai. Sai kuma na ga wani babban wajen bautar ahlul kitabu an bude shi sabo a kusa da gidanmu. Kullum ina jiyo kida mai dadi kuma ina ganin yara sanye da riguna masu kyau da takalmi, an rufke kansu da ribon su na ta wucewa. Abin yana bani sha'awa sosai dan haka sai in tafi in tsaya ina kallonsu, har na fara zuwa bakin qofa ina leqawa daga nan na fara shiga ciki.
Da Madam Beatrice ta ganni a ciki sai ta ji dadi dan haka bata hana ni ba, bata fadawa mahaifina ba kuma balle ya hana ni.
Na kasance ina bautawa abinda suke bautawa, dan haka da wannan addini na budi ido kuma ya shiga cikin zuciyata sosai ina fahimtar abinda suke cewa kuma. Ina cikin yaran da aka zaba wadanda suka iya rawa dan haka ni ce a gaba.
Mahaifina yana ta waqar zainsakamni a makarantar boko da ta islamiyya amma kuma yana tsoron ya kai ni makaranta in an tashi in bata. Bai tashi ankara ba sai da abu ya yi nisa sosai, gaba daya ya ga na canja halayyata, babu maganar tausayi, jin qai a cikin lissafina, dan ina dukan yara kamar zan karya su idan suka zo tsintar kwakwa. Sannan ya ji kalamaina sun sauya daga maganar kisa sai daba wuqa, sai ya cika da mamaki da fargaba.
Dan haka ya dauko min malami dan ya koya min karatun qur'ani, sai na qi na dinga tafka musu da su akan ni addinina ba haka ya ce ba. Su ka ji wasu karatun da bai taba sanin a in da na koyo ba.
Da ya ga yadda nake wasa da mucizai sai ya yi mamaki ya rasa a ina na saba da su haka, kuma ya tabbatar ina jin yarensu su na jin nawa. Ya tsorata matuqa kuma a lokacin ya zage dantse dan ceto rayuwata amma ina ai ya makara. Ga ni taurin kai, ga gardama ga rashin tsoro, tabbas ya tabbatar akwai matsala.
Ya fadawa abokinsa halinda ake ciki sai ya bashi shawara akan ya auro matar da zata zauna da ni ta kula da ni, shine kadai mafita dan in daina fita ko ina.
Ya yarda da shawararsa ya auro wata bafillatana bazawara, amma fa muguwar gaske ce har ta fi Mummy tsana ta. Ta zo da wasu yaranta agololi guda uku, su suke shaqatawa a gidan ubana kuma abinda Daddy yake gudun dai shine ya faru ban sami wata kulawa ba, sai kyara.
Aka saka ni a makarantar boko ina zuwa ina dawowa tare da yaranta, da yake babu nisa. Ba na dawowa gida da wuri daga can sai in shiga wajen bautarmu na ji wa'azi. Idan na dawo gida sai ta yi min duka, amma gobe ma haka sai na tafi.
Islamiyya kuwa bana zuwa ko an tura mu, sai dai sauran su je. A haka na tsinci rayuwata bana qaunar bil-adama sai wadannan mucizai. Su ne kadai farin cikina ko a cikin bacci tare da mu ke shawagi a duniyarmu.
Babu wanda ya lura da cewa mucizan illa ne a tare da ni har sun zame min jiki, sun rikide sun zama aljanu sun shiga jikina. Kafin in gama firamare muka dawo Lagos aka saka ni a makarantar kwana ta firamare wacce yayana Imam Malik yake, a lokacin har ya kusa gama sakandire.
Sai a lokacin Imam Malik ya kula ya gane halinda nake ciki, bayan na hadu da yara inyamurai matsafa, mu ka dinga fafatawa dan nawa sun fi na su qarfi. Na gagari duk wani mugu a mafarki ko a ido biyu, ta kai ta kawo har wata sarauta aka bani, har ma da manyan makarantar su na jin tsorona. Sannan ya tabbatar ban taba shiga cikin musulmai ba ba na kiran kaina ma da musulma. Hankalinsa ya tashi ya tashin haiqan akaina baya raga min. Saboda tsoronsa ne ma na rage yin wasu abubuwan a makarantar na rashin ji da rashin tausayi da rashin Imani. Kin san waye shi?" Ta tambaye ni.

Na zabura na girgiza kai na ce " ban san shi ba."
Ta yi murmushi ta ce "shine mutumin nan da kika zo kika samu a kan teburin nan rannan, yana yi min tsawa. Shi kadai gare ni duk duniya, shine ya fi kowa damuwa da ni, ina na tafi ina na ke? Me na ci? Lafiyata da rashin lafiyata. Shine a kowanne hoto za ki ganmu tare, uwarmu daya ubanmu daya kuma kamarmu daya.
Ban dawo na gane musulumci ba sai da na gama sakandire lokacin yaya Imam Malik ya gama jami'a, ya fita da first class Jami'a ta riqe shi ta bashi aiki.
Da qarfin tsiya ya dauke ni ya kai ni qasar Sudan wata makarantar mata ta kwana, baa fita in ka shiga ka shiga kenan har tsawon shekaru biyu cur. Sai kin sauke, sauka mai tafe da hada, baa yin hutu, baa zuwa ziyara. Ban fito ba sai da na haddace qur'ani kuma addinin ya shiga jikina sosai.
Na so in dawo Nigeria in yi karatu amma ya qi amincewa ya zo ya nemo min jami'a ya ce in karanci shari'a law kasancewar karatun qur'anin da na yi zai taimaka min sosai wajen zama lauya a fanni musulumci."
Na tambaye ta yaya maganar aure?"
Ta harare ni, sai na ji gaba na ya fadi ta yi shiru zuwa wani lokaci mai tsawo sannan ta ci gaba da magana.
Ta ce " maganar aure bata gabana tabbas ban taba ji zan iya yin aure ba. Da farko babu wanda ya damu amma da na gama jami'a aka ga bana kula kowa sai aka fara damuwa. Ga ni da farin jini sosai a wajen maza a wajen mata ne ma dai gaskiya bana shiri da su.
An yi ta surutu an ce aljani ne ya aure ni, in har da gaske aljanin ya aure ni toh gara ma haka. Rayuwata a haka na fi jin farin ciki."
Na tambaya "Me ya kawo ki garin Bauchi kuma?"
Ta yi murmushi ta ce "na zo Bauchi ne don yin bautar qasa amma kuma ina so in zauna kusa da dangin mahaifina, saboda zumuncin ya yanke shi yayi nesa sannan ya hadu da mata mararsa kirki basa son danginsa su je. Mu jinin sarauta ne garin namu ne.
Wannan shine dalilin da ya sa kika ganni anan mahaifina da iyalansa dukka su na zaune a Abuja yanzu.
Matansa biyu dukka basa sona daga su har yaransu, dan haka ban damu da sai na je wajensu ba, sai dai in ta kama dole idan na shiga Abuja in shiga a tsatstsaye, mu gaisa. Idan kuma bana so ma in je sai in sami mahaifina a ofis dinsa mu yi maganar in yi tafiyata in sauka a hotel ko a gidan Imam Malik ko su na nan ko basa nan ina da mukullina.
Wannan shine labarin rayuwata."
Sai na ji ta bani tausayi matuqa na yi tagumi ina saurarenta. Na sake tambayarta "yaya labarin mahaifiyarki da dan uwanki Umar?"
Ta tabe baki ta ce "Dan uwana Umar ban taba haduwa da shi sai da na gama jami'a, haka ban ga mahaifiyata ba sai a lokacin su ka zo suka ganni daman shi Imam malik ya na zuwa . Umar yayi aure ya tara iyalai yayi karatu a turai kuma Daddy ne ya biya masa kudin karatunsa tun yaba yaro har ya gama.
Mamana ta sake yin aure acan har ta haifi wasu yaran da yawa. Ban damu da su ba, mahaifina kadai na sani shi kadai nake so.
Ki fada min ta yaya zan yafewa mutumin da ya munana min? Ta yaya zan bar Mummy da Aunty amarya da suka azbtar da ni? Kin san dole sai na rama, na yi musu irin abinda na yi miki naki ma nafila ne akan na su."
Na zazzare ido ina kallonta a tsorace.
Ta ci gaba da cewa " tun ina sakandire da aka yi hutu da qafafuwansu suka shigo har bangare na da zummar zasu yi min wulaqanci Hmmm sai da aka fitar da su.
Fatiti ki na nufin yin kanki kika ne kika zo dazu? A' a ni na kira ki dan in koya miki darasi. Yanzu next target dina shine Usman dinki."
Na zazzare ido na dafe qirji ina makerketa.
Ta ci gaba da cewa " na dade ina bibiyarsa akan abinda yayi min rannan da safe da yasa har mota ta kusa kade ni. Ya zo rannan a ko? Har kin gan shi anan gidan ai amma ba ni ba ni na kira shi ba da kansa ya zo.
Ya ce min ya zo ne akan ya bani haquri wai yana ta shiga bala'ai kala-kala shine yake ta tunanin shin wa ya taba zalumta, wa ya yiwa laifi ya batawa rai? Shine ya tuna da ni ya ce ya san ina gaba da shi kuma ya bata min rai, dan haka in yafe masa.Na yafe amma ba zan manta ba kuma sai na rama."
Hankalina ya tashi na shiga yi mata magiya na ce ni dai ta yi min duk abinda zata yi min amma ta yafewa Usman kada ta yi masa komai.
Ta yi dariya ta ce "yanzu fa na baki labarina, ban san soyayyar kowa ba tun ina yarinya sai mutane biyu yayana da babana. Mutane biyun da nake so ina yarinya ma tsautsayi ya hau kansu sun tafi sun bar ni. Kin san tsakanin miciji da mutum babu wani alkhairi sai kisa ko? Toh haka nake tsakanina da duk wanda ya taba ni bana yafiya."
Wasa-wasa matar nan ta riqe ni a gidanta anan na yi magruba da isha'i, bata bar ni na fito ba sai qarfe tara na dare bayan na barke mata da wani sabon babin kuka.
Ta ce zata bar ni in tafi saboda Haidar mai shan nono amma akan sharadi daya, kada in sake in fadawa kowa wannan abinda ya faru .
Na amince nan da nan babu musu, ta dauko mukulli ta bude, tana budewa na fito da gudu mayafina da takalma sai watso min ta yi ta mayar da qofarta ta rufe. Jikina yana rawa na sauko qasa gidan Safiya. Na samu qofar a bude kawai na fada cikin falon, a qasa akan kafet na fadi ina makerketa.
Hankalin Safiya ya tashi ta rirriqe ni ta gan ni babu dankwali, babu takalma, na kasa daukowa acan na barsu. Na kasa fada mata komai sai kuka da ihu nake.
Na ce mata wallahi yau ba zan iya kwana a gidana ba, tsoro nake ji a gidanta zan kwana.Ta dauka da wasa nake amma da ta tabbatar zazzabi ne a jikina ina kuka ina makerketa sai ta amince ta kai ni dakinta ni da yarana gaba daya hankalinsa ya tashi.
Ta nemo lambar Usman wacce na kira shi jiya ta kira ya qi amsawa. Sai qarfe goma sha daya mai gidanta ya dawo, ta shaida masa halinda nake ciki shine ya kira Usman din, ya tabbatar masa gani a gidansa bani da lafiya. Ko a kai min wayar mu yi magana? Amma Usman ya ce A ' a Allah Ya sawake ba sai mun yi magana ba a bar ni in huta in sha magani kawai.
Na tabbatar Usman yanzu bai damu da ni ba ga shi har ya qi yarda mu yi magana kuma bani da lafiya. Gani yake hadin baki ne dan kawai muka yi dan ya dawo.
Su na da magunguna kala-kala a gidan dan haka Dr.Isa ya bata magunguna ta kawo min, na karba na sha na kwanta. Na riqe hannun Safiya gam na ce kada ta tafi ta bar ni mutuwa zan yi.
Safiya ta dinga lallaba ni har qarfe daya na dare tana tare da ni, daga nan ta sulale ta gudu wajen mijinta.
Daga na rufe ido sai in ga mucizai, da bayan duniya, da kuma fuskar Mufidah. Ina ta addu'a ina kuka babban tashin hankalina ma da Usman ya juya min baya baya son ganina baya so ya ji muryata. Innalilahi wa inna ilaihi rajuun.
Ban rintsa ba sai da aka fara kiran sallar asuba, gari na wayewa yara suka tashe ni, na makara ma na tashi da sauri na yi sallah.
Ina kan abin sallah ina addua Allah Ya sassauta zuciyar Usman ya daina fushi da ni, sai ga Safiya ta shigo da sauri dauke da waya a hannunta ta miqa min.
Gami da cewa "ga mijinki yana nemanki."
Dadi ya kama ni na ce a raina na san ba zai iya bacci ba, tun da ya ji bani da lafiya.
Na karba da sauri ina murmushi na kashe murya na yi masa sallama.
Maimakon in ji muryar namiji sai na ji muryar mace, mahaifiyata ce ta ambaci sunana, sai na gaishe ta.
Na ji ta a cikin murna tana ta faraa ta ce " mun boye ba mu fada miki ba saboda Usman ya ce kada a fada miki hankalinki zai tashi. Mahaifinki ne fa ba lafiya, wannan ciwon cikin nasa dai da kika sani shine yayi tsanani, ya tashi sosai."
Na daka tsalle na miqe tsaye na dafe qirji na ce "innalilahi wa inna ilaihi rajuun wayyo Allah Babana."
Ta ce "dakata kada ki yi min wannan kwakwazon na ki. Ba ki ji ni ina faraa ba ne? In akwai matsala ai wayar ma ba zan iya amsawa ba. An yi masa aiki ya warke garau, naira dubu dari da ashirin Usman ya biya dukka."
Sai kawai na sulale na zauna a gefen gado, na ce "na shiga uku, Iyata na kashe kaina."
Ta tambaya "me ya faru? Na fada miki an yi aiki lafiya. Ki riqe mijinki, ki yi masa biyayya, ko bayan raina in kika

7 / 11