KISHIN BALBAL BOOK 2 HAUSA READ NOVELS BY JAMILA UMAR TANKO.doc

Author :  Jamila Umar Tanko Category :  Romance

Chapter   5 / 11

12K to 15K   out of 31.6K words

tunkaro inda nake sai ta tafi kan doguwar kujerarta daga tsaye ta fada 'rimm' sai ta fara bacci mai kama da suma.
Na tabbatar wannan abin ba na lafiya ba ne, daga nan maganar boka ta dinga dawo min da ya ce ba zan iya da Mufidah ba shu'uma ce, ya ce shi ma kansa ta fi qarfinsa asiri ba zai ci ta ba. Na tuna irin abubuwan da ta yi kwanaki har sai da Usman yayi mata rukiyya, sai na tabbatar yau na kawo kaina babu mai fitar da ni kuwa sai Allah.
Na zabura na tafi da gudu na murda qofa amma qofa a kulle, an kuma yasar da mukullin a qasa. Na yi wuqi-wuqi ina tunanin mafita, na ce ko ta windo zan haura in dira qasa? Na tu na ai akwai qarafe masu qwari ba zasu banqaru ba.
Wata murya na ji mai amsa kowa, ma'ana anan ake maganar amma kuma tana amsawa daga can nesa. Na waiwayo da sauri Mufidah na gani a cikin wani yanayi wanda ba zan iya kwatantawa ba, kamanninta sun juye, idanuwanta sun firfito sun yi manya-manya tana magana da labbanta amma muryar maza ce.
Ta ce " Ke Fatiti kin dame mu amma yau ita ce ranar qarshe da za ki sake takurawa godiyarmu. "
Ai tunda na ji an ce god'iya na san iyayen gidan ne wato jinnu, dan haka sai na daka tsalle na fadi a bakin kicin ina karkarwa, gaba daya addu'oin tsari da na qona aljanun da na iya a baya a yau dai na manta su.
Ta na zaune gashin kanta ya rufe mata fuska, kanta a sunkuye a qasa sai na ji wata guguwa ta taso, falon gaba daya ya hau girgiza ina ga dai an yaye rufin kwanon ne gaba daya, yadda na ga komai na kadawa.
Na tashi da gudu na bude labulen falon ina kurma ihu ko Allah zai sa su Tanimu su jiyo ni su kawo min dauki.
Wannan muryar dai mai amsa-kowa ita ce, ta ce min "ai a halin yanzu babu mai iya jinki saboda ba kya cikin duniya, yanzu a bayan duniya kike kin zo garinmu."
Hawaye da gumi da majina ban san wanda ya fi wani yawa ba, gaba daya fuskata ta yi sharkab. Ina neman ceto da agaji daga Rabbil samawati. Ashe jiya ban ga masifa yau ne ainahin masifar take.
A ka ci gaba da zayyano min manyan lefukan da na aikatawa god'iyarsu har da qazafin da na sha yi mata a waje Usman. Sai a lokacin su ka sanar min cewa ina da ciki kuma na 'ya mace shiyasa ma zasu sassauta min. Ban san ma ina da ciki ba amma dai ina ta jero musu godiya akan sassaucin da su ka yi min.
Bayan wannan muryar na sake jin muryoyi daban-daban, wannan ya zo yayi gargadi ya tafi, wancan ya zo yayi ya koma. Wasu maza wasu mata wasu matasa wasu tsofaffi. Kowa yana yi min gargadi akan in kyale Mufidah bata lissafi da ni, ba ta lissafi da mijina, ita ba biladama zata aura ba ma. Su ka bani labarin zuwana wajen boka kuma suka gargadi ni kada in qara taba Murjanatu Bibi qawarsu ce masoyiya. Na ce na yarda ayi ahakuri, a durqushe nake na daga hannayena sama na yi saranda. Amma kamar ma ba daga bakin Mufida maganar ke fitowa ba na ganta a kwance kamar mai bacci bata motsi.
Sai na ga kamar an yi wurgi da ni, saboda ni da nake bakin kicin sai na ganni a bayan wata kujera, na tabbatar an dirgo da ni cikin duniya. Sai na ga falon ya daidaita na daina jin qarar guguwa, iskar ta daina kadawa.
Na tashi na ga yadda na zama, takalma duk sun kama gabansu, mayafina a gefe, dankwalina a can nesa, dankunne daya ma ya bata. Na leqa fuskar Mufidah a hankali sai na ga ta bude ido ta dube ni, sai ta bude ido ta kalle sannan ta zabura ta tashi zaune kamar mai bacci da alama bata san duk wannan gumurzun da aka sha ba. Abin mamaki da na dubi agogo na ga har azahar ta yi qarfe biyu, ni da na shigo gidan da qarfe takwas da rabi na safe.
Ni da ita muka hau kallon kallo ta cika da mamaki da ganina a gidanta. Alamunta sun nuna tana tambayar zuciyarta me ya kawo ni gidanta?
Na je na har hado kayana na riqe a hannu, dan bani da nutsuwar da zan sassaka.
Na ce "Anti Mufidah bude min qofa zan tafi."
Ta yi shiru bata amsa min ba, can ta miqe ta nufi ciki dakinta ba jimawa ta fito da ta tashi fitowa sai gata dauke da qatuwar kwarya. Gabana ya na ta faduwa na ja da baya na tsaya ina qyarma in tsoron ko ni zaa saka a cikin kwaryar ko kuma kurwata.
Ta zo ta zauna ta ajiye kwaryar sai ga wasu mucizai manya-manya guda biyu ta saka daya a wuya dayan kuma ta dora akan cinyarta tana shafa su, su na ta maqalqale ta.
Na watsar da kayan hannuna na kurma ihu na haye kan dining table dinta na tsugunna, ina neman afuwa.
Ta dube ni ta yi dariya ta ce " zo ki taya ni wasa da abokaina. Au ashe ban taba baki labarin cewa na kware wajen yin wasa da miciji ba ko? Toh kinga abokaina shiyasa kullum nake gida bana shiga harkarki."
Ina fashe da kuka na ce "na gani amma dan Allah ki bude min qofa in fita na bar yara a gida su kadai qanana. In ci alfarmarsu, su na sonki ke ma kina sonsu."
Ta kwashe da dariya wata irin dariya wacce ba irin ta mutane ba.
Ta ce "au ki na tausayin yaran amma jiya kika tafi kika barsu? Kika ci kwalliya da takalmi silifas a qafa daya, daya qafar kika saka takalmi sau ciki ki tafi tun daga safe har dare? Yau ma kuma ba zasu ganki ba, sai gobe mu na nan daga safe har dare watakila ma mu kwana muna hira.
Kin san kidnapping ko? Na yi kidnapping dinki sai mijinki ya zo zai biya kudin fansa idan ya kasa biya kin zama baiwata. Amma fa ni bani na kawo ki ba ke kika shigo da qafarki har da takalma a qafarki kika taka min kan kafet din da nake sallah."
Na rusa kuka na ce "na ji dukka na san laifina ne amma ki yafe min. Dan Allah mufidah na daina ba zan sake shiga harkarki ba har duniya ta nade."
Ta kwashe da dariya ta ce " ni da ke fa mutu ka raba babu mai rabamu sai dai mutuwa, ai daga yau kam mun zama daya, kin zama ta mu."
Sai a lokacin na fara tunawa da wasu ayoyi na cikin qur'ani wanda ake tunkarar mugu da aljan. Na yi ta karantowa da qarfi ina yi ina kuka ina karkarwa, duk inda na cafka sai ta qarasa min .
Mucizan nan su na jikinta tana ta sunbatarsu. Tabbas na yarda shu'uma ce asirin ma ba zai ci ta ba.
Mufidah ta fara magana da su wani lokacin ta yi wani yare, ta yi musu da Hausa, ko ta yi turanci, sai ta yi musu fito ko busa da nski da kunnuwanta ko ta yi shuuu da baki kamar wacce ta ci yaji. Su ma mucizan su na yi mata fiton kenan tana jin yarensu su na jin na ta.
Wannan karon sakinsu ta yi a tsakar falon su na ta shawagi, tuni na haye kan Dining table daga nan na kama windo na tsaya har sai da na ballo mata da labule.
Dariya take ta gyagyatawa kamar cikinta zai fashe. In ta ce su yi kwana sai su yi kwana idan ta ce su dawo wajenta sai su dawo, idan ta ce su shiga kicin sai su shiga.
Na yi ihu da magiya har sai da muryarta ta disashe, matar nan imanina kadan ne.Ba ta ji tausayina ba ko kadan, sai da taga na kusa shidewa zan suma sannan ta kira su suka koma wajenta. Dan fa ta ce da daya ya hau kan windon da nake, har ya fara hawa.
Daga qarshe ta ce su shiga cikin kwaryarsu su kwanta suka shiga suka kwanta luf.
Sannan ta dube ni ta ce in sauko sun yi bacci. Na sauko yayin da hannuwana da qafafuwana dukka sun kunbura sun yi jajawur.
Ta ce in shiga bandaki in yi alwallah in yi sallah, ga shi har la'asar ta yi ita hutun sallah take, kada alhakin rashin sallata ya kamata.
Na ce nima bana salla hutu nake. Saboda fatana ta bude min qofa in fita kawai.
Ta girgiza kai ta ce "mafita daya ki yi duk abinda na ce ki yi, idan kina yi min gardama wallahi sai na cika falon nan da mucizai ga su can cikin daki. Na san kina sallah ki wuce ban dakin falo ki yi alwallah ga sallaya da hijab ki yi sallah sai mu dora daga inda muka tsaya."
Na tafi qafafuwanta sun kasa tsayuwa waje daya sai rawa suke saboda jigata. Na leqa bandakin na ga babu muciji, daman fitsari ya cika min mara na yi ta addua sannan na tsugunna na kama ruwa, na yi alwalla ban sani ba ma ko na yi daidai oho. Na fito ta bani hijab na saka na fara salla ina yi ina waiwaye dan kada ta sakar min miciji.
Raka'oin ma ban kirga ba ina ta yi ina sakewa har sai da ta ce min sun isa. Na daga hannu sama ina ta karanto "la'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minal zalumin" a bayyane ita kuwa tana amsa min da Amin. Muka shafa.
Na sake zuwa gefenta amma daga nesa nesa durqusa ina magiya akan ta bar ni in tafi gidana.
Ta ce komai ya wuce amma bata da 'yan taya hira nice zan taya ta zama. Kuma tana jin yunwa abincin data dafa, ni na sa ya qone dazu dan haka in shiga kicin mu yi girki tare.
Na fasa kuka na ce "wallahi ban iya girki ba"
Ta ce zata koya min yadda ake farfesu da naman miciji. Na kula duk wata kalma da zata tayar min da hankali ita take fada min in ba haka ba ai ta sani ta tayaya zan ci naman miciji. Na tabbatar matar nan yau ba zata bari in tafi ba sai na saddaqar da cewa kiyamata ta zo dan haka na yi sabuwar kalmar shahada na dora da istigfari.
Fargaba daya ita ce zan mutu mijina yana fushi da ni. Kuma ban yi masa sallama ba ban yi sallama da yarana ba. Na san ko da na fito daga gidan nan a raye, da alama a haukace zan fito ba zan qara yin hankali ba kuma. Na ga abinda ido bai taba gani ba, an kai ni inda bil-adama bai taba zuwa ba.
Da alama wannan matar ko a cikin matsafan ma babba ce, kungiyarsu ba a qasar nan kadai ta tsaya ba ta hada da matsafan turai da china da India.
A gaba ta sakani muka shiga kicin ta bani kayan miya da albasa ta ce in gyara mata, hannuna na rawa ina yankawa, dan rainin hankali wai hira take yi min, har da dafa kafadata tana min magana mai dadi.
Ta ce " Fatiti shin sanda na zo ganin gidan nan ni da Bar. Ibrahim abokina ba ke ce kika dage akan sai na zauna a sama kusa da ke ba? Safiya ta dage sai na zauna a qasa tare da ita, kika jawo hannuna muka hau sama kika ce anan zan zauna ba?"
Na gyada kai na ce " an yi haka."
Ta ce "me yasa daga baya kika tsane ni, kika min qazafi, kika harhada min tuggu, har ki na fatan in tashi?"
Na yi shiru wannan karon wata qatuwar wuqa naga ta daga sama kamar zata caka min kamar kuma zata yanka naman da ke hannunta.
Na zabura na ce "na dauka ke matar aure ce wannan mutumin mijinki ne, shine na so ki zauna kusa da ni ki koya min yadda zan yi tattalin mijina dan na ganki a waye. Daga baya na gane baki da aure sai hankalina ya tashi."
Ta gyada kai ta ce "na zargi hakan nima. Amma me yasa za ki tsani mace dan bata da miji? Allah ne bai bata ba. Ita bata taba nuna alamar tana son mijinki ba kuma. Shin baki yarda da kanki ba ne kina ganin zai fi sonta da ne?"
Na yi wuqi-wuqi da ido na kasa amsa mata. Ta bani balander ta ce in markada kayan miya sannan ta hada ni da yankan tafarnuwa, gashi bana son warin tafarnuwa haka dai na dinga yunkurin amai na dage sai da na kammala.
Ta na jero min tambayoyi akan Usman wadanda ban isa in qi amsawa ba, idan na yi shiru sai ta kalli kwaryar mucizan nan da suke falo daga nan sai in bude baki.
Ta na tambayata ne wanne dadin zama na ji da mijin da yake marina da har nake kishinsa? Saboda fari ne tas? Dan gayu? Dan boko?"
A dole na ce mata "eh hakan ne yasa?"
Ta sake maimaitawa ta ce "sai dai ni baya burge ni kuma ma na ji na tsane shi saboda yana da girman kai da ji da kai."
"Hamdala na yi a cikin zuciyata, na ji hankalina ya kwanta.
Ta dafa mana fried rice, na ce ba zan ci ba ta ce ai dole ne ba roqona take yi ba. Muka hau kan dining table muna ci gami da juice da yankakkun fruits. Yayi dadi abinci amma na kasa tantance me nake turawa ma, daman akwai tsohuwar yunwa a jikina tun ta jiya. Kuma ta tabbatar min sai na cinye tas idan ina so in bar gidanta.
Ta na ci tana kallona fuskarta cike da murmushi, ta sa hannu ta shafa gefen kumatuna ta ce Allah sarki duk kin kode, fuskarki ta yi jajawur saboda kuka. Ki na tsoron mutuwa ne? Na zaci kin sadaukar da rankin gaba daya wajen yaqin kwatar mijinki. Ga ki mai kyau dake amma ki na ta zalumtar rayuwarki, kin qi ki hutawa zuciyarka. Kin san da cewa tunda na ganki farkon ganina da ke na ji ina so mu yi qawance da ke? Saboda kina da fara'a da wayo da iya hira da Jan mutum a jiki. Sai daga baya na ga ashe duk ba haka kike ba. Na shaqu da yaranki ina sonsu, Haidar in ya ganni sai ya kwanta a jikina yayi shiru in rungume shi sai in ji sanyi a raina amma gaba daya kika raba mu. Fatiti ki na nufin zan yafe miki yadda kika cutar da zuciyata akan abinda take so?"
Na quara mata ido ba tare da na san amsar da zan bata ba, tabbas ta nuna min qauna ni da yarana a dole na bar ta.
Ta surnanao da hawaye ta ce "da kin san labarina da za ki gane cewa a cikin tsarina bana qawance da bil-adama saboda irin wannan matsalar ta ku."
Kawai na ji na kware saboda firgice, sai ta taso ta dafa ni tana dukan bayana ta bani ruwa na sha.
Ni dai gaba daya na sake firgita dan na ji tana ambaton bil-adama kuma tana killace kanta daga mu.
Na tamabaya cikin gigita "ke mutum ce ko aljana? A ina nake yanzu? A bayan duniya ko a cikin duniya?"
Ta yi dariya har da kyakyawa ta ce " a ada ni ba mutum.ba ce ina tunanin yanzu na zama mutum. Dazu bakya cikin duniya amma yanzu kin dawo cikinta."
Na fada a bayyane "innalillahi wa inna ilaihi rajuun Ya Rabbi ka dauki raina akan in ci gaba

5 / 11