KISHIN BALBAL BOOK 2 HAUSA READ NOVELS BY JAMILA UMAR TANKO.doc

Author :  Jamila Umar Tanko Category :  Romance

Chapter   2 / 11

3K to 6K   out of 31.6K words

duniya ta nade ya rabu da Murjanatu Bibi saboda wulaqancin da ta yi masa ba zai taba mantawa ba. Na barke da kuka ina karkarwa da kyar na samu ya sake ni ya yi cilli da ni sai gani akan wata kujera na kasa ganewa ko waccece ma a cikin kujerun. 2 seater ce, ko 1 seater, ko kuwa 3 seater? Oho. Na ga masifa na ga abinda ban taba gani ba na tashin hankali a wajen Usman.
Ya suri mukulin motarsa ya fice a fusace ban qara ganinsa ba sai qarfe goma sha biyu na dare. Ya iske ni a zaune a falo na yi kuka har na gaji na kode na jeme na zaci zai ji tausayina kamar yadda ya saba amma ya harare ni ya wuce.
Ya na shiga dakinsa sai ya ji na riqo shi ta baya, ina kuka ina bashi haquri na ce me nayi masa ya tsane ni.
Ya ce ba ni ya tsana ba Murjanatu ya tsana da Mufidah kuma na qi rabuwa da su. Da kyar na samu ya huce shima ya bani hakuri akan baqaqen maganganun da ya fada min.
Na samu dai ya ci abinci yayi wanka muka kwanta. Mun sha hira amma cikin tashin hankali yake magana ya ce bashi da kudi bashi da in da zai samo kudi, an yiwa yara hutun makaranta yana ganin har su koma ba zai iya hada kudin makaranta ba. Ya ce ga maganar haya, ta fi wata uku da qarewa ga Godwin har ya fara yi masa waya.
Na ce ai da bai turawa Umma kudin nan dukka ba da ya rage kudin haya. Ya ce ko da wasa baya so tsofaffin nan su ji labarin baya aiki hawan jikinsu zai tashi ga bikin 'yar auta ya kusa Umma ta tashi hankalin ta.
Bacci kadan yayi na ga ya tashi yana ta sallah yana kai kukansa wajen Allah mai kowa mai komai.
Na shiga damuwa sosai nima musamman da na tashi da safe na ga kicin dina a share babu wani abin kirki komai ya kusa qarewa. Ina ta jiyo qamshin soye-soye daga gidan Safiya da Umma musamman daga kicin din Mufidah domin daga dukkan alamu ta yi girki musamman idan wannan baqon nata zai zo, ta dinga soyawa tana dafawa, kayan alatu kala-kala.
Usman ya iske ni a kicin na dama custard powder babu madarar kirki, jikina a sanyaye. Ya lura da halinda nake ciki sai ya shiga yi min nasiha ya na lallashina. A haka dai muka sha ya ce bari ya fita ya zagaya ya gani. Ni da shi abin tausayi ya fice na ci gaba da harhade harden abinda zamu ci.
Umma ce ta shigo gidana mun dade muna hira, mata mai lura da hangan nesa ashe ta san duk halinda mu ke ciki. Ta dauko kudi mai yawa da leda a cike da biskit da alewa da pampers din yara. Har hawaye na yi dan murna ina ta godiya.
Sai ta dauko min maganar Safiya ta ce ta lura ba ma tare yanzu amma kuma bata tsaya bincike ba kawai ta yi min nasiha akan mu yi haquri da juna rayuwar ma nawa take.
Na ce ma ta na gode, ta tashi zata tafi sai na raka ta. Maimakon ta sauka sai naga ta nufi qofar gidan Mufidah. Kawai sai na ji wani maqaqi da daci ya rokare min qahon zuciyata.
Raina ya baci na tambaye ta me zata yi a gidan Mufidah? Da alama ta yi mamaki da wannan tambayar ta kalle ni ya yi shiru na wani lokaci sannan ta yi murmushi ta ce "haqqin maqwabtaka ne, ta yi tafiya ta dade ya kamata in ta dawo a yi mata sannu da zuwa ko?"
Na tambaya cike da zumudi "ina ta je?"
Ta ce " Amurika."
Zan sake tambaya sai ga Mufidah ta bayyana cikin wasu kaya riga da wando masu kyau, baqaqe ta tufke gashinta babu kallabi akanta. Har ta fara harare- harare da yake idanuwanta akaina suka dira sai daga baya ta lura da Umma, wani lallausan murmushi ta sakar mata gami da rungume ta cike da murna.
Na yi mamakin ta in da suka saba da juna haka. Tabbas akwai munafukai da 'yan shishshigi a duniya. Su Umma an cusa kai.
Na harare su sama da qasa na watsar na tura qofata na shige na ci gaba da leqensu ta jikin hudar qofa, suka shige ciki Umma ta dade sosai sannan ta fito. Ina tsaye ina kallonsu
Mufidah ta rako ta har da wata galleyar leda a hannun Umma daga dukkan alamu tsaraba ta bata amma ni da na shiga gidan ai bata bani ba, saboda ta tsane ni kamar yadda na tsane ta.
Wandon nan ya dame ta haka rigar ma tsamammiya ce dukka aurar jikinta kaf sun bayyana amma dan wautar Umma a haka ta bari zata raka ta har qasa. In ta yi kicibus da mijinta fa? Qaryar namiji ya ga mace irin Mufidah ya ce bai hadiye yawu ba sai dai idan yana da matsala ne kuma.
Na koma ta windo na ci gaba da leqensu. Gidan Umma yana qasan gidana, gidan Safiya ne a qasan gidan Mufidah. Dan haka bata shiga ba anan su ka tsaya suka bude sabuwar hira.
Tabbas na ji na fara tsanar Umma duk da daman ba wani shaquwa muka yi ba amma dole in yi takatsamtsam da ita.
Motar Usman ce ta danno kai cikin gidan, na tabbatar zaa hadu kuwa. Sai na ji hankalina ya tashi gaba daya, na yi kamar zan fito in taro shi amma yadda na ga ya harari in da take ya kawar da kai sai na ji dadi. Na ji muryar Umma ta gaishe shi amma ba su yi magana da Mufidah ba dan bana hango su sosai.
Ya shigo falo a sanyaye da alama ya na cikin damuwa bai samo komai ba. Ya zauna ya yi tagumi, gaba daya ya fara fita hayyacinsa babu gayun nan, farinsa ma ya fara disashewa.
Wake da shinkafa da mai da yaji na dafa, yara sun ci na su sai nawa da na sa. Na zubo na kawo gabansa ya kalla sai ya girgiza kai alamar tausayin kanmu da kanmu.
Mu na ci, ni ce mai qirqiro hirar amma kamar baya son yin magana. Na nuna masa kudin da Umma ta bani naira dubu biyar shine fa na ga ya fara walwala. Ya yi mata addua sosai amma kuma ya ci gaba da tuhuma ta yana zargin ko ni na fada mata halinda muke ciki.Na tabbatar masa ban fada ba, kawai dai ta lura ne ta kawo min.
Ya ce " wato har mun fara zama abin tausayi an fara taimaka mana. Amma abin tausayin ma yana nan gaba in ba Allah ne ya kiyaye ba."
Na dube shi cikin fargaba na tambaya "kamar yaya?"
Ya yi jugum sannan ya ci gaba da cewa " ranar da zaa zo a yi mana watsi da kaya ba mu biya kudin haya ba da ranar da yarana zasu daina karatu da kuma ranar da zamu rasa loma daya ta abinci. Allah Ya kiyaye. Kin ga amfanin yin karatun mace da iya sana'arta ko? Fatiti lokaci ya zo da kike girbar abinda kika shuka, yanzu ko mutuwa na yi a haka za ki yi ta fama da yaranki saboda baki san komai ba a rayuwarki, kin gina ta akan kishi kadai ki zargi waccan da tana son mijinki, ki zagi waccan."
Na yi cilli da cokali na hau bambamin fada na ce ai ba ni na dora masa talauci ba da zai zarge ni, anan dai hirar ta watse, ya shiga daki ya rufe kansa.
Rayuwa babu dadi kowannemu yana cikin damuwa. Gadon dakinsa da kujerun falo da a dining table ya ce in kira dilaliya ta zo ta siya.
Innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Da farko na qi yarda amma da na ji wuya babu cin yau balle na gobe sai na amince, cikin dare aka zo aka kwasa. Ko kudin bai kalla ba ya ce gobe in je kasuwa in siyo kayan abinci.
Ya siyar da babbar wayarsa ya sayi qarama yana amfani da kudin wajen zuba mai a mota yana fita yana dan bubbugawa. Wataran ya samo kadan wataran babu, shima bai iya kasuwanci ba aikin bankin nan ne kawai madogararsa.
Rannan da daddare muna zaune muna cin tuwo da miyar kuka babu nama sai dai tasha wake, da ni da shi da yara gaba daya. Sannan an yanke mana wuatar lantarki sabida mun yi watann bamu biya ba, sai hasken kyandir.
Wayarsa ce take ta ruri bai dauka ba, na dubi wayar babu suna sai lamba. Ya kalle ni na kalle shi, ya tabbatar na zargi wani abu.
Bayan mun kammala ya ce yara su je su wanke hannu su kwanta. Tun kafin in yi magana ma ya fara bani labarin boyayyen al'amarin da ya dade yana boyewa.
Ya murtike fuska ya fara magana" ba kowa ke kira na ba sai Jalilah, maganar gaskiya sun bani aron kudin nan ne saboda wata manufa. Jalilah ta qi auren kowa ta ce sai ni, sai na ga kamar su na so su yi amfani da qarfin dukiya su saye ni su dinga juya ni ne.
A halin yanzu dai na fada musu ba zan iya aurenta ba saboda wasu dalilai amma kuma sun fara nuna min in ba zan aure ta ba in dawo musu da kudinsu, sun bani wata daya kacal ko in hadu da bacin rai."
Ina zaune amma na sankare na kasa magana ba dan a duhu ba ne da ya ga yadda na jiqe sharkab da gumi. Tashin hankalin da ban taba ji ba shine ya rikito min. Kafin in tanka masa sai da na tashi na zagaya bandaki saboda cikina ya karta.
Tabbas ajalina ya tunkaro ni kenan, tunda in har Usman ya shiga takurar da ya rasa yadda zai yi, ya amsa musu da cewa zai aure ta ni kuma zan mutu.
Na dawo na iske shi ya yi tagumi ga ruwan wanke hannu a roba amma ya kasa wankewa.
Saqonni ne suke ta shigowa cikin wayarsa babu adadi bai bude ba balle ya karanta, na yi karbi hali na dauki wayar na bude na fara karantawa. Sakonnin daga Jalilah ne tana mai bashi haquri akan maganar da 'yan gidansu suka fada masa ita dai tana son koda bashi da komai, ya zo a daura auren kawai.
'Dif' na ga kamar na daina gani saboda munin sakonnin. Na yi wurgar da wayar gefe cikin rawar murya na ce " me yasa ka ce ba zaka iya aurenta ba?"
Kai tsaye ya bani amsa "saboda bana sonta, ban taba jin ina sonta ba. Kuma basu da hujjar da zasu yi min dole saboda ina talaka, ni mutum ne na bawa ba"
Eh wannan amsar ta wanke shi a wajena, kuma na ji dadinta.
Na sake tambaya "yanzu a ina za ka samo musu kudinsu ka basu, kudi har naira miliyan daya?"
Ya girgiza kai ya ce "babu in da zan samu, na yarda su yi min dukka hukuncin da zasu iya yi min ko da kisa ne."
Ya riqe hannuna yana hawaye ya ci gaba da cewa "Fatiti ke nake tausayi amma na fi tausayin yaran nan ko da mutuwa na yi dangina kakaf babu mai abin hannun da halin da zai iya riqe ku. Ban gina muku gidan da za ku zauna ba ko a kano. Amma Alhamdulullah gidan mahaifina babba ne za mu iya komawa mu zauna a wannan dakin da kika fara zama kina amarya kafin na dawo dake Bauchi. "
Na zabura na ce " kamar yaya? Daki daya ciki da falo babu bandaki da kicin sai na tsakar gida, shine zan je in zauna ni da kai da yara hudu? Zaman kISHIN BAL-BAL zan koma mu ci gaba da yi ni da su sahura da Aliya matan yayyanka?"
"KISHIN BAL-BAL " menene kishin bal bal?" Usman ya maimaita.
Na ce kishin bal-bal shine kishi tsakanin facaloli wannan kishin ya fi kishin kishiya da kishiya zafi. Ka manta fadan da muka sha yi a baya kafin in dawo Bauchi komai nawa sai da suka farfasa min dan hassada balle yanzu yaransu sun girma. Gaskiya ba zan iya kishin bal-bal ba."
Usman yayi shiru can ya dago da jajayen idanuwansa ya dube ni ya ce "ina fada miki ne in har aka kama ni aka daure, ki koma gida ki ci gaba da haquri, daga dukkan alamu sai na yi zaman kurkuku."
Na zabura na miqe tsaye na dora hannu aka na fasa kuka ina ta kai kawo a tsakiyar falo ina surutai. Dakyar Usman ya lallashe ni na dawo na zauna kuka dai ya ci qarfinmu daga ni har shi. Rayuwarmu kuwa sai yadda Allah Ya yi da mu.

*** *** ***
Usman ya ci gaba da samun matsala ga takura da barazana daga wajen her excellency, musamman ma da ta ga qanwarta 'yar autarsu Jallah ta shiga wani hali irin na damuwa a sandiyyar ciwon so. Ta na tsoron kada ta rasa ta dan haka ta tsani Usman. Wayar safe daban ta rana daban ta sha alwashin sai ta wulaqanta shi in bai dawo musu da kudinsu ba.
Amma na tabbatar ta tafka babban kuskure ba zata taba samun Usman ta wannan hanyar ba. Dan bashi da kwadayi kuma ba zai taba aikata abinda baya so a cikin zucciyarsa ba, baya daukar wulaqanci kuma.
Kullum sai ya fita nema amma bai fada min in da yake zuwa ba, yakan samo mana na cefane naira dubu biyu ko dubu uku ma in an dace. Amma fa muna shan matsi daga wajen Godwin maganar kudin haya kullum haqurin nan muke bayarwa mun san ya fi mu gaskiya dan mun qara watanni bakwai ba mu biya ba.
Makarantar yara kuwa an koma kuma sabon aji har sun fara zuwa aka kore su.
Bayan magruba na fito zan sauko qasa in kwaso kayan shanya sai kawai na ga qofar falon Mufidah a bude sai ga Usman dina muraran a zaune akan kujera yana magana da Mufidah, su na fuskantar juna. Ita bata magana ta dora qafa daya kan daya tana danna waya. Sanye take da wani hadden leshi ja da baqi, kanta babu dankwali.
" Me nake gani, kamar Usman dina. Ko dai gezau idanuwana suke yi min ne?" Zuciyata ta tambayi kanta da kanta yayin da ta fara dukan uku-uku, gumi ya keto min.
Ban san sanda na afka gidan ba, na tsaya a kansu ina girgiza kamar 'yar tauri. Da alama Usman ya razana ya yi qiri-qiri yana kallona amma ita ko gogiyar ko a jikinta, bata ma kalle ni ba.
Ya yi cimak ya miqe kafin in tara masa mutane. Kalmar da ya fada ta qarshe ita ce "na gode."
Ita kuma ta ce "babu damuwa, sai anjima."
Na saka shi a gaba muka fito kai tsaye zuwa falonmu. Na mayar da qofa na datse na kama qugu ina girgiza na ce " talauci yayi talauci, me ka shiga yi gidan waccan mutsiyaciyar? Neman rance ko neman iri?"
Ya ajiye mukulli yayi tsaki ya wuce cikin dakinsa a fusace. Anan ne aka kwashi 'yan kallon dan tun baya kula ni har ya gaji ya tanka min.
Har yanzu dai babu amsa daya da ya fada min ta dalilinsa na shiga gidanta.
Kwana da kwanaki mu na zaman 'yar tsama da shi. Ina ta fushi shima yana ta fushi. Dan haka ban san hidimar da yake ciki ba haka nima, kudin cefane take ajiyewa ni kuma in ajiye masa abinci wataran ya ci wataran ya qi ci. Gaba daya zuciyata ta kasa kwanciya, ga Jalilah ga Mufidah ga Minat, na daina yarda da shi.

2 / 11