Author : Jamila Umar Tanko Category : Romance
sabawa Usman ban yafe miki ba. Yaron kirki gaba daya kudin shi ya biya, a lokacin da 'ya'yan na cikinmu suka kasa hada kudin nan wata da watanni ana ta fada ana maganar daki-daki sai an hado daidai da daidai alhali wasu basu da shi basu da dalilinsa."
Iyata ta fashe da kukan dadi, yayin da na fashe da kukan nadama. Cikin kuka na ce a bawa Usman waya. Ya karba, da na yi sallama sai ya amsa kafin in ce wani abu sai ya ce zan kira ki, ya kashe wayar.
Daman wayar Dakta ce zai tafi aiki yana jira, Safiya na tsaye a kaina tana kallona ina kuka. Na miqa mata wayar na ce ta sake kira min Usman, ta yi ta kira amma ya qi amsawa.
Na ce ba damuwa ta kai masa wayarsa kada mu bata masa lokaci.
Yara suka baibaye su na kallona jikinsu yayi sanyi su na tambayata ko Abbasu ne bashi da lafiya.
Na sharce hawaye na ce "A a Baban kano ne amma ya ji sauqi.
Su ka ce "tunda bama zuwa makaranta mu tafi kano mu dubo shi kawai."
Na ce "tafiya ai ya zama dole mu je."
Na tattaro kansu na ce mu tafi gida mu yi wanka. Safiya ce ta shigo bayan ta sallami Dakta da mas'ab sun tafi.Ta dafa kafadata cike da tausayina don hawayen da suke zuba sun kasa tsayawa.
Ta ce "dole akwai matsala amma ki na boye min tsakaninki da Usman, ba haka kuke ba. Me yake faruwa ne? Duk a dalilin rashin aikin ne?"
Na girgiza kai na ce mata ba komai Babana ne ba lafiya shiyasa nake kuka.
Ta yi masa addu'a sannan ta ce in fito falo mu ci abinci, ta dafa da mu. Na san babu abinda zan bawa yara idan ma mun je gidan dan haka muka bi ta falo. Dankali da wainar kwai da shayi mai kauri ta hada mana,. Wai! yaushe rabon duniya da ayyaraye? Mun jima ba mu ga irin wannan ba, yaran nan sai da suka.kunyata ni kamar 'yayan yunwa suka dinga santi su na wawaso. Mu ka ci muka qoshi duk da ni na kasa ci dakyar na hadiye lauma biyu.
Safiya dai ta yi ta tambaya har ta gaji na qi fada mata komai. Tayi-tayi ta ji ina na je jiya amma na qi fada.
Ta ce kuma ai sama na hau ba ta ga saukowata ba. Har Tanimu ta tambaya ya ce bai ga fitata ba kuma ta je saman ta dinga buga qofar falona shiru.
Na ji gabana ya yanke ya fadi sai na zabura na miqe na ja yarana muka hau sama da sauri, ta na ta so ta raka ni har sama na qi jiranta dan bana so ta ga kayana a zube a qasa a bakin qofar gidan Mufidah, takalma da mayafi. Sai hijabinta ma na saka da silifas dinta na hau sama.
Safiya dai kallona take kallon da take yi min ya fi kama da kallon tabbabiya take yi min. Koma dai yaya ta dauke ni hakan nake na yarda wallahi. Hakan ne ma na haukace daman ai na fada ko na fito daga gidan Mufidah da raina tabbas a haukace zan fito.Na sami takalmana da gyalena a yashe a qasa.
Yara su ka tafi da gudu su ka dauka su na cewa "Lah Mama ga mayafinki da dankwali da takalmanki a qofar gidan Aunty Mufidah anan ki ka manta su ashe."
Hannuna na rawa na bude gidana da sauri tsoro nake dan kada ta fito ta ganni. Mu ka afka cikin gida da sauri na kulle qofar. Ina dire Haidar a tsakar falo sai na shiga daki na rufe kaina na fasa kuka na dora hannu akai na yi zaman 'yan bori a qasa.
Na fada a bayyane "Allah sarki Usman ashe saboda Babana ya zama direba yana daukan fasinjoji dan ya tara kudin da zaa yi masa aiki.
Da wanne ido zan kalli Usman? Me zan ce masa? Ashe duk saboda ni ya kasa hutawa dare da rana yana fita yana kwadago yana tara kudin da zaa yiwa mahaifina aiki, amma ina can ina zarginsa."
Na yi kuka har na gaji sannan na tashi na yiwa yara wanka nima na yi na saka wata qaramar riga marar nauyi mai gajeren hannu. Na zo falo na kwanta akan kafet ina bacci marar dadi mai kama da suma ko bugun aljanu.
Na ji yara su na tashina su na cewa yunwa suke ji. Sai na ji gabana ya fadi na shiga tunanin abinda zan dafa musu. Na miqe tsaye ina ta layi, na je daki na dauko naira dubu daya na miqawa Ahmad na ce ya kaiwa Tanimu ya ce ya siyo min kayan miya, kada ya tsaya a ko ina idan ya kai ya shigo gida.
Ya karba ya bude qofa zai fita, ya na bude qofar falo sai muka yi ido hudu da Godwin shi da wasu maza guda uku. Abinka da marar sallah kai tsaye ya fado min gida, su ma su na biye da shi a baya suka shigo ba tare da sun taaya na basu izini ba. Na yi firgigit na tashi zaune ina tambayarsu ko lafiya su ka fado min ba tare da maza?
Cikin gadara ya ce "ai ku yanzu ba 'yan haya ba ne ku na zama ne kawai kafin a samu masu shiga, yanzu ga masu shiga an samu domin watanni takwas ku ka qara. Kullum labari daya kuke fada zaa biya-zaa biya.
Tashin hankali mai tsanani ya rufto min sai na ji tamkar baa cikin wannan duniyar nake ba, na tafi duniyar jiya ta su Mufidah.
Na tashi da sauri na shiga daki na dauko hijabina na saka sannan na fito jikina yana ta rawa, gumi yana ta keto min na rasa yadda zan yi, ga shi babu wayar da zan kira Usman.
Na fito da sauri na cewa Godwin ya bari in sauka qasa in ari waya in kira mijina baya gari.
Godwin ya ce "kawai dakunan zamu gani, ki raka mu ciki ya gani idan yayi masa zamu baku sati daya kacal ku tashi, ko kuma kotu ta zo ta yi muku watsi da kaya.
Mufida ce ta bayyana cikin kayan lauya da alama daga wajen aiki take, tana qoqarin bude gidanta ta shiga sai ta hango Godwin, da ni da maza guda uku, mun yi carko-carko da yake falon a bude yake wanwar. Sai kuma ta lura da cewa kuka nake.
Godwin ya kwalla kiran sunanta ya ce "Bar. Mufidah zo mana, dan ki zama shaida."
Ta shigo a sanyaye ta na kallon falon da alama bata san mun kwashe komai ba. Ta tambaya cikin sanyin murya "me yake faruwa ne anan?"
Godwin ya gabatar da abokan aikinsa lauyoyi guda biyu, ya nuna dayan ya ce sabon maqwabcinta ne shine zai kama wannan gidan.
Wannan karon Mufidah kallona ta yi da sauri cikin dimuwa da rashin fahimta.
Ta yi murmushi sannan ta tambaye ni ta ce "saboda abinda ya faru jiya shine za ki tashi? Amma kuma kamar kin dade da fara hada kaya dan na ga babu komai a gidan."
Amma kuma kukan da ta ga ina yi ya bata mamaki. Ta sake tambaya cikin daga murya "ku fada min abinda yake faruwa anan ?"
Godwin ya ce " basu biya haya ba watanni takwas suka qara, kullum su na magiya ayi haquri, na gaji na samu mai shiga. Na basu sati daya su tashi kawai, yau zan karbi kudin wannan."
Ta dube ni ta tambaya ta ce "haka ne?"
Na sharce hawaye na ce "ya tafi Kano nemo kudin hayar, baya aiki yanzu.Amma Godwin kai kanka ka san Usman baya maka wasa da kudin haya."
Mufida ta fusata ta kalli Godwin ta ce "A a wannan bai kamata ba Godwin. Ina ruwan matar gida da maganar kudin haya? Ka jira mijinta ya dawo mana kuma ba ku da lasisin da za ku fado mata gida kawai ku ce kun zo da me ganin gida."
Nan fa na ga an rikice ana ta zubo dogayen turanci tsakanin lauyoyi uku ana ta kiran section na dari da hasim da section na dari biyu da hamsim na kudin sharia. Wannan mata akwai kwakwalwa sai da ta qure su gaba daya ta yi musu fata-fata.
Ta ma juya maganar gaba daya, laifi ya koma kansu kuma ta tabbatar musu sai ta kai su qara hukumarsu ta lauyoyi don sun karya doka a fadarta. Su ka shiga bata haquri, ta juya a fusace suka bi ta a baya har gidanta ban san yadda ta kaya ba.
Na mayar da qofata na rufe, ina mamakin yadda Mufidah ta taimake mu alhali jiya ta gama cewa ta tsane mu. Gaskiya yau ta taimake mu sosai dan ko bata hana a kore mu ba, amma dai dole su jira mijina ya dawo.
A ranar Safiya ta shigo gidana da dadare ta bani naira dubu biyar ta ce in ji mijina ya cewa Dakta ya bani kudin cefane, daga nan na tabbatar ba shi da niyyar dawowa, wato ya tafi ya bar ni daga ni sai halina.Tabbas na san ya yi fushi ba kadan ba tunda ada kwana daya ya ce zai yi sai gashi da alama ma babu ranar dawowa Safiya ta tsaya tana kallon falon tana ta mamaki.
Ta zauna a sanyaye ta ce " tashi za ku yi ne amma baki fada min ba? Dazu na ga Godwin da wasu maza sun hawo, da suka sauko na ji su na cewa gida yayi kyau zaa kama. Daman nan gidan ne? Na dauka ma gidan Mufidah ne za ta saki."
Na girgiza kai na ce "nan gidan ne ba can ba ne."
Da ta ishe ni da tambaya a dole na bata labarin halinda mu ke ciki.
Ta tausaya min sosai, jikinta yayi sanyi.
Ta tabe baki ta fada cikin isgili ta ce "duk da kin karya asirin har yanzu Murjanatu ba ta zo ta taimaka muku din ba ne?"
Na yi shiru na rasa amsar da zan bata, na langwabe kai na ce " ai bata qasar ma. Kuma ko tana nan ma ya ce har abada baya son taimako ko digo daga gare ta."
Mun jima da Safiya mu na jajantawa sannan ta tashi ta tafi.
Bayan kwanaki biyu, ina zaune da daddare a cikin duhu, yara sun yi bacci kowa ya dora kansa akan cinyata na rasa ma abinda zanyi ko kyandir ban kunna ba saboda tsananin qaunar da nake ji a cikin zuciyata. Sai kawai sai na ga hasken wuta ya haske falon, har zan tashi da gudu a gigice, sai na daure ina zaune ina ta salati har na dawo cikin hayyacina na tabbatar wutar lantarki ce ba gobara ba ce.
Na cika da mamaki dan na san an dade da yanke mana wuta, dukka maqwabta su na da wutarsu banda gidana. Har ma mun saba da duhun, tun Usman ya na nan.
Abin mamaki sai na jiyo murya Mufidah tana magana da masu gyaran wuta a bakin matattakala .
Ta ce musu "eh wutar ta su ta gyaru. Nawa ne ma kudin sabuwar wayar da ka siyo ka hada? Gobe ka je ofis ka biya musu kudin wutar da ake binsu dukka na watannin da basu biya ba don kada su dawo su sake yanke musu."
Sai kawai na ji ina hawayen murna amma na cika da mamaki akan ta yadda aka yi duk abin nan da aka yi amma tana ta taimakona. Gashi Usman din ma baya nan balle in zargi ko sabpda shi take yi. Na rasa abin da zan yi shin zuwa zan yi in yi mata godiya ko kawai in share? Ban je ba itama bata zo ta fada min ba.
*** *** ***
Kwanakin Usman biyar cur sannan ya dawo da dadare, ina zaune kawai na ji ana buga qofa na cika da mamaki da fargaba. Muryata na rawa na tambaya waye? Ya fada a murtuke "a bude mana."
Dadi ya rufe ni da na ji muryarsa, na tafi da sauri na bude sai ga Usman ya baiyana fuskar nan murtuke babu faraa kuma ya qi kallon fuskata.
Na sa hannu zan karbi wata qatuwar jaka daga hannunsa sai ya kauce ya shigo gida, da alama yayi mamaki da ganin wutar lantarki, don yana ta kallon fitilun falon.
Bai tambaya ba sai ya tafi wajen yara yana shafa musu kai dukka sun yi bacci da alama addua yake yi musu domin shi gwanin yi musu addua a ne a koda yaushe. Ya shige dakinsa ba tare da ya amsa sannu da zuwan da nake ta faman yi masa ba. Gashi gidan mun cinye abincinmu tas amma ban damu ba dan na san ma yadda take fushin nan ba zai ci ba.
Na bi shi dakin na murda qofar na ji a kulle daga ciki sai na hakura dan kada in sake bata masa rai. Na gyarawa yara shinfida na kwantar da su, na shiga nawa dakin na yi wanka na saka rigar baccin da ya taba saka min, mai shigen irin ta Mufida 'yar qarama mai tsaga har cinya, dan in ja hankalinsa. Amma da ya fito dauke da wasu ledoji manya sai ya shiga kicin ya jera kayan da kansa, kayan shayi ne da su man gyada.Ya siyo naman kaza gasassu amma bai nuna min ba ya ajiye akan durowar kicin.
Ina tsaye a gefensa ina ta taya shi jera kayan amma ko kallona bai yi ba balle ya ga shigar 'yan duniyar da na yi saboda jan hankalinsa.
Na tamabaye shi "yaya jikin Baba?"
Harara ta kawai yayi ya wuce. Abinda ban taba gani ba a wajen Usman ba sai yau. Na koma gefe na tsaya na yi kalar tausayi amma ko a jikinsa ya shige dakinsa, abin mamaki ya datse. Ya bar ni anan a falo ina ta bilin-bitu-wata. Na yi ta buga qofar ya qi budewa.
Da gari ya waye ma dakin yaransa gaba daya ya qaura, suka dinga sha'aninsu, Usman baya kallon fuskata balle ya amsa min maganar da na ke yi masa.
Abincina ma bai ci ba, ya dauki mukullin motarsa ya fice ba tare da yace min komai ba.
Usman ya dawo gida da yamma, yayi sallama ya shigo daman ya ga yara a qasa su na wasa da keke ni kadai ya iske a falo. Na goya Haidar ina lallashi don yana ta kuka akan sai ya sauka qasa wajen yara yayi wasa tare da su, na hana shi saboda na san buge shi zasu yi ba iya hawa keken zai yi ba.
Na sha kwalliya kuwa da hoda da janbaki na dandasa wani baqin leshina wanda farar fatar jikina ta haska shi, ko ni da kaina na san na zuba kyau.
Abinci kuwa na shirya masa har kala biyu ina jiransa, bayan gida ya dauki qamshin turaren wuta.
Na yi masa sannu da zuwa bai amsa ba sai ya saka hannu a aljihu ya dauko wata farar takarda ya miqa min yayin da komai na jikina sai da ya sage tun daga tsakar kaina har zuwa qafafuwana, na tsaya sororo ina kallonsa cike da fargaba na gasgata takardar saki ce kawai.
Ya daka min tsawa ya ce "ki karba ki duba mana ki gani."
Na girgiza kai na ce "takardar meye toh? Ba zan karba, ba ka fada min da baki kawai."
Ya ce " resit ne yanzu Godwin ya kira ni a waya, na fadi in da nake ya kawo min shaida ce na an biya mana hayar gidan nan amma kuma ya qi ya fada min wacce ta biya, ya ce mjn dai mace ce. Wa kika roqa kika ce ta biya mana hayar gida saboda na gaza?"