NIDA MALAMATA BOOK COMPLETE

Author :  Fatima Batula Category :  Love

Chapter   9 / 20

24K to 27K   out of 57.2K words

yana jira idan mun je kin mishi tsakin"

Suna fitowa daga shagon motor shi,gaban Sabreen ya faɗi amma ta ɓata rai.

Daman ya lafiyar giwa balle tayi hauka,wanda ko farinciki yake ya ga damar ya ɓata rai balle
kuma.

Bai ɗago kai ya kalle su ba,har suka shiga cikin motar,harar shi sabreen ke yi ta gefan ido a
ranta tana faɗin"Ban kaddara da me zai haɗa ni da kai,kuma burina yana cika na son ɓatawa
Haulat rai zan rabu da kai ne,dan ba zan iya rayuwa da kai ba"

kiran wayar farrah ne ya katse musu shirun da suke yi,ƙawarta ce,ita kuwa farrah ko a jikinta ta
saki jiko suna fira akan bikin ma,hayaniyar ta fara damun shi

ya daka mata tsawa"Keee baki da hankali ne"

Bata san lokacin da wayar ta faɗi a hannun ta ba,jikin ta ya fara rawa,Ita kuwa Savreen ko a
kafaɗar ƙafarta.

A haka suka isa Gidan su ya fara sauke ta,sanan ya zo gidan na su.

Hankali kwance tayi wa Farrah Sallama harda faɗin "Sai goben kenan,ki fito da wuri"

A tsora ce farrah ta ce" toh"

Ba wanda ya kalli juna a cikin su.

~~~~~~~~~~
Ta isa falon ta hango hajia zaune akan kujera.

"Hajiyata ya baki tasu kin min oyoyo ba"

Ganin hajia wani iri yasa ta ce"Hajia lafiya?

Saida ta ƙaraso gurinta ta rungumeta"yanzu shikenan xaki barni ni kaɗai"

"Waya gayamiki ba inda zani ina nan"

"Zaki barni mana,zaki koma gidan Naufal"

Gabanta yai mummanan faɗuwa"zan koma gidan Naufal"

"Eh tare zaku dunga yin komai"

Ai sai hawaye ta ƙara rungume hajia,tana kuka ita ma hajiar kuka take yi,basu iya lallashin
junan su ba,saidai gajiya suka yi da kukan,a ɗakin Hajia ta kwana.

~~~~~~~~~~~~~

Naufal ƙasa barci yayi abin duniya ya dame shi.

"Meyasa Sabreen zata min haka?
"Yanzu ya zanyi da Haulat na mata alkawarin aure?
Ba zanyi iya rayuwa da Savreen a matsayin matar aure na ba?

"Haulat nake so, ita ce zaɓina ita ce ra'ayina"

Tsanar Sabreen tana ƙara yawa a ranshi,amma na banza tunda ba abinda zai iya"Ban taɓa
ganin irin wanan rayuwar ba"

"Sabreen sai kin gayamin dalilinki na ɓata rayuwa"

Ƙasa barci yayi duk tsawon daran ganin abu yana son mishi yawa yasa ya tashi ya ɗauro
alwala ya fara sallar ko ya samu sassauci,ya kowa samu raka'a shidda yayi barci yai awan gaba
da shi.

~~~~~~~~~

Tun a masallaci suka fita shi da Dady.

Yau Juma'a
Yau ne ya kama bikin Sabreen muh'ad mai taƙama tare da Angonta Naufal mai taƙama.

Gaba ɗaya Abuja da kewayan ta sunyi labarin wanan bikin kuma suɓ hallara,ƴaƴan government
tana manyan yan kasuwa da na ma'aikata duk sun hallara,dubbanin mutane ne suka hallara
gurin ɗauren Auran.

Chan na hango Naufal cikin Shadda purple harda malum-malum kayan sun mishi kyau
matuƙa,amma kallo ɗaya zaka ma fuskarshi ya gane yana cikin wani yanayi wanda ba wanda
zai iya tantance wa,amma yanayin yafi kama da damuwa,kusa da shi Dady kalar kayan su iri
daya komai da komai,kai ka ce Dady ne Angon dan yadda yake washe baki yana farinciki. Ƙarfe biyu za'a ɗaura Auren wanda yanzu saura minti ashirin da takwas a ɗaura auren.

~~~~~~~~~~~~

Da gudu ta faɗo ɗakin a ruɗe tana haki tana nishi "Haulat Haulat!!

Haulat wacce ke kwance tana mulka barcin ba abinda ke damunta.

Ganin ba zata tashi ba yasa ta ɗaka mata doka a baya "Haulat ke tashi banza kina nan kina
barci baki san abinda ke faruwa ba"

"Ke dallah kinsan bana son ina barci a tashe"

"Au haka zaki ce ko"

"To me ya fara?

"ina ce Naufal ɗan Alhaji mai taƙama ne saurayinki?

Yamutsa fuska tayi"Eh shi ne lafiya dai

"Hmm ina lafiya to wllh yau za'a ɗaura mishi aure yanzu haka an hallara gurin ɗauren Auran..

Tsaki Haulat taja"Ke ni bana son irin wanan abun kawai zaki so ki ɗaga min hankali"

"Haulat kenan kina ganin wasa ne to shikenan ba zan matsa miki akan sai kin yarda da ni
ba,amma nasan gaskiya zata baiyana,tana faɗa ta fita daga ɗakin.

Ita kuwa Haulat ƙara komawa barcin ta tayi,ko a jikinta.

Ƙarfe biyu daidai aka ɗaura auran Naufal da sabreen fiye da mutane dari sun shaida ɗaurin
auren.

Tunda aka ɗaura auran jikin Naufal yayi sanyi zuciyar shi sai faman bugawa take yi,kamar
wanda ya tashi daga dogon jinya haka ya ke ji.

~~~~~~~~~~~
Zaune take akan gadonta tasha kyau har ta gaji,ita kanta jikinta yayi sanyi"hmm ko bakomai
yanzu na ɗauka fansa akan ki Malama Haulat tunda na aure wanda kika fi so a duniya kina ji
kina gani ba abinda kika iya akai,Naufal ni ba tsarar auranka ba ce kamar yadda nasan kai ni
ba ra'ayinka ba ce,dan haka bazan zauna da kai ba,nan da ƴan wasu lukuta kaɗan zan rabu da
kai"

"Aunty Sabreen tunanin me kike yi"Farrah ta faɗa ta ƙarfi haɗe da jijjiga Sabreen ɗin.

"To meye na tunani bayan an ɗaura auran Naufal ya zama naki ke kaɗai,ko tunanin rabuwa da
hajia ne"

Harara ta mata"Ke baki jin magana ko nace karki kira ni da Aunty ki"

Dariya farrah tayi sosai ta ce"Maida wuƙar ƴan mata"

~~~~~~~~~~~~~
Ba su suka samu damar zuwa gida ba sai ƙarfe biyar da wani abu,suka shigo gidan lokacin ba
mutane sosai a gidan,kowannen su ya nufi ɗakin shi.

Yana zuwa ya faɗa kan gado,haɗe da sauke nannauyar ajiyar zuciya,ya daɗe a haka yana
tunani Tunanin Haulat kawai yake yi ita yake so ita ce ra'ayin shi ita yake da burin ya
aura"bazan karaya ba Haulat ina sonki zan kuma aureki dan ke ce muradin raina" ya fili ya faɗa.

Ringin ɗin wayar Dady ne ya shigo wayar,yana ji ya ɗauka

"Naufal karka Zauna fa akwai dinner da za'ayi karfe shidda kayi sauri ka shirya sun gama shiri
kai kawai suke jira gidan hajia zaka ku tafi tare da Sabreen ɗin" yana gama faɗa ya kashe
wayar shi.

"Why Sabreen? i cant i cant,ba zan iya rayuwa da ke ba Sabreen" idanowan shi sukai jajir.

Da gyar ya iya sarrafa jikin shi yayi wanka ya fito,kallon kayan drower ya tsaya yi ,ya rasa
wanda zai saka,wata baƙar suit ya ɗago mai haɗe da ash colour ya saka sun mishi kyau
ainun,kallon kanshi a madubi yayi.

"Wai ni aka ɗaura wa aure da Sabreen yanzu ni mijinta ne?

ya nuna kanshi"Ni Naifal nine mijin Sabreen"

Ƙasa yayi da kanshi yana sauraran bugun zuciyarshi wanda take buguwa da ƙarfin gaske.

Turaran da ya shafa sunfi kala goma ta ko wacce gaɓa ya shafa mata turaran da ake shafawa.

Bayan ya gama shiryawa ya fito cikin ƙasaita da izza yana tafiya kanshi aƙasa,baiyi mamaki
ba ganin ba kowa a falon,yana fita yaga motoc irin na alfarma gudu shidda kalar su ɗaya ash
colour irin kayan shi,sun ganin fitowar shi daga gidan suka fito,suka buɗe mishi kofa ya shiga
cikin isa da mulki.
~~~~~~~~~~~~~

"Sabreen ki saka wanan kalar tafi kyau"

"Ke ni bana son shi,wan xan saka,ta nuna wata dugowar riga baƙi da ash kala,rigar ta haɗu iya
haɗu

"To bana matsa miki ba Amarya"

Tana saka kayan aka fara mata makeup waw masha allah ashe haka Sabreen ke da kyau ,tayi
kyau har ta gai.

Ba'afi minti goma da gama makeup ɗin ba aka aiko Naufal ya iso su fito,taɓe baki Sabreen tayi.

Rigar dugowace sosai tana tafiya tana binta Farrah da hajia su suka riƙo ta har wajen gurin
motorcin,motor da yake aka buɗe mata ta shiga,tana shiga wani irin sinadarin ƙamshi ya doki
hancinta har saida ta lumshe ido.

Kusa da juna sosai suka zauna hakan ya ƙara haifar musu da matsanaicin bugun
zuciya,kowanne yana jin fitar numfashin kowa

"Bata sonka ko kaɗan"

"Na sani kuma kema kin san bana sonki"
"But why Sabreen?

Bata kalle shi ba,daman ko ɗazun bata kalle shi ba"Saboda ɗaukar fansa"

wanan karon saida ya kalleta ,zuciyarshi ta buga dan ta bashi tsoro ganin irin kyaun da tayi
gashi kalar kayanshi ta saka,cikin wata siga wacce shi kanshi bai san lokacin da ya tsinci kanshi
da shiga yanayin tausasawar ba ya ce"Sabreen!

Lumshe idanowa tayi tana jin daɗin yadda yake kiran sunanta a tata cewar da indiyanci yake
kiran sunanta.

Shi kanshi saida yai jimm,bai san abinda ya yasa shi yin hakan ba,ganin bashi da niyyar
magana ya ce tace mishi"Nima ba zan zauna da kai ba,zamu rabu ne,dan wata manufa na
aureka,karka ji wani avu nasan baka so na ka kwantar da hankalinka zamu rabu"

Da mamaki yake kallonta kanshi ya ɗaure hali irin na Sabreen yana bashi mamaki yadda take
mishi magana ma abin mmk ne har ya buɗe baki zai mata magana motor ta tsaya tana tsayawa
aka buɗe musu kofa.

Yana sauko da kai idanowan shi sukai arba da ƙaton hutun su wanda suka yi matuƙar kyau
mamaki ya ƙara kamashi ganin yadda Sabreen tayi murmushi a hoton kamar wacce take son
shi,ga hoton yayi kyau kamar ba haɗa shi aka yiba,a tare aka yi shi.

Tana fitowa taga ƴan jarida da masu ɗaukar photo a ranta ta ce" Za'ayi vedio kuma za'a nuna a
tibi,wanan dama ce"

Daman yana tsaye yana jiran fitowar ta,murmushi ta fara mai ƙyayatarwa tana kallon masu
ɗaukar hoton su kuma sai ɗauka suke yi.

ji yayi ta riƙe mishi hannu da sauri ya juyo ya kalleta cikin mamaki,wani irin murmushi ta mishi
mai ɗaukar hankali bai san lokacin daya maida mata da martani ba,a daidai lokacin wani mai
hoto ya ɗauke su,suna kallon juna suna murmushi gashi hannuwan su a riƙe da juna.

~~~~~~~~~~~~~
Waw guri ya haɗu ya haɗe abin kamar ba'a 9j ba ,waiyo ni batula abun mamaki daga gefen
hannun daman Sabreen sai ga shadow da my Aunty nabeela,waiwai su khadija da fatima shariff

suma suna gefe mr parrot da hauwa sule bakin su yaƙi rufuwa ,hauwa'u da ramb kuwa suna
gefe sai satar kallon Naufal suke yi,my sis khadija da nafisa kuwa suna kusa da farrah sai fira
suke yi,Dr halimatu ma ta faso ita da jermielat , wai su hafsat da safiya abudullahi kuwa
hankalinsu yayi gurin kaji, Aysha zango ita da mrs sunusi sai kwaso shoki shoki suke yi,ita kuwa
sarauniya jidda ta saki baki tana kallon yadda Naufal ke yamutsa fuska.

Ina zan manta da ku yanzu dai na hango ku,cunkuso ne ya rufe ku iyalan jamliya,dan tsabar
ɗauki tun ranar da Sabreen tace Naufal zata aura suka hallaro,daga chan gefe gudu kuma
jamar batula fans novels ne suka baiyana suma ba'a barsu a baya ba,chan kuma sai ga iyalan
bintu Ahmad wato ƴan gidan Shabihaty suma sun ɗan yi kara,iyalan lipton ma na hango wasu
ƴan ƙaɗan,tawagar farida kuwa tun kafin a buɗe gurin suka iso,ƴan tangantakar mu,kuma na
hango ku,amma ku da alama ƴan team ɗin Haulat ne,tawagar waye sila,kuma sannunku da
ƙokari,wai ai idan ba'a ganku ba wa za'a ganiiyalan tawan,ku da tun kafin a ɗaura aure kuka
iso,chan taro ya fara nisa sai ga wasu gungumin al-umma,masu yawan gaske gashi ban gane
su ba,gaba ɗayan jama'ar gurin kallon su ake yi ,kasa hakuri Sabreen tayi,ta tambaye su daga
ina,

"Mu masoyanki ne masu miki fatan alkairi,muna da nisa amma haka muka ɗugunzumo mu
tayaki murna,kuma ki miƙa mana gaisuwa gurin batula"

Suka gayamata haka sanan suka zamu guri suka zauna.

Taro yayi taro al'umma sun hallara taya Sabreen da Naufal murna,chan na hango wasu manyan
mutane,tun isowar su aka fara buɗa musu hanya,Abin mamaki Sai na ga Aunty Nabeela ta tashi
da murnar ta,guri na ta iso tana murmushi ta kalle ni ta ce"My batul zo muje ki ga waɗan da
suka zo"
Kallonta nayi nai murmushi na ce"Toh muje my Aunty"

waiyo allah na wa zanga ni Sarah ce da alfaga da kuma mutumina Sul harda Ruƙaiya,nayi
mamaki sosai ganin su gurin Bikin Sabreen.

Hhhh baku ga da Sarah da zauna kusa da Sabreen ba,kunga Sabreen kuwa sai tai wani irin
mugun muni,to kyau na gaskiya ya baiyana a gabanta.

"Toh wai ko yarima mu'utasim ya zo kuwa?

hhhh to ya zan sani tunda ba ganinshi zanyi ba.

Ina cikin wanan tunanin Aunty nabeela ta ce min"My batul yarima mu'utasim yana gaisuwa"

A ruɗe na ce"My Aunty ya zo ne"

"Eh kin shiga ruɗani ne"

Wanan shine *Ruɗani* ,littafin Sarauniya beelat(My Aunty nabeela).

biki yayi biki Tunda manyan mutane suka hallara bikin harda su Yarima mu'utasim,na so ganin
baba me gadi dan yaban dariya.
.
[12/16, 5:41 PM] �° � D°�⭕Y: _ �σѕт у �яσυρ � � �уρє �αυѕα
�σνєℓѕ σσк нαтѕαρρ 08064400100_
[12/22, 5:26 PM] �° � D°�⭕Y: *NI* *DA* *MALAMA* *TA*


*By*
*fatima* *Batula*
*~✍✍GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍✍~*

Page 11
............................................................
_*Manzon Allaah(ﷺ)* *ya ce;{WANDA YA RUFE WA MUMINI WANI SIRRI(NA LAIFI)
KAMAR YAYI CETO NE GA WANDA AKA BINNE DA RAI!.}*_

```[Sahihut Targib;2337]```
~~
_Duk wanda ya rufa ma mumini sirrinsa na laifi, bai ba mutane labarin abinda ya sani game da
shi na sharri ba, to kamar an binne shi da rai ne sai ya ceceshi. Allaahu a'alam._

```Allah ta'ala yasa mudace```

ﻚﻧﺎﺤﺒﺳ*_ ﻢﻬﻠﻟﺍ ,ﻙﺪﻤﺤﺑﻭ ﺪﻬﺷﺃ ﻥﺃ ﻻ ﻪﻟﺇ ﻻﺇ ،ﺖﻧﺃ ﻙﺮﻔﻐﺘﺳﺃ ﺏﻮﺗﺃﻭ _*​​.ﻚﻴﻟﺇ

....................................................................................

Ansha shagalin baki abun ba'a cewa komai, sai wanda ya gani kawai.

Kallon ta kawai Naufal yake yi yana mamaki gashi sai washe baki take yi ,maganar da ta
gayamishi yake tunowa"Bana sonka ba zan iya rayuwa da kai ba,na aure ka ne dan ɗaukar
fansa"

A haka taro ya watse hankalin shi baya tare da shi abubuwa sai yawo suke mishi kwakwalwa
,daga sun haɗa ido ya su harara juna suja tsaki.

Ƙarfe Tara taro ya watse,kowa ya kama gaban shi,su kum suka ɗau hanyar zuwa gidan su
hajia.

Kallonta yayi rai a ɓace ya ce"Sabreen meyasa kika min haka kin san bana sonki kika ce zaki
aure ni"

Ɗagowa tayi ita ma ranta a ɓace ta kalle "Hmm to kai me kake tunani ,ni Sabreen zan iya auran
haka kawai allah ya kyautamin da auran....

yaji zafin maganar matuƙa ya janyo ta jikin shi da karfi ya rungumeta ɓacin ran da yake ciki bai
bar shi ya saurara feelings ɗin da yaji ba "Ke ni tsaranki ne zaki gayamin irin wanan maganar,ni
wllh ko banga dalilin da zai sa na aureki ba,dan banga abinda zanyi da ke ba,ko a jerin mata
ban saka ki ba,balle ki xama class ɗina,ke kanki kinsan ke ba aji na ba ce,banda kaddara da
wallahi ko kallan ki bazan yi ba"

Ran Sabreen kai ƙololuwa gurin ɓaci idanuwanta sunyi jajir dan takaici gashi ya matseta,cizo ta
ganna mishi a hannu da ƙarfin gaske da sauri ya sake ta.

Har yakai hannu zai janyota farrah ta buɗe kofar

"Am. .. sorry"

Har zata maida kofar ta rufe Sabreen ta fito rai a ɓace,gaba tayi ta barshi a ciki.

Wani ƙululon takaici ya kama shi,idan har haka sabreen zata tunga mishi bai jin zai iya riƙe
alƙawarin Dady,ya daɗe a cikin motor kafin ya fito.

Yana isa falon gaban shi yai mummunan faɗuwa ganin kowa da kowa yana falon,har ya samu
wani guri gefe zai zauna Dady ya ce mishi"Naufal matso nan kusa da matarka."

Ba Naufal ba ita kan Sabreen zaida taji haushi.
Ba musu ya matsu kusa da ita ya ɗuka dan a kasa suke harda ita ɗin.

Dady yayi gyaran murya ya ce"Naufal mun gama magana da kai,ni yanzu ba abinda zan ce
maka,illa na ƙara tunatar da kai haƙƙin aure wanda su ma kasan su."

Juyowa da kallon shi yayi gurin Sabreen ya kalleta duk da ƙarancin hasken da ke ɗakin amma
yana hango fuskarta "Sabreen yanzu zaki shiga wata sabuwar rayuwa wacce baki saba yin
irinta ba,abinda nake so da ke sabreen kinga Naufal ɗan uwanki ne,ki riƙe shi, ki mishi biyayya
ki bi umarni shi wannan ce shine haƙƙin mata akan mijinta,nasan kina da hakuri amma sai kin
ƙara,Sabreen ku riƙe junanku da amana,sanan duk abinda ya miki ki same ni ki faɗimin kina
jina?

Ɗaga mishi kai tayi alamar taji.

Kallon hajia da Momy yayi ya ce"Toh baku da abin faɗi ne?

A hankali momy ta buɗe baki saida ta fara gabatar da addu'ar buɗe taro sanan ta ce"Naufal ba
wata magana mai tsawo zanyi ba,kasan Sabreen marainiyace karka cutar da ita ka riƙe ta ƴar
uwarka ce ,sanan wanan auren shi ne alkairi a gare mu da kai ma,bansan ko zaka fahimce
abinda nake nufi ba,sabreena alkairi ce a gareka dan haka ka Naufal ka kula da Sabreen"
Tunda suka fara magana gaban shi ke faɗuwa,ya rasa wani irin tunani zai yi ma.

Hajiya kuwa kasa magana tayi sai kuka sabreen najin hajia ta fara kuka ita ma,ta fara yi,kusa da
ita hajia ta zo ta rungumeta suna ta kuka ba wanda ya dakatar da su.

Naufal ma ji yake yi ina

9 / 20