Author : Fatima Batula Category : Love
kan shi bai san ya ci da yawa ba,"Yawwa nawan saura magani,"yana gani ta ɓallo
magani dan daman likitan ya gaya mata yadda zata bashi.
Miƙa mishi tayi ba musu ya amsa ya sha,saida ta ɗan gyara gurin sanan ta dawo ta zauna.
Murmushi tayi ganin irin kallon da yake mata,gashi tana son yi mishi maganar su Dady tana jin
tsoro.
"Ki ce wani Abu."
Saida ta murmusha sanan ta ce,"To na gaji da magana ni kaɗai saidai kayi ta kallo na ka ƙi
magana."
"Ina jin daɗin yadda ya kike magana."
Dariya tayi sosai ta ce,"nima ina jin daɗin yadda kake magan har dariya kake ban"
Lauya harshe tayi ta ce,Ki ce wani Abu," ta fashe da dariya ta ce,"Haka kake magana fah."
Dariya yayi yadda tayi maganar y mishi daɗi,suna nan zaune aka kira sallah da sauri ta tashi
tayi yana kallon har da iddar tayi addu'a tana zaune a gurin ya ce,"Amin!
Bayan ta tashi ta dawo ta zauna,"Me kika roƙa ne?
"Me kuwa banda allah ya ba miji na lafiya."
Dariya yayi yana jin wani irin farinciki na ratsa zuciyar shi,duk ya manta da komai da kowa.
A haka su ka cigaba da fira cikin farinciki da jin daɗi musamman Sabreen duk wata kalma da
zai faɗa dariya ta ke bata,har lokacin la'asar ta tashi tayi sallah yana kallon ta har da idar ta
dawo ta zauna suka cigaba da fira jikin jin daɗi.
Bayan maqrib su Dady su ka dawo tare da abinci,ko wannen su yana son ganin naufal amma
suna tunanin ganin zai iya jan matsala shiyasa ba wanda ya tunkari wani da maganar,kai tsaye
office ɗin doctor zain su ka nufa bayan sun gaisa Dady ya ce,"Doctor ya koƙari ya me jikin?
Fuskar ɗauke da annuri ya ce,"Alhmadulilah! jiki yayi sauƙi sosai abin mamaki gaskiya yaran
nan su na son junan su sosai,amma zaku ƙara hakuri da rashin ganin shi har nan da kwana
biyu da zuwa lokacin insha allah jikin zai yi sauki sosai."
"Ba komai likita allah ya ƙara sauki,am..zamu iya ganin sabreen ɗin?
"Why not bari na kira ta,"yana gama faɗa ya fita.
Da sallama ya isa ɗakin fuskar shi ɗauke da annuri ganin yadda su ke fira ko gajiya basu yi abin
ban sha'awa.
"Kai wanan irin so haka."
Murmushi Sabreen tayi a ranta ta ce,"Wani so ana zaune ƙalau."
A fili kuwa murmushi tayi ta ce,"Ya koƙari doctor?
Saida Naufal yaji wani irin abu ya soke shi a zuciya ganin yadda sabreen ta ke zubawa doctor
xain murmushi,shi ma zai murmushin yake yi,lokaci ɗaya ya ɗaure rai,yai ƙasa da kai.
"Alhmdulilah! ya me jiki?
"Jiki yayi sauƙi."
"Ai kuwa naga alama,allah ya ƙara sauƙi Sabreen ki zo ki amsar mishi magani.",yana faɗa ya
juyo bai tsaya jin amsar da xata ba shi ba.
Wani irin haushi mai ɗauke da mugun kishi ya kama Naufal taya zai ce ta bi shi,kuma harda
kiran sunan ta,a hankali yaji zuciyar shi ta fara mishi zafi.
Hannuwan ta,ta ɗaura kan ƙirjin shi,lumshe ido ya fara yi yana ajiyar zuciya a hankali ga tsigar
jikin shi ta ke tashi.
"Ya dai magani zan amso fah,koma ba daɗewa zan yi ba,wai ba ka son gaji sauƙi ne kafi son
ganin mu cikin damuwa."
har lokacin bai buɗe ido ba,a hankali yake sauke ajiyar zuciya,muryarta na ratsa kunnan shi
tana shiga cikin zuciyar shi.
"Ya hakuri yanzun zan dawo."
Jikin shi ya mutu bai jin zai iya yin magana kai kawai ya ɗaga mata alamar eh,ganin hakan yasa
ta janye hannuwanta daga ƙirjin shi,ta fita saida yaji wani iri.
Kai tsaye office ɗin ta nufa,ganin su dady yasa ta washe baki ,gurin dady tayi ta rungume shi
tana jin son shi na ratsa sassan jikin ta,sun daɗe rungume da juna kafin su ka janye,cikin jin
daɗi da soyayya su ka gaisa da kowa,bayan sun gama gaisawan zasu tafi har bakin motor ta
raka su,Dady ya kalle ta ya ce,"Sabreen Kin cika ƴa abin alfahari allah yai miki albarka ya ba
mijin ki lafiya da zuri'a ɗaiyaba."
Saida tayi ƙasa da kai sanan ta ce,"Amin Dady n gode."
Duk sukai sallama da juna su ka tafi,kamar tayi kuka ta daɗe a gurin kafin su ka tafi,saida ta
ɗauki abincin sanan ta wuce ɗakin,na zuwa yayi barci,kusa da shi ta zauna ta ƙura ma fuskar
shi ido tana jin wani irin abu a zuciyar shi.
Har lokacin sallar isha'i bai tashi ba,har ta idar ta sallar shiru,ta ci abincin bai tashi ba,har ta gaji
ta kwanta.
"Kiyi hakuri karki barni zan rayu da ke,ina buƙatar ki.."cikin wata irin sigar numfashi mai ɗauke
da nishin kuka yayi maganar.
"Ah..Ahh ..ni ka barni bana soo...
"Ɗan allah..."firgitt ya tashi yana nishi da haki ga wani irin abu da ya ke ji a zuciyar shi mara
daɗi,idan da sabo ya ci ya saba da irin wanan mafarkin amma ya kasa savawa,ya daɗe yana
sauke ajiyar numfashin ,kafin ya ɗago kan shi,a ɗayan gadon ya hango ta,tana barci
kasancewar ɗakin da haske bata kashe wuta ba,ji yayi kamar ya tashi ya tunkare ta dan yana
cikin tsananin sha'awa,da ƙyar ya iya faɗa da zuciyar shi akan tai hakuri,a haka har barci
ɓarawo ya ɗauke shi.
Asubar fari sabreen ta tashi alwala tayi da tada sallah har ta idar da sallar asuba bai tashi
ba,bayan ta idar ta tawo ta zauna kusa da shi,idanuwa ta zuba mishi,har ƙarfe tara naufal bai
tashi ba,doctor zain ya shigo ya duba shi,har su Dady su ka xo bai tashi ba,sun daɗe kuma sun
leƙo sun gan shi,har su ka tafi bai tashi ba. .
Kuyi hakuri posting din dazu an samu tsallake sai dai Kuyi hakuri wlh sbd ba laifina bane nima
a haka littafin yazo min.
.
[12/23, 2:29 PM] ° D°⭕Y: _ σѕт у яσυρ уρє αυѕα
σνєℓѕ σσк нαтѕαρρ 08064400100_
[12/23, 2:34 PM] ° D°⭕Y: *NI* *DA* *MALAMA* *TA*
*By*
*Fatima* *Batulah*
*~✍✍GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍✍~*
Page 21 (last)
.......................................
Asubar fari sabreen ta tashi alwala tayi da tada sallah har ta idar da sallar asuba bai tashi
ba,bayan ta idar ta tawo ta zauna kusa da shi,idanuwa ta zuba mishi,har ƙarfe tara naufal bai
tashi ba,doctor zain ya shigo ya duba shi,har su Dady su ka xo bai tashi ba,sun daɗe kuma sun
leƙo sun gan shi,har su ka tafi bai tashi ba.
Ƙarfeɓgoma sha biyu da kwata daidai ya farka lokacin tana zaune kusa da shi akan kujera,akan
fuskar ta idanuwan shi su ka ƙarasa buɗewa,murmushi tai mishi ,shi ma murmushin yai mata.
"Ka tashi? ya jikin? yau ka daɗe baka tashi ba,kasan yanzun ƙarfe nawa ne?abincin ka har yayi
sanyi."
Murmushi yayi wanda saida haƙuran shi su ka baiyana,ganin yadda ta ke magana ba ko
tsayawa.
Tunowa yayi bashi da tsarki da sauri yai koƙarin miƙewa,taimakon shi tayi ya miƙe zaune,ta
kalle shi ta ce,"Ya dai?
"Bani da tsarki zan yi wanka."
"Baka da tsarki." ta faɗa cikin rashin fahimtar inda ya dosa a mgnr tashi.
"Eh xanyi wankar tsarki bani da tsarki."
Bata tambaye shi ta shige bayi,ta haɗa mishi komai da komai,sanan ta fito ta temaka mishi ya
tashi ya shiga bayin,saida ta ƙara gyara gurin tsabb,bayan ya fito ya zauna ta sulale ta fita ganin
yana koƙarin cire kaya a jikin ta,murmushi yayi kawai,ya saka kayan shi,yaji daɗin jikin shi
sosai,kafin ta shigo har ya fara sallah,ko da ta ahigo ta ga yana sallat taji daɗi ,guri ta samu ta
zauna tana kallon shi,saida yayi lzahar ta kwana ukku sanan ya idar,bayan ya idar ya dawo su
ka zauna ta bashi abinci ya ci kaɗan sanan ya sha magani su ka cigaba da firar su cikin jin daɗi.
Yau kwanan Sabreen ukuu a asibiti tare da Naufal,yanzun kam jiki yayi sauƙi sosai da
sosai,shaƙuwa ta shiga tsakanin su mai ƙarfi,musamman Naufal wanda ya gama tabbatar da ya
kamo da ciwon son Sabreen,wanda yake jin duk wani fitar numfashin su tare su ke fita,ga wani
irin mugun kishi.
Zaune ta ke kan kujera shi kuma yana zaune kan gado idanuwan shi duk sua kan ta,tunani ta
ke yi a ran ta,"Ta ina zan fara mishi maganar su dady gashi yau za su zo gurin shi,yanzun ya
zan yi," ɗago wa tayi haɗe ido su ka yi tai murmushi murmushi da ido yai mata magana da lafiya
kuwa dan ya ga fuskar ta akwai abinda ta ke son faɗi.
Saida ta ja garuwar ajiya zuciya sanan ta ce,"Ɗazun su Dady sun zo kana barci,"idanuwan ta
suna kan shi dan taga yanayin da zai shiga.
ƙasa yayi da kai wani abu yana bijiro mishi a rai,ganin hakan yasa ta kama hannuwan shi ,ta
raunana murya ta ce,"Dan allah karka ji wani abu wllahi dady da momy duk sun yafe
ma,kaddara ce,ka kwantar da hankalin ka."
Runtse idanuwan shi yayi abubuwan da suka faru suna dawo mishi,ahankali ya buɗe su,saida
sabreen ta tsorata ganin yadda idanuwan su ka canza sukai jajir,rungume shi tayi,"Dan allah
kayi hakuri kar wani abu ya same ka,ba wanda ke fushi da kai."
A hankali yaji zuciyar shi tana mai sanyi,amma yana jin nauyin iyayen shi harda sabreen
ɗin,saidai ya kasa gane dalilin da yasa ya aikata irin wanan ɗayan aikin ki,ji ya ke kamar ba shi
ba,taya zai yi zina abinda ya tsana a duniya,wasu zafaffan hawaye sukai nasarar zubu
mishi,ƙokarin yin magana yake yi amma maganar taƙi fitowa.
Kuka Sabreen ta fashe da shi,saida yaji wani radaɗi a ran shi,cikin kukan ta ce,"Dan allah kayi
hakuri nasan ba laifin ka ba ne laifi na ne,bana sun su dady su zo su ganka a haka,kayi shiru."
Shafa kan ta yayi yana jin zafin hawayen ta,tamkar shi ke yin su,janye ta yayi su ka fuskanci
juna da ido yayi mata magana da tayi shiru,zuwa yanzu Sabreen ta iya magana da ido sosai ,ita
ma da idon tayi mishi magana ta yayi hakuri ya natsu,share mata hawayen yayi,shiru su ka yi
kowannen su yana ƙokarin samawar zuciyar shi.
Sun ɗau lokaci a haka suna kallon juna kafin sabreen ta janye jikin ta,kasa ce mata komai yayi
duk da kasancewar ba ji daɗi ba,bayi ta shiga wa wanke fuska sanan ta fito,ta dawo ta zauna
ɗan nisa da shi sanin su dady zasu iya zuwa any time,kallon ta kawai yake yi yana mamakin
hali irin na ta,yasan ya mata mugun laifi amma bata nuna mishi ba ko kaɗan sanan har ta ke
ɗaurawa kanta laifi,lallai yasan halin dady kuma ba xai manta kalaman shi ba,yanzu ya yafe
mishi wanda ko shakka babu sabreen ɗin ta buƙaci haka,runtse idanuwan shi yayi yana ƙara jin
wani irin mugun azababben son sabreen na ratsa zuciyar shi lallai ta haifu,shi kuma yaci
amanar iyayen shi da marainiyar allah.
ganin yadda ya kulle ido yasa sabreen kiran sunan shi,"Ya Naufal!,kai tsaye zuciyar shi ta
amsa saƙon muryarta,a hankali ya bude idon.
"Yah kayi hakuri dan all..
"Ke kin hakura."
"Na hakura ai baka min laifin komai ba,ni ka hakura duk abinda haulat tayi dan na ji haushi ne
sann.....
Sallamar su dady ne ya katse ta,da sauri ta ƙarasa gurin shi,amma ta kasa rungume shi,shi ne
ya rungumu ta,shi kuwa naufal yana jin su yai ƙasa da kai wata irin kunya ta mameshi
musamman momy.
Kowannen su kallon su naga naufal wanda yai ƙasa da kai,farrah ce ta fara ƙarasawa gurin
shi,fuska ɗauke da annuri ta ce,"Brother ya jikin?
kan shi a ƙasa ya ce,"Da sauƙi sosai."
"Allah ya kara sauki yaya.",yaji daɗin yadda yaji tana mishi magana wanda hakan yasa ya ɗan ji
daɗi.
"mutum india ya jikin? kabar amarya da damuwa gaskiya kaji sauƙi kasan bana son ganin
damuwar ta,gashi ka siye zuciyar mu," cikin dariya ta ƙasara maganar,dariya kowa yayi harda
momy da dady wanda ba ƙaramin daɗin hakan yaji ba.
Kusa da shi kaɗan momy ta matso shi kuwa har lokacin kan shi na ƙasa bai hadda ido da kowa
ba,duk sun fahimce kunyar su yake ji sai tausayin shi ya ƙara kama su.
"Naufal ya ƙarfin jikin."
Rawa bakin shi ya fara ji,"da saauƙƙii."
ganin ya fara daburewa yasa ta faɗin,"Sauƙi sosai,dan yau zamu koma da kai gida, gidan duk
ba daɗi ",idanuwan ta na kan shi,ta ƙarasa maganar,lumshe ido yayi yana jin wani irin sanyi a
ranshi momy ce ke mishi magana kamar yadda ta saba kenan batai fushi da laifin da ya aikata
ba,ganin yanayin da ya shiga yasa dady ƙarasowa inda yake ya ce,"Naufal halan dai baka son
zuwa gida ne."
Lokaci ɗaya yaji bugun zuciyar shi na ƙaruwa,koƙarin faɗa da numfashin shi ya fara yi wanda ke
koƙarin ɗaukewa,ganin hakan ya ruɗa su dady sosai,zama yayi kusa da shi ya dafa kafaɗar shi
ya ce,"Naufal gudun iyayen ka kake yi? kana tsoran mu ne? naufal ba ka da wasu bayan mu,ko
meye ya faru mu iyayen ka ne,plss my son ka kwantar da hankalin ka,kaddara ce wanda,Allah
da kan ce ya ce," *Idan* *yana* *son* *mutum* *da* *alkairi* *sai* *ya* *jarabce* *shi* ."
Saida ya numfasa sanan ya ɗaura da faɗin,"Naufal allah yana son ka da alkairi ya jarabce ka
dan ka kiyaye gaba,ba lalai abinda ka aikata ɗabi'ar ka ba ce,ko kana da kuɗirin aikata hakan
ba saidan kaddara ce jarabta,mun ƙara fahimtar abubuwa da yawa faruwar wanan abun,wanda
ni kai na,na gane kuskure na,na gaya ma irin waɗan nan kalaman ,wanda yanzun allah ya nuna
min,kuskure na duk sanadin faruwan hakan,sry my son mubar hakan a matsayin kaddara," jin
hawaye na son fitowa daga fuskar shi yasa ya tsaida maganar badan ya gama ba.
Maganganun Dady sun yi tasiri sosai a jikin su,musamman naufal wanda yake jin shi wani iri
tamkar an canza mishi duniya,rungume Dadyn yayi wasu zafafan hawaye su ka fara bin fuskar
shi haɗe da kuka mai sauti,shi kan shi dadyn hawayen da yake makalewa su ka fito,haka zalika
ko wanne da ke ɗakin saida ya kuka,sun daɗe a haka su na kuka ba wanda ya kalle wani balle
yai kuƙarin ba da hakuri.
Shafa kan shi dady yayi yana faɗin,"Is okk kayi haba kai fa namiji ne."
ai kamar ƙarawa naufal kukan ya ke yi, daɗi ya haifar mishi da kukan,jin ya ƙara sautin kukan
yasa sabreen ta kara fashe da matsanaicin kuka,da sauri hankalin su ya dawo gare ta,dariya su
ka yi dukkan su har dady da naufal ɗin sanin abinda yasa ƙara kukan.
"Ka gani ko," dady ya faɗa yana kallon naufal ɗin wanda shi kuma idanuwan shi yana gurin
sabreen.
"Ga gani ko,ni kai shiru dan allah dan ta samu tayi shiru ita ma," cewar hajia wacce idanuwanta
ke kan naufal.
fashe wa da dariya su kara yi,ita kuwa sabreen gurin momy tayi tana kuka ta rungume ta.
"Kiyi hakuri kin ji,ƙyale su ba ruwan mu da su," cikin rarrashi tayi maganar su kuwa,dariya su ke
kasa-kasa.
Sun sake jiki sosai kamar ba wani abun da ya fara,duk yadda su ka so naufal ya sake jiki ya
kasa,dan ya kasa haɗa ido da kowa a cikin su,yana son kallon sabreen amma ya kasa dan tana
jikim momy,yana dai ɗan taɓa fira kaɗan kaɗan,ba su damu ba dan sun san daman ba sai son
mgn ba ne.
Tun daɗe suna fira jikin jin daɗi da nuna kulawa,wanda naufal yaji daɗi matuƙa wasai yake jin
zuciyar shi sai wani daɗe ma ta jake ji mara misaltuwa,tun mantar da shi abinda ya faru,sun so
a sallame su yau amma doctor zain ya ƙi,dole sai gobe shi kan shi naufal ɗin bai ji daɗi ba,ya so
zuwa gida,amma ya nuna musu yau da gobe duk ɗaya ne a gurin allah,har gurin motor sabreen
ta raka su farrah sai zolayarta ta ke yi bata kula ta,anan ma saida su ka rarrashe ta sanan ta
ɗaurr bata yi kuka ba,tana tsaye har motor su ta bar asibitin sanan ta juya lokacin an kira sallar
maqrib,tana zuwa ɗakin yana fitowa daga bayi,kallon juna su ka ji yayi kamar ya shekara bai
ganta ba,murmushi su kai wa juna,da saure ya ɗauke kai tuno yayi alwala,sallaya ta shimfiɗa
mishi ya hau,ita ma bayin ta shiga ta ɗauro alwala,baya da shi kaɗan ta tayi.
Tana zaune tana lazimi ya idar da sallar har ya gama lazimin ya juyo ƙura mata ido yayi yana jin
wani abu yana tasar mishi,saida ya lumshe ido sanan ya ce cikin nakasassar muryar shi,"Me
kika roƙar mana."
ɗagowa tayi ta kalle haɗe da sakar mishi murmushi,"Wa zan ma addu'a idan ba ku ba,kai
Dady hajia momy farrah,ku ne duniyata rayuwata."
Tausin sabreen ya ƙara kama shi,"lallai bata waɗan da su ka fi mu,zan raini ki sabreen zan
kula zan miki gata,kin min komai kin temaki ni kin min gata..
"Ya dai? ina kallon ka ɗazun kasa cin abinci ka yi."
Tashi yayi ya ɗauke sallayar ya koma ya zauna,da ido ya kira ta,kusa da shi ta zo janyota jikin
shi yayi ya rungume ta tsamm,wata irin ajiyar zuciya ya fara sauke wa,zuwa wanan lokacin
sabreen ta saba da runguma gurin naufal,saidai bata bari yai mata kiss duk yadda ya so.
"Ka ci abinci ka sha magani ",ta faɗa tana kokarin janye jikin ta.
"Meye sa ki kuka ɗazun?
saida ta gama janye jikin ta sanan ta ce, "ba komai."
Runtse ido yayi yana sauraran bugun zuciyar shi wanda ke buguwa da son sabreen,"Allah yasa
ki amci da soyayyata sabreen ban san lokacin da zuciyata