NIDA MALAMATA BOOK COMPLETE

Author :  Fatima Batula Category :  Love

Chapter   8 / 20

21K to 24K   out of 57.2K words

abu ya haɗa su..

"Haulat sha'awarshi kike yi ko sonshi?

"Duka biyu"

"Hm Haulat kenan ni yanzu ƙawarki ce dole na baki sha'awa"

"Yawwa ƙawar Arziƙi mu je ɗaki na"

Ashe duk wanan maganar da suke yi a falo ne.to allah ya kyauta.

Zama suka yi akan gado salma ƙawar Haulat ɗin ta kalle ta tace"Irin waɗan nan mazan a
hankali da dubara ake binsu,tunda ya nuna yana jin tsoran wani abu ya faru,to karki matsa
mishi ,idan ba haka ba kuwa zai fara ja da baya,hankali xaki haɗa mishi tarko daya faɗa
shikenan"
Dariya Haulat ɗin tayi suka taɓa" shegiya ƙawa shiyasa nake sonki,yanzu ba wanan baki na
kira faisal(tsohon saurayinta) dan a matse nake,yaushe rabo na,nayi ma ƙokari"

"Ke Haulat baki da dama,ni kuwa kinga tun lokacin da na rabu musa(saurayinta)ban ƙara
saduwa da wani ba,saidai ƴan abun da ba'a rasa ba,yawwa ban tambayeki amma zai aureki dai
ko"

Kallonta Haulat ɗin tayi tai dariya"Aure ni da aure yanzu ina,allah ya kyauta haka kawai na
haihu na tsofa,ke ma kin san bani da ra'ayin aure yanzu,shi dai tunda bai waye ba,daya min
maganar auren nake katse shi"

Shiru Salma tayi tana mamaki ina da ita ta samu irin wanan damar"Haulat ni kin ban tsoro na
ɗauka kin cire wa kanki wanan ra'ayin banzan,Ina jiye miki abun da zai iya biyo baya"

"mtseww na me? ba abinda zai faru"

"hm murmushi tayi kawai suka cigaba da firar su mara amfani.

~~~~~~~~~~~~~

Saida nayi da ƙyar na iya gane Sabreen ban taɓa tunanin tana kyau irin haka ba sai yau,nayi
fitinan kyau,makeup ɗin ya amshi fuskarta ainun,cikin wata dugowar riga wacce ta ɗan kama
ta,pink da golden colour kalan ya ƙara fito da ita ga ɗaurin ɗan kwalin ,ita kanta rigar abun kallo
ce,bayan an gama yin makeup ɗin aka ɗauke ta hoto na,kala-kala,idan ba ita ta gayama ba son
auran take yiba,ba zaka taɓa yadda ba,dan yadda ta saki jiki tana zabga fara'a.

Kallon ta farrah tayi tana washe baki"Da yaya ya ganki na tabbata bazai gane ki ba,ko yanzu sai
yayi da ƙyar zai iya gane ki balle an haɗa pic ɗin ku"

Murmushi Sabreen tayi bata ce komai ba,ita yanzu yarda zata haɗu da malama Haulat take yi
gashi bata da number ta.

Sunyi yawo sosai da n farrah saida ta je gurin ƙawayanta,ta gaya musu,Da aka haɗa hoton
abun ba magana kamar a tare suka yi hoton sun dace sosai ita kanta Sabreen da taga pic ɗin
saida taji gabanta ya faɗa da ƙarfi wanda bata san dalilin faɗuwar shi ba.

Gidan su momy suka sauka bayan sun dawo ita ma lokacin bata daɗe da dawowa ba,taji daɗi
sosai musamman da taga an haɗa hoton sai ta ƙara tabbatar da sun dace da juna,ita ma nayi
siyayya sosai da kayan da zasu saka da komai da komai.

Ana idar da Sallar maqrib Su dady suka dawo,a lokacin suna zaune a falo suna fira akan
bikin,Da sallama suka shigo,Sabreen tana jin muryarshi gabanta yai mummunan faɗuwa.

Ko kaɗan bai kula da Sabreen tana nan ba,dan shi ba mutum ba ne mai kalle-kalle ba,har suka
iso falon suka zauna bai kula da ita ba.

Dady ya kula da ita tun isowar shi ɗakin yana zama ya kirata"Ƴar aljanna zo nan"

Jin dady ya kira sunanta yasa ya ɗago kai da sauri haɗa ido sukai wani abu ji ya soki ƙirjin
shi,da sauri da kau da idonta,a harɗe ta ƙaraso gurin dadyn kanta a ƙasa ,hannu ta Dady ya
riƙo yana murmushi ya ce"Ƴar aljanna ya kike"

Kamar me tsoron magana ta ce" lafiya qalau"

"Momyn ku ta gayamin kun fita ke da farrah ,kunyi siyayya,kuɗin sun isa ko kuna buƙatar wasu?

"Am..dam..sun is..

Charab farrah ta ce"Eh dady ba mu gama ba,kuma sai maganar holl ɗin da za'ayi...

"Eh baku da matsala da wanan zanyi komai ni da yayan duk mun shirya komai"

Ko kaɗan Naufal bai gane ba,mamaki yake yi,wani abu xa'ayi..

Bai ƙarasa yin tunanin shi ba Wayar Momy ta fara ringin duk hankalin su ya koma gurin ta.

Ganin mai kiran yasa momy tayi murmushi ta kalli Dady shi ma murmushin yayi,ɗaukar wayar
tayi.

"Assalamu alaikum,Haba hajia tun kafin Ayi Auran zaku rike min ita ,yanzu idan aka yi auran
shikenan"

"A'a hajia ba haka bane,kin san basu dawo da wuri ba ne,kuma...

"To naji yanzu dai ku turomin ita"

Tana gama faɗa ta kashe wayar.

Dady ya kalle ta yana murmushi ya ce"hajia ku"

ya juyo ya kalli Naufal ya ce"Naufal kai Sabreen gida"

"Toh"
Kawai ya faɗa Amma ranshi a ɓace baya son raini Sabreen kuwa ƴar raini ce,bai tsaya jiran
wani abu ba ya fito daga falon yana hura hanci.

Momy ta ce "zo nan Sabreen"

A kunya ce ta isa gurinta,zaunar da ita momyn tayi kusa da ita "Sabreen ki kwantar da hankalin
ki kinji,gobe da sassafe zan zo ni da Farrah mu fita,ki tashi da wuri dan da safe zamu zo"

"To momy"

"A'a ya zaki ce ta tashi da wuri"

Murmushi momy tayi ta kalle shi ta ce" hmm tafi abinki Sabreen yana jira ki gaida hajia"

"To saida safen ku"

"Yawwa ki tashi lafiya suka faɗa a tare.

A hankali take tafiyar har ta isa gurin motar shi,gaban motar ta buɗe ta shiga,bata ce mishi
komai ba.

"Mtseww! ya ja tsaki Sabreen ta tsani tsaki a rayuwarta,bata san lokacin da ita mata ta ja tsakin
ba.

A fusace ya ɗago kai,hannun shi yakai kan lips ɗinta masu taushin gaske ya tsungule su da
kunbar shi,ƙara tayi da ƙarfi ta ce "Waiyo hajia"

"Wa kike wa tsaki ni tsaranki ne,hajia ko kirata ta zo"

Jin xafi yasa ta cije shi a hannu ,yaji zafi ya cire hannun shi da sauri.

Kallonta yayi ya kalli hannun shi inda ta cije shi ɗin,bai ce mata komai ba yaja motar suka fita
daga cikin gidan su,sai da ya raba tafiyar tsakanin gidan su da gidan su hajiar sanan ya tsaida
motar,ganin ya tsaida motor yasa ta ce"Me muka tsaya yi a nan ,ni ka kaini gida"

"Ke ba kin raina ni ba,ni kike so ki maida direba ko,janyo ta yayi jikin shi,ya rungumeta wani irin
abu yaji yarr tsigar jikin shi ta tashe wani irin shuƙi ya kama shi ,bai taɓa tunanin zaiji wani iri
ba,da ko kaɗan baiyi karanbanin haɗa jikin shi da nata ba,ya raina Sabreen ne,kallon kwaila
yake mata.
lokaci ɗaya ya tsinci kanshi cikin wani yanayi gashi ta ƙasa natsuwa sai goga mishi dukiyar
fulaninta take yi a ƙirjin "Waiyo Allah na hajia ,ka sake ni ,ka sake ni,bana so ni ba ƴar iska ba
ce"

Da sauri ya sake ta,yana maida numfashi sama-sama shi kaɗai yasan abinda yake ji,"Meye
yasa nake jan abinda xai sa yarinyar nan ta ƙara rainani? wanan tambayar yake wa zuciyarshi
yana me jin haushin zuciyar shi

Jan motor yayi da gudu nan da nan ya isa gidn,yana tsaida motor ta fito da ƙarfe ta tura
motar"Allah ya isa"

Tana faɗa ta wuce tana tafiyarta hankali kwance.

Dokan kujerar yayi inda ta tashi haɗe da jan wani dogun tsaki yana jin tsanarta a ranshi.

**********

" Alhaji gobe ya kamata ka gayamishi tunda zai ga mutane sun fara zuwa"

Cikin tausasawa ya kalleta ya ce"Xan gayami shi,ki kwantar da hankalinki nasan Naufal ba zai
ja da ni ba,ban taɓa saka shi abu yaƙi yi ba komai girman abun,nasan zaiji wani iri amma na
ɗan ƙankanin lokaci ne"

A haka ya kwantar ma hajia hankalin.

~~~~~~~~~

"ohhh ni Allah ƴar aljanna tun yanzu zaki fara min haka"

Idanuwanta tabb ta kwalla ta ce"Hajia ba zan iya nisa da ke ba,ko yaushe zan kasance tare da
ke,wa gare ni banda ke,hawayen da suka maƙale suka gangaro.

Ita ma hajiar kuka ta fara yi haka suka kwana suna kuka.

~~~~~~~~~~
Haka ya koma gida jikin shi a mace yana ƙara jin tsanar Sabreen, amma wata zuciyar tajin
shauƙin yadda take abubuwanta kai tsaye ba tare da jin shakkar komai wai ta kalli shi ta ce
mishi allah ya isa, shi mamaki ma abin ya bashi, kashe wayar shi yayi gaba ɗaya.

Yau ma irin mafarkin nan yayi,tashi yayi yana keta zufa,haɗe da sauke nannauyan numfashi
"Idan har haka zaki dunga min ki daina zuwar min mafarki" ya faɗa kamar wanda yake jin tsoron
maganar,wankan tsarki yayi ,sanan ya fita zuwa masallaci salar asuba,yana dawo wa ya shige
ɗakin shi,wayar ya kunna,sakonin Haulat ne suka fara sintirin shigowa,number ta ya kira,tayi
ringin tayi har ta katse bai iya kira sau ukku ba iyaka biyu shi ma idan ya matsu yake yin shi.

~~~~~~~~~~~~~

"Yanzu taya xan haɗu da Malama Haulat gashi bani da numberta kuma ban san gidan
su,dole na haɗu da ita,numberta ya kamata na samu"

Hajia ta shigo ta ganta ita kaɗai a zaune kan gado tana magana ita kaɗai "Sabreen ke dawa?

Juyowa tayi ta kalli hajiar a ranta ta ce" *NI* *DA* *MALAMA* *TA*

"eyyah ki dawa kike magana ki kaɗai?

Murmushi tayi ta ce"Hajia ba kowa ina tuno wani abu ne"

"Meye shi?

"Hmm Hajia ta ba komai "

" to na yarda tashi ki je kiyi wanka ,yanzu xaki ga su Momyn ku"

"Toh tana faɗa ta tashi ta faɗa toilet"

~~~~~~~~~~~~

Tana farkawa ta duba wayarta ganin kiran Naufal yasa ta ruɗe ta shiga kiran shi da sauri,a
lokacin yana ɗakin shi yana duba laptop din shi kiran ta ya shigo yana jin ringin ɗin ya ɗau
wayar
ita ta fara magana"Hello dear lokacin ban tashi ba,kuma wayar bata kusa da ni sai yanzu na
tashi"

"ok ba komai,kin tashi lafiya?

"Lafiya lau,meyasa kake min haka dear,dan ina sonka shine na cancanta irin wanan
wulaƙancin"

cikin sigar lallashi ya fara bata hakuri"ba haka ba ne,duk lokacin ina tare da Dadyne mun fita.

"to shikenan bana
iya fushi da kai ko kaɗan"

A haka suka cigaba da fira cikin so da ƙaunar juna.

Suna gama wayar Dady ya kira shi yace mishi ya fito falo,yayi mamaki bai ga su hajia ba ya kalli
dadyn ya ce"Dady ina zu hajia naga ban gansu ba?

"Eh sun fita zasu je gurin su Sabreen wai zasu je gurin gyaran jiki"

Murmushi yayi ya ce"Mata ƴan kwalliya"

Gyaran murya Dadyn yayi ,ya ƙara gyara zama ya tattara dukkan hankalin shi gurin Naufa ya
ce"Naufal ka natsu kaji abinda zan faɗa maka da kunnan basira"

Yadda yaji Dadyn yayi maganar yasa ya tattaro dukkan natsuwar shi yai ƙasa da kai "Ina jinka
Dady"

"Naufal Naufal Naufal,Sau nawa na kira ka?

"Sau ukku!

"To ina son ka ji avubuwa ukku da zan gayamaka,ka ɗauke su ka saka su a cikin kwakwalwarka
da tunaninka"

Zuciyar shi ta fara buguwa da ƙarfin gaske kamar zata fasa ƙirjin shi ta fito.

"Abu na farko Naufal ni na haifeka kuma ina sonka ina alfahari da kai,baka taɓa faɗa min rai ba
,ko na saƙon ɗaya kullum cikin bin umarni na kake,wanan dalilin yasa na son na tausasaka
akan hukuncin da na yanke akan rayuwarka ba tare da naji naka ra'ayin ba,Naufal gobe zan
ɗaura ma aure da Sabreen
Dumm Dumm zuciyar shi ta fara buguwa da ƙarfin gaske wanda tai nasarar sandarar da
tunanin shi komai ya tsaya mishi chikkk ,sai zufa da take keto mishi ta ko ina a jikin shi,gashi ya
kasa ɗaga kai ya kalle Dady.

"Ban san ra'ayinka akan ta ba,Naufal da wanan nake cewa kayi hakuri.

"Abu na biyu Naufal Inhar ka ɗauke ni uba to ina so ka ɗauke Sabreen a matsayin matarka
kuma ƴar uwarka,ko kaɗan karka nuna mata ƙiyayya idan ka nuna mata ƙiyayya ban yafe maka
ba..

A zabure ya ɗago kai da jajayen idanuwan shi ya kalli Dadyn na shi.

"Sabreen ina sonta fiye da yadda nake son ka,idan ka cutar da ita ko bayan ba raina ban yafe
maka ba,Naufal,kuma idan har ka ɓata mata rai ta zubda hawaye Naufal ban yafe ma ba.

"Sai Abu na ukku wanda shi zan roƙe ka akai ,idanuwan shi sukai jajir muryarshi ta fara rawa
abinda bai taba faruwa ba kenan tunda Naufal yazo duniya bai taɓa jin mahaifin shi a irin
wanan raunanniyar muryar ba.

"Naufal dan allah dan annabin Rahma Naufal ka riƙe amanar marainiyar allah nan,ba dan hali
na ba...

"Dady...dad..dady ka..

"A'a naufal wanan ba umarni ba ne,roƙan ka neke yi,Sabreen amana ce a guri na,zan danƙa
mata ita,Naufal ka riƙe ta amana.....
.
[12/16, 5:36 PM] �° � D°�⭕Y: _ �σѕт у �яσυρ � � �уρє �αυѕα
�σνєℓѕ σσк нαтѕαρρ 08064400100_
[12/16, 5:41 PM] �° � D°�⭕Y: *NI* *DA* *MALAMA* *TA*

*By*
*fatima* *Batula*

*~✍✍GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍✍~*
Page 10
...................................................

مالسلا_* مكيلع ةمحرو
الله اكربو *_هت

مسب*_* الله نمحرلا _*ميحرلا
_*Manzon Allaah(ﷺ)* *ya ce;{IDAN ALLAAH YAYI NUFIN MUTANEN WANI GIDA DA
ALKHAIRI, SAI YA MUSU JAGORAR (SAKA) 'KOFAR SAU'KIN HALI(A GIDAN).}*_
°
```[Silsilatus Saheeha;523]```

_Duk gidan da suke da saukin hali to lallai Allaah Ya na nufin su da alkhairi. Arziki ne babba
mutum ya siffantu da saukin hali. Allaah Ya azurta mu da shi. Allaahu a'alam._

```Allah ta'ala yasa mudace```

ﻚﻧﺎﺤﺒﺳ*_ ﻢﻬﻠﻟﺍ ,ﻙﺪﻤﺤﺑﻭ ﺪﻬﺷﺃ ﻥﺃ ﻻ ﻪﻟﺇ ﻻﺇ ،ﺖﻧﺃ ﻙﺮﻔﻐﺘﺳﺃ ﺏﻮﺗﺃﻭ _*​​.ﻚﻴﻟﺇ

................................................
Kasa ƙarasa maganar Dady yayi,jikin shi ya mutu ga kwalla ta cika mishi ido.

Cikin wani irin yanayi Naufal ya ce "Dady baka yarda dani ba ne, Dady komai girman abu zanyi
shi idan har ka saka ni yinshi k....

"Ba haka nako son ka ce ba Naufal ina son naji ka ɗau alkawarin da zan baka ne"

Cikin raunanniyar murya Naufal ya ce"Na ɗau alƙawari zan riƙe Sabreen,zan kula da ita kamar
yadda zan kula da kai na,ba zan bari wani abu ya faru da ita ba,nayi alkawari"

wata irin raguwar ajiyar zuciya Dady ya sauke"Kasan daraja da muhimmanci alƙawari ,ba sai na
tunatar da kai ba.

"Naufal tun farkon rayuwarka kake min biyayya,amma ban taɓa jin daɗi abunda ka min irin na
yau ,na gode Naufal"

"Dady dan allah ka daina gode min"

"Dole ne,amma Naufal karka yarda ka ƙara min alƙawarin da ka ɗauka,karka wulaƙanta

Sabreen ,wllh Allah idan makamancin hakan ta faru zan iya fushi da kai ,zan iya rabu da
kai,daga ranar ma karka ƙara kira na da sunan Dadyn ka"

Wasu zafaffan hawaye suka fito mishi zuciyar tana radaɗi da zafi,yau shi mahaifinshi ke
gayama irin wanan maganganun masu zafi gaske "Dady ba zan ƙara alƙawari"

"Na sani Naufal kai jini na ne,ina ƙara ma ƙarfi ne yadda zaka riƙe da muhammanci,Sabreen
tana sonka ita ta fara magana,na san kai ma kana son ta"

A razane ya ɗago yana kallon dadyn maganar da yayi tana mishi yawo a cikin kaI"Sabreen tana
sonka ita ta ce tana sonka" kai anya ina wa...

"Naufal bamu ga ta zama ba,tashi mu fita gobe ne fah

Gaban shi ya faɗi" gobe gobe!!

"Ba'ayi biki haka ba,bakin ƴaƴan gata ka tashi mu fita,baka da wani abu da kake son ayi"

ƙasa yayi da kai,dan kanshi yayi nauyi.

"Naufal ko auran dole ne"

"uhm ina tunanin abinda za'ayi ne"

"to mu fita"

dadyn ya fara fita yabar nan,da ƙyar ya iya jan jikin shi,ba abinda yake tsorata shi irin da yaji
Dady ya ce wai sabreen ta ce tana sonshi,tabbas yakan sabreen bata son shi,ko kaɗan" to
meyasa zata min haka? dan tsana"

ya tambayi kanshi ya kuma bawa kanshi amsa"meyasa Why?Sabreen ke wacce iri ce kin
dagula min rayuwata,da kika haɗa rayuwar mu tare,bana sonki bana ra'ayinki amma saida kika
cusa kanki a rayuwata meyasa baki gane bana sonki ba, am helpines,ba zan iya komai ba
Sabreen kin cuci ni kin....
"Naufal kayi sauri ina jiranka, dady ya katse mishi tunanin daya ke yi"

~~~~~~~~~~~~~

Su Sabreen manya ana chan ana gyaran jiki ita da farrah harda Momy ma, tasha lalle wanda ya
fito da yar madaidaiciyar hasken jikinta,yaƙe kawai take yi amma bata jin daɗi a zuciyarta.

"Toh yanzu taya zan haɗu da malama,ko na bari bayan an ɗaura aure"

"Keeee tunanin me kike yi Aunty Amarya"

Ɓata rai Sabreen tayi"Farrah ki daina ce min aunty bana so"

"To matar yaya"

harara da gallama ta "waye matar yaya?

Dariya Farrah tayi "Kai Sabreen lamarin ki sai ke,ranar da kuka ,kina son yaya ya ɗaura muku
aure amma yau wa waye matar yaya kike tambaya"

"ina son Yaya allah ya kyauta me xanyi da ɗan kilibibin nan"A zuciyarta tayi wanan maganar ,A
fili kuwa harar ta tayi.

Momy bata gurin su kaɗai ne,ita ta koma gida dan tayi wasu aikin.

Sun daɗe har bayan maqrib suna nan ana abu ɗaya.

~~~~~~~~~~~~

Bayan su dadyn sun dawo ya tambayi momy ina su Sabreen ta gayamishi suna gurin gyaran
jiki,Ɗadyn ya ce Naufal ya je ya ɗauko su.

***********

Wayar Farrah ya ya kira"Hello Ki fito ina waje" Ya katse wayar

Kallon Sabreen farrah tayi"Angon ya ƙaraso"

"Mitsewww!

"Ni tashi mu je

8 / 20