NIDA MALAMATA BOOK COMPLETE

Author :  Fatima Batula Category :  Love

Chapter   7 / 20

18K to 21K   out of 57.2K words



"ina kwana dady

"Lafiya lau Naufal baka tashi ba ne?

"Na tashi dady

"To ka fito ina jiranka a falo"

"to ganin nan zuwa ,tun kafin ya rufe baki ya tashi ya fito,a ranshi yana tunanin me yasa dadyn

nashi cikin farin ciki tsakanin jiya da yau,sanin ba zai iya bawa kan shi amsar ba yasa shi ya bar
maganar.

A Falo ya same su,da dukkan alama suna cikin jin daɗi,shi ma aro annuri yayi yasa wa fuskar
shi,xai da ya zauna sanan ya kalli momy cikin kulawa ya ce "Good morning

"Morning Naufal

Farrah ma ta ce"Ka tashi lafiya Yaya Naufal"

"Lafiya lau"

Allah sarki momy tana son Sabreen amma bata son ya aure wacce baya so,dan ƙiyayyar namiji
bala'ai ne.

A tare suka yi breakfast cikin son da ƙaunar juna,bayan sun gama Dady ya kalle shi cikin
kulawa ya ce mishi"Naufal tashi muje yau akwai abubuwa masu muhimmanci da xamu yi"

Cikin rashin fahimtar abinda dadyn ke nufi ya ce"To Dady A office ne?

"A'a wanan yafi aikin offfice tashi dai mu tafi"

A ranshi ya fara tunanin wani irin avu ne wanda yafi aikin su mahimmanci.

"Gidan hajia zamu fara zuwa"

"to Dady ya faɗa ba komai a ranshi.

~~~~~~~~~~~~~

Zaune take akan tanƙameman gadonta ,gaba ɗaya jiknta ya mutu sakamaƙon mafarkin da tayi
Naufal ya tsare da ido yana mata wani irin kallo wanda ƙaramar kwakwalwarta ta ƙasa gane ina
kallon ya dosa.

"Ina haba Sabreen tun yanzun zaki karaya,dan ɗaukar fansa zaki yi fa,bai kamata ki karaya ba"
Zuciyarta ke mata wanan maganar a fili ta ce haɗe da yin murmushi "Sabreen ƴar aljanna ƴar
gatan hajia,duk abinda nasa gaba sai nayi shi"

Zuciyarta ta ƙara yin ƙarfi duk wani tsoro da fargaba ya fito,Cike da izza ta tashi tai toilet fuskar
nan ɗauke da annuri.

A Falo suka iske hajia ,hajia tana ganin Naufal ta sake wani irin murmushi,ta ce "Mutan India
manya Har ka fara ƙamshin dogon buri"

Cikin rashin fahimtar zancen ta ya ce"Ina kwana hajia"

"Lafiya lau,yanzu fah ka ɗau hanya"

Banza yayi da ita tunda shi bawai ya iya hausa sosai ba ne,baya gane magana cikin
magana,dan ma su momy suna mishi hausa da ba zai iyata sosai ba,a ranshi ya ce"To yau
kuma ita ma naga tana cikin farinciki Sabreen fa?

"Sabreen meye nawa da ita,duk a zuciyar shi yake wanan maganar,ya kas....

"Naufal hau sama ka kira Sabreen"

Hajia ta katse mishi tunanin da yake yi,kallon ta yayi ta sakar mishi wani irin murmushi,kallon
dadyn yayi shi ma murmushin yake yi.

Tsaye ya miƙe ya hau saman a ranshi ya faɗin"Meyasa hajia zata aike ni ɗakin ta?

Tura ƙafar yayi,lokacin ta fito daga toilet daga ita sai towel dan ƙarami iya karshi gwiwa.

Jin an buɗe kofa yasa ta juyo"Waiyo!! ta faɗa a tsora ce.

Ƙamewa yayi a tsaye zuciyar shi tana bugawa da karfin gaske kuma ya kasa sauke idanuwan
shi da suka kafe akan brest ɗinta,lokaci ɗaya jikin shi ya mutu wani irin bakon yanayi ya fara
ziyarta zuciyar shi,wanda ya ke tunanin yafi ƙarfin ya kira shi da sha'awa.

"Laaa.....fiii....y...yaa...me...y..yaaa....k.k..ka.wo..ka.."Ta faɗa a ruɗe.

Bai ma san tana magana ba,dan gaba ɗayan hankalin shi baya tare da ita.

Idanuwan shi ta kalla ai sai ta ƙara ruɗewa ganin yadda suka chanja kala,gashi ta ga nonowan
ta ya zubawa ido,A ruɗe ta faɗa kan gadon ta ƙudundune da bargo tana ihu.

Ringin ɗin wayar shi ne yai nasarar dawo da shi haiyacin shi,lumshe idon shi yayi waɗan da
suka rine.

Da ƙyar ya iya sarrafa hannun shi gurin lalubo wayar da ke ringin ɗin,ringin ɗin kiran Haulat
daban ne amma saboda tsananin shiga wani irin yanayi bai iya tantance ringin ɗin ba.

ya san ko ya ɗauka ba zai iya magana ba ,yasa ya kasa ɗaukan,ga shi kafafuwan sun mishi
nauyin da zai iya saukar da kan shi ƙasa.

Hawaye ne taji sun fara bin fuskarta a hankali ta ce "daman ɗan iska ne! kuma zan aure shi"

Tuno irin yadda taga ya kafe nonowanta da ido tayi haba sai hawaye shaaa kamar an kunna
famfo.

Ko kaɗan su hajia basu kawo komai a ransu ba ,daman tayi hakan ne dan suyi magana ita da
dadyn.

Jin sheƙar kukanta yasa shi ya ƙasa shigowa ɗakin "Keee ya daka mata tsawa,uwar me kike
yiwa kuka,wani abu ne ya faru banza kawai kiran ki aka ce na zo nayi"

Yana gama faɗa ya fita a fusace ranshi a ɓace,kan me zata yi kuka wani abu yayi mata,ji ƙarfin
hali irin na Naufal ko tabarmar kunya dai zai naɗe.

Ai wani sabon kukan Sabreen ta ƙara fashe wa da shi,abinda ya ɓata mata rai tsawar daya
ɗaka mata,wacce saida tasa hanjin cikin ta yin kuka,dan tsoro,kuma meye nashi idan tayi
kukan,ba shi ne yaja ba"

"Ko me zaka min ba zan fasa aurenka ba,kuma na baka bashin tsawar da ka dakamin amma
bazan yafe ba"

Ita kaɗai tai tai maganganun ta,tana kuka.

baƙin glass yasa kafin ya sauko kasan,yana isa hajia ta ce mishi

"Tana ina?

"Gata nan zuwa"ya faɗa cikin wata irin murya,fita yayi daga falon yaji daɗi da dadyn bai hanashi
ba ,yaɗai ce mishi ya jira shi a motor

A motor ya zauna ya jingina kai da sitiyarin motor zuciyar shi tana bugawa,kamar wanda bai
taɓa ganin makamancin haka ba,yasha ganin mace tsirara amm bai taɓa jin irin na yau ba,ko
Haulat tasha ɗaukar hoto da towel a jiknta ta turomishi,amma yau sai yaji wani irin abu wanda
ya kasa ganewa.
"Mtseewww me yakai ido na jikin wanan wawiyar yarinyar yanzu zata raina ni,dan taga irin
kallon da na mata mtseww"

Ya faɗa cike da jin haushin zuciyarshi da idanuwan shi.

Hajia da dadyn sun gama magana akan ranar juma'a za'a ɗaura aure,hamshaƙin aure irin na
ƴaƴan gata,Sanan sunyi magana akan gidan da zasu zauna da komai da komai,sanan dady ya
bata maƙudan ƙuɗi dan yin wasu abubuwan,sanan ya tashi a falo ya tarar da shi.

"Ya Aka yi ne Naufal"

"Ba komai dady ya aro murmushi ya ɗaurawa fuskar shi"

Hoto nan gidaje Dady ya nuna mishi "Wanne yafi kyau Naufal"

Gaba ɗayan gidjen sun haɗu kamar ba'a 9j ba,saida ya tsaba wani madaidaici mai ɗankaran
kyau sanan ya nunawa Dady ya ce"Waw dady wanan yafi kyau"

Murmushi yayi sanan ya ce"Sabreen zata so shi ko"

"Sabreen me ya kawo maganar Sabreen a nan kuma?ya tambayi kan shi a zuciya murmushi
yayi tuno komai za'ayi sai idan yayi mata sanan ake yi.

"Eh dady zai mata kyau ai yana da kyau"

hhhhh Shiyasa baka da masoya Naufal dan baka gane komai.

Murmushi dadyn yayi "Yawwa.

********
Ganin ta daɗe bata fito ba yasa Hajia ta shiga ɗakin ganin ta a kwance yasa hajiar ta ruɗe"Ƴar
aljnna lafiya? ta ƙarasa gurinta da sauri.

Tana jin hajia ta ƙara duƙunƙunewa kamar me barci.

"Ƴar aljanna buɗe mana lafiya"

Cikin irin muryar barci ta ce"Barci nake ji hajia ki barni nayi"

Cikin nuna kulawa ta ce"Kin tabbata barci kike ji"

"uhm.. ta fara kukan shagwaba ta ce"Barci hajia ki barni"

"To ya isa haka,ta faɗa ta tashi ta fita.

*******

Kallon farrah momy tayi ta ce"farrah Naufal zai aure Sabreen cikin satin nan"

"What? ta faɗa haɗe da zaro idon.

"Taya momy Ya Naufal ɗin?

"Hmm nima saida naji wani iri anya kina ganin ba za'a zamu matsala ba kuwa"

"Tabbb gaskiya momy da kamar wuya a ƙi samun matsala dan Yaya ma yana da budurwa"

Jikin momy ya mutu "Waya gaya miki yana da budurwa farra?

"Yasan da maganar auren?

"A'a me sani ba"

"Hmm to saidai kawai muyi addu'a dan yaya dai baya son Sabreen ita ma ɗin,amma zasu dace
ita ce daidai ce,idan ya fara sonta zai chanja,na kam naji daɗi bari ma taje gurinta"

Tana faɗa ta tashi jiki na rawa,ita kuwa Momy jikinta ya mutu tausayin Naufal ya
mamayeta,amma ya zata yi.

Cikin zumuɗi da rawa jiki Farrah ta isa Gadan a falo ta isake hajia ta washe baki ta ce "Hajiya
ashe muna da babban biki"

Ita ma hajiyar washe baki tayi "Bari dai farrah zamu sha biki ,ya hajiar ta ku"

"Tana lafiya ita ta gayamin ma,hajia ina Sabreen"

"Tana ɗakinta barci take yi,amma halan ta farka"

ai tun kafin hajiyar ta gama magana ta haye sama.

Tana isa ɗakin ta faɗa kan gadon"yeeeh Amaryar Yaya,shi ne ba za'a gayamin ba na shirya
faty"

Sabreen tana jin Farrah ce ta tashi yana mutsike fuska cike da ƙarfin hali ta kalle farrah tana
murmushi.

Dungurinta tayi akai tana dariya ta ce "Gayamin yaushe kika fara son mutumin naki?

Bata son ta gaymata dan kar da gayawa hajia,murmushi tayi ta ce"Tun shekaran jiya na nayi
mafarkin shi"

Dariya farrah tayi sosai "Ah lallai wato mafarki wani irin mafarki?

"Ke nidai karki ishe ni,da tambayoyi kamar wata ƴar jarida,yanzu dai faty nake so a haɗa.

Ƙara farrah tayi"Yeehhh ai lallai ana son yaya Wai nifa abin mamaki yake ban Wai Sabreen ɗin
d na sai ƴar aljanna ƴar gatan hajia wai ita ke son Yaya Naufal ɗan iyayi da kinibibi"

"To meye"

"A'a ba komai duk love ne,amma abin da mamaki fa"

"Ni kidaina mamaki ,ki tsaya muyi magana"

"To na tsaya Aunty Sabreen"

Doka sabreen ɗin ta kai mata"Waye Aunty?

"Sabreen amaryar yaya"

"Ke fa ai"

"Ni me? yaushe ne bikin naji ance cikin satin nan ?

"Jibi!

ƙara farrah ta buka ta haye kan Sabreen ɗin tana ihuu.

"Wai hajia farrah zata kashe ni"

ɗaga ta farrah tayi tana dariya "Lallai Sabreen tun yanzu to gaba wa zaki kira ya taimake ki?

Cikin rashin fahimta ta ce"Hajiata mana"

Dariya farrah tayi sosai ta ce "Akwai wata ƙawar momy tana gyaran jiki na amarya ya kamata
momy ta kai mu gobe,abubuwan ne sun matse kamar wata wacce ta ƙagara za'a sa biki kwana
ukku,haba ace mai taƙama family zasu aurar da yara biyu yaran ma ƴan gata ace ba abinda
za'ayi haba,gaskiya ba zai yuwu ba yadda nake da buri akan bikin wani daga cikin ku"
Ta kai hannu ta doki cinyarta,ƙara Sabreen tayi"Ann Haba farrah ke mugu ce daman"

Dariya farrah tayi ta ce"Tab akwai aiki kuwa yaya zai wahala,to nidai gasky tashi yanzun nan mu
je kasuwa,muyi siyayya ya kamata ma kuyi photo fa wanda za'a sa a memo da jaka da wanda
za'ayi amfani da shi gurin faty"

Kallon farrah Sabreen tayi "to yanzu ya za'ayi"

"yawwa ina da pic ɗin yaya zai muje ki ɗauka sai a haɗa kamar kunyi tare,daga nan sai muje a

haɗa mana memon da jaka"

"to bari ta saka kaya" ta faɗa tashi tayi daga kan gadon ta je gurin drower towel ɗin ya zamo.

"Waiyo ni gaskiya Sabreen yaya zai ja kaya irin wanan hips haka"

Cikin rashin fahimtar abinda Farrah ke nufi ta watsa mata harara ta ce"To yanzu ina zamu samu
kuɗi?

"Dady zaki tambaya"

harararta ta ƙara "baki da hankali kawai sai na tambaye shi kuɗi.

"Ke nidai yi ki saka kaya kuɗi ba matsala ba ne hajia zata ba mu,momy ma nasan zata ba mu"

Tana sa kaya suka sauko ƙasa farrah ta gayawa hajia zasu fita su fara shiri,hajia taji daɗi sosai
ta basu kuɗi sosai,har zasu tafi ta ce su jera tare zata gurin Momy suyi magana.

Ko da suka isa gurin momy ,momyn tana ganin su cikin farinciki ita ma farincikin ya
kamata,musamman da taga Sabreen ta tuno da maganar da dady yayi"Idan har jini na ke yawo
a jikin Naufal to jinin Sabreen ma yana yawo ajikin shi zai so ta idan har yana so na"

Hankalinta ya kwanta sosai,ta saka a ranta zai so ta ne.

Ita ma ta ƙara musu kuɗi masu yawan gaske ta kuma kira idan zasu je ai mata makeup sanan a
haɗa hotonsu tare,kuma a haɗa komai da komai wanda za'a saka photon,kuma ta ce zata kama
tsadaddan holl wanda za'ayi fatyn,sanan suka fito,ita kanta hajia daɗi ya mamayeta ainun.

.
[12/16, 5:35 PM] �° � D°�⭕Y: _ �σѕт у �яσυρ � � �уρє �αυѕα
�σνєℓѕ σσк нαтѕαρρ 08064400100_
[12/16, 5:36 PM] �° � D°�⭕Y: *NI* *DA* *MALAMA* *TA*

*~✍✍GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍✍~*

*By*
*fatima* *Batula*
Page 9

.............................................

مالسلا_* مكيلع ةمحرو الله اكربو _هت

”_* مسب الله نمحرلا _ميحرلا

_*ZIKIRAN DA AKEYI BAYAN IDAR DA SALLAH*_
:
.
_*(1)* -“Astagfirullahi” sau uku,(3)_
.
_*(2)*“Allahumma Antas Salam, Wa minkas Salam, Tabarakta Yaa Zal Jalal Wal Ikram”_
_*[Muslim ne ya rawaito shi].*_
:
_*(3)* -“Laa ilaha Ilal Lahu, Wahdahu La sharika Lahu, Lahul Mulku, Walahul Hamdu, Wa huwa
Ala kulli Shai’in Qadiir._
.
_*(4)* Allahumma La mani’a lima aadaita, Wala mu’udiya lima Aaxait, Wala Yanfa’u Zal Jaddi
Minkal Jadd”_
_*[Bukhari ne ya rawaito shi].*_
.
_*(5)* -“Laa ilaha Ilal Lahu, Wahdahu La sharika Lahu, Lahul Mulku, Walahul Hamdu, Wa huwa
Ala kulli Shai’in Qadiir._
_La haula wala quwwata illa billahi, Laa ilaha illal Lahu, Wala Na’abudu Illa Iyyahu, Lahun
ni’imatu Walahul Fadlu, Walahus sana’ul Hasan, Laa ilaha Ilal Lahu, Mukhlisina lahudden,
Walau karihal Kafiruun”_
_*[Muslim ne ya rawaito shi].*_
:
_*(6)* -“Subhanallah, Wal Hamdu Lillahi, Wallahu Akbar” Sau talatin da uku.33_
:
_*(7)* “Laa ilaha Ilal Lahu, Wahdahu La sharika Lahu, Lahul Mulku, Walahul Hamdu, Wa huwa
Ala kulli Shai’in Qadiir”_
_*[Muslim ne ya rawaito shi].*_
:
_*(8)* La Ilaha Illallahu Wahdahu La Sharika Lahu Lahul- Mulku Wa Lahul-Hamdu, Yuhyi Wa
Yumitu Wa Huwa ala Kulli Shai'in Qadir.._
_*sau goma(10)bayan sallar Asuba da magariba*_
:
_*(9)* -“Allahumma A’inni Ala Zikrika, Wa shukrika, Wa Husni Ibadatika”_
_*[Abu Dawud ne ya rawaito shi].*_
:
_*(10)* - Karanta ayatul Kursiyyi, da suratul Al-ikhlas, da Falaqi da Nasi *dai- dai.......1 -1*_
_*Sanna (Sau uku-uku)3-3* bayan sallar magariba da asuba_
_*[Nasa’i ne ya rawaito shi].*_
:
_*(11)* - Fadin “Allahumma Inni As’aluka Ilman Nafi’an, Wa zirqan Xayyiban, Wa amalan
Mutaqabbalan”_ _*[Ibnu Majah ne ya rawaito shi]*_

_Bayan an yi sallah daga sallar asuba._
:
_An kar6o daga *Aisha – Allah ya yarda da ita* ta ce, “Manzon Allah ( ىلص الله هيلع ملسو ) ya
kasance yana bude sallah da kabbara, karatu kuma da “Alhamdu Lillahi Rabbil Aalamin”.
Hakanan ya kasance idan ya yi ruku’u baya daga kansa sama, kuma baya sunkuyar da shi
qasa, sai dai yana sanya shi tsakanin haka. Idan ya dago kansa daga ruku’u baya sujjada har
sai ya daidaita a tsaye, hakanan idan ya dago daga sujjada baya komawa sujjada har sai ya
daidaita a zaune. Ya kasance yana faxin tahiya a dukkan tsakanin raka’o’i biyu. Hakanan ya
kasance yana shimfida kafarsa ta hagu, ya kafe ta dama (a zaman tahiya). Ya kasance ya hana
zaman shaidan (zama akan dugadugai), yana hana mutum ya shimfida tsintsiyar hannunsa
kamar yadda dabbobi suke yi. Yana qare sallah
:
ﻚﻧﺎﺤﺒﺳ*_ ﻢﻬﻠﻟﺍ ,ﻙﺪﻤﺤﺑﻭ ﺪﻬﺷﺃ ﻥﺃ ﻻ ﻪﻟﺇ ﻻﺇ ،ﺖﻧﺃ ﻙﺮﻔﻐﺘﺳﺃ ﺏﻮﺗﺃﻭ ​.ﻚﻴﻟﺇ
.............................................
kallon Momy Hajiya tayi ,tana murmushi ta ce"Hajiya kinji yadda muka yanke shawara ba mu
tambayi ra'ayinki ba"

"Ah haba Hajiya ba komai kun isa ne,kuma shawarar tayi daidai naji daɗi sosai, ubangiji Allah
ya haɗa kan su,ya basu zaman lafiya da zuri'a ɗaiyaba"

"Amin ya Allah"

"Bari nima na tashi ba'ayi biki haka ba,naje nayi siyayya na gaiyaci ƴan uwa da abokan arziƙi"

"To gaskiya kuwa abin ne yazo da sauri"

Bayan sun gama maganar su Momy ta kawo Hajia gidan ta,ita kuma ta wuce kasuwa daga nan
ta tafi gidan su gurin iyayan ta.

~~~~~~~~~~~~~

Tun Safiyar ranar da Haulat ta tashi take jin ɓacin rai duk saboda Wayar Naufal a kashe tun jiya
da ya kashe bai kunna ba, da safen ma ta kira bai shiga ba,ranta ya ɓaci haka nan ta tafi
makaranta ranar student sun sha zagi da bala'i ,ganin bata ga Sabreen ba yasa ta ɗan ji
daɗi,amma bata ji labarin wani abu ba,akan sharrin da ta haɗa mata ba.
Tun a makarantar ta kira shi yafi sau biyar amma yaƙi ɗauka a lokacin suna tare da dady.

Haka ta dawo gida jikinta ya mutu.

"Haulat wai ke ba zaki ragewa kanki wanan irin mugun son da kika ma wanan mutumin ba"

Saida ta ɗago tai mata wani irin kallo sanan ta ce"Ni ban san meyasa yaƙi ɗaukar wayata ba

tun ɗazun nake kiran shi,ko yana fushi da ni ne"

"Fushen me?

saida taja guntun tsaki sanan ta ce"Shi wani iri ne kamar bai waye ba,ni na ɗauka ma baya
sha'awa ne"

"Kamar ya kika ce a india yayi karatu"

"A nan ne ,amma karki ga yadda gudu na,idan kika ga yamin kiss to ba ƙaramar sha'awa yake ji
ba,ni haushi nake ji "

"Kai Haulat,yanzu ke da zaki yi alfahari da hakan,kana gani dai kowa burinshi ya taɓaka,amma
har ki samu wanda ba jikin ki yake so ba,amma kina wata magana,kin san komai haulat a.....

tun kafin ta ƙarasa maganar ta katse ta"ke allah dan baki ganshi ba ne,amma ina tabbatar miki
duk macen da ta ganshi sai taso wani

7 / 20