Author : Fatima Batula Category : Love
tureta da ƙarfi har saida ta ɗan bugu ta murfin kofar.
Gaba ɗayan ilahirin jikin shi rawa yake yi ga idanuwan shi sun chanja kala a yadda yake ji ba
zai iya tabuka komai ba,amma da yake zuciyar na buguwa da ƙarfin tsoro ta haddasa mishi
ƙarfi,wanda hakan yasa ya maida rigarshi ya kuma gyara wandon daya kusa fita daga jikin shi.
buɗe motar yayi ya turata ta fita,kai ka ce ba zata ƙara kula shi ba,dan yadda ya turota ɗin duk
wacce ke da zuciya a ƙirjinta kuma tana bugawa ba zata ƙara kula shi ba,amma kasan cewar
anyi hakan yafi a ƙirga yasa nasan sai ta ƙara kula shi.
Jan motor shi yayi da ƙarfin gaske yabar nan a kasa.
~~~~~~~~~~~~~
Da Sauri ta tashi a firgici sakamokon mafarkin ta tayi Naufal ya tsareta da idanowan shi yana
mata wani mugun kallo.
A fili ta ce "ta allah ba taka ba kurwata tafi ƙarfin ka" kamar yana ganin tayi maganar haɗa
murguɗa baki da harara.
Zaukowa tayi jikinta duk ya mutu toilet ta shiga ta watsawa kanta ruwan sanyi.
Bayan ta fito da saka kaya mara nauyi duguwar riga ce baƙa tayi mata kyau sosai ko mai bata
tsaya shafawa ba ta sauko ƙasa.......
.....................................................................
[12/9, 1:11 PM] ° D°⭕Y: _ σѕт у яσυρ уρє αυѕα σνєℓѕ
σσк нαтѕαρρ 08064400100_
[12/9, 1:13 PM] ° D°⭕Y: *NI* *DA* *MALAMA* *TA*
*By*
*fatima* *Batula*
*Dedicated*
*~✍✍GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍✍~*
_________
Page 6
_________
_*Manzon Allaah(ﷺ)* *ya ce;{IDAN KANA DA HALAYE HU'DU, TO KAR KA DAMU DON KA
RASA WANI ABU NA DUNIYA; TSARE AMANA, GASKIYAR MAGANA, KYAWUN HALI,
SASSAUCI A CIN ABINCI.}*_
```[Sahihut Targib;1718]```
_Duk wanda Allaah Ya azurta da Wa'yannan halayen guda hudu to ya samu arzikin Duniya da
Lahira, kada ya damu don ya rasa wani abu na Duniya, don ya riga ya samu abubuwan da suka
fi alkhairi. Allaah Ya azurta mu da su. Allaahu a'alam._
```Allah ta'ala yasa mudace```
Na gode na gode sosai da sosai allah yabar kauna ke ɗin dai ta hannun daman batula.
.
Ba kowa a falon,daman tayi tunanin hakan dan tasan lokacin da Hajia ke zama a falon,zama
tayi akan kujera ta kunna tibi,gaba ɗaya hankalin ta ya koma akan film ɗin da ake yi.
"Ƴar Aljanna" da ƙarfi Hajiya ta kirata.
A tsorace ta juyo "Na'am Hajiya ta"
"Sai kiran ki nake yi,ki zo na baki abinci"
cikin shagwaɓa ta ce"Na ci da kai na,yanzu na girma ba sai kin ɗinga bani abinci ba"
"To ni baki girma a guri na ba"
Dariya tayi sosai sanan ta ce" na sani ni yarinya ce a gurikin ki,kuma bana son na girma a
gurinki , amma a idanan wasu kallon yarinya suke min,kuma ni na girma,a zuciyarta ta ce "Irin
su Naufal"
Cikin shagwaɓa ta kwanta jikin Hajiar ta ce"Hajia gobe ina son zuwa makaranta"
"To Ƴar aljanna allah yakai mu da rai da lafiya"
"Amin hajiyata"
~~~~~~~~~~~~~
Ko da ya isa gidan nasu ba kowa falon yaji daɗin hakan dan duk wanda ya ganshi a irin wanan
halin yai yayi zargin wani abu.
Yana shiga ɗakin shi ya faɗa bayi ya shiga ya daɗe a bayin yana zubawa kanshi ruwa kafin ya
fito daga bakin.
Kan gadu ya faɗa yana kallon sama a hankali yake lumshe idanuwan shi haɗe da sauke wata
irin ajiyar zuciya ,a hankali ya buɗe baki ya ce" Why! Why Haulat idan kina min hakan wata
rana ba zan iya control ɗin kai na ba"Runtse ido yayi,ya san halin mahaifin shi,da irin tarbiyar
daya bashi.
Ya daɗe a hakan kafin barci yai awan gaba da shi.
Duniyar mafarki ya faɗa,bari na bishi na ɗauko mana rahuto..⛹♀
Wani guri ne mai mugun kyau wanda tsayawa rubuta yadda tsaruwar shi take faɗa lokaci ne.
"Meye sa kike tafiya ki barni bayan kin ɗanɗana min zumarki wacce ki sa na fita haiya shi na"
Murmushi naga tayi sanan ta ce "Kai ne baka shirya zama da ni ba"
Idanuwan shi suka kaɗa sukai ja,ilahirin jikin shi ya mutu,yanyo ta yayi jiki ba ƙwari ya shiga
kissing ɗinta " uhmm....huuum.. na shirya zama da ke,ki zauna da ni ba zan iya rabuwa da ke
ba....sanbato yai tayi kamar sabon kamu.
Sunyi nisa sosai har ya fara gigicewa,ta fara jan jikinta tana faɗin "Kabar ni" ita kanta da ƙyar
tayi maganar.
"kar...k..kar...min..h..hak.. kasa yin maganar yy dan numfashin shi yana kokarin
ɗaukewa,hawaye ne ya fara bin kyakyyawar fuskarshi har sautin kukan yana fiɗa.
Ita kuwa ƙara janye jikinta take yi daga na shi,faɗa ya fara yi da numfashin shi yana faɗin"karki
min haka!!!!!
Da sauri ya farka da kalmar "Karki min haka" ga numfashin shi yana harɗewa,kokarin daidaita
numfashin ya fara yi,ya daɗe kafin ya samu numfashin ya daidaita,wata irin nannauyar ajiyar
numfashi ya fara yi,dafe kanshi yayi haɗe da runtse idanuwanshi.
Yana jin wani irin abu yana yawa a zuciyarshi,ko kaɗan bai ji daɗin mafarkin ba.
Ya ɗau sama da minti talatin yana sauke ajiyar zuciya kafin ya samu ya shiga toilet nan ma ya
daɗe yana watsa ma jikin shi ruwan sanyi kafin yayi wankar tsarki ya fito.
Yana fitowa kiran Haulat ya shigo wayarshi har ta kusa katse sannan ya ɗauka shiru dukkan su
suka yi,daga bisani ta ce mishi a hankali cikin wata irin murya wacce tasan tana kashe mishi
jiki"Naufal dear!
Saida ya runtse ido sanan ya ce mata shi ma a hankali "Yess dear!
Kina son mu faɗa halaka koh?
Taɓe baki tayi kamar tana kallon shi"Ba halaka ba ne ,kawai dai muna ɗan rage zafi ne,kuma ai
aure zamu yi to meye"
Hura hanci yayi a ranshi ya ce"Ban san da wani yare zan fahimtar da ke ba Haulat"
A fili ya ce"Haulat mu manya ne kuma muna da addini ya hana mu zina,wanan abun da kike
kokarin ki ga munyi zina ce"
Taɓe baki take yi ,ta tsana wanan wa'azin da yake mata,dan ma karya ishe ta ce "Eh gani
nan,dear momy tana kira na later" tana faɗa ta kashe wayar haɗe da jan tsaki a fili ta ce "Ni ban
taɓa ganin handsome guy kamar ka ba,gashi a india kayi karatu amma duk a banza tunda baka
waye ba"
To idan baka mutu ba zaka ga abubuwa wai yanzu fa idan mutum mai aikata zina bai waye ba
tirrr allah ya tsare ya tsare zuciyar mu amin ya rahimm.
~~~~~~~~~~~~~
Duk da kasancewar ta tashi jikinta ba ƙwari amma haka nan ta fara shirin makaranta,bayan ta
shirya tsabb na kafa mata ido wata ba ƙaramin kyau kayan suke mata be.
Ƙasa ta sauko tana saukowa taga hajia ɗauke da plate a hannun ta murmushi Sabreen
tayi,saida ta ƙaraso sanan ta ce "Ni da kaina zan ci "
Murmushi hajiar tayi "inah ni zan baki"
Zama tayi a hannun kujera dan ta san halin hajiar.
"Yauwo ko kefa ƴar aljanna" hajiyar ta faɗa sanan ta fara bata abincin ta shi kaɗan sanan
hajiyar tai mata rakiya har gurin motar.
Tun kafin su isa makarantar gaban Sabreen ya fara faɗuwa bata kawo komai a ranta kuma bata
ba abin wani muhimmanci ba balle tayi zargin wani abu.
Kasancewar ta je da wuri ba mutane sosai yasa ta zama ita kaɗai a class,rubutun malam Haulat
da ta gani a jikin allon ne yasa ta tuno da ita,dan Sabreen bata da riƙo ko kaɗan shi yasa ɗuk
abinda aka mata sai ta rama dan karta riƙe mutum.
Murmushi tayi a filli ta ce"Su malama Haulat ƴan kilibibi manya,ina fah kika iya kilibibi ai kilibibi
sai Ya Naufal"
Dariya tayi tuno yadda yake gudanar da al-amuranshi.
Tana cikin tunani ƴan ajin suka fara isowa kowa tambayarta ya ke yi lafiya ,suna son Sabreen
dan ta iya abin dariya gashi bata gani ta ƙyalle sai ta tanka.
Cikin ƴanga da iyayi da kilibibi Haulat ta shigo ajin,gaba ɗayan su suka miƙe tsaye suka gaida
ita harda Sabreen dan yanzu bata riƙeta ba.
Kamar yadda suka saba gani sai ta gaya abinda ta ga dama sannan ta amsa musu gaisuwa
yanzu ma hakan ne,har Sabreen zata zauna dan ta gaji da tsayuwar Haulat ta ce su zauna.
Haulat na miƙewa ta hango Sabreen wani daɗi taji murmushi tayi ta taka har gurin Sabreen ɗin
ta ce"Sabreen ya ƙafar ko ita ce ta hanaki zuwa makaranta kwana biyu"
Ita ma murmushi tayi ta ce"No kike cewa ko?
"to No ba ita ba ce"
Murmushi Haulat tayi a ranta ta ce"Yarinya kenan wai da ni zaki ja"
A fili ta ce"Okkk
Tana faɗa ta juyo gurin allon kamar yadda ta saba karantar da su haka yau ma tayi,bayan ta
gama ta fita tana murmushin mugunta.
"Hello kana ji na yau ta zo,ka shirya lokacin break ni kuma zan san yarda zanyi ta fito.
"Okk baki da matsala Haulat"
Ana kaɗa musu ball masu fita suka fara fita dan Sabreen ita bata zuwa break.
Tana Zaune tana fira da ƙawayanta wata yarinya ta shigo ta ce "Ina Sabreen muha'd mai
taƙama?
kallon yarinyar tayi ta ce " gani wake naima na,wani uncle ɗin ku ne yana waje" yarinyar tana
gama faɗa ta fita daga ajin.
"Toh gani nan zuwa"ta faɗa bin bayan yarinyar tayi ,tana fita bata ga yarinyar ba,tafiya ta fara yi
tana waige-waige.
Yana ganinta ya nufu ta,ga gurin ba mutane sosai,bata lura da zuwan shi ba,kawai sai taji ya
bangaje ta,wani abu ja me irin jan jini ya watsa mata.
"Innalilahi wa'inna ilairaji'um Sabreen ta faɗa tana kallon jikin ta.
"Subhnanllah! yi hakuri ban kula ba,mu je dan allah ki wanke kar ya kama uniform ɗinki.
Ba musu kuwa ta bishi har wani ɗaki me kama da office,suna shiga ta tsaya mamaki ya kamata
ganin yana cire rigar jikin shi,wani irin nishi ya fara yi.
Gaba ɗaya Kan Sabreen ya ɗaure bata gane abinda yake yi ko nufi ba,shi kaɗai yake wani irin
abu,dan akwai tazara a tsakanin su da shi ma.
ƙwanƙwasa ƙoka aka fara yi,kallon kofar take yi tana kallon shi,da ƙarfi aka buɗe kofar aka
shigo wani uncle ne mara mutunci wani irin kallon mamaki yake mata"Me zan gani daman haka
kike"
Cikin rashin fahimtar inda zancen shi ya nufa ta ce"Haka nake kamar ya"
"Rufe min baki ƴar iska kawai daman haka kike"ya daka mata tsawa.
"Iskanci!" ta faɗa cikin rashin sanin inda zance ya nufa.
"Dallah karki wani nuna baki san komai ba yau asirin ku ya tuno"
"Waiyo allah na shiga ukku wllh yau ne kawai kuma yau ɗin ma ba muyi koma....
Tsalla rufe min baki yau sai kun bar makarantar nan.
Gaba ɗaya kan Sabreen ya ɗaure ta kasa gane abinda suke nufi kalmar iskanci ya duki
zuciyarta.
jiki ba ƙwari kamar wacce aka yiwa dukan tsiya ta ce "Ƴau ne kawai ku....
Tun kafin ta ƙarasa maganar taji zaukan Wani wawan mari wanda ƙarar saukar shi ya tsayar
mata da jin magana,ga hawaye ya ƙasa xubuwa.
Hannunta ya ja har office ɗin principal ɗin,har suka isa bata jin abinda suke cewa.
Suna shiga daman su huɗe ne malama suka gaya wanan mara mutunci ne ya ce mishi "A ɗakin
sani naani su ka kama su suna iskanci"
Wanan kalmar ita ta duki kunnan Sabreen zuciyarta ta buga ta karfin haske sai yanzu hawaye
suka samu damar zubuwa.
A ruɗe principal ya ce "What! yana kallon ta no it c...
"Ya isa haka ki kwantar da hankalin ki Naufal ya zama naki"
A zuciyarta ta ce" Hmm Malama Haulat kenan ba kin ce naje na aure jahili ɗan ƙauye iri na
ba,to zaki ga jahili ɗan ƙauyen,zan iya yin komai dan ɗaukar fansa akan ki,dole na aure miki shi
kuma ya zauna da ni"
"Ƴar Aljanna ya isa haka bana son jin kukan ki,kiyi shiru kinji"
"To Hajiyata zanyi shiru"
"Yawwa ko kefa"
"Hm Malama Haulat sai kinga ramuwar gaiya,wacce zata tsorata ki ,ta ɗaga miki hankali" a
zuciyarta take wanan maganar.
Sun daɗe a ɗakin kafin suka fito falo suka zauna,hajiyar ta kalleta ta ce"Bari naje na kira Alhaji"
"Toh kawai ta ce mata.
can ƙasan zuciyarta tana jin tsoro ya Naufal zai ɗauke maganar tasan baya sonta ita ma bata
son shi ko kaɗan hali da ra'ayin su ba ɗaya ba,amma guguwar ɗaukar fansa ta hana ta yarda
da jin tsoran yadda abuvuwa zasu kasance,ta ɗaukar wa kanta komai rintsi komai wuya sai ta
ɗau fansa.
~~~~~~~~~~~~~
Xaune yake a cikin office ɗin shi yana duba wasu muhimman takardu,kiran hajia ya shigo wayar
shi,da sauri ya ɗauka haɗe da tattara dukkan hankalin shi,cikin girmamawa da biyayya yai mata
sallama.
"Wa'alaikum salam"
"Hajia ya gidan ya Sabreen?
"Muna lafiya
"Ya jikin na ta?
"Jiki yayi sauki,ina son muyi wata muhimmiyar magana da kai idan ka tashi ka biyo"
"To shikenan zan biyo insha allah!
"Yawwa allah ya kawo ka lafiya
"Amin.
ita ta fara katse wayar.
~~~~~~~~~~~~~
Cikin sigar jan hankali take mishi magana"Dear meyasa kake min haka ne,kasan irin son da
kishin da nake maka kuwa,kasan yadda naji da ka katsi min waya kuwa"
Kamar wanda ke koyan magana ya ce"Haba haulat meyasa kike da zargi ne,na kaya miki wata
ƙan wata ce ta ɗau wayar ,kuma bata iya amfani da wayar ba shiyasa ta katse"
"To bata iya amfani da waya ba kuma"
"yes village girl ce ya fada had'e da ta'be baki.
"me ya haɗa ka da wata village girl kuma? ba wanan ba yaushe zaka zo?
numshe idanuwan shi yayi ,yana son zuwa gurinta tunda yana sonta,amma yana jin tsoran
abin..
"Wai meyasa kake gudu na ne,ta katse mishi tunani.
"Ba gudunki nake yi ba dear ,ina son na yiwa zuciya faɗa ne"
Ɗan guntun tsaki ta ja"Kana ɗai gudu na kamar wata maiya anya kana sona kuwa"
"ina sonki Haulat"
Saida tsigar jikinta ya tashi dan yadda yayi maganar gaba ɗaya feeling ɗinta ya tashi.
Cikin sigar da tasan zata ja hankalin shi ta ce"prove it!
katse wayar yayi dan ya tabbata idan ta cigaba da mishi magana a haka ba zai kai labari
ba,kashe wayar yayi ma, dan yasan zai ta kara kira tunda maiyace anace.
~~~~~~~~~~~~~
Gaba daya ya rasa natsuwar shi tunda sukai magana da hajia, ƙarfe da ƙyar ya tsaya yayi salar
maqrib a office ɗin,cikin gaggawa da hanzari ya iso gidan su hajiyar.
Suna zaune a falo ƴar aljanna tana kan cinyar hajia kamar yadda ta saba indai suna tare da ita
to a kan cinyarta take kwanciya.
"Assalamu alaikum"
Sabreen tana jin sallamar shi ta miƙe
Hajia ta amsa mishi sallamar,yana ƙarasowa yayi gurin Sabreen ɗin fuska ɗauke da Annuri ko
wani irin yanayi yake ciki idan yaga Savreen zai yaji farinciki.
"Sabreen ya jikin ki"
kanta a ƙasa ta ce"yayi sauƙi Dady"
"Alhmdllh! allah ya ƙara miki lafiya Sabreen"
Hajia ta katse shi da faɗin"ƴar aljanna je ki ɗaki"
"to kawai ta faɗa ,ta tashi ta hau sama ,duk da tasan dady ba zai ƙi amincewa ba amma saida
ta tsinci kanta da faɗuwar gaba wanda ta rasa dalilin yin shi.
Bayan sun ƙara gaisawa ta kalle ta ce"Alhaji kana jina koh?
"Eh ina jinki hajiya"
"Yawwa to,tun lokacin da likita ya ce ayi wa Sabreen aure na shiga tunani da wa za'a haɗa
ta,tun a lokacin Naufal ya faɗomin a rai ,domin bana son mu ba wani wanda bamu sanshi
ba,kar ya cutar da marainiyar allah,amma zai ban nufe ka da maganar ba,kuma kai ma nasan
kayi irin nawa tunanin ,duk ba mu san muyi mata dole shiyasa ba muyi wa juna maganar ba"
"Wanan haka ne hajia kuma ɗazun malamin makarantar su ya kira ni ya shawurce ni akan muyi
mata aure"
"To alhmdllh! Allah yaga zuciyar mu ya ga kuma tsoran mu,yau tana dawo wa daga makaranta
da tabbatar min da tana son Naufal"
Wani irin farinciki ya mamaye alhaji"masha allah alhmdllh,hajia allah ya dube mu,daman muna
tunanin ko ba zata so shi ba,amma abin allah gashi tana son shi,ba ƙaramin daɗi naji ba,cikin
gaggawa kuwa za'a ɗaura auran nan"
"Yawwa ni kaina naji daɗi mara misaltuwa,yanzu zai a tsaida ranar auren.
"To kwana nawa kike ganin ya kamata a saka"
"To bari mu sai gobe idan munyi magana da ita"
Hmm tofah ana wata ga wata,ko ya naufal xaiji idan yaji maganar auren shi da Sabreen,ga
kuma mutumiya haulat.
Bayan ya tafi hajia ta shiga gurin Sabreen ɗin ,a kwance ta ganta tayi lamo kamar me barci,tana
jin an buɗe kofa ta tashi zaune,kusa da ita ta zo ta zauna.
"Ƴar aljanna bana son ganin ki kina damuwa Naufal ya zama naki,yaushe kika so a ɗaura muku
auren?
Dumm dumm zuciyarta ta fara buguwa wani irin abu zuciyarta ke bijiro mata da shi me kama da
tsoro,amma dan tsabar ƙarfin hali irin na Sabreen ta ce"Sati ɗaya,A'a kwana huɗu ranar juma'a
kenan,sati ɗayan ya mata yawa.
"To baki da matsala yanzu ai a fara shiru"
"Hajita ina