Author : Fatima Batula Category : Love
ɗaya
hajia ta ruɗe .
Ko mutsi daga inda yake bai yiba,kallon su kawai yake yi yana murmushin mugunta.
Sabreen ga raki kasa tashi tayi ita kuwa hajia ta ƙara ruɗewa.
chin chiɓar ta aka yi har cikin motar,shi kuwa ko gyalenta bai taɓa ba,gashin kanta ya mishi
kyau bai taɓa tunanin a 9j xa'a samu me kyaun gashi ba.
Motar shi ma ya shiga ya fara tafiya a hankali yake jan motar yana jinta tana raki,murmushi
kawai yake yi.
"Yanzu ina zamu?
ya faɗa hankali kwance.
Cikin faɗa hajia ta ce "wacee irin magana ce haka,gana ganin halin da muke ciki"
"hajia daman naji ta ce wai tana son na kaita duk inda na sani ne"
"Toh a hakan"
ta juyo da kallon ta gurin sabreen ɗin "Sannu kinji ko muje asibiti ne?
Da sauri ta ce "A'a muje gida ki shafa min magana "
"to yadda kika ce ƴar aljanna"
Wanan karan har saida haƙuranci suka baiyana "Wai ƴar aljanna"
Gida ya maida su ,amma bai shigaba a harabar gidan ya tsaya suka sauka yai wucewar shi.
Ranar a ɗakin ta hajia ta kwana.
~~~~~~~~~~~~~
Ƙiran sallar farko hajia ta farka,ɗakinta ta koma.
Sai shidda saura Sabreen ta farka tana farka ta ma manta da tana da ciwo a kafa saida taji
zafi,amma haka nan ta ɗaure tayi sallah,ko kaɗan sabreen bata wasa da ibada.
Bayan ta idar ta sallar wata dubara ta faɗo mata,da sauri ta tashi ta hau shirin makaranta,Cikin
kankanin lokaci ta gama shiryawa,ƙafar tana mata mugun ciwo amma haka nan ta ɗaure ta
sauko ƙasa.
Ɗakin hajia ta nufa tana kiranta"Hajiata! hajiata?
Da sauri hajiar ta durgo daga saman gadon ta "Ƴar aljanna lafiya ƙafar ce..
ganinta da kayan makaranta yasa ta ƙasa maganar.
Murmushi Sabreen tayi dan tasan kallon da hajiar ke mata,mugun ƙarfin hali tayi ta ƙara gurin
hajiar cikin tafiya mai kyau ta ce "Kin gani ko hajia naji sauƙi sosai yau ina da test ne shi yasa
zanje da ba inda zani"
Cikin wata irin siga hajiar ta ce"Sabreen kiyi hakuri karki je"
Murmushi Sabreen ɗin tayi ta ce "Hajiata wai baki yarda da ni ba ne,baki ga yadda nayi tafiya
ba ne,naji sauki sosai zamu yi test ne shiyasa"
Tana ƙarasa maganar ta isa gurin hajiar kwanciya tayi akan ta.
"To Sabreen duk abinda kike so shi zanyi ,dan bana son ɓacin ranki ko ƙaɗan"
Wani lafiyayayyan murmushi Sabreen ɗin tayi ta ce"Hajiata ina sonki !
"ni ma ina sonki Savreen ki kula sosai kinji bana son wani abu ya same ki"
"to hajita zan kula sosai,bari na tafi kar tana yi latti,byee sai na dawo,tana gama faɗa ta tashi.
Hajiyar ta ce "ba zaki bari na raka ki ba "
"Eh ki huta abinki lokacin har ta bar ɗakin.
Gaisawa da direban suka yi sanan ta shiga motar,a tsorace yake dan jiya yasan planing ɗin su
bai yiba,kuma yasan Sabreen bata yafiya ba hakura zata yiba taurin kai gareta.
Jin bata ce mishi komai ba har suka isa makarantar ya bashi mamaki tunani ya farayi wani irin
hukunci zata ɗauka kuma.
Ba mutane a makarantar sosai.
office ɗin malama haulat ta nufa kai tsaye ta shiga.
Zaune take akan kujerarta tana duba wasu litattafai cikin wani tsadaddan material wanda yai
matukar yi mata kyau,fuskar nan a yamutse kamar kullum.
Saida ta tsorata jin an buɗe kofa ba'a ƙwanƙwasa ba.
Cikin ɓacin rai ta kalli Sabreen"Ke wacce irin dabbace jahila mara hankali"
Har Sabreen ɗin zatai magana ta fasa ko meye ta tuno? ohoo.
Takai tsawon minti talatin a tsaye a gurin ,ita kuma malama haulat ganin bata da niyyar magana
yasa ta fita lamarinta ta cigaba da abinda take yi.
Ganin mutane sun fara yin yawa yasa Sabreen ta kalli Malama Haulat ɗin cikin ɓacin rai ta
ce"Ke wawiya karki ƙara kira na da waɗan nan sunayen"
"Ɗago kai Haulat tayi cikin mamaki tsaye ta
tashi tana kallon Sabreen ɗin.
Ganin ta tunzura yasa Sabreen ɗin kara faɗin "ni ba wawiya bace ke ce wawiya kuma dabba
jahila"
Ran Haulat ɗin yai mugun baci,bulalar take kan tebur ɗin ta ɗauko,ta zubawa Sabreen a jiki.
Haba ai abin naima ya samu ai da Sabreen ta sake wani irin gigitaccen ƙara ta zube ƙasa tana
ihuun gaske tana birgema a kasa haɗe ta faɗin " waiyo Allah na zata kashe ni ƙafata ciki na
waiyo kaina kai na nashi ukkku hajiata ku taimake ni zata kashe ni!!!
Dan tsabar mamaki Malama haulat tsayawa ma tayi tana kallon ta jikin ta duk ya mutu.
gafin ka ce me office ɗin ya cika da mutane Sabreen tana ganin haka ta fara nishi tana ɗauke
numfashi ai sai suka ƙara ruɗewa ga malama Haulat tsaye da bulala a hannunta.
A ruɗe aka ɗauke Sabreen wani ɗaki aka kaita ita kuwa sai ɗauke numfashi take yi tana kiran
hajia.
Ganin za'a mata allura ai sai ta fashe da kuka tana faɗin" waiyo ƙafata ku kaini gurin hajiata
ƙafa ta ta ƙaryamin ƙafa"
da sauri ya duka ƙarfa ya ganta taji ji kuma ta kumbura duk da ba wani haske gareta ba amma
ƙafar tayi ja.
Gaba ɗayan malaman makarantar sun ruɗe suna tsoron kai wani abu ya faru da Sabreen ɗin.
Allura ya mata tana ihuu tana kuka dan bata son allura amma haka nan suka mata cikin
ƙamƙanin lokaci barci ya ɗauke ta.
~~~~~~~~~~~~~
Ranshi a ɓace ya kalli haulat wacce ita ma ranta a ɓacen yake ya ce mata"yanzu me kika aikata
kina son ki ja mana wani abu ne a makaranta dan baki san waye wanda ke ɗaukan nauyinta ba
ne,duk abinda ta miki ba zaki iya kawo kararta ba,zaki yi mata irin wanan dukan yanzu ga shi ta
samu matsala a ƙafa,ni wllh yanzu ban san yadda zanyi ba,ansa ya miƙa mata wata takarda.
gabanta yai mummunan faɗuwa kallon takardar ta tsaya yi.
"Ki ansa nace" ya faɗa cikin faɗa.
jiki na rawa tasa hannu ta ƙarɓa.
"mun takatar dake na sati biyu"
Dumm Dumm gaban haulat ya fara faɗuwa da ƙarfin haske haɗe da zaro ido tana kallonshi.
"Tashi ki fita ya faɗa rai ɓace"
jiki ba ƙwari ta tashi...
..........................................
tirkashi!!!!
gaskiya ni comment na ke so,bana son wani tnx ko wata heart haba ga tawa ga taku ai sai
tamin yawa.
ku ƙara gyara zama dn zanyu zan fara.
.
[12/9, 1:07 PM] ° D°⭕Y: _ σѕт у яσυρ уρє αυѕα σνєℓѕ
σσк нαтѕαρρ 08064400100_
[12/9, 1:10 PM] ° D°⭕Y: *NI* *DA* *MALAMA* *TA*
*By*
*fatima* *Batula*
*~✍✍GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍✍~*
Page 4
...................................................
Fita tayi daga cikin ajin ranta a ɓace,ita kuwa ko a jikin ta daman hakan take so ,tana jin zafin
maganganun da Aunty ke gaya mata,shiyasa ta ke son ganin ɓacin ranta.
" *Sabreen* *Muhammad* *mai* *taƙama*"
Da ƙarfi ya kira sunan cikin faɗa.
"Kina ina?yana maganar yana kallon ƴan class ɗin.
Gaba daya ajin yayi shiru kamar ba halitta a ciki dan ko numfashi a hankali suke yi dan tsabar
tsoron wanda ya shigo ajin.
Cikin nuna ko a jiki na ta tashi daga gurin da take zaune ,hankali kwance ta nufi inda
suke,kallon Aunty ta fara yi wacce tare suka shigo class ɗin da shi.
Saida ta matsu kusa da shi sosai sannan ta tsaya ,ta kuma zuba mishi manyan idanuwanta
wanda ba alamar tsoro a tare da su.
"Me kika cewa Malama *Haulat* *Hashim* *Kabir* ?eyeeh ba dake nake ba,kin kafe ni da ido"
Saida ta kalle malama Haulat ɗin sanan ta dawo da kallonta gare shi "Ce mata na yi ni bana jin
turancin ƴan chaina,tamin na ƴan nigeria"
Shi kanshi bai san lokacin da dariya ta suɓuce mishi ba,dan duk makarantar kowa yasan
iyayenta gurin turanci amma ba wanda ya taɓa mata magana sai Sabreen.
Ganin shi ma ya fara dariya abin ya ɓata mata matuƙa ga yan ajin suna dariya,a fusace tabar
class ɗin,tsanar sabreen kuma da niyyar ɗaukar fansa.
Ganin ta fita yasa shi ma yai sauri yabar ajin.
wani annuri ya baiya na a fuskar sabreen dan jin daɗin yadda ta ga ranta a ɓace,komawa tayi ta
zauna amma duk ji take yi bata rama hulaƙancin da malama haulat ɗin ke mata.
Zaune take ita kaɗai a staff room tana tunanin wani irin abu zata ma Sabreen ta
huce,murmushi naga tayi wanda ya ƙara baiyana kyawun ramammiyar fuskarta,wato abinda
zata ma Sabreen tayi shi yasa ta yin murmushi.
Ƙarfe ukku daidai aka buga ƙararrawar tashi,koya hankalin shi ya koma gidan, gaba ɗaya
malamai da ɗalibai sun fito kuwa ya nufi hanyar gurin ajiyar motoci.
Har aka gama zuwa ɗaukan dalibai Sabreen tana zaune ita kadai ,ranta ya ɓace sai huci take
yi,tana turo baki,tashi tayi zata fita bakin get.
Da mugun gudu motar malama Haulat ta zo wuce wa,ta gabanta kamar zata ɗauke ta,da sauri
a ruɗe sabreen ta matsa har saida ta faɗi kasa,wani irin ƙululon takaici ya kamata,da zafin
nama ta tashi ta nufu motar.
Tana ganin ta nufota ,ta fito daga motar tana wani yamutsa fuska kamar wacce tai arba da
kashi
" U are very no what u are,okkk i forget u are illiterate ,baki da gwagwalwa ne ko a garin
mahaukata aka daukoki da kina ganin mota ba zaki iya kaushewa ba"
Tunda ta fara magana Sabreen ki binta da idanuwa wadanda sukai jajiir dan tsabar takaici.
Ita kuwa malama Haulat ganin ta cinma burinta yasa ta wuce ta barta anan tsaye, ta kuma ja
motar da karfi har saida ta watsa mata kura.
Wani lafiyayyan hawaye ya fara bin fuskar Sabreen wanda ita kanta bata san da zuwan su ba,
sai jin su tayi a fili ta ce tana huce kamar wacce tai faɗa da zaki "Hmm baki san waye Sabreen
Muhammad mai taƙama ƴar Aljanna ba ne,bana yafiya kuma bana biyar bashi zan rama
ramuwar gaiyya"
Tana faɗa ta sa hannuwanta ta fara goge hawaye tana faɗin "Hm kika sa ƴar aljanna hawaye
zai kin biyasu"
"To yah zanyi idan na gayawa hajiya ,A'a ba zan gayawa hajiya ba,ni da kai na zan ji da ita "
Ita fitowa bakin get ɗin direban ta ya zo ,bata ce mishi komai ba ta buɗe motar ta shiga.
"ƴar aljanna kiyi hakuri wallahi faci tayar motar tayi,jikin shi har rawa yake yi dan tsoron karta
gayawa Hajiya"
Banza tayi da kamar bata san da wani a cikin motar ba.
Sai magiya yake mata akan karta gayawa hajiya.
"To naji amma zai kamin abu ɗaya ta faɗa tana kallon shi
"to zanyi ƴar aljanna koma meye zanyi"
Murmushin mugunta tayi da jin daɗi ,harda sauke ajiyar zuci.
Daidai wani katafaren gidan direban yayi horn aka buɗe mishi,giɗan ya haɗu iya haɗuwa abin
sai wanda ya gani,dan tsayawa kwatanta muku sai ya ɗauke ni lokaci mai tsawo.
Tana jin ƙarar motar su,ta fito da sauri har bakin motar ta fito tana wace baki ,ita da buɗe mata
kofar hade da faɗin "Ƴar aljanna kin dawo tun ɗazun naji shiru ina ta jira hankali na ya tashi ina
fatan dai kina lafiya"
Murmushi tayi sannan ta rungumeta "Kina lafiya hajiyata yau bamu fito da wuri ba ne,wanan ƴar
iskar malamar ce ta tsayar da mu"
"Cikin nuna damuwa ta janye jikin ta tace"Wai ko sai na tura anje gurinta ne aja mata kunne,ko
na fitar da ke daga makarantar gaba ɗaya ma"
"A'a Hajiya ki barta kinji "
"to ni bansan duk wani mahalukin da zai ɓata miki rai,zan iya yin komai akan farincikin ki"
Daidai da isar su cikin katon falon wanda shi ma ya ƙyyatu har tsoro yaban dan tsabar kyaun
shi,ga wani asirtaccen kamshi wanda ya haɗe da AC ɗakin.
Murmushi tayi cikin shagwaba ta ce "Nima na sani hajiyata,amma tunda na ce ki barta kawai ki
barta zanyi maganin ta ,zan gwada mata ni ɗin ƴar gata ce"
"Hajiya bari na hau zama nayi wanka sai nayi sallah na huta"
"Yawwa ƴar aljjanna na manta ban gaya miki ba,ɗan india ya dawo an jima sai ki je ku gaisa"
Yamutsa fuska tayi yin sunan wanda ya dawo din"Wanan dan iyayin wanda aka je ɗauko mu
tare"
"Eh shi fa"
"Tabbb gaskiya ni ba zani ba saida shi ya zo "ta faɗa tana hada rai
"to shikenan ba zai kin ɓata rai ba,zan sa ya zo da kanshi,kinji hankalinki ya kwanta"
ta washe baki "eh hajiyata,ta haye sama ,a ranta tana faɗin yadda zata ganshi dan tun sanin
farkon da ta mishi kafin yaje india dan iyayi da kinibibi ne,to bari yanzu da yaje india....
.....Cikin yanga da ƙasaita take saukowa daga matakalar benan gidan, idan ta ɗaga kafa daya
kafin ta ƙara ɗaga ɗayar ta sai ta ɗau saƙonni,duk wanan abun cikin kayan makaranta take
yi,sikit ne ɗan ƙarami iya gwuwarta nevy blue sai rigarta fara mai ratsi-ratsin blue ba hijjab a jikin
ta sai hular da ke kanta.
Wata kyakykyawar dattijowar matar da ke zaune a cikin tanƙameman falon ta hango yadda take
saukowa daga benan murmushi tayi sanan ta ce "ƴar aljanna!! ke kullum sai kinyi latti,kinsan
ƙarfe nawa ne yanzu kuwa?
cikin tausasawa take mata maganar.
It kuwa wacce aka kira da ƴar aljanna ko a jikinta banda ma ƙara rage saurin da tayi.
Wanan dattijowar bata ƙara ce mata komai ba, binta da kallo da tayi ko kaɗan bata nuna
alamun ɓacin rai ko wani abu makamancin haka a fuskarta ba banda ma wani lafiffayan
murmushi da take yi .
Ƙamar ta ƙarye dan tsabar yanga,ta iso falon,kan jikin dattijowar ta faɗa ,kanta matar ta
taɓa,cikin so na nuna damuwa ta ce "Ƴar aljanna ko ba zaki makarantar ba ne? idan ba zaki ba
muje ki cire kayan sai ki gayamin inda kike son zuwa mu je"
Kamar mai tsoron magana ta buɗe bakinta cikin shagaɓa ta ce "Zani *Hajiya* bana son wahala
ne gashi wanan ƴar iskar malamar ce maiyar turanci zata fara shiga ajin ,ta kai ƙarshen
maganar haɗe da ramutse fuska tana kallon Hajiyar.
"Kam to kina jina,duk abinda aka miki ki kira ni,zasu ga wanda ya tsaya miki,ni da su ne shege
ka fasa ɗan halar sai yanka"
Washe ƙaramin bakinta tayi ,tana jin daɗi da alfahari,rungume hajjiyar tayi "Ina sonki hajiyata"
Tana faɗa ta tashi tabar falon cikin jin daɗi.
"Nima ina sonki ƴar aljanna sai kin dawo"
Tun kafin hajiya ta gama maganar ta bar falon.
Ɗaidai waata ƙatowar makaranta wacce kallo daya zaka mata ka fahimce makarantar bata
ƴaƴen yara ba ce,ta tsaro da navy blue da farin fanti,yanayin makarantar idan ka gani ka ce ba'a
j9 ba ne dan yadda suka tsarata,ƙatowar motar ta tsaya.
horn ɗaya direban yayi aka buɗe ya kunna kai,saida ya isa inda ake faking ɗin motoci sannan
ya tsaya,bata wani tsaya ɓata lokaci ba ta fito.
J S S 3
Aka rubuta a saman ajin,kai tsaye ta kutsa kai ba tsoro ba tantamar komai,kanta a ƙasa.
"Hy how dare u enter me class without any excuse"
Saida nayi da ƙyar sanan naji abinda take faɗi,dan yadda take turanci kamar ba ƴar 9j ba,ko
wacce tai karatu a kasar turai.
Ko ƙadan bata ji tsoro ba ta ɗago kai ido biyu suka yi,da wacce tai maganar
Tsaye take a gaban Allon,kyakykyawa ce ajin farko kallo daya zaka mata ka fahimce yadda
tsarin halitar jikinta yake,ƴar gajerace ba cancan ba,sirirya ce ga dogon hanci kyakykyawa,bata
da wani girman jiki amma kana kallon fuskarta zata san cewa wanan ba yarinya ba ce,dan ta
kwana biyu.
Tun a kallo na farko na gane ƴar iyaye ce,dan yadda take yamutsa fuska kamar tana kallon
ɗanyen kashi.
Ido cikin ido suke kallon juna,bata ɗauke idanta ba ta fara tafiya.
"Keee wacce irin dabbace mara hankali da wayau kuma jahila"
Cikin ɓacin rai da kausassaiyar murya ta faɗa.
Wani irin mugun kallo ta bita da shi mai cike da tsana ,amma sai naga ta sake wani ɗan karamin
murmushin keta ta ce "Au sari kinsan bana jin turanci balle irin naki me kama da yaren chaina"
Tana rufe baƙi yan class ɗin suka fashe da dariya wanda daman tunda ta shigo hankalin su ya
dawo gareta dan sun san sai anyi drama...
yawan comment yawan typing
.
[12/9, 1:10 PM] ° D°⭕Y: _ σѕт у яσυρ уρє αυѕα σνєℓѕ
σσк нαтѕαρρ 08064400100_
[12/9, 1:11 PM] ° D°⭕Y: *NI* *DA* *MALAMA* *TA*
*By*
*fatima* *Batula*
*~✍✍GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍✍~*
Page 5
__________________________.
Sabreen bata daina dariyar ba har saida ta gaji ,ta tsaya dan kanta, ta juyo ta kalleshi ya ɗaure
fuska kamar me shirin yin kuka,sai ya ƙara bata dariya ta ƙara fashewa da dariya.
Ya