NIDA MALAMATA BOOK COMPLETE

Author :  Fatima Batula Category :  Love

Chapter   6 / 20

15K to 18K   out of 57.2K words

son a tsara bikin nan sosai irin na ƴaƴan gata"

"ke ƴa gata ce Sabreen karki ji komai ko da ɗukiyar alhaji zata ƙare akan yasa ki farinciki zai
kashe,za'a haɗa biki irin wanda sai ƴaƴen manya ƴan gata"

Wani irin farinciki ya mamaye Sabreen ,amma a ƙasan zuciyarta tana jin wani iri.

~~~~~~~~~~~~~

Ko da dady ya koma gida suna zaune a falo suna fira.

duk da sun san dady da fara'a amma yau kuwa sunyi mamakin ganin irin fara'ar da ke fuskarshi
kamar wanda akai wa bushara da aljanna,zama yayi suka yi fara sosai sai ƙarfe goman tare
kowa ya tafi ɗakin shi.

"alhaji wai yau naga kana cikin wani irin farincike ne"

murmushi yai mata sanan ya ce" hmm wani irin abu ne kike ganin zai sani irin wanan farincikin"

"eh to abu ɗaya ne zuwa biyu na farko dai magana akan Savreen na san ko...

da sauri ya katse takYawa uwar gida,ma tso kusa na baki labari"

Ba mutsu ta matso"to ina jikin ka

Saida yai gyaran murya ya kara natsuwa sanan ya ce"Kin san lokacin da likita ya ce ayi wa
Savreen aure hankali na ya tashi akan da wa zana haɗa ta wanda sai riƙe ta da amana yaji
tausayin maraicinta"

"Haka ne ni kai na abin yana damu na domin Sabreen abin tausayi ce"

"To allah ya ga zuciyar mu,ita da kanta ta ce tana son Naufal kinga faɗuwa ta zu daidai da
zama,yanzun mun kama magana da hajia daman ba wanda ta cancanta da ya aure sabreen sai
shi,kuma cikin satin nan za'a ɗaura auren nan"

Ba ƙaramin daɗi momy taji ba,dan tana son Sabreen tana jin tausayinta,amma abin da ya ɗaure
mata kai daya ce wai Sabreen ta ce tana sonshi,a iya ganinta basu shiri dan ra'ayin su bai zo
ɗaya ba.
"To Naufal yana sonta kuwa?

"Tunanin me kike yi?

Murmushi tayi ta ce"Naji daɗi sosai da sosai amma shi Naufal ɗin ka ji ta baki....

Da sauri ya katse ta da faɗin"Ba buƙatar jin tashi Sabreen ƴae uwarshi ce dole ya sota yana ma
sonta,idan jar jinin jiki na ke yawo a jikin shi,to na Sabreen ma yana yawo a jikin shi,kuma idan
har yana so na to yana son Sabreen,kuma kar yaji wanan maganar sai ranar da za'a ɗaura
aurank
Ganin rance ya fara ɓace yasa tai saurin tarar shi cikin sigar lallashi ta ce"Ba wai ina nufin wani
abu ba ne,ina nufin ya kamata ace ya san da maganar ne...

"To idan bai sani ba ,wani abun zai yi?

Shiru tayi dan taga alamar ya hau sama,tashi tayi ta fita a ɗakin....

lallai Sabreen saboda ɗaukar fansa zaki aure wanda baya sonki baki son shi.
.

Sir Dboy
[12/9, 1:13 PM] �° � D°�⭕Y: _ �σѕт у �яσυρ � � �уρє �αυѕα �σνєℓѕ
σσк нαтѕαρρ 08064400100_
[12/16, 5:46 PM] �° � D°�⭕Y: *NI* *DA* *MALAMA* *TA*


*By*
*fatima* *Batula*

*~✍✍GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍✍~*

.............................................

_*YAWAITA SALATI GA ANNABI S.A.W ARANAR JUMA'A*_
➖➖➖➖➖➖➖➖
_*Annabi s.a.w* yana cewa: (Yana cikin mafificiyar Ranakunku Ranar Juma'a, dan haka ku
yawaita yin Salati agareni acikinta, domin ana bujuromin da salatinku gareni)._
_*@Saheehu Abu Dauda.*_

_*Annabi s.a.w* yace: (Duk wanda yayi salati a gareni, *Allah* zaiyi masa salati Guda Goma)._
_*@Saheehul Jami'i*_

Page 7
___________

Kallon Sabreen ɗin yake yi cikin mamaki,ya ƙasa yarda da abinda aka gaya mishi dan yanayin
ta ba irin na matan nan ba ne,ga kuma hawayen da yaga tana yi.

"Dan Allah kayi hakuri karka kore ni,bamu taɓa yi ba sai yau.

Kamar wata wawiya ta juyo ta kalli shi,tana hawaye.

Shi kanshi principal ɗin kan shi ya ɗaure ganin yadda sani nani yake magana,gashi ita ta kasa
cewa komai.

"Daman ba tun yau ba nasha ganin ta tana zuwa toilet ɗin maza" cewar wani mai aikin
makarantar.

Kallon shi cikin mamaki da tsoro Sabreen tayi, duk bakin Sabreen yau naiman shi tayi ta rasa.

"A hukunta su daidai laifin da ta aikata" cewar uncle ɗin maths ɗin su wanda shi ma yana cikin
office ɗin.

Kallon su kawai Sabreen ke yi tana zubarda zafafan hawaye zuciyarta na ƙuna.

Saida yaja numfashi sannan ya ce" ku bani guri zanyi magana da ita"

Basu su hakan ba musamman sani nani shi da yaso jin hukunci da wulaƙancin da za'a
mata,amma haka nan suka fita.

Kallonta yayi cikin jin tausayi ya ce"Sabreen mai ya faru?

Sai yanzu kuka mai sauti ya kamata,kuka mai tsuma zuciya ta fara wanda tunda ta zo duniya
bata taɓa yin irin shi ba.

"Kiyi magana ganin ba zata yi ba yasa ya ce mata" to ya isa hakan.

A zuciyarshi y ce" kukan ki ya tabbatar min da baki aikata komai ba,amma dole zan yi hukunci
dan dukace amma tabbas zan rufa miki asiri ba zan tuzarta ki ba"

Wata ƙararrawa ya danna alamar su shigo,cikin zuguɗin abinda zai faɗa suka shigo.

Kallon su yayi ya ce "Kamar yadda duka ta tanadar za'a gayama iyayenta sannan a koreta daga
makaranta,amma ba zan koreta ba,zan dai gayama iyayenta sanan bana son jin wata ƙaramar
magana na,kai sani ya kalle shi

"Kai ne abin ji wallahi idan har iyayenta suka ji wanan labarin ka bani,baka san matsayin su ba
ne,balle ta tabbatar mu da ƙarya kake mata,ba kai ba har makarantar gaba ɗayanta ka ja mata
kalle ta ya nuna Sabreen ɗin wacce dan tsabar kuka jikinta ya mutu yayi tiɓiss.
Sanan ya ɗaura da faɗin"Hm kai kasan komai,ni bani da abinda zan ce a cikin ku waye ma
gaskiya ,amma abu ɗaya tabbas idan har iyayenta suka ji kai ne mara gaskiya dan sai sun
hukunta ka.

Jikin sani yayi sanyi tabbas yasan bashi da gaskiya ko kaɗan.

Kallon shi principal ɗin yayi yaga yadda jikin shi ya mutu sanan ya ce"Hmm zaka iya taimakon
kanka ta hanyar ƙin gayama kuwa dan wllh idan ka yarda iyayenta suka ji wanan mgnr ka kaɗe"

Kallon sauran malaman yayi ya ce musu"Ku kuma nasan kun waye mahaifinta kuma kun san
abinda zai iya to wllh ku rufama makarantar nan asiri domin idan ba haka ba,kun san abinda zai
biyo baya,kuma wllh duk idan naji wani yayi kokarin gayan wata magana a bakina aikin shi"

Gaba ɗayan su jikin su yayi sanyi dan sun san mai taƙama,musamman sani.

"Kuma abinda yasa ba zan koreta ba ,dan gudun kar ayi zargin wani abu,ina fatam kunji abinda
na gaya muku da kyau"

"Eh munji suka faɗa a tare sanan kowa ya gama gaban shi.

Har suka gama magana suka fita Sabreen na kuka.

"Sabreen na san ƙarya ya miki,yana da wata manufarshi na yin haka,shiyasa ba zan matsa sai
ya gaya ba domin idan nayi hakan wasu zasu ji daɗi,shiyasa na rufe musu baki,sanan ke kuma
kiyi hakuri tunda kin san baki aikata komai ba,plsss Sabreen kiyi hakuri kuma karki gaya ma
kuwa abinda ya faru harda gidan..
Sai yanzu Sabreen ta samu bakin magana cikin shekar kuka ta
ce"Ban...s..san..abin..da..suk...ke..magana...b...n rantse da girman allah bansan...

"Ya isa haka ya ƙatse ta,na sani shiyasa na ce ki kwantar da hankalin ki,idan kika nuna danuwa
waɗan da suke son ganin kin tuzarta daɗi zasu ji"

Allah sarki Sabreen baiwar allah ko kaɗan bata kawo Haulat a ranta ba,bata ma yarda wani zai
iya mata hakan ba dan yasa ta wulaƙanta tabar shi a matsayin an samu kuskure.

Ya daɗe yana lallashin ta,har lokacin an kusa tashi ma,sanan yasa ta shi toilet ɗin office ɗin ta
wanke fuskarta,ta wuce classa
ɗin su.

Number Alhaji ya fara naimo wa cikin sa'a kuwa ya ganta ya danna kira,ringin ɗaya tayi ya
ɗauka.

"Assalamu alaikum Alhajn ya faɗa.

"wa'alaikum sallam Alhaji ya gida ya kokari ya iyalai.

"Alhamdulilah komai lafiya

"Mash allah! Alhaji daman ina son yin wata magana ne akan Sabreen"

yana jin ya kira sunanta ya natsu ya tattara dukkan hankalin shi"ina jinka lafiya take dai ko"

"Lafiya qalau take daman shawarace zan baka da wasu malaman suka lura suna ganin ya
kamata ayi wa Sabreen Aure"

Zaida Alhaji yayi jim kaɗan shi ma bai kawo komai a ranshi ba dan likita daman ya gaya musu
suyi mata aure.

"Ba komai insha allah daman nasan da zancen auren ina wani shiri ne dan Sabreen bata kula

maza ni kuma bana son yi mata dole"

Ba wani fahimtar maganar yayi ba ya ce"to haka ne kam za'a mata dole ba"

A haka suyi sallama.

Ita kuwa Haulat ta kasa kunne taji labari ya fara yawo amma shiru bata ji komai ba gashi bata
ga sani ba,gashi har an tashi gida.

Duk wanda yasan Sabreen idan ya ganta yau sai ya gane chanji ƙarara dan fuskarta a ko
yaushe ɗauke da annuri amma yau kuwa ba annuri ba alamar shi sai ma yanayin ƙunci da ya
baiya na a fuskar.

Tana tsaye tana jiran direba,kanta a kasa idanuwanta cike da hawaye dan ba abinda ya taba
ɓata mata rai a duniya irin wanan abun taji zafi kamar me.

lallai akwai aiki kuna ganin idan Sabreen ta gane aikin haulat ne zata iya hakura?

Cikin salon yanga da iyayi da kinibibi Haulat ta fito daga office ɗinta,hango Sabreen da tayi yasa
tayi murmushin mugunta musamman da ta hango yanayin da take ciki.

Sabreen bata san Haulat ta matso kusa da ita ba sai ji tayi ta ce"My illiterated student! yadai

Ƙasa ce mata komai tayi dan bata cikin yanayin.

Ganin hakan yasa Haulat murmushi tana ganin kamar tayi nasara ta ce"Tun kafin a baiyana
abinda kuka aikata har kin shiga wani irin hali.

Cikin rashin fahimta Sabreen ta kalleta.

Murmushin mugunta Haulat tayi ya ce"Yess! baki kina tunanin zaki iya ja Haulat ba har kika sa
aka bani suspension,to bari ki ji ni na haɗa komai na biya sani,ke ba kin sa an bani suspension
ba,ni kuma zan sa a wulaƙanta ki ,ki tozarta ki kunyata kuma a koreki a makarantar sanan a
gaya ma iyayenki abinda kika aikata, daman baki son karutu ke jahila ce sai a haɗa ki da jahili
ɗan ƙauye irinki,dan ko mai washe bola ba zai iya auren ki ba"

Wasu irin zafafan hawaye ne suka fara bin fuskar Sabreen zuciyarta na ƙona tana mata radaɗi.

Ganin halin da take ciki yasa Haulat farinciki cikin dariyar mugunta ta ce"Hmm ja da Haulat ba
irin ki ba jahila ƴar kauye kuma yarinya,hmm karki wahalar da kwakwalwarki gurin yin tunanin
zaki iya ɗaukar fansa akai na yarinya domin ni ba tsararki ba ce,tana gama faɗa wushe tabar
Sabreen tsaye da zafin zuciya.

Hmm ikon allah yau Sabreen baki ya mutu.

Wani irin kuka mai tsuma zuciya ta fashe da shi,daidai lokacin direban ya iso ,tana ganin shi ta
ruga da gudu ta buɗe motar ta shiga tana kuka.

A ruɗe yake tambayarta lafiya dan ko a mafarki bai taɓa tunanin akwai abinda zai sa Sabreen
irin wanan kukan ba.

Suna isa gidan ta buɗe motar ta fito da gudu a falo ta hango hajia zaune gurinta tayi ta faɗa kan
jikinta tana kuka,a ruɗe Hajiar ke tambayarta"Lafiya Sabreen ke da waye???????

A ranta ta ce" *NI* *DA* *MALAMA* *TA*.

Tsananin kuka ya hanata magana.
Hajiya ta ruɗe tana faɗin"Na shiga ukku ke dawa me ya faru wa ya taɓa ki,ko baki da lafiya
ne????

charab ta ce"Bani da lafiya

Ai hajia sai ta ƙara ruɗewa ta ma rasa abinda zata yi,ganin hakan yasa Sabreen,faɗin "zan
kwanta ki kaini ɗaki na"

A ruɗe hajiar ta tallabo ta suka hau sama,suna shiga ɗakin Sabreen ta kwanta hajiar har ta rufe
ta.

Amma Sabreen bata
daina kuka ba tuno kalaman malama Haulat take yi,tana jin zafi a zuciyarta.

Ganin hankalin hajia tana ƙara tashi yasa ta daina kukan ta fara yin na zuciya,tayi lamo kamar
tayi barci,tana jin hajia tana ta maganganu,A haka har barcin ya ɗauke ta.

~~~~~~~~~~~~~

A hankali ta fara jin muryar hajia da na Momy da na farrah,bata ji muryar shi ba amma ƙamshin
shi ya tabbatar mata yana nan,a hankali ta fara kokarin fuɗe ido domin taga a inda ta ke.

Akan hajia idonta ya saura dakin da mutanan da ke ciki ta fara ƙarewa kallo,ɗakinta ne,chan
daga bayan su akan kujerarta ta hango shi fuskar nan kamar kullum a yatsine.

Sannu suka mata ɗaga musu kawai kawai take yi.

Momy ta kalle shi ta ce"Naufal baka ga ta farka ba"

Bai ce mata komai ba ya ƙaraso gurin tana ganin shi da juya kanta.

Taɓe baki yayi ya ce"Ya jikin?

Ɗaga mishi kai kawai tayi,bai damu ba,ya koma ya zauna ta gefan ido yake satar kallon ɗakin
,ɗakin ya mishi kyau ga wani irin ƙamshi irin wanda yake ji a jikinta,ya shagala gurin satar kallon
ɗakin.

Momy kalleta ta ce"Ƴar aljanna bari mu barki ki samu ki watsa ruwa"

Bata ce bata komai ba suka tashi suka fita yana jin hakan ya riga su tashi,kash saidai ya manta
da wayarshi a hannun kujerar da ya tashi a kai.

Hajia ta kalleta ta ce"Zaki iya wankan"

Murmushi tayi ta ce a hankali "zan iya"

"To ki kula kinji"

Kai kawai ta ɗaga mata,hajiar ta fita.

Tana ganin sun fita ta sauko daga kan gadon ,ta cire kayan makarantar ta ɗaura towel,har zata
shiga bayi ringin ɗin waya taji kalle-kalle ta farayi charab idanta ya sauka akan wayar Naufal ɗin
wacce ya manta da ita a ɗakin.

Ƙarasa gurin tayi tana faɗin"Garin ya ya manta da wayarshi a ɗaki na?

Tana kai hannu ta ɗau wayar ,tsaro idanu tayi tana ƙara tabbatar a abinda idanuwanta suka ga
ni.

"Malama Haulat! ta faɗa ita ɗince pic ɗinta ne ya baiyana a gaban wayar har kiran ya katse
Sabreen bata sani ba ,dan mamaki ƙara shigowar ringin ɗin ne ya dawo da ita daga duniyar
mamakin abinda ba abin mamaki ba ne.

Katse wayarta"Malam haulat ita ce kenan"

Wani kiran ya ƙara shigowa a fusace ta ƙara katse kiran.

"Ya Naufal ne wanda keke mugun so daman"

Jin tafiyar mutum yasa tai sauri ta ajiya wayar ta faɗa toilet ɗin da sauri.

Farrah ce ta shigo ɗakin ta ɗauki wayar daya aikota ta ɗauko mishi.

"Sabreen zamu tafi amma anjima zamu dawo momy tayi baki"farrah ta gaya tana kallon toilet
ɗin,bata tsaya jiran amsar Sabreen ɗin ba ta fita daga ɗakin dauke da wayar a hannunta.

"Malma Haulat"

Ta faɗa tana tuno kalaman da ta gaya mata.

kamar wace abu ya tsikara tayi zumbur ta mike ta ɗaura towel ɗin ta fito,tana fitowa hajia na
shigowa,tana ganin hajiar ta fashe da kuka mai tsanani ta faɗa kan gadon.

A kiɗime hajia ke tambayarta"Lafiya Sabreen ki gayamin abinda ke damunki ko meye shi zan
miki magananin shi"

Cikin kukan ta ɗago kai ta kalle hajia ta ce"Ya Naufal na ke so,kuma ya Aure ni"

Ba hajia ba ni kaina saida taji wani yarr

"Naufal kike son aura

"Eh kuma a wanan satin" Tana faɗa ta ƙara fashewa da kuka.

Cikin sigar lallashi hajiar ta ce"Kiyi hakuri indai Naufal ne ya zama naki ke kaɗai kuma ko gobe
kike so za'a ɗaura muku aure!

tirƙashi!!!

waiyo me kike shirin aikatawa Sabreen duk ɗaukar fansar ne!!
.
Dboy
[12/16, 5:46 PM] �° � D°�⭕Y: _ �σѕт у �яσυρ � � �уρє �αυѕα
�σνєℓѕ σσк нαтѕαρρ 08064400100_ [12/16, 5:35 PM] �° � D°�⭕Y:
*NI* *DA* *MALAMA* *TA*


*By*
*fatima* *Batula*

*~✍✍GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍✍~*

مسب الله نمحرلا ميحرلا

_*Manzon Allaah(ﷺ)* *ya ce;{KAYI ALKHAIRI, KUMA KA BAR LAIFUKA. ALLAAH ZAI

MAYAR DA LAIFUKAN KA(NA BAYA) BAKI 'DAYA SU ZAMA ALKHAIRI.}*_

```[Sahihut Targib;3164]```
~~
_Duk mutumin da Allaah Ya azurta da halin kirki ya rin'ka aika alkhairi, kuma ya guji aikata
sabon Allaah, toh sai Allaah Ya mayar da laifukansa na baya ma su zama masa alkhairi.
Allaahu a'alam._

```Allah ta'ala yasa mudace```

ﻚﻧﺎﺤﺒﺳ*_ ﻢﻬﻠﻟﺍ ,ﻙﺪﻤﺤﺑﻭ ﺪﻬﺷﺃ ﻥﺃ ﻻ ﻪﻟﺇ ﻻﺇ ،ﺖﻧﺃ ﻙﺮﻔﻐﺘﺳﺃ ﺏﻮﺗﺃﻭ _*​​.ﻚﻴﻟﺇ

Page 8
.......................................

Kamar yadda ya saba yin mafarkin yau ma hakan ne,
Ya kai tsawon minti ashirin yana nazari akan mafarkin wanda yanzu abun ya fara tsorata shi,
dan saidai idan har bai kwanta ba, amma sai yayi mafarkin ta.

Tashi yayi ya shiga toilet ya daɗe yana watsa ma kan shi ruwa kafin ya samu yayi wankan ya
fito.

Cikin jallabiya baƙa ya shirya ,ta mishi kyau ainun,ga ƙamshi da ke tashi a jikin shi saboda
yawan saka turare yasa ko mai shafa ba,jikin shi yake ƙamshi.

Kallon agogon bangon dake ɗakin yayi ƙarfe tara na ranar laraba,ya mutsa fuska yayi haɗe da
hura ɗan ƙaramin hancin shi,wayar shi ya ɗauko ya kunna,yana kunnawa saƙonnin Haulat suka
fara shigowa,shefar da wayar yayi haɗe da jan tsaki.

Gaban shi yai mummunan faɗuwa jin ringin ɗin kiran Dady da sauri ya ɗauka murya a harɗe ya
ce"Assalamu alaikum"

Cikin jin daɗi da annashuwa Dadyn ya ce"Wa'alaikum salaman"

6 / 20