Author : Fatima Batula Category : Love
ƙasa tashi ya fita kuma ya ƙasa mata magana kallon ta kawai yake yi,yana murmushi wanda
bai san dalilin yin shi ba.
Bayan ta gaji da dariyar ta matso da litattafan gaban shi har ya É—auka ya buÉ—e aka kira wayar
shi yana ganin kiran na waye yai wani irin murmushi.
Kallon shi Sabreen tayi a zuciyarta ta ce "Ikon allah waye kuma da ake mishi irin wanan
murmushin"
Duk yadda Sabreen ta so jin abinda yake faɗi ta ƙasa dan yadda yake maganar ko maciji ba zai
ji ba.
Sun daÉ—e suna wayar har sabreen ta fara gajiya sai wurga mishi harara ta gefen ido take yi.
guntun tsaki taja ta tashi ta haye sama.
Bayan ya gama wayar ya ga ba Sabreen a gurin yamutsa fuskar yayi ya tashi ya wuce abinshi.
~~~~~~~~~~~~~
Yau ma ƙarfe ukku da rabi da dawo daga makaranta,kamar yadda suka saba zama a falo kafin
a kira sallah yau ma hakan ne,kiran sallah shi ya tashi su kuwa ya wuce É—akin shi dan gabatar
da ibada.
Bata yi sunanin Ya Naufal zai xo ba,cikin ƙananan kaya da sauko kasa kanta ba ɗan kwalli
,lokacin hajiya ma bata fito ba.
Cikin salo da ƙarya murya yayi sallama ,kasancewar tibin a kashe yake yasa taji
sallamar,amsawa tayi ba tare da ta juyo ba.
A yatsine ya shigo ya zamu kujera ya zauna,yana zama kiran Haulat ya shigo.
"Hello ita ta fara faÉ—a.
"Hi my dear ya kike?
"Lafiya qalau ya su momy,gaskiya yau ina son ganin da wuri jiya kawai amma ji nake kamar na
shekara ban ganka ba,kasan irin damuwar da nake shiga kuwa idan ban ganka ba,plsss ka zo
kar zuciyata ta fashe"
Murmushi kawai yake,ita ke kira kuma ta fishi yin magana.
"Ok to zan zo karki damu"
Duk wanan maganar da suke yi Sabreen bata jin komai,tana jin ya gama wayar ta juyo ta
kalle,bai san lokacin da murmushi ya kuɓuce mishi ba.
Yaƙuna fuska tayi ta ce "Ina wuni tana faɗa bata tsaya jiran amsar shi ba ta tashi ta hau sama"
daman bashi da niyyar amsa mata gaisuwarta.
Da jakar ta fito ,tun daga sama ya hango ta ,da sauri ya sauke kan shi ƙasa,duk sai yaji ya ruɗe
kamar wanda bai taɓa ganin macce da irin wanan shigar ba.
Ita kuwa hararar shi ta dinga yi har ta matso kusa da shi ta aje jakar ta zauna,ganin bashi da
niyyar cewa wani abu yasa ta ce "Gashi
Ɗagowa yayi fuskar nan a ɗaure tamau ya amsa littafin yana ɓuɗewa kira ya ƙara shigowa
wayarshi,É—aukar wayar yayi yana murmushi ya ce " my dear"
Wanan kalmar kuwa Sabreen tayi sa'ar ji a ranta ta ce "Dear tabb yanzu wanan yana da
budurwa ita kuwa wacce iri ce? eh fah saidai irin shi dan idan ba irin shi ba wacce zata iya da
shi" har ya kama wayar idonta yana kanshi.
Ƙafin ayi karatun nan kuwa haulat ta kira yafi sau biyar,har Sabreen ta lura da tafi damuwa da
shi,dan shi duk da bajin abinda yake cewa take yi ba,tasan ta fishi yin magana dan tana lura da
bakin shi.
~~~~~~~~~~~~~
Har sati ya zagayo sun ƙara turuwa a gidan su ɗin.
Sabreen har ta ƙama lura da Haulat tafi son shi,dan kullum a gabanta sai ya ƙira shi a gabanta
sama da sau biyar.
Yanzu ya rage bata dariya akan maganar shi,tayi mamaki da ta gane yana jin indian ,gashi tana
mugun son yaran indiyanshi.
~~~~~~~~~~~~~
Yau sati ranar monday Haulat zata koma bakin aikinta.
Zaune take akan kujerar dake falon su tana latsa wayarta.
A fili naji ta ce "Hmm Sabreen kin sa an bani suspension ke kuma a makarantar zan saka a
kore ki gaba daya baki san hali na ba, da zaki ce zaki ja da ni"
" ke dawa kuma aunty Haulat"
Kallon wacce tayi mata maganar tayi ƙaramar kanwar ta ce sadiya.
Murmushi Haulat É—in tayi ta ce"Yarinyar da ta ja aka bani suspension"
"allah karki raga mata,ki ci mutuncinta"
Murmushin ƙeta haulat ɗin tayi ta ce"Ke ma kin san hali na ba zan raga mata ba,ko kaɗan"
Dariya suka yi,nidai ce kin ɓuture Sabreen ko wani sharrin zata miki kuma?
Ance ramin mugunta gina shi daidai kai dan haka sai ki bi ahankali Haulat ko ta kife da ke.
~~~~~~~~~~~~~
"Hajiyata"
"Na'am Æ´ar aljanna yadai
"Ina son zuwa yawo ne,
"To wa kike so ya kaiki?
"Ya Naufal a'a direba
"Direba ko Naufal"
"Naufal.
"je ki shirya bari na ƙirashi|
Tashi tayi ta hau sama,gurin kayanta ta nufa tana tunanin wani iri zata sa,tamfa ta É—auko me
ruwan maron da Ash da pink da brown a jikinta amma brown din yafi yawa.
kayan sun mata kyau ainun ga mayafinta brown tayi kyau kamar saman alale.
~~~~~~~~~~~~~
Kasan cewa Naufal bai sama kanshi son Aure a ranshi ba yasa har yaje india ya dawo bai taɓa
sex da wata ba,amma tunda ya fara mafarkin yana saduwa da wata wacce bai san ko ita waye
ba ya fara son aure kamar tsiya yanzu ko kiss yaga anyi sai yayi wanka.
Ita kama Haulat macce ce mai mugun sha'awa duk kawaicin Naufal saida ta sa ya fara biye
mata suna taɓe taɓe da lashe-lashe yana jin sauƙi sosai idan ya je gurinta.
Kamar dai yadda ya saba yin mafarkin saduwa da wata yau ma hakan ne,jikin shi har ɓari yake
yi É—an tsabar sha'awa,cikin hanzari ya tashi yayi toilet wankan tsarki yayi,ya fito wayarshi ya
É—auka number Haulat ya shiga kira ringin É—aya yayi ta É—auka shi ya fara magana cikin wata irin
murya
"Hello dear!
Saida tsikar jikinta ya tashi dan jin irin muryar da yayi maganar da ita.
Ita ma cikin irin muryar ta ce" my kana buƙata ne ka zo ni a shirye nake daman kai ne ka ƙi
yarda"
Saida sparm ya fito mishi dan tsabar sha'awa cikin harÉ—aÉ—iyar murya ya ce mata "No Haulat mu
ƙara hakuri har lokaci yayi zan zo yanzu"
Haulat bata ji É—aÉ—in maganar shi ba,dan yadda take jin sha'awarshi shi baya jin sha'awarta duk
wani jan hankali da dubara tana mishi akan ya yarda amma yaƙi daga yaji yana kokarin biye
mata sai ya tureta ya ja motar shi ya dawo gidan,dan Naufal yana jin tsoran zina a rayuwarshi
baya son ya aikata ta.
Cikin ɗauki da zumuɗi ya fara shiri saida ya ƙara yin wanka sanan,wasu ƙananan ƙaya ya
É—auko masu kyawun gaske ash colour sun mishi kyau yana cikin saka takalmi wayar shi tayi
ƙara jin ringin ɗin dadyn shi yasa ya ɗau wayar da sauri haɗe faɗin "Assalamu alaikum"
"wa'alaikai sallam Naufal yi sauri yanzun nan ka je gidan hajia zasu fita kai so ke son ka kai su
kayi sauri sun shirya kai suke jira"
Bai tsaya jiran amsar shi ba ya katse wayar.
Jifa yayi da wayar yana jin wani irin mugun takaici a fili ya ce "Wani irin abu ne wanan kuma duk
wanan mara kunyar yarinyar nan ce Sabreen ita zata ce ni take son na kai su dan ta raina ni"
Hhhh allah sarki yana sauri yaje ya rage zafi gurin Haulat Sabreen zata hanashi.
Ranshi a ɓace ya tashi ya ya ɗau key ɗin motarshi rai a ɓace sai hura hanci yake yi ,a ranshi ya
ce "Zan gyara miki zama Sabreen sai kin yi dana sanin cewa ni zan kaiki"...
wai ke kuwa sabreen kin ɓuture kowa yana son ɗaukar fansa a kanki.
Idan kuma ta afka da su shikenan.
Ranshi a ɓace ya isa Gidan,yana shiga falon ya hangota da irin kalar kayan shi ranshi ya ƙara
ɓace,ji yake yi kamar ya janyota yayi mata mugun duka.
"Sai dai ka mutu dan baƙin ciki amma ni ba zan chanja kaya ba,kuma sai ka kaimu yawo"
Sabreen ta faÉ—a a zuciyarta tana watsa mishi harara ta gefan ido.
Hajiya ta kalle shi ta ga yana ɓata rai ta ce mishi"Kai Naufal nifa ban san irin haka idan ba zaka
kai mu ba,ai da ka gayama wanda ya turoka ,ka zo kana baÉ—a rai kamar wanda aka yima wani
laifi"
Banza yayi da ita,shi a tunanin shi bata sonshi ko kaÉ—an,dan kullum cikin tsungama da faÉ—a
take mishi
Jiri Sabreen ta fara ji amma dan tsabar ƙarfin hali haka suka fito ita ce a gaba ma,duk dan ta
bashi haushi yasa ta hau gaban motor tana murmushin ƙarfin hali.
Har sun fita daga layin su,cikin Sabreen ya fara murÉ—awa tun tana daurewa har ta kasa wani
rikitaccen ihu ta sake.
"Innalilahi wa'inna ilairaji'um shi ta fara faÉ—a.
"Waiyo allah na hajiata faÉ—awa kan jikin Naufal tayi da sauri ya taka burkin motar ya tsaya a
ruÉ—e.
Hajia kuwa har ta fara kuka tsabar ruÉ—ewa.
Ai motor ta musu ƙarama dan yadda Sabreen ki juyi tana birgema a ruɗe Naufal ya ɗauko ta
kamar ƙaramar yarinya suka fito waje,ƙanƙame shi tayi tana ihu mai ratsa zuciya.
Gaba ɗaya ta kashe mishi jiki dan yadda ta maƙalƙale shi gaba ɗayan ƙirjin ta manne su a nashi
ƙirjin.
Ganin ta fara ɗauke numfashi ya ƙara ruɗa su,cikin azama da zafin nama ya sunkuce ta,bayan
motar yasaka ta hajia ta shiga,a kiÉ—ime yake jan motar da gudu.
Allah yasa basu da nisa da Special Hospital,suna zuwa likita suka amshe ta da gaggawa aka
kaita emergency.
Gaba É—aya hajia ta ruÉ—e sai kuka take yi "Waiyo allah na Sabreen karki barni dan allah da me
xanji ga rashin mahaifin ga naki"
Naufal ya janyota jikin shi a hankali cikin sigar lallashi ya ce mata "Kiyi shiru hajia ba abinda zai
sameta kiyi hakuri"
Duk irin lallashin da Naufal yayiwa hajia taƙi hakuri,sai yanzun ne yaƙe ƙara tabbatar da mugun
son da hajia ke mata.
Bayan minti talatin likitan ya fito,hajia tana ganin ya fito ya nufe shi da sauri tana kuka ,cikin
kukan ta ce"Liki...likita Æ´ar...
"Zamu iya ganinta,Naufal y faɗa ganin hajia ta ƙasa magana.
"Eh zaku iya ganinta ,yaew ka same ni a office"
"okk tnx"
Tun kafin su gama magana hajia ta shige,tana shiga ta ganta a kwance an saka mata drip da
alamun barci take yi,kusa da ita hajia ta je tana kuka ta shafa kanta ta ƙasa magana.
Kallonta Naufal yayi tundaga ƴan yatsun ƙafarta har zuwa fuskarta,ɗan guntun murmushi yayi
ganin fuskar ta É—auke da annuri duk da kasancewar barci take yi,tsintar kanshi da jin mugun
tausayinta yayi,tuno yadda take da tsiwa da ƙarfin hali amma gata kwance," hmm banda ciwo
da yaushe yarinyar nan zata ƙanƙame ni kamar zata haɗe jikinta da nawa guri ɗaya" ya faɗa a zuciyarshi cike da jin tausayinta.
"To meke damunta?
Wanan tambayar da yayi wa kanshi ita ta tuno mishi da kiran da likitan ke mishi.
"Hajia bari naje gurin likitan ,bai tsaya jin cewarta ba ya wuce.
Zaune yake a cikin office ɗin likitan bayan sun ƙara gaisawa likitan ya jefu mishi tambaya"
Kwana nawa take yi idan tana al-ada kuma duk bayan wata nawa take yi"
Zare ido Naufal yayi dan bai san ta inda zai fara bashi amsa ba.
Murmushi likitan yayi ganin halin da yake ciki,sanan ya ce "ba kaine mijinta ba"
Da sauri ya ce"A'a ni yayan ta ne"
"ok to ina mahaifiyarta"
"Mahaifiya ya faÉ—a a hankali cikin rashin sanin amsar da zai bada.
"A gurin wa take zaune" likitan ya ƙara jefo mishi wanan tambayar.
"Hajia bari na kirata"Naufal ya faɗa y miƙe tsaye ya fita jiki a mace"
Yana zuwa ya ga hajia zaune kusa da Sabreen ɗin tana kuka,tausayin sabreen ya ƙara ji.
Sai yanzu ya tuno da bai gayama su momy ba,wayar shi ya É—auko ya kira momyn ringin É—aya
tayi momy ta É—au wayar.
"Hello momy muna asibiti fa Sabreen bata da lafiya"
"innalilah wa'inna ilairaji'un momy ta faÉ—a a ruÉ—e.
"Wani asibitin?
"Special hospital.
Yana faÉ—a ta katse wayar.
A tare suka zo asibitin ita da Farrah,har lokacin sabreen bata tashi ba.
Har gurin ƙarfe goma na dare,Naufal ya so ta farka yana nan,amma taƙi haka nan suka dawo
gida,Haulat ta kira shi yafi sau biyar bai É—auka ba ,bai ma ga kiran ba dan a motor yabar motar.
Yana isa É—akinshi ya kirata ya sanar da ita abinda ke faruwa,bata ji daÉ—i ba,shi kanshi ya nuna
mata bai ji daÉ—i ba.
Ƙarfe goma sha ɗaya Sabreen ta farka,ta ganta a gadon asibiti tuno abinda ya faru tayi tsaki ta
ja tuno yadda tayi wa Naufal ranta ta ce"Yanzu zai raina ni" í ¾í´£ji bala'i irin na Sabreen.
~~~~~~~~~~~~~
Tunda sassafe Naufal ya tashi kamar yarda ya saba dai mafarkin nan yau ma hakan,wanka yayi
sanan ya shirya,zama yayi yana duba computer tarshi.
kiran Dady ne ya shigo da sauri ya É—auka haÉ—e da sallama,faÉ—a dadyn ya fara mishi mai yasa
bai gaya mishi Ankai Sabreen asibiti ba.
Naufal yayi mamaki irin son da suke yiwa Sabreen.
Ƙarfe tara suka shirya suka tafi asibitin har lokacin Sabreen bata tashi ba,dady ya ruɗe ganin
halin da Sabreen ke cike.
Shi da hajia suka je gurin likitan tambayar hajia yayi awata nawa take al-ada,Hajiar ta ce
mishi"takan kai wata uku ko huÉ—u ko biyar bata yi bayi ba,amma idan ta fara takan yi kwana
bakwai"
Likitan ya ce "To gskeyi dole idan har ana son ta daina wanan matsanaicin ciwon ciki a mata
aure.
"Aure! hajiar ta furta a hankali.
Alhaji ya kalli likitan ya ce "to mun gode sosai ya miƙa mishi hannu,sanan suka fito jiki ba ƙwari
kowanne da abinda yake tunani a ranshi.
Har lokacin Sallah Sabreen bata tashi ba,Naufal bai so ba,bayan sun tafi sallah ta farka da ƙyar
ta samu ta ci abinci sanan tasha magani ta ƙara kwanciya.
Kwana nan Sabreen Ukku a asibiti aka sallame su,har lokacin ba su haÉ—u ba,Kuma dady ne
yakai su gida.
~~~~~~~~~~~~~
Cikin sky blue ɗin material riga da sikit sun mata kyau matuƙa,tafiya take yi tana yanga kamar
zata ƙarye dan yadda ta ke rangwaɗa ga dugun takalmi ta saka a bakin glass,tana isa cikin
glass É—in É—aliban suka tashi tsaye.
"Goodmorning Aunty Haulat!
Saida ta zauna ta gama iyayinta da yamutsa fuska sanan ta amsa musu.
Kamar yadda ta saba koyar da su cikin iyayi da kilibibi yau ma hakan tayi.
Tunda ta shigo cikn ajin ta ke wurga ido ko zata ga Sabreen amma bata ganta ba,tayi mamaki
da bata ganta ba,har ta fara tunanin ko latti zata zo nan ma shiru ba amo ba labarin Sabreen a
makaranta.
~~~~~~~~~~~
kwance take akan cinyar hajia ,kallon film É—in idia take yi ,ita kuma hajiar tana shafa mata kai.
"Kitsonki ya tsufa Ƴar aljanna"
"Uhmm nifa bana son kitson nan,hajia gobe zanje makaranta"
"Me? bazan barki ba sai kin ƙara jin sauƙi haka kawai
Hankalinta ya karkata ga film É—in da take kallo,dariya ta fashe da ita.
Daidai lokacin ya sako kai cikin falon" Kin samu lafiya kenan" ya faÉ—a a ranshi a fili kuwa cewa
yayi "Assalamu alaikum" cikin muryar shi wacce ya saba magana da ita.
ƙamshin turaran shi taji da sauri ta ɓata rai kamar ba wacce ta gama yin dariya ba.
Hajiya ce a amsa mishi fuska É—auke da annuri.
Saida ya zaunan sanan ya ce "Ina kwana hajia ya me jikin?
bai jira amsawar hajia ba kalli Sabreen yadda yaga tasha guno ya bashi dariya aran shi ya ce
"yarinya ce ke" a fili kuwa ya ce "Sabreen ya jikin? yana wani yatsina fuska kamar yadda ya
saba.
Hajiar ta ce "Lafiya lau mutan india ya kokari"
"Alhamdullah!
Ganin Sabreen bata da niyyar amsawa yasa hajia ta ce mata"Ƴar aljanna yana miki ya jiki,baki
ga É—awainiyar da yayi ba yayi kokari sosai"
"Da sauki ta faÉ—a ko kallan inda yake bata yi ba"
Shima bai bi ta kanta ya tashi haushin kanshi ya fara da haushinta ta samu yana gaishe ta
amma zata mishi haka.
"Hajia bari na tafi momy tana gaida ku,tana faɗa ya bar falon a fusace da ƙudirar ba zai ƙara
mata magana ba.
~~~~~~~~~~~~~
Hau ma haka Malama Haulat ta isa cikin ajin bata ga Sabreen ba.
Bayan an tashi har mutane sun fara watsewa ita tana nan daman jira take yi a watse É—in.
Wani É—an matashi ne da dukkan alamun ma'aikaci ne a makarantar,kusa da ita ya matso wani
ƙazamin kallo tai mishi sanan ta ce "Yau ma bata zo ba,amma nasan zata zo,ka tabbatar da
kayi yadda na faÉ—a maka kana ji na ko
Murmushi yayi ya ce" Ai ko fyaÉ—en kike son nayi mata zanyi ni ba abinda ba zan iya ba akan
kuÉ—i"
"No idan kai mata fyaÉ—e asirin mu sai tuno za'a gane dan iyayenta manyan mutane ne ba zamu
iya ja da su,kawai kayi yadda na ce ma,ina son ta tozarta ta wulaƙanta gaban mutane a nan
kuma nasan kurar ta za'ayi a makarantar,ta ƙarasa maganar tana murmushin mugunta.
"Waw kanki na ja Haulat"
~~~~~~~~~~~~~
Kissing ɗin juna suke yi cikin zaƙuwa da ɗauki ta ko ina a jikinta yake kissing wanda ita ta bashi
damar hakan dan ita ta cire rigar jikinta,ƙokari take yi ta cire mishi wandon jikin shi,cikin mugun
zafin nama ya