Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

FALAK Book Auren Sirri 1 & 2 By Zainab Habib

Author :  Zainab Habib Category :  African Stories & Novels

Chapter   4 / 19

9K to 12K   out of 54.7K words

masoyi, ta6 ga dukkan alamu littafinnan zaiyi dad'i barin karanta pegi d'aya sai in duba system d'ina, tasa wayarta a silent.
A hankali take bin hausar tana gane karatun, sosai kuma take mamakin mutanen da suke tsayawa 6ata lokacinsu akan soyayya "mtswww indai tsoyayya littafin ya k'unsa wlhi nabar karantashi wannan ai 6ata lokaci ne"
Tana mita Munira ta shigo tana cewa "anata shirye-shiryen tafiya ko? kafin ki tafi please ki tambayi Ummu muje Shan ice cream" Falak ta zaro ido kafin tace "Hamm bakinsan abinda ke wakana bako?" to dad yace kar'in sake fita, Munira ta zauna kusa da Falak kafin tace "wai nikuwa ya labarin mutanen da suka kamaki?" Falak tace "tun yaushe suna station ai basuyi kwanan farinciki ba...

Afuwan for the late.
Masu son shiga group d'ina na WhatsApp ga numberta mata zallah please 08141799224


#Tem Falak kunyi bacci ne?
Mom Islam
*FALAKšŸ’*


Mom Islam


E.O.W


Page 13-14
Washe gari, duk wani shirye-shiryen da su Ummu zasuyi tun dare aka gama had'awa Falak,
Yau jirginsu ya tashi zuwa Germany.
Zaune na hango dad bakinsa yak'i rufuwa ya nannad'e hannayensa yanata baza ido, hango Falak yayi tana sakkowa daga matattakalar benen jirgin fuskarta d'auke da fara'a, cikin d'aga murya tace "oyoyo my dad"
Dad ya tako a hankali ta fad'a jikinsa tana cewa "dad ya aiki" dad yayi murmishi kafin yace "Falak ai aiki kam baya tafiya inda ya kamata saboda Babu ke.."
Daga nan suka shiga mota bayan yasa kayanta suka wuce company d'in dad wato (F&A) meaning..Falak Abubakar.
Washe gari ta fara gudanar da aiki sosai cikin fahimta,
Switzerland
Wani irin shewa Maleek ya saka tare da shafo gashin kan wata baturiya dake kusa dashi, cikin yarensu tace "ka matso ya naga kamar baka farinciki da zuwana?"
Maleek yayi dariya kafin ya shafo Brest d'inta da suke a tsatsaye yace "nayi kewarsu, ashe kina hanya, yau bazan koma gida ba"
Budurwar daya kira da Hindu tace "Maleek yaushe zamuyi aure?"
Cikin mamaki nace to bayan matarsa maman beauty yanada wata budurwar kenan?"
Maleek yace "karki damu akwai wani abun da nake jira gagarumin biki za'ayi na kece raini Wanda zai girgiza mutane"
Ta had'e bakinsu guri d'aya tana wani tsotsa abin dai gwanin..suna tsaka da hakan Manaf ya shigo da sauri yana cewa "Yaya Falak ta dawo"
Kan Maleek ya fara juyawa da sauri ya janye Hindu daga jikinsa kafin yace "me kake nufi dama tana raye?"
Maleek yaja dogon numfashi kafin yace "Hamm wlhi idona idon Falak bari kaga videon da nayi mata lokacin da take zaune itada oga Abubakar"
Maleek ya zaro ido lokacin da yaga Falak ta k'ara kyau mai ban sha'awa,
Maleek yace "anya wanna yarinyar ba aljana bace?"
Ya Mike cike da masifa ya kama hannun Manaf suka tafi yabar Hindu a gurin, dogon tsaki Hindu taja kafin tace "nasha alwashin lasa maka sweet honey ta yanzu komai nawa ya rushe Amma akwai wata hanyar"
Ta mik'e da fingilar rigarta tabar gurin.

A wani babban filin maleek inda brothern Beauty yake aiki suka tsaya shida Manaf, Maleek yace "Manaf bani ingantacciyar shawara akan waccar maiyyar" Manaf ya dafa kafad'ar yayan Nasa kafin yace "hamm, ai shawarar dai itace ka auri yarinyar"
Maleek yai saurin juyo da kansa kafin yace "menene dalili?"
Manaf yayi dariya yace "kace zaka mallakawa oga Abubakar dukkan dukiyayon daka mallaka kaga idan ya baka auranta tunda komai nasa a hannunta yake mun haye sama"
Maleek ya shek'e da dariya yana cewa gaskiya brain d'inka tana aiki yanda ya kamata"
Falak..
Dad yace "anjima zamu shida d'akin muga kayayyakin nan amma bazaki ma shiga ba kici gaba da kularmin da aikin dake gabanmu"
Falak ta d'ago fararen idanuwanta kafin tace "dad akan me?"
Dad yace "babu dalili k'arfe 1:am na dare zan shiga" Falak tace "to kafin taci gaba da sarrafa system d'inta.
1:am idanunta ko alamar bacci babu abinda take hagowa ta cikin system d'inne yaja hankalinta, kamar a sama taji dad na magana ba sosai ba, ta ajiye system d'in tare da tafiya gurin k'ofar Sirrin tabbas anan taji kiransa, ta bud'e k'ofar farko taga baya nan, ta bud'e ta biyu nanma haka ta bud'e ta uku, ananne gansa tsaye sai had'a gumi yake, Falak tace "dad meke faruwa?"
Dad ya sharce zufar dake sintiri a fuskarsa kafin yace "na rasa jinin bud'e k'ofa ta hud'u, kuma banga zanen taswirar k'ofa ta biyar inda yake ba, bayan nan ban sauya musu gurin zama ba"
"Uhm" Falak tace "kafin ta k'arasa gurin k'ofar tasa hannunta sai gashi ta bud'e, a k'ofa ta biyar ne jikin dad har kyarma yakeyi, dan a tunaninsa d'akinnan babu abinda zai samu, ta d'aga riga ta bud'e cikinta, sai ga zanen taswirar ya baiyyana"
Dad ya zaro ido cikin mamaki yace "Falak waye yayi miki wannan abun?"
"Bama wannan ba mu shiga mana"
Falak ta d'aga kafad'a tace "a'a zan koma bakin aikina"
Yayi mata rarrashi harya gaji tak'i saukowa, tunowa a cikin ma wani abu ka iya samunsa yasa bishi batare da tayi magana ba.
Da shigarsu sukaga abubuwan (Zinarai) na 6allowa suna fad'uwa, dad ya kalli Falak koda wani temakon da zatayi masa, ga mamakinsa ko uffan batace ba tana tsaye kamar gunki ko motsi batayi ba"
Dad na ganin dukiyayoyinsa zasu hallaka cikin d'aga murya yace "daughter kiyi wani abun mana, please kice wani abu"
Bud'ar bakin Falak tace "dad bazan 6oye maka ba, a cikin ma'aikatanka akwai munafukar ba kai kad'ai suke yiwa aiki ba abinda nakeso ka sani anan shine "sunada fuska biyu kai kuma ka basu sirrukanka, kasan inba ni ko kai ba babu wanda zai shigo d'akinnan sai wani abu ya faru".
Ta d'aure dad da jijiyoyin jikinsa dan koda za'a kasheshi bai san waye nunafukinsa ba gurin ba,
Yace "nidai my daughter a taimakeni komai yayi normal, Falak ta ta6a gefen abun cikin ikon Allah sai gashi komai ya tsaya.
Wasu cups dad ya fito dasu Falak ta shige can ciki, dad yana "cewa bamuzo da komai a hancinmu ba Falak akwai abubuwan da ka iya zamowa guba a garemu kizo mu koma"
Yana maganar tana Kuma shigewa ciki ko saurararsa batayi ba,
Da sauri wani abu ya fad'o a wani d'aki data shiga, cikin mamaki ta durk'usa tana shinshinar abin, Falak tayi murmishi kafin tace Dad zokagani" dad yazo zai gani wasu abubuwa kamar kifiyoyi suka tareshi ya kurma inhu, Abin ma dariya yaba Falak ta kalli kifiyoyin da suke harrinsa ta kalli Dad d'in nata, tana zuwa gabansa ta dafa Dad d'in bubuwan suka 6ace, tana komawa taga babu abinda takeson nunawa dad"
Cikin tashin hankali dad yace "zomu wuce Ina bazan iya wannan wahalar ba"
A fad'ace Falak tace "lallai dad bakasan abinda ke wakana anan gurin ba ko?, uhm dad akwai gagarumar matsala wallahi"
Dad yayi shiru yana kallon Falak kafin yace "Falak meyasa yanzu kike neman sauyamin? A da daga kinga wani abun zai faru da komai namu kina magana Amma ..musamman yau kink'i d'aukar mataki"
"Dad bafa haka bane, nidai yanzu abinda nakeso dakai yakamata a bincika komai na cikin ma'aikatarnan, kasani dad babu wanda yasan da zaman d'akinan ko? to ni Ina tunanin akwai wanda yasan da zaman d'akinan d'an lek'en asirinmu ne shi"
Dad ya zaro ido, cikin tashin hankali ya zauna a d'aya daga cikin kujerar zinaren itama ta zauna wacce ke kallon dad kafin tace "sa'idonmu da k'ok'ari gurin gano masu shige da fuce su zamu afkawa a halin yanzu.
Dad ya sauke nannauyar ajiyar zuciya kana yace "Falak bawai naki taki ba, idan nace bakyamin kokari akan komai nawa wlhi nayi k'arya, abinda nakeso ki fahimta anan shine, mutanan nan mugaye ne bazamu iya dasu ba"
"Kenan dad kana neman kace mu zuba musu ido suyi abinda sukaga dama ko?" to wallahi wataran ma d'akinnan nasu zai zamo"
Cikin rashin jin dad'in kalaman nata dad yace "yanzu bayanin taswira da jinin ya za'ayi?"
Falak tayi Jim kafin tace "nidai a halin yanzu dad nafison a gama da waccar matsalar kafin wannan muje kawai, ya fito hannunsa rik'e da cups biyu na zinare sukayo waje dak'yar.
Tunda suka fito Falak ta fara baza ido akan duk wasu masu hada hadar kaiwa da kawowa da shigowa da kayayyakin da aka sarrafa, sosai kanta yad'au zafi dan zuciyarta ta dagula ko kiran waya bata d'agawa daga k'arshe ma ta kashe wayar, shi kansa dad d'in shima yau yana cikin aiki bayada lokacin kansa sai na sallah.
Switzerland
Maleek na zaune a gidansa suna y'ar k'aramar walimah wacce Beauty ta rasa ko menene dalilin yinta.
Brother yana zaune suna shan wani abun naye wanda bansan sunansa ba, Beauty dake la6e taji Baban nata yacewa brother, Arif ya cinikin jiya ya kasance, labari aka bani kawai shiyasa na shirya maka wannan walimar?"
Arif yace "baba jiya an Sami ribar da ba'a ta6a samu ba saboda kayan sunyiwa nasu siya kyau, nima idan nahek'a karkaga inda nake jina kamar a wata duniyar"
Maleek yace "yayi yarona aci gaba da gashi, kace gidan rawa kake son in bud'e maka ko?"
Cikin murna Arif yace "eh baba"
Wasu zafafan hawaye ne suka fara ambaliya a fuskar Beauty cikin tsananin tashin hankali ta fad'a kan gado tana kuka, a fili tace "kowa yayi sa'ar uba Amma nikam a'a, kowanne iyaye suna bawa yaransu tarbiya Banda namu uban, Momy tana iya bakin k'okarinta gurin ganin ta bamu tarbiya amma baba ya dinga rugujewa, nayi alk'awarin dak'ile duk wata 6araka dake neman tasowa, nayi alk'awarin mayar dakai mutumin kirki da yardar Ubangiji"
Tana gama fad'ar haka ta mik'e jiki babu k'wari, jiri na d'ibarta tayi hanyar da zai sadata da d'akin momynta, tana shiga ta samu momyn na zaune tana ninkin kaya, tace "momy inason zuwa Germany ranar Sunday"
Momyn tata tayi shiru, Abu na farko data fara tunani shine Maleek "ko ya za'ayi ya barta oho"
Momyn tace "bakya tunanin babanki?"
Beauty tace "banaso ya sani ko kad'an bana buk'atar saninsa"
"Me zakije yi"
"Momy ina wannan yarinyar wata y'ar Nigeria ana ce mata Falak yarinya Oga Abubakar Sarkin Zinarai na Germany to ita"
Momy tace "Ina jinki"
Beauty tayi shiru can kuma tace "momy baba ne suke neman kai musu hari a satinnan wlhi bom sukacr zasu sa musu ga mahaifinta kin tunda lokacin da bani da kud'i ya biyamin kud'in makaranta?"
Momy tace "lokacin dana kwanta hospital ma shi kika Kira ai, ina bayanki shin wane taimako kikeso ayi masa?"
"Inason d'aukar video na duk wani abu da su baba sukeyi in tura ma K'awata Falak nasan zata buk'aci hakan"
Ashe tunda suka fara magana Arif yana zaune yana jinsu gashi zuciyarsa ta bushe irinta Maleek baya tsoron komai hasali ma sai ya taro rigima da kudinsa, sbda zuciyarsa ta kangare sakamakon wasu abubuwa da Maleek take bashi tun yana yaro.
Gaban momy ya fad'i, cikin tsananin tsoro tace "Arif my son dama kana hanya?"
Ga mamakinta yau ko rashin kunyar nan daya saba yi mata Babu, yace "eh momy na gwada wayarki a kashe"
Momyn tayi murmishi dan ko waiwayarta bayayi tace "Aiko a kunne take"
Arif yayi kamar beji komai ba, ya fice fuskarsa babu yabo Babu fallasa, momy tace "inaga fa Arif yaji maganarmu"
Beauty tace "ko kad'an beji ba, dan banji alamun tafiyarsu ba"
Momy ta d'auki mayafi, tace "zanje gidan Ummi Amal please ki kula da gida zuwa yamma zan dawo kuma ki gyara ko Ina"
Momy na fita Arif ya biyo ta k'ofar baya kafin ya shigo yana wani irin murmishi Wanda babu wanda yasan ma'anarsa, zama yayi jikinsa na gogar na beauty yace "wallahi naji duk maganar da mukeyi, so yanzu za6i ya rage gareki, koki amince da abinda zan gaya miki ko in gayawa baba kinsan sarai zai kashe momy"
Zufa ta fara karyowa Beauty tace "mene zanyi please karka gaya masa"
Arif ya shafi gashin kansa yace "zan dingayin sex dake kullum da asuba da dare ma idan nazo kwanciya, akwai wasu tablet da zan dinga kawo miki saboda gudun d'aukar ciki, idan hakan yayi miki go ahead"
A firgice ta kalleshi ta kalli idanuwansa kafin tace "wannan ba magana bace abu mafi girma kuma mafi daraja a rayuwata ka kyaleni ka kawo wata shawarar, ya danna number baban nasu, rin daya ya d'aga, Arif yayi mata nuni da wayar" jikinta na rawa tace "na amince .....

Kuyi hak'uri jiya nayi typing ya goge masu son WhatsApp group d'ina suyimin magana WhatsApp only mata zalla please
*FALAKšŸ’*


Mom Islam

E.O.W


Page 15-16

Arif ya wani rungumeta tana tureshi.

Tun bayan tafiyar momy, Beauty ta kasa koda d'aga tsinke sosai jikinta yayi sanyi, har momy ta dawo.
Sallamar momyn ne yasata share hawayen dake ambaliya a fuskarta, momy ta taho da sauri tana cewa "Beauty lafiya? kafin in fita mun rabu da farinciki yanzu kuma nadawo naga akasin hakan"
Beauty ta d'ago shanyayyun idanuwanta kafin tace "momy babu komai ciwon mara ne yake damuna"
Momy ta rungumeta tana bubbuga bayanta alamun rarrashi.
Maleek••
Dariya ya kwashe da ita, a yayinda yake ganin sun shiga d'akin sirrin. Dad tunda ga taswirar a hannunsu, sun shirya shiga d'akin ranar Asabar kasancewar dad yana hutawa a gida ranar shida Falak ko gurin aiki basa zuwa, infact madai ma'aikatar a kulle take.
Maleek da Manaf da Arif dukkansu suna zaune a wani babban d'aki su ukun suke duba taswirar, Maleek ya nuna wata hanya wacce itace ta fitowa yace "tanan zaku shiga "idan zaku fito, ya nuna hanyar shiga yace "tanan zaku fito"
Manaf yace "shikenan abubuwan d'akin ko?"
Maleek ya danna number wani wanda yake yiwa dad aiki, kuma shima yana yi masa aiki, yace "oya hau WhatsApp yanzu sbda maganar bazatayi a baki ba"
Cikin k'an-k'anin lokaci saurayin yahau tare da kunna data, zanen taswirar daya turawa Maleek yagani ya d'auki hotonta ya turo masa, Maleek yace "kwana nawa akeyi kafin a fito daga cikin d'akin sirri?"
Saurin yace "Oga Abubakar yanayin 1days basan ko ku zakukai kwanaki nawa ba, sbda d'akin yanada tsayi da girma ni kaina duk kusancina dashi ban ta6a jin wani 6oyayyen sirrinsu ba, bawai dan babu ba akwai sosai ma".
Maleek yace "idan sun shiga a kwana biyu ko d'aya, mu a wuni zamu shiga mu fito"
Arif yayi dariya,
Yau saura kwana biyu su shiga d'akin sirri, sunata k'ok'arin dak'ile inda za'ayi Falak ta gansu harma tasan da shigarsu, sun shirya bi ta k'ofar baya, sunkuma yi nasarar samun keys guda biyu, duk k'ofofin guda biyar sun gano inda zasu shiga, amma basusan a k'ofa ta nawa akesa jini ba.
Friday, tunda Falak ta tashi ko breakfast batayi ba, tayi wanka tana gama shiryawa ta taho gurin aiki, tabar dad a gidansu kasancewar babban gida ne part d'inta daban nashi daban.
Tana zuwa bayan ta ansa gaisuwar ma'aikatan gurin, ta fara kallonsu d'aya bayan d'aya,
Da sauri ta haura steps zuwa d'akin ajiyarta ta ajiye system d'inta kafin dawo taci gaba da kallonsu, a lokacin sai data rage mutane goma Sha biyar cikin masifa take korarsu ciki harda mutanen Maleek yawancinsu ma na Maleek d'inne tunda ya riga ya siyesu akan tahowar da zasuyi ranar Asabar.
Dad ya fito daga wanka yaji wayarsa na ring, yaje ya d'aga da sauri sbda ganin number ma'aikatansa ne,
"Oga Hajiya tazo tana ta korar mutane ko kanada masaniya akai"
Cikin sauri dad ya shirya ya fito hannunsa rik'e da keys security d'in dake tsatsaye kota Ina ya kalla bayan sun risina sun gaishe shi, ya wurgawa driver key kafin yace "muje company"
Dad na daga cikin mota yana mamakin zafin rai irinnan Falak ga saurin yanke hukunci bata bin komai a hankali, yana zuwa bakin get d'in ma'aikatar y'an Jarida sukayi masa caaah da tambayoyi Wanda shi kansa bai san ma'anarsu ba, hasali ma to mezaice"
Falak na fitowa ta k'araso da dad d'in ciki, tambayar ta koma kanta, cikin k'warin guwaiwa Falak tace "mu muna taimakawa masu k'aramin K'arfi ne, Kuma duk wanda mukaga zai karya dokar wannan company waje zeyi"
D'aya daga cikin y'an Jaridar yace "bakya ganin idan akayi haka ba'ayi rashin adalci ba?"
Falak ta gyara gashin kanta kafin tace "eh su zasuga hakan amma mu munyi ne domin kawo gyara please ku barni haka inada abunyi, sosai dad ya tsaya yana kallonta gata da k'arancin shekaru amma ko tsoron wani abun batayi "oh Falak" dad ya fad'a a hankali tare da shigewa ciki.
Ba iya masu aiki a company dinba hatta mutanen gari sun zagi Falak sun Kuma alak'antata da rashin Imani.
Yau bawani aikin kirki tayi ba, sakamakon wani yanayi da takejin kanta a ciki, lokaci-lokaci takanji gabanta ya fad'i ta mik'e zubur, dad ya kira wayarta yakai sau uku tana gani tak'i d'agawa, tunda yaga haka yasan yau daru ne ya motsa bari ya je inda take tunda you tana kan Sarauta, yana shiga ya sameta ta had'a kai da guwaiwa idanunta sunyi jawur, ta d'ago ta kalleshi, da ganin hakan yasan akwai gagarumar matsala wacce yake tsoron afkuwarta, jikinsa na rawa, yaja kujera kusa da ita ya zauna, kafin yace "haba y'ar albarka mai taimakawa dad d'inta mekuma zai faru please ki sanar dani'
"Dad zanje d'akin sirri, an rasa Taswira ko?"
"Eh an rasa harda kwalbar jini"
Kwalbar jini kai ne ka yarda ita ina tunanin tana cikin d'akunan, taswira kuwa akwai wasu wanda sukeyi mana aiki sune suka sace"
Dad ya zube a gurin zai fashe da kuka Falak tace "naga akwai gurin da akasa numbars ko kuma barmin komai a hannuna dad jeka kwanta"
Muryar dad kamar ta mai kuka yace "Falak wace irin kwanciya Ni bazan iya kwanciya ba"
Falak tace "Ina zuwa"
Bata jira abinda zaice ba ta shige da uban gudu tasa key ta bud'e d'akin duk iya k'warewarta hanyar bincike da baiwa da Allah yayi mata bata isa ta bud'e k'ofofinnan kai tsaye ba, batare da ta duba taswira ba, bata k'arasa cikin d'akin ba ta fara dube-dube, tana danna wasu numbobi a jikin k'ofar k'arshe tana yakice zufar dake sintiri a fuskarta, da sauri tabar gurin tana hamdala, kuma duk numbers d'in data sauya akwai a taswirar.
A inda tabar dad anan ta sameshi, ta duba agogo, tace "nashiga k'arfe 9:am na fito k'arfe 12pm, alhmdulilh, dad ya sauke nannauyar ajiyar zuciya kafin yace "Falak baki sanar dani komai ba"
Falak ta zubawa dad idanu kafin tace "dad akwai masu kawowa d'akin hari, yau ko gobe jibi ko gata, Allah shine masani nidai nabawa gurin kariya ne, am bazamuzo aiki Sunday ba dama, haka Monday ma zamu zauna a gida dad karka damu ni nasan me nakeyi"
"Falak, kinaso komai namu ya lalace ne? akwai mutanen da mukayi alk'awari dasu zasuzo su kar6i kaya Kuma na had'a musu me kike ganin zai faru"
"Komai mukasa gaba mu rok'i za6in Allah wlhi dad inhar kace

4 / 19
Connection failed: SQLSTATE[HY000] [2002] Operation not permitted