Author : Zainab Habib Category : African Stories & Novels
aurenka Amma akwai sharud'a guda uku, inhar ka yarda to auranmu ya tabbata"
Sheik Abdul-Latif ya lumshe kyawawan idanuwansa kafin yace "ina jinki"
Falak tace "na farko bawai dan ina sonka zan aureka ba na biyu kuma shine sharad'i mai tsauri, koda munyi aure karya kai wata uku zaka sakeni Kuma a auranmu babu buk'atar rayuwar aure"
Yayi wani killer smile kamar tana ganinsa kafin ya shafi kwantaccen sajen fuskarshi yace "na amince, nikuma kafin lokacin idan ban koyar dake soyayyata ba kiyi duk abinda kika fad'a, idan har ban dasa miki soyayyar sheik Abdul-Latif a zuciyarki ba kibar aurena"
Falak tayi tsaki mtsw kafin tace "baka da ikon samun wata shirme wai soyayya bansan me mutane suka d'auki soyayya ba kun d'auketa a Abu Mai muhimmanci nikuwa inayi mata kallon 6ata lokaci tare da aikin banza"
Ta kashe wayar gaba d'aya.
A 6angaren sheikh Abdul-Latif ya daka tsalle yana rawa yana cewa "wow nafi kowa sa'a wlhi abin dai kamar a mafarki, kafin nan barinje ma'aikatar mu, nasan a jiragen da zasu tafi anjima bom d'in zai shigo nikuma zanyi iya bakin k'okarina gurin kare faruwar hakan.
Nigeria
Gobe dad zai koma Germany Ummu sai wani shagwa6e masa takeyi kai kace yarinya k'arama, zuwa dare ya koma d'akinsa Dan haka kawai yaji yanason ya ke6e shi kad'ai, yasa kayan bacci tare dayin alwalah ya dawo yayi adu'ar bacci ya kwanta, can dare yayi mafarki wannan tsohon yazo, yana cewa "hak'ik'a yarinyarka ta had'u da wani saurayi d'an baiwa wanda dole ya kasance suna tare a koda yaushe abinda nakeso dakai shine, ka amince da maganar auranta dashi sannan kuma ka janyoshi a jiki ba macuci bane, haskene a gareka"
Da sauri dad ya farka yana mutsike ido kafin ya tashi zaune ya rafka tagumi yana tuno mafarkin da yayi, yasan dole cikin ikon Allah inhar yayi mafarkin wannan mutumin sai abu ya faru to yanzu dai zai zuba ido yaga ikon Allah.
Sai wajen asuba bacci yayi awon gaba dashi, Wanda har saida Ummu ta shigo ta tasheshi sannan ya tashi ya jingina kansa a kafad'ar Ummu, kana yace "ki tayani da adu'a am zanbi jirgin 11:am Ummi tace "koda yaushe inayi maka adu'oi sosai insha Allah nasan sun kar6u a gurin ubangiji".
Dad ya rungumeta kana ya mik'e yayi alwalah ya tafi masallaci.
Bayan yayi sallah ya dawo kai tsaye d'akin Ummu ya wuce ya sameta tayi wanka tayi kwalliya tasa atamfa super Holland yawancin adon atamfar brown ne sai fari da yellow sosai atamfar tayi mata kyau, yana shigowa Ummu ta tayasa cire kaya already ta tara masa ruwan wanka, yana gamawa ya fito d'aure da towel, Sam ta hanashi shafa mai ita da kanta ta shafa masa kana ta ciro masa kayan dazaisa tare da wanda zai koma dasu dukda ba wasu masu yawa bane, lokacin daya gama shiri k'arfe 9:20 a gurguje yayi breakfast yana cewa "to Allah yayi na kammala"
Ummu ta marairaice fuska tace "wlhi bana son tafiyar nan taka sam nikam ka zauna kawai"
Yasan rigima irinta Ummi some times haka take masa Alhalin tasan abincinsa anan Allah yatsaga.
"Kodai so kike in 6ata adon da kikayi?"
Ummu tasa dariya tare da cewa uhm nidai..nidai.."
Dad ya gyara kwalar rigarsa tare da kamo hannun Ummu kai kace k'aramar yarinya suka shiga bedroom d'insa, kallon agogo yayi yaga k'arfe 10 dai-dai, ya kalli Ummu idonsa a d'an lumshe kafin yace "matata tana buk'atar mijinta amma taki sanar dani, idan ban biya miki bukatunki ba ai na cutar dake sbda bana dawowa da wuri"
Ummu ta cusa kanta jikinsa tana dariya marar sauti sosai,
A hankali ta 6alle ma6allin suit d'insa tare da zuge zip d'in wandonsa idonta a lumshe take hakan, lokacin dad ya rabata da komai na jikinta daga nan ya mik'ar da ita akan gado ya fara bin kowacce ga6a ta jikinta da kiss sosai k'amshin turaren Ummun ke kawo masa ziyara yana kuma kwad'aitar dashi, kan kace me yayi mata rumfa yana kallon lokaci karya k'ure, sosai yake shigarta cikin salo irin na dad har Ummu ta gamsu sannan ya mik'e ya fad'a toilet yayi wankan tsarki tare da goge jikinsa ya fito ya sauya kaya dan wad'annan sunyi squeezing.
Har parking space Ummu ta rakashi ya shiga mota kafin ta dawo zuciyarta cike da kewar mijinta.
Saudart••
Zaune take a main parlo hannunta rik'e da mai sunan dad, wanda suke kira da big boy, sosai kamarsa da ubansa ta fito musamman ma da Hamma Aliyu ya mik'o hannu zai d'aukeshi, Saudart tace "habiby inason zuwa gidan Ummu yau"
Hamma Aliyu ya waro ido kafin yace watanki biyu nefa sweetie ki Bari jikinki ya sake k'wari, ta had'e rai bata ce dashi komai ba harya fice, dawowa yayi da big boy ya mik'a mata ya had'e hannunta data mik'a masa ya damk'e tare da mik'ar da ita yace "wato kinyi fushi ne,
Dama wannan ranar zatazo?"
Saudart ta juyar dakai tare da lumshe ido alamar ma bazata had'a ido dashi ba, nocking d'in da akayi ne ya sa Hamma Aliyu nufar door d'in tare da son ganin waye mai shigowar, Hibba da Munira ce dukkansu sunyi k'iba ga wani kyau dukda bawai a wuya suke ba a gidan nasu, amma aikin da sukeyi hankalinsu na kwance.
Saudart ta washe hakora tana cewa "oyoyo sannunku da zuwa"
Suka k'araso suna tsokanar Hamma Aliyu, suna cewa "kaga yaronnan kamarku d'aya sak"
Hamma Aliyu yace "wato kun rainani sam bakwa girmamani tunda kukaga kunyi tsayin k'afa ko?"
Sukasa dariya dukkansu.
Egypt
12:am na dare, Granny ce la6e a k'ofar su Abdul-Naseer tana jiyo dariyarsu tana zaro ido, da sauri ta koma ciki tana gyara d'aurin zaninta, sakamakon jin tafiya alamun za'a bud'e k'ofa, lokacin data shiga d'akinta bata lura ba ta bige da bango, batasan sa'adda ta tsala ihu ba harda cewa "shikenan na mutu bani da amfani"
Abdul-Naseer daya fito zai koma d'akinsa yajiyo ihunta jikinsa na sanye da d'an pants ya d'ameshi, shima dai a kid'ime ya shige "yana granny meya faru?"
Idanunta na zubarda hawaye tace "kawai ji nayi an bigeni inaga akwai aljanu a wannan d'akin naku, yo inba haka ba ya za'ayi a bigeni banji ba ban gani ba"
Abdul-Naseer yace "d'ago muga gurin bigewar"
'Dagowar da granny zatayi idanunta suka sauka kan d'an pant d'in dake manne a jikinsa, ta zaro ido tare da k'ara tsala mahaukacin ihu Wanda ya ninka na d'azu har tana yi kamar zata shid'e ta runtse ido, bai san meye dalilin yin hakan da tayi ba, dan haka yaje zai rungumota ya rarrasheta tace "dan darajar iyayenka ka fice na warke"
Abdul-Naseer ya fice kamar inda ta buk'ata,
Sai daya koma d'akinsa ya tuno abinda take yiwa ihu ashe da wannan shigar ya tafi d'akin granny ga joyst d'insa daya mik'e tunda Fadwa ta gama mutsitsikesa tace tana period, yazo zai tafi d'akinsa shine ya jiyo ihun granny yayo d'akinta.
Yana fita granny ta shafa gomshinta tare da runtse idonta tace "gulma tayi dadi gaskiya sai nayi sati guda ban kuma zuwa gulmar ba"
Germany.
Alhmdulilh jirginsu dad ya sauka lafiya, har driver yazo ya tafi dashi gida, cikin farinciki Falak take gudanar da aiyuka, a can k'asan zuciyarta kuma tunanin cutar da dad d'in da ake shirinyi ne yasata sauya annurin dake fuskarta zuwa 6acin rai, da wuri ta tashi yau ta wuce gida, Allah yasa gogan bai zoba bare ya buwayeta.
Tana isa ta hangi dad zaune a saman kujera yana sarrafa system d'insa, da fara'arta ta k'arasa tana cewa "dad ko hutawa dad Kaga inda kayi kyau kayi k'iba kuwa?"
Dad yana dariya yace "eh to nagode amma ke meyasa naga kin rame ko duk a cikin aikin ne?"
Falak tayi murmishin yak'e gami da cewa "uhm dad ai aiki alhmdulilh tunda kullum ana ciniki idan ka huta zuwa Monday ka duba shagon zakaga ya sake ciga wlhi dad Kaya sun dad'u ammafa tunda ka tafi ban kuma shiga d'akin sirri ba"
Dad yace "to iya kayan shagon aka dinga siyarwa, shagon Sharif fa kina lek'awa?"
Falak tace "eh duka lissafin kud'ad'en suna hannuna duk abinda aka siyar a lissafe yake kamar inda ka tsara tun farko"
Dad yace "alhmdulilh Ummunki tana gaisheki ga dambun nama tace a kawo miki"
Cikin farinciki ta kar6a kana tace "dama inason ince tabayar a tahomin dashi, Allah sarki Ummu nagode sosai"
Daga nan ta wuce da ledar dambun naman d'aki, dan yau batajin cin abinci duk da taga baban tayi abinda takeson ci.
Koda ta shiga d'akin nata sallah kawai tayi tana shirin mik'ewa daga kan sallahya message ya shigo kamar jiya, "karki mance gobe da safe ne"
Tayi tsaki tare da bugar goshinta ta duba agogo, k'arfe Tara na dare, cikin tashin hankali tace "kodai inje gurin dad ne"
Bata tsaya yin shawara da zuciyarta ba ta fice da gudu, tana isa bedroom d'in dad ta samu ya jingina da gado har yanzu aiki yake, tayi sallama ta zauna a kan kujera wace take ajiye a nesa da gadon, dad ya gyara mazaunin gilashin sa kafin yace "Daughter Ina jinki"
Falak tace "dad please inba damuwa inason yin magana mai muhimmanci dakai dad"
Dad ya rufe laptop kafin ya maida kallonsa ga Falak yace "Ina jinki"
Falak taja dogon numfashi kafin tace "dad akwai wani Ina tunanin zaga ganeshi sunansa sheik Abdul-Latif yana yawan siyayya a gurinka"
Dad yace "eh na ganeshi meya faru?"
Falak tace "wai yana Sona har.."
Dad ya katseta da cewa "kema kina sonsa ne?"
Ta girgiza kai alamar a'a kafin tace "dad gobe da safe da misalin k'arfe 1:40pm kasandai lokacin al'umar da suke cikin ma'aikar nan sun tafi sallah ko? to da lokacin ne za'a kawo bom ciki domin babu kowa, sunason su tashi ma'aikatar daga aiki"
Da sauri dad d'in ya kalleta kafin yace "me sheikh Abdul-Latif d'in yayi?"
"Uhm cewa yayi wai inhar na amince zan aureshi wlhi babu wanda ya isa yazo ko kusa da ma'aikatar nikuma dad babu aure a tsarina"
Cikin rashin hankali da rarrashi dad yace "Falak ki dubi Allah ki dubeni ki dubi 6arnar da ake shirin tafkawa ki dubi soyayyar da kike yiwa dad d'inki kice gobe ya turo iyayensa koba komai shid'in haskene a garemu tabbas.....
Masu so daga farko ga numberta 07141799224
*FALAK🍒*
Mom Islam
E.O.W
Page 43-44
Falak ta girgiza kai kafin tace "dad nace masa inada sharad'i akan auran kuma ya amince da hakan"
Da sauri Dad yace "sharad'in meye daughter?"
Falak tace "koda ya aureni 5 months zanyi ya sakeni ko 3 bayan haka kuma babu wata mu'amala a tsakaninmu yace ya amince"
Dad ya zaro iso tare da cewa "Falak yaushe kika iya tsara magana haka, kina nufin auran mekenan zakiyi? Falak tayi shiru, can kuma tace "Dad nafasa wannan auren"
Ai da sauri ya kamo hannunta yana cewa "gobe ne Falak shikenan kinason jefamu a halakar rayuwa ko?"
Falak tace "Dad na amince amma ka yarda da sharud'a na"
Dad yace "na amince daughter"
Washe gari.
Sheikh Abdul-Latif ko runtsawa beyi ba, yana can ma'aikatar su yana son ya gano jirgin da za'asa bom din yakai company d'in dad, cikin sa'a ya gano jirgin ya d'auki video ya turawa Fakak, tana gani ta tafi gurin dad daya dawo daga masallaci yanzu ta mik'a masa tana cewa "dad ka kalla dakyau, ka kira sheikh Abdul-Latif kace "na amince"
Hannun dad na rawa ya danna number sheik Abdul-Latif a wayar Falak kafin yace "nine mahaifin Falak, da sauri sheikh Abdul-Latif yace "barka da asubha dad"
Dad yace "barka ina fatan ta sanar dakai akan ka turo iyayenka?"
Sheikh Abdul-Latif yayi shiru kafin yace "eh tayi magana"
Dad yace "good yanzu dai ya ake ciki?"
Sheikh Abdul-Latif yace "na dakatar da duk wani jirgi dazai kai kaya Germany saboda karsu shigar ta 6arauniyar hanya"
Dad yace "to alhmdulilh godiya muke gaskiya shigowarka rayuwarmu babban abun alkairi ne"
Sheik Abdul-Latif yayi murmishi.
Falak ta harari dad kana tace "haba Dad kamarka kana k'as k'antar da kanka a gurin sheikh Abdul-Latif wannan bai dace ba"
Dad ya kalleta kafin yace "ni ai naga dacewar hakan"
Yau kam basu fita aiki da wuri ba saboda tattaunawar da suka tsayayi su biyun.
K'arfe 12:pm suka isa company kowa sai gaishesu yakeyi suna amsawa cikin mutunci, har suka k'arasa office.
Dad ya wuce 6angarensa itama ta wuce nata, bata wani yi aiki ba sai tunani daya d'auke mata hankali, musamman ma akan amincewar da tayi na auranta da sheik Abdul-Latif, tana tsaka da tunani CC tv ya nuno shigowar sheik Abdul-Latif cikin office d'in dad, da sauri ta juyar da kanta dan ko burgeta bayi yake ba, gashi dai fari sol harya fita haske duk kyawunta idan suka tsya zaka iya cewa yakusa finta kyau,
Bayan sun gaisa da Dad sheikh Abdul-Latif yace "nagode da k'ar6ata da kayi Dad iyayena suna hanya gobe ni d'an Switzerland ne amma ina aiki anan Germany ma'aikatar kula da zirga zirgar jiragen k'asa"
Dad yace Masha Allah "muna son sanin anguwarku"
Sheik Abdul-Latif yace mahaifina ba wani 6oyayye bane hasali ma shine liman a babban masallacin Juma'a na Switzerland ana kiransa da Imam Abdurraman"
Dad ya rik'e baki kafin yace "babu buk'atar bincike ai mutumina ne, ko makonni uku da suka shud'e yazo yasiyi zobuna a gurina dan haka sai sunzo"
Daga nan sukayi sallama akan gobe iyayensa zasu iso,
Zuwa dare dad yahau WhatsApp lokacin Ummu tana online, bayan sun gaisa ta dinga bashi labarin missing d'insa da tayi tare da yi masa adu'oin nasara a rayuwarsa,bayan sun gama magana yayi gyaran murya, tare dayi mata voice yace "Albishirinki Y'arki ta sami miji insha Allah bazamuyi dana sani ba ni kaina ada naso k'in auren yanzu kam ina ganin akwai alkairi"
Ummu ta saka emoji na alamar zaro ido kafin itama tayi voice d'in tace "amman nasan ba lallai Falak ta amince ba sbda tanada taurin kai, to shima d'an Nigeria ne ko ya akayi?"
Ummu ta tambaya cikin son jin inda saurayin yake,
Dad yace "a'a anan Switzerland yake yaron limamin can ne"
Ummu tace "idan alkairi ne Allah ya tabbatar idan sharri ne Allah ya watsa lamarin".
Dad yace "Amin"
Sukayi sallama.
Sai yamma liss suka koma gida, sam dad ya kasa gano inda Falak d'in ta dosa, abinda bata ta6a yi masa ba yau shine takeyi masa, fushi sosai takeyi.
Bayan sun isa gida, Baaaba mai aiki ta jere musu abinci kala-kala da wanda Dad yakeso dakuma wanda ita Falak d'in takeso, daga haka tayi musu sannu da isowa ta fice.
Dad ya kalli Falak dake shirin mik'ewa ya k'irk'iro murmishin yak'e kafin yace "daughter bazan yi miki auran dole ba inhar bakya sonsa a fasa auran?"
Falak ta kalli Dad, sosai tausayinsa ya kamata tace "dad zan aureshi amma inhar ka yarda da sharad'ina"
Dad ya k'ara cewa "na amince"
Daga haka ta fice, sbda kiran sallahr magariba da akeyi, shima dad d'in ya fice masallaci.
Switzerland
Bom biyu Maleek yasa aka fitar, d'aya za'akai Germany d'aya kuma India duk ma'aikatar mutane, sosai abin yaba Maleek mamaki ta inda yaga an sauya jirgin da aka sanya bom din aciki I zuwa wani daban, ya fara tunanin akwai me yi musu lek'en asiri kodai Manaf ne munafukinsa?
Ya mik'e a zuciya ya fice kai tsaye gurin aikin hodar ibilis d'in da akeyi masa ya nufa, ya sami Manaf ya zubawa acikin wata leda babba ma'ana yana gudanar da aikin kamar inda ya kamata, Maleek ya girgiza Kai tare da shafa saman zuciyarsa yana lumshe ido, yasan inhar ya kashe Manaf to komai nasa zai koma baya, koba komai yana taimaka masa,amma zeyi masa last worning akan fitar masa da sirrin sa.
Acan gidan momy anata shirye-shiryen komawarsu sabon gidan beauty da Arif, Beauty sam ta rasa nutsuwarta harta fara tunanin guduwa dan tana ganin su momy sunyi san ransu ne kawai.
Ranar laraba da safe, 9:30am momy ta kira beauty bayan tazo tace "ga akwatuna nan Arif ya kawo, Wanda a zahiri Maleek ne yayi su babu laifi kayan sunyi kyau gasu Kuma masu tsadar gaske,
"Sunyi miki?"
Momy ta tambaya sbda taji ra'ayina,
"Eh tace "
"Amman kinsan da cewar jibi ne zaku koma gidanku ko?, dan babanki yace baya san wani taro"
"Tom"
Kawai beauty tace kanta a k'asa,
Tun yau Momyn take ta bata wasu jik'e-jik'e wanda Sam ba dad'i sukeyi mata a bakinta ba,
Washe gari momyn da kanta ta kar6o Kaya a gurin d'inki kayane ba irin namu ba dan babu atamfa aciki daga sari sai Pakistan da sauransu,
A ranar momy tayiwa Ummu Shukura waya tace "magar tarewar beauty ya tashi amman karta gaiyyaci kowa"
Ummu Shukura ta shirya itama ta taho da nata maganin Kona meye oho aka dinga bata tanasha, in taki suyi mata masifa dole ta sha.
Washe gari suka rakata gidanta dake can k'asa dasu anguwarsu babu nisa tsakaninsu da momyn, gidan ya had'u babu k'arya ko mak'iyi albarka amman a zuciyar beauty sam babu abinda ya burgeta bare ya bata sha'awa, ko kwana basuyi ba suka dawo gida suka barta ita kad'ai sai kace maiyya, tayi kuka kamar zata tsiyayyar da idanuwanta amma Babu Wanda yasan tanayi balle ya kawo mata agaji, ga gidan tafkeke sai kace ma'aikatar guda, ta mik'e jiki a sanyaye ta fara Zagaye ko ina tana share hawaye, a tsorace ta jingina da bango dan tagaji da yawo jiri ya fara d'ibarta, ta zube akan doguwar kujerar data gani a d'akin, bayan jirin ya lafa mata ta tako a hankali ta bud'e wani d'aki, babu kowa a ciki Amma a shirye yake da makeken gado da drowa masu kyau da kafet a tsakiyar d'akin kamar an sata ta bud'e drowar tana ja da baya, cikin sauri ta kulle tana ambaton "innalilahi wa inna ilaihir"
Ta toshe bakinta tana wani irin kuka, ta kasa janyo k'afafunta daga gurin bare ta samu tabar d'akin, jikinta ya fara karkarwa abinda ta gani ya dinga dawo mata tana jijiga tashi d'aya kanta ya fara neman juyewa, da k'yar ta fara karanto sunayen Allah bakinta na rawa, sannan ta Sami k'warin guwaiwar ficewa tanayi tana tangad'i har ta koma sashen da aka ajiyeta, a daren tayi kuka harma ta rasa inda zatayi, idanunta sun k'ank'ance muryarta ta dashe, ko tafiya sosai bata iya yi, itada bata k'etare lokacin Sallah, yau kam ko sallahr isha'i batayi ba balle magariba haka ta kwanta sbda tsoron abinda ta gani ya mugun tsumata.
FALAK••
Asabar basu fita aiki ba, kafin zuwan su Imam Abdurraman Dad yayiwa manyan abokansa maganab akan sirikinsa zai zo, basu bashi matsala ba sukayi masa halacci irinna mutanen arzik'i, nan danan aka fara yi musu special food gida ya game da k'amshi, Falak ko tana kwance a d'aki ko breakfast batayi ba bare tasaran mik'ewa, dan tun