Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

FALAK Book Auren Sirri 1 & 2 By Zainab Habib

Author :  Zainab Habib Category :  African Stories & Novels

Chapter   16 / 19

45K to 48K   out of 54.7K words

zare mata idon Amma a banza tak'i saurarsa,
Da abin ya gagareshi yaga tana wahala ya Kira dad yace masa "Saudart fa tak'i zuwa asibiti Kuma batada lafiya"
Dad yace "kace mata injini inhar bata je hospital ba wlhi zan 6ata mata rai"
Dole Saudart ta shirya jiki babu k'wari taje hospital, anyi mata gwaje-gwajen abubuwan daya kamata, aka bata guri ta zauna tajira sakamako, wani doctor ya fito hannunsa rik'e da farar takarda ya mik'awa Saudart, bayan ta kar6a yace "congratulations madam an sami juna biyu har na wata d'aya"
A zuciyar Saudart tayi hamdala sosai musamman ma da taji ba'asin ciwon nata, tayi alk'awarin bazata nunawa Hamma Aliyu ba inhar Allah ya bata lafiya sai dai yaga cikin a jikinta,
Ta dawo gida zuciyarta cike da farinciki, tana zaune a parlo yamma tayi har k'arfe shida da rabi 6:30pm Hamma Aliyu ya shigo hannunsa rik'e da ledoji manya, masu d'auke da fruits, Saudart taje yimasa sannu da zuwa, yana rungumeta ta wanke masa jiki da amai, Hamma Aliyu yayi tsaki kana yace "Saudart meyasa kike wulakantani ko wani lefin nayi miki ai sai kiyimin bayani ba kidinga tozartani ba, duba kigani yanzu kin 6aramin jiki hankalinki ya kwanta ko? kinayin abu kamar k'aramar yarinya"
Saudart ta share siraran hawayen da suka sami damar sulalowa daga fuskarta tace "Hamma na kayi hak'uri haka kawai na tsinci kaina wlhi bawai da niyya nayi hakan ba"
Ya ajiye d'ayar ledar da be mik'a mata ba ya shige ciki hankalinsa a tashe da bak'incikin sabon halin da Saudart d'in ta d'auko Wanda besan dashi ba.

Germany••
"Dan Allah ka zubarmin da cikinnan ko nawa ne zan biyaka"
Doctor ya kalli beauty yace "baki da miji ne koke budurwa ce sannan kuma meyasa kikeson a zubar miki da ciki?"
Beauty ta fashe da kuka saboda jin tambayoyin daya jero mata tace "ka taimakeni idan zaka iya ba sai kasan wani abu game dani ba, idan har bazakayi ba zanje gaba akwai me yimin"
Doctor ya girgiza kai kafin yace "a zubarda ciki cikin biyu za'ayi d'aya, ko cikin ya fita ki rayu ko cikin ya fita ki mutu"
Cikin sauri tace "ai rayuwata a duniya bata da amfani Sam banga amfaninta ba shiyasa nakeso hakan ya zamo hanyar ajalina"
Cikin azama doctor ya kama hannunta kamar me tafiya da ita wani guri ya turata waje tare da rufo get d'in hospital d'in, a zuciyarsa yana ambaton astagfirullah Allah ka yafemin kamar inda na d'aukarwa Mama alk'awarin bazan cutarda d'an kowa ba insha Allah bazan cutar d'in ba, Amma inajin wannan yarinyar kamar munada dangantaka tsakaninmu, kai koma menene taje gaba mu anan bamayi"
Yana gama maganar ya zube akan kujera ya safe kansa tare da fad'awa duniyar tunani, har abokin aikinsa yayi nocking ya sakeyi har sau uku doctor din beji ba, dole yasa abokin aikin nasa ya kirashi a waya, kasancewar zuuu d'in da takeyi ne ma yasan ana kiransa anda yasa a vibration, firgit ya mik'e kamar me bacci tare da d'aga wayar yana cewa "Umar lafiya?"
"Eh mana tunda kana jina kak'i daga waya saboda wulakanci"
Doctor mai suna Adeeb yace "Hamm shigo ka zauna in baka wani labari"
Umar yace "labarin naka da baya wuce wannan yarinyar da kaga an hasko a TV mai suna Lina?"
Adeeb yace "nifa yau ina gaya maka wlhi Raina ya matuk'ar 6aci, sakamakon zuwan wata yarinya Wai a cire mata ciki"
Umar yace "ciki?"
Adeeb yace "eh ciki, wai har cewa take, tana son ta mutu"
Umar yace "k'yalesu shegu y'an iska suje su aikata iskancinsu sannan suzo suna cewa wai a taimakesu, k'ila bata so a gidansu asan tayi ne"
Adeeb yace "haka kawai nakejin wani abu game da yarinyar nan tausayinta ya addabi zuciyata"
Umar ya ta6e baki yana dariya ya nuna Adeeb yace "kodai kana sonta ne kaga sai kuyi rainon yaron"
Adeeb yace "Amma zanci uwarka haba dan Allah daga magana sai ka siffantata da wata kalma wacce batada ma'ana"
Beauty na tafe tana kuka, batayi tsammanin akwai Wanda ke binta a baya ba taji anyi mata horn, "shiga in taimaka miki"
Driver ya fad'a yana kallon Beauty, Arif dake backside yayi murmishi kafin ya kalli mudubin gaban motar wanda kana iya hango Wanda yake zaune a gaba,
Ga mamakinsa yaga yau tayi mugun ramewa kamar wacce tayi tafiyar k'afa bai San kuwa tafiyar k'afar tayi ba.
A wani tamfatsetsen gida drivern yayi horn suka shiga ciki, Beauty ta zaro ido kafin tace "driver nikuma me zanyi anan nida kace zaka taimaka ai ko a gefen hanya zaka ajiyeni"
Cikin rashin tsammani dakuma bazata taji muryar Arif,
"Ina kikaje nan gidan ne ya dace dake domin hutawa dole ki dawo gidannan wancan yayi miki k'ank'anta so nan ne dai-dai ke"
Cikin sauri ta waiga gabanta ba dukan uku-uku, ta wani kalleshi kamar me ciwon wuya sai Kuma ta sunkuyar da kanta k'asa,
Jinin jikinta yana bata ba lafiya ba, ita dai har ga Allah wannan gidan bawai ta yarda dashi bane, Anya akwai k'amshin gaskiya a tare dashi? bata da mai bata amsar maganar hakan yasa tayi tsaye tana jiran kalma ta biyu da zata fito daga bakinsa,
"Mrs Arif well come to the new house"
A halin yanzu tunda ta sami cikinnan sai taji ko kad'an bata San muryarsa ta tsaneshi shi da cikin jikinta,
Ganin bazata taho ba yasa shi d'agata cak ya wuce da ita had'ad'd'en parlon, koni da nake baku labarin mutuwar tsaye nayi sakamakon aljannar duniyar dake cikin parlon kaya ne akasa nagani na fad'a, a zuciyarta tace "d'azu fa na baro gida tayaya aka sami wannan gidan, kodai Arif yanayi mata shigo-shigo ne ruwan ba zurfi"
Ganin zancen zuci zai iya fitowa fili ya sata yin shiru ta tsaya cak akan kujerar ma bata zauna ba tsabar tsoro,
My everything nan ne gidanki momy ta koma can, akwai komai da kike buk'ata momyn ma tace zuwa gobe muje tana yi miki albishir da gobe ne zagayowar ranar aihywarki"
Tak'aitaccen murmishi tayi na gefen baki kafin tace "momy tayi fushi dani danme zanje gurinta?"
"Arif ya Kira wayar momyn Ring d'aya zuwa biyu ta d'aga cikin fara'a momyn tace "ah my son Ina Islam?"
Abin ya matuk'ar bata mamaki Anya wad'annan sababin gidaje da fara'ar da momyn takeyi Babu wata manufa?"
Bayan ya mik'a mata wayar momy tace "My daughter nayi kewarki ashe har k'aruwa muka samu bani da labari?"
"Oh momy kamar me ta6in hankali"
Beauty ta fad'a tare da kawar da zancen ta hanyar cewa "momy ashe gobe ne birthday d'ina?"
Momy tayi dariya tace "kin mance ne ai duk shekara munayi liyafar dana shirya miki harda na jikana sai kinzo d'in dai kawai"
Batare da tacewa momyn komai ba ta mik'awa Arif wayar tare da gyara zamanta akan lallausar kujerar mai zaman mutum biyu.
"Zo kigani"
Arif ya janyo hannunta ya kaita wani d'aki Wanda ya kasance bedroom d'inta, mutuwar tsaye tayi sakamakon ganin uban dukiyar da aka kashe, shi kansa gadon ma Mai remote ne gadon yana hade da katifar Kuma koda yaushe Ac na kad'ashi, beauty ta dinga ta6a gadon tana mamaki tsakanin sati guda a ina suka sami wad'annan mak'udan kud'ad'en?"
A man bedroom d'in ya barta ya fito parlo kasancewar bak'in da k'ararrawa ta sanar masa yayi, anan kan gadon tayi bacci sakamakon laushin katifar ga wani k'amshi da take fitarwa abin ba'a cewa komai,
Har akayi sallahar magriba bata tashi ba, shikuma Arif d'in baya gidan sun fita da bak'in da sukazo d'azu, saukar ruwan saman da taji ne ya sata farkawa sakamakon sanyi da yayiwa jikinta yawa, ta fara neman bargon rufa, idonta har yanzu da ragowar bacci ta d'ago ta kalli agogon dake manne a jikin banti, taga har k'arfe takwasa 8:pm alamun har anyi sallahr isha'i, da sauri ta mik'e tare da duba ina ne toilet d'in ina ne Kuma wasu k'ofofi da tagani a bedroom d'in, cikin sa'a k'ofar da ta bud'e itace toilet d'in ta tsaya tana k'arewa komai na toilet d'in kallo gashi komai sabo, a zuciyarta tace "duk wani namiji yana Gina gida domin yasa mace a ciki to nima ya Gina wannan domin ya sani a ciki ne kokuma da wata manufa?"
Nigeria
12:31am na dare, juyi Dad yake tayi a bed d'insa kasancewar yau baya tare da Ummu yana d'akinsa"
Wannan mutum yazo masa cikin mafarki yana cewa "an d'auki dukiyoyin jaririnmu an mallaka maka, an d'auki sirri. tsibirinmu an nuna maka sannan an wakilta jaririyarka da sunan siffarmu, wace makomace a gareku dukkanku da ahalinku gabaki d'aya?"...."
Yanzu wasan ya fara, amma zakuyimin afuwa book two zai kasance paid saboda wasu dalilai domin samun posting akan lokaci, Ina fatan bazaku nunamin rashin adalci akan hakan ba, zanyi Free pages guda biyar a book2 sannan muci gaba da paid group zaku sameshi akan 300 only dominku masoya domin neman Karin bayani 08141799224.

Mom Islam



*FALAK🍒*

Book2 sabuwar cakwakiya🥱

Mom Islam


E.O.W


Page 1-2

Dad ya tashi a firgice cikin azama ya tofar da miyau a gefensa na haggu, sam ya kasa ban bance abinda yayi mafarki bare ya samu damar bawa wani labari, yanata so ya tuna amma abin ya gagara, ya dinga mai-maita innalilahi wa inna ilaihir har bai San iya adadin da yayi ba,
Baccine a idonsa dole ya koma ya kwanta jiki a sanyaye.
Acan 6angaren Ummu baccinta takeyi harda mafarki mai dad'i , rabi mafarkin nata akan auta Falak tayishi, wai ta aihu twins yaran kyawawa ga surutu.
Washe gari Dad ya tashi jikinsa sam babu K'arfi, haka ya tafi masallaci bai dawo ba sai da gari yayi haske sannan ya dawo, kai tsaye ya wuce bedroom d'in Ummu, ya sameta a zaune a bakin gado tana d'aura agogonta mai kyau a hannunta, tana ganinsa ta sauka k'asa tare da cewa "ina kwana Habibyna"
"Lafiya Lau kin tashi lafiya?"
Ummu tace "sumul kai fa naga mood d'inka ya sauka ko lafiya?"
"No babu komai karki damu am fine"
Tunda yace mata babu komai yayi k'ok'arin kawar da damuwa daga ransa kafin yace "yau zanyi breakfast da wuri yunwa nakeji"
Ummu tayi dariya tare da rungume dad kana tace "baka da matsala su Hibba tun d'azu suka shiga kitchen"

Germany
Inda tana gara haka taga dare, saboda tsoron abinda yake tunkarota gashi ta kasa yarda da Sheik dama tun tuni bawai ta yarda dashi d'in bane, babban kuskuren da dad yayi damk'a masa company d'in da yayi a hannunsa yanzu bata da damar k'ar6a tunda k'arfinsu ba d'aya ba,
Gashi duk wani k'arfinta na taimakon kare kanta daga cutarwa ko ta dinga ganin Wanda zai cutar da Dad bata gani Sam, tarasa meke shirin faruwa da ita,
Har k'arfe 3:am na dare yayi idonta biyu tana zaune a parlo sai dai gyangyadi ya fizgeta lokaci zuwa lokaci,
Acan bedroom d'in nasa kuwa baccinsa yake shara kamar ba shi yayi maganar dazu ba, Kiran sallahr asbha da ake tayi daga masallatai da dama ne ya sashi farkawa sai Kuma ya tuna ashe yabar y'ar mutane a parlo, da sauri ya sakko daga kan bed d'in tare da nufar parlo, yana zuwa ya sameta sai bacci takeyi, sheik Abdul-Latif yayi murmishinsa mai kyau kafin yace "my heartbeat ina matuk'ar sonki"
A zabure ta farka saboda jin d'umin jikinsa da tayi, cikin k'araji tace "ka saukeni ko inyi maka ihu"
"Haba Falak nifa mijinki ne meyasa kike haka?"
Abin ya bata mamaki, muryar yanzu da muryar d'azu da banbanci, duba da yadda yanzu yake maganar cikin tausasa kalami sai kace ba shine ba,
"Zo muje muyi nafila kafin a Kira sallahr asbha"
Batace masa komai ba, yana d'auke da ita ya kaita toilet d'in d'akinsa kana yayi alwalah yace "yi sai muje muyi Sallah, sanin darajar sallahar ne yasata aminta da hakan badan sallah yace ba da wlhi ko bangon gidan batayi alk'awarin ta6abawa ba,
Bayan ya shimfid'a musu sallahya suka kabbara sallah, binsa kawai take har sai da sukayi raka'a bibiyu har takwas sannan yayi sallama itama tayi, kafin ya gyara zama ya d'auki alkur'ani itama ya mik'a mata, "meye nufinsa?"
Ta fad'a a cikin ranta,
Inkaji inda yake rangad'a kira'a sai abin ya baka nishad'i, muryarsa ginin daɗi.
Bayan sun kammala yayi adu'oi itadai ta d'aga hannayenta sama, tana bin adu'ion da yakeyi a zuciyarta, kafin suka shafa ya matso kusa da ita yace "barka da safiya bugun zuciyar Sheik Abdul-Latif"
Falak tayi kamar kurma,
Ya Kuma cewa "barka da safiya bugun zuciyar Sheik Abdul-Latif"
"Nifa ka isheni ka fito ka fad'amin asalinka da shirye-shiryen kashe Dad d'ina da kakeyi shi kawai nakeson ji wata k'ila in rufa maka asiri ta wani 6angaren"
Bai gane abinda take cewa ba saboda duk zancen da takeyi bai zan da zamanshi ba, cikin sanyin murya yace "me kike nufi kina nufin zan kashe Dad ne?"
"Eh da bakinka ka fad'a jiya ko k'arya nayi?"
Sheik Abdul-Latif ya k'ura mata kyawawan manyan idanuwansa kafin yace "wlhi Allah ni bamuyi wata magana dake ba haba, Falak ki tambayi kaf family d'inmu babu Wanda ya ta6a kisa bare yawo da makami"
"Hamm haka kace narantse da Allah wata biyu nayi ko minti uku bazan sake yi a gidannan ba"
Sheik Abdul-Latif yace "ai wata biyar akace na kuma rubuta na ajiye"
"Ina wata biyu zanyi inbar gidannan"
Bai ce mata komai ba ya mik'e kai tsaye kitchen ya nufa, ya d'auki flaks Wanda already Mommahan sa ta saka ruwan zafi a ciki, ya had'a musu tea a cup biyu ya jere a faranti, ya d'ora gwangwanin Madara da bonbita a ciki sannan yasa d'ora robar zuma, ya nufi bedroom d'insa dashi, tana kallo ta kawar da kanta, saboda zuciyarta ta rigada ta sharad'a mata yasa maganin mutuwa a ciki,
Yace "heart beat Bismillah"
"Nifa bance Ina son cin komai ba, na d'auki azumi"
A inda take maganar sai ya baka dariya saboda ita ba ma'abociyar son fad'a ko hayaniya bace, wannan dinma da takeyi na dole ne,
Batayi aune ba taji hannunsa sak'ale a cikin rigarta ko me yake nema oho,
Shiru tayi bata hanashi ba tanaso taga gudun ruwansa, har ta tafi duniyar tunani taji yafara murza mata kan nipples d'inta da hannuwansa biyu, Falak ta zaro ido cikin sisiriyar muryarta tace "wato iskanci zakayi kenan wlhi wannan abin bai kamaceka ba, d'azunnan mukayi sallahar asbha kafin sai da mukayi nafila mukayi karatun alkur'ani sannan yanzu Kuma kana neman hallaka kanka da kanka iskancin banza da wofi"
Sheik Abdul-Latif yayi murmishi kafin ya lashi pink lips d'insa yace "kefa matatace a jikinki babu abinda aka haramtamin sai saduwa ta baya"
"Mtew sai akace maka shi nake nema kokuma shi Dad ya turoni yi?"
"Idan ba shi kikazo yi ba ai babu maganar d'aurin aure a tsakani" sheik Abdul-Latif ya fad'a yana son sake tura hannunsa cikin rigarta, da sauri ta bige, ta mik'e tsaye, ganin yanayin dirin jikinta ya Kuma saukar masa da kasala doguwar rigar shaddar da sukayi anko tasa anyi mata stone work ga wasu flawoyi da aka sassaka gashi kamar ba wacce tayi aure ba tayi k'iba, a zuciyarsa yace "Masha Allah nayi dacen cikakkiyar mace"
Tana shirin fita ya rungumota ta baya yana manna joyst d'insa a mazaunanta, FALAK ta fincike jikinta da sauri jikinta na 6ari tayi d'akin da batasan ko na waye ba tayiwa k'ofar key har yanzu jikinta na rawa"
Tunowa da lokacin da ta farka kafin ya d'auketa ta tura wayarta aljihun rigarta, yasa ta danna number dad' Ring d'aya kamar me jira ya d'aga nan danan kud'in wayarta ya k'are, saboda yanayin kud'in da suke cirewa da yawa, kuka tasa a fili tace "wancan d'an iskan dazan yi masa magana da gudu zai siyamin katin Amma wlhi bazata kulashi ba, ta bud'e Whatsapp cikin sa'a dukkansu wand'anda take son yin magana dasu suna online, tayi hamdala tare dayin voice a lambar dad,
Tace "Dad wlhi kayiwa sheik Abdul-Latif magana"
Gaban Dad ya fad'i ya d'auka wani gagarumin abune ya faru, dad yace "Falak meke faruwa sanar Dani"
Cikin shagwa6a Falak tace "wlhi Dad iskanci yake yimin"
Dad ya danna emojis na alamar zare ido sai yayi mata typing yace "haba Falak Ina iliminki yaje da zaki dinga yin Abu kamar wacce bataje makaranta ba?"
Harga Allah bata fahimci abinda Dad dun yake cewa ba, ta Kuma cewa "Dad wlhi iskanci ba Abu bane Mai kyau kayi masa magana koni in koya masa hankali"
Tanaso ta gayawa Dad maganar da sheik Abdul-Latif ya gaya mata jiya tana tsoron inda Dad d'in zai d'auki maganar tasan Kuma komai yana iya faruwa dangane da ciwonsa ko wani sabon ciwon ya shigesa lokaci d'aya,
Dad ya lalla6ata tare da cewa "naji zanyi masa magana nidai fatana duk abinda ya saki kiyi dan Allah karki bani kunya kinji"
"To kawai tace"
A k'asan zuciyarta kuwa babu tabbacin zatayi hakan, tace to d'inne domin to bata karya wuya kar hankalin dad d'in ya tashi,
Sukayi sallama yace "karta kuskura ta sake gayawa wani wannan maganar koda Ummunta ne"
Kasancewar soyayyar da take yiwa Dad da tausayinsa yasa tayi masa alk'awarin babu Wanda zata sake gayawa komai zata dinga shanyewa, sai dai idan har taga ranta zata rasa,
Tunda Falak ta fita ya kwanta akan bed tare da fad'awa duniyar tunani, shin hakan zamansu zai cigaba tsakaninsa da Falak kokuwa zasu samu sauyi nan bada jimawa ba,
A fili yace "duk runtsi duk wuya zanyi k'ok'arin nusar da ita ya akeyin so da Kuma soyayyata,
Ya mik'e ya fad'a toilet, wankan tsarki yayi kafin yayi na soso da sabulu ya fito k'ugunsa d'aure da towel fari ya zauna a bakin gado, rabi tunaninsa na Falak d'inne wayarsa tayi ringing, duba mai Kiran nasa yayi yaga ansa Mommah ya runtse ido ya bud'e kafin yayi k'ok'arin saita muryarsa yace "aslamu alaikum Mommah"
Daga can 6angaren tace "zaka shigo yau ne?"
"Eh sheik Abdul-Latif yace tare da ce mata akwai matsala ne?"
"A'a ka bani matar taka mu gaisa"
Gaban sheik Abdul-Latif ya fad'i cikin inda-inda yace ba..ba..tanan.. tana toilet"
"Okay a gaishe ta"
Mommah ta nuna kamar bata fara fahimtar wani abu a game dasu ba.
Bayan Falak ta gaisa da Ummu ta yiwa Saudart ya jiki saboda tun ranar da zasu taho dad yace bata da lafiya yaga yanayinta, sun danyi hira ba sosai ba ta sauka ko su Munira bata yiwa magana ba, gashi Kuma alamun sunyi mata magana, ta gaji yasa bata basu amsa ba.
Switzerland
Yau kwananta d'aya a gidan amma duk a tsarge take, har yanzu bata gama yarda da komai na gidan ba, gashi Arif bai ce mata komai akan fitarta da tayi ba, abin ya dameta duk da dama bawai tanason taji yayi maganar bane,
Yaune Kuma zuwanta gidan momy, tunda Arif d'in

16 / 19