Author : Zainab Habib Category : African Stories & Novels
tare da yi masa jinjina, kafin yace "Abdurraman naji maganarka kaima Umar naji maganarka hukuncin da zan yanke shine abarwa Umar komai a hannunsa idan ma ginin za'ayi masa kusa da ita duk Babu lefi ai shi yace yana sonta"
Abdurraman ya rasa inda zesa kansa dama yasan hakan zata faru, tunda Umar da Sarki y'an uwan juna ne, Abdurraman ya bar gu cikin sanyin jiki, tare da alk'awarin ko meye yazo ze sami Falak bazai Bari a cutar da ita ba sai dai idan har sunfi k'arfinsa to dole ya hak'ura ya Mik'a musu komai,
Germany
Sheik Abdul-Latif yace "ina sonki so mai tsanani ina kishinki Falak yaushe zaki gane soyayyar da nake yi Miki?"
Yau yasha alwashin kar6ar hak'k'insa tunda ya bita ta laluma abun ya gagara,
Cikin rashin tsammani hannunsa ya sauka kan tudun breast d'inta, ya waro ido kamar me tsoron wani abu, jikinsa ya fara rawa yana wani irin sauke numfashi,
Mutuwar tsaye tayi saboda inda taji yana wani mammatsa Mata su sai kace ta sashi, a hankali ta shammaceshi ta buge hannun tana hararasa, lokaci d'aya ta mik'e zaune cikin wani irin K'arfi ta k'wace jikinta sakamakon ganinsa da takeyi tamkar dodo,
Ta matuk'ar firgita har da wani irin rawa kanta keyi a hankali ta rarrafa tabar d'akin, shikuwa yana zaune yafara surewa da lamarin Falak shin duk a cikin k'iyayyar da take yi masa ne yasa take hakan ko me?
A hankali yayi ajiyar zuciya tare da mik'ewa akan gadon yana ambaton innalilahi wa inna ilaihir wannan wace irin rayuwa ce tabbas ina cikin tashin hankali "ko in Kira Malama Nuriyya ne?"
Yanajin nauyin gaya Mata abinda ke faruwa dashi baki-da baki ya yanke shawarar yayi mata sako a whtsapp tunda suna yawan gaisawa,
Da farko yayi Mata sallama kafin ya sanar da ita duk abinda ke faruwa ya k'ara da cewa yanason tazo gidansa domin ta gyara masa zamansa da matarsa,
Bata online hakan yasa yabar sak'on yana hawa lokaci-lokaci ya duba ko tahau amma sai yaga har yanzu bata online d'in.
Acan bedroom Falak ta runtse idanuwanta, sakamakon ciwon da kanta keyi har wani bak'i-bak'i take gani, a hankali ta fara karanto adu'oin tsari ..
Wayarta tayi Ring, cikin azama ta janyo wayar taga Ummu, abin mamaki sai ta katse ta Kira, Ummu na d'agawa Falak ta fashe da kuka tana cewa "Ummu kaina Ummu kaina Ummu ki taimakeni Ummu na rasa inda zanyi"
Hankalin Ummu a tashe ta fashe da kuka ta katse kiran saboda ta kasa furtawa Falak ko kalma d'aya,
Falak ta fashe da kuka saboda tsananin ciwon kan da yake damunta yasa batajin motsin komai sai dummm kawai takeji.
Acan Nigeria Ummu tasa dad a gaba da kuka akan sai ya kaita taje taga halin da Falak take ciki, gashi dad yak'i Kiran Sheik bare yaji abinda ke faruwa,
Cikin kwantar da hankali dad ya cewa Ummu "karki damu munyi waya da Abdul-Latif Falak tana lafiya, Alhalin yayi ne kawai dan ya kwantar Mata da hankali, duk da haka bata yarda ba sai da yayi mata alk'awarin zai biya mata taje ta dubota.
Jikin Saudart yayi sauk'i sosai, koda ta dawo gida bata wani fuskantar damuwa a gurin Hamma, musamman ma daya gano ai wannan cikin ne ya sa take wannan abun,
Can 6angaren iyayensa kuwa an tsayarda maganar aure wata uku, shikam a halin yanzu ce musu yayi ace ya janye bayaso, iyayen nasa sukace ai k'arya yakeyi baze mayar dasu k'ananun mutane ba, dan haka biki na nan daram, Hamma Aliyu ya matuk'ar tsorata saboda Saudart ya kasa sanar da ita komai akan maganar auran gashi doctor sun ce karya kuskura ya dinga sanar da ita abubuwan da zasu sata fad'uwar gaba ko 6acin rai zuciyarta zata iya bugawa cikin k'an-k'anin lokaci.
Ranar da Hamma Aliyu ya dawo daga gurin aiki, ya sami Saudart tayi kwalliya kamar budurwa, gabansa yayi mummunan fad'uwa sakamakon sabon auran daya tuna Wanda tsakaninsa da Allah inhar yayi bazai iya adlaci ba tunda dama yafi son Saudart dalilinsa na neman aure kuwa ranar ya tashi da matsananciyar sha'awa, yaje ga Saudart ta kwararo masa amai dalilin da yasa zuciyarsa ta tunzura kenan...
Littafin kud'i ne 08141799224
Ga tsarin biyan kud'in Account number 3175689751 Zainab Habibu first Bank
Shedar biya ta wannan number 08141799224
Katin mtn da Vtu ta wannan number 08163626370
Shedar biya ta wannan number 08141799224
Y'an Niger zaku tura da katin Airtel ta wannan number 08141799224
Mom Islam