Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

FALAK Book Auren Sirri 1 & 2 By Zainab Habib

Author :  Zainab Habib Category :  African Stories & Novels

Chapter   10 / 19

27K to 30K   out of 54.7K words

gagareni musamman ma da dad baya nan ni zan kula masa da komai, ko ka mance abaya abinda na gaya maka?, bani da time d'in soyayya, domin.."
Shaikh Abdul-Latif ya d'aga mata hannu, ta mik'e tsaye cikin zafin rai kana tace "kai waye da zaka shigo min office kana min fighting ficemin bana son k'ara ganinka"
Shaikh Abdul-Latif ya fice yana gyara zaman gilashin dake fuskarsa.
Kunsan tun da muka fara labari shimfid'a muketayi, har yanzu bamu shigo cikin labarin ba, ma'ana yanzu zamu shiga can ciki..
Wacece Falak?
Meya jawo arzikin dad?
Me sheikh Abdul-Latif yake tak'ama dashi?..
Menene asalin beauty..
Asalin labarin FALAK
GARIN GOMBE
Wuro shi 'i'
Anguwace mai yalwar mutane, iri-iri, can na hango wani gida mai get da alamun masu gidan suna tashen arzik'i, gidan Alhji Nasir gidane Mai d'auke da mata d'aya tanada yara biyu Abubakar da Usman, lokacin Abubakar yanada shekaru 10yrs a duniya shikuma Usman yanada shekaru 7yrs sun taso cikin kulawa da tarbiya ingantacciya, kullum suna hanyar zuwa makarantar boko da Islamiya, sana'ar Alhji Nasir itace siyarda goro, yana ajiyesu a kasuwa, yanada manyan shaguna acan, sosai ake d'aukar goron zuwa gari-gari a manyan motoci, tashi d'aya Alhii Nasir ya zamo hamshakin Mai nera,
Asiya itace mahaifiyarsu Abubakar da Usman, suna kiranta da Ummi shikuma Alhji Nasir suna kiransa da Abba, asalin bafulatana ce haifaffiyar Gombe, fara ce sol tanada gashi har gadon baya, irin fulaninnan ne mazauna cikin gari.
Shekarar Alhj Nasir saba'in da uku yabar duniya, kasancewar ciwon k'afa data uzzura masa, lokacin da Ummi ta gama takaba manema suka dinga fito mata Sam tace bazata sake aure ba, taci gaba da kula da y'ay'anta, shekarar Abubakar 30yrs lokacin ya jima da kammala karatunsa, kasancewar aikin Dss ya karanta, cikin hukuncin ubangiji komai yake tafiya dai-dai, shikuma Usman ya cigaba da kula da sana'ar mahaifinsu siyarda goro,
Dukkansu biyun Allah ya d'aukakasu fiye da tunanin Mai karatu, kwatsan Abubakar ya biyawa mahaifiyarsu Makkah, tayi murna sosai, bayan dawowarta ta samu yafara gininsa anan kusa da gidansu Babu nisa, shima Usman yana gini kusa da gidansu.
Wata ranar Juma'a bayan anyi sallah ya fito daga masallaci, wani tsoho yazo bara gurinsa, Abubakar ya k'irgo dubu goma ya mik'a masa, tsohon ya zube a k'asa yana kuka yace "Allah yayi maka albarka insha Allah a cikin albarka zaka tashi har k'arshen rayuwarka"
Abubakar yace "nagode baba"
Tsohon yace "Ni nan daka ganni ba mutum bane amma na fito a cikin bil'adama domin taimakawa irinku"
Abubakar ya kalli tsohon kallon tsanaki yaga bashi da k'afa, a tsorace yace "to nagode baba ni zan wuce"
Tsohon yace "karka tsorata akwai abinda nakeson gaya maka, inason ka nitsu kajini karka kuskurewa duk wani abu"
Abubakar yace "to"
Tsohon yace "kanada sa'a a rayuwarka, abinda nakeso dakai shine, ka kar6i wannan dutsen dazan baka, ka bar k'asar nan dashi, kaje can wajen k'asarnan ka nemi shagon da babu kowa a cikinsa ka ajiye dutsen da Bismillah bayan ka ajiye sai ka kalli gabas kace alhmdulilh"
Abubakar yace "inada kud'i amma bazan..."
Tsohon yace "karka damu arzik'in da zaka samu sai yafi Wanda nake yi maka magana akai"
"Bazan sake dawowa gareka ba har sai kabar k'asarnan ka koma inda nace makaKanada damar aura za6ar duk k'asar da tayi maka nikuma zan dinga zuwa kawo maka ziyara dani za'ayi komai"
Abubakar yace "to" jikinsa a sanyaye
Zuwa dare, Ummi taga ya shiga damuwa fara'arsa da walwalarsa duk sun ragu, ta kirashi ta zaunar dashi, cikin tausasa murya ummin tace "Babana" kasancewar sunan babanta aka sanya masa,
Ya amsa da "na'am"
Tace "tun d'azu na ganka a cikin damuwa shin akwai abinda yake damunka wanda bazaka iya gayamin ba, Ko d'an uwanka?"
Abubakar yace "Ummi na had'u da wani tsoho a masallaci nan d'azu" ya gaya mata duk abinda yace ta jinjina kai tare da cewa "me sunan baba, zan siyarda gonata ta gado domin kaje k'asar da kakeso na yarje maka zanci gaba dayi maka adu'a Ina rok'on ubangiji ya ji6anci lamuranka"
Ummi ta fad'a cikin k'arfafa masa guwaiwa tanajin a tafiyar tasa akwai alfanu,
"Ummi aikinmu fa ya zanyi dashi?"
Ummin tace "karka damu zanyi maka adu'a Allah yasa musu fahimtarka a ransu"
Anan ne hankalinsa yad'an kwanta, Usman ma daya shigo aka bashi labari, shima yace akwai kud'i da zai k'ara masa.
Bayan kwana biyu.
Ranar ta kasance Monday ranar aiki, Abubakar yaje da jakinsa a ninke yaje babban ofishinsu bayan sun gaisa a nitse yace "nazo akan maganar ajiye aiki ne"
Babbansu ya kalleshi yayi murmishi kafin yace "Abubakar kenan haka ake ajiye aikin?"
Abubakar ya sunkuyar da kansa k'asa cikin jin kunya yace "ayi hak'uri shugaba"
Yace "zauna mana"
Abubakar ya zauna yana jiran hukuncin dazai biyo baya.
Shugaban nasa yace "Abubakar rashinka zai iya janyo wa aikinmu matsaloli, bance idan babu kai aiki bazai yiwu ba, zanyi magana a duba maganarka"
Da wannan zancen Abubakar yayi masa sallama dan yau jikinsa a ma ce yake yakasa sukuni,
Washe gari yana zaune a main parlon Ummi, wayarsa tayi ringing, da sauri ya ciro a aljihu tare da karawa a kunne yace "Allah ya taimaka"
Shugaban nasa yace "munyi zama yau da daddare akan barinka aiki, hak'ik'a mun fahimci juna, akan maganar da kayimin kace kanason yin kasuwanci, mezai hana ka dinga kasuwancinka Kuma kana yi mana searching masu lefuka? kobaka zo koda wane lokaci ba, ya kamata kadinga lek'omu"
Abubakar yayi matuk'ar murna da k'aunar da suka nuna masa.
Sati d'aya da faruwar hakan ya fara shirye-shiryen barin k'asa ba tare daya banbance k'asar da zashi ba.
Ana i' jibi zai tafi, Ummi ta kwanta rashinafiyar 6ari d'aya, wannan rashin lafiyar ya tada hankulan gabaki d'aya family d'insu Ummi, magani har angaji dayi, dole Abubakar ya hak'ura da tafiyarsa, wata ranar talata, sun gama d'awainiya da Ummi shida Usman kasancewar y'an uwa sunyi iya bakin kokarinsu sun gaji, sai masu zuwa jefi-jefi.
Ya zabga tagumi tsohonnan ya diro gurin yace "mahaifiyarka tana kwance babu lafiya, nayi iya bakin k'okarina domin ganin na roki Allah ya biya mana bukatunmu, ciwon ya ta6a jinin jikinta sai dai muyi fatan warkewarta"
Abubakar yace "to baba nagode"
Yana shiga gida ya samu Ummi a kwance tana juyi, da sauri ya k'arasa gurinta yana cewa "ummi..Ummi.."
Ta juyo a hankali tace "Ina Usman?"
Cikin ikon Allah sai gashi ya shigo,
Suka durk'usa a gabanta, Ummi tace "hak'ik'a nagodewa Allah daya bani ikon yi muku tarbiya ingantacciya, ba fahariya nake yiba ko zuwa gaba bazaku ta6e ba, wannan mutumin daya yi maka hanyar wannan dutsen kayi masa biyayya, inaji a jikina masoyinka ne"
Usman yace "Ummi me kike fad'a haka"
Iko sai Allah, Ummi ta fara kalimatusha hada cikin nutsuwa rai yayi halinsa fuskarta na d'auke da murmishi,
Usman ganin abin yake kamar almara sai cewa yake "meye haka Ummi, ba'a Wasa da mutuwa meye haka kikeyi?"
Sai Allah ya sakowa Usman dauriya yace "haba Yaya Abbakar meyasa kaima kake haka?"
Kulinafsin za'ikatul maut, Allah hu Akbar, duk Mai rai makaci ne, shiyasa kayi k'ok'arin aikata alkairi kafin mutuwa ta riskeka kace inda babu halin shawara da wani.
Dangi ta ko Ina sun hallara a gidan, abin mamaki sai ga tsohon nan yazo gaisuwar rasuwa ya dinga adu'oi,
Tun daga nan duniya ta fara yiw..

Ban dawo gida ba har yanzu Ayimin uzuri nakusa komawa.


Banyi editing ba

*Mom Islam*
*FALAK🍒*


Mom Islam

E.O.W


37-38
Rayuwa kenan, yau watan Ummu biyu da rasuwa, abubuwa sun sauya, Usman harkarsa ta bunk'asa sai samun d'aukaka yakeyi ta fannin siyarda goro, Abubakar mutuwar Ummu ta ta6ashi sometimes har sumbatu yakeyi, sai da wannan mutumin ya dinga taimakawa da adu'oi sannan abubuwan suka fara warware wa.
Cikin hukuncin ubangiji ya cigaba da zuwa office suna gudanar da aiki, a d'aukan albashinsa na biyu ne ya samu kud'in zuwa Germany, bayan yayi musu bayanin sana'ar da yakeson farawa, babban ogansu ya taimaka masa da kud'ad'e masu yawan gaske, kasancewar ya shigo da k'afar dama duk suna sonsa.
Ana saura kwana goma tafiyarsa ya gama komai na hada hadar shiga jirgi ya zamana jiran lokacin kawai yakeyi, sai da yaje dangin Ummu yayi musu bankwana tare da fatan su tayashi da adu'a, kafin ya dawo gida.
Ana gobe zai tafi, sun dad'e suna hira da Usman kamar bazasu rabu ba,
Washe gari ya fitowa zuwa airport shida Usman da wannan tsohon a siffar mutane, koda suka isa airport d'in tsohon yace "idan ka ajiye duwatsun zasu zamo guda goma, inkana siyarwa gurin zai ha66aka sosai, bayan nan kuma da kaina zan cigaba da aiwatar da komai har zuwa lokacin da komai zai bunk'asa"
Abubakar ya dafa kafad'ar Usman yana kuka yace "d'an uwana umarnin Ummu zanbi kawai ka yafemin"
Usman yace "baka yimin komai ba wlhi Allah ya yafe mana"
Daganan jirginsu ya d'aga sai Germany,
A hankali-a hankali ya fara cigiyar shago, cikin sa'a ya samu abin mamaki, yana biyan kud'i ya ajiye wannan dutsen sai gashi ya yawaita ciniki kamar me kowa burinsa yaje shagon yayi siyayya.
Haka rayuwa taci gaba da juyi arzikinsa sai dad'a yad'uwa yakeyi, wata ranar asabar yashiga gari lokacin yakai wata biyar da zuwa, yana cikin tafiya wannan mutumin ya tareshi a hanya yace "Abubakar akwai sa'a a tattare dakai inaso inhar kakai shekara d'aya kabar garinan kaje ziyara k'asarka domin duba y'an uwanka"
Tun abin yana bawa Abubakar tsoro yanzu har ya dena ya rungumi abubuwan da yake zuwa masa dasu,
Lokacin daya cika shekara d'aya ya fara shirin zuwa Gombe, cikin ikon Allah ya isa garin kasancewar ya gayawa abokansa da Usman harda babban ogansu sukazo airport tarbarsa, daga nan suka wuce gida, y'an uwa sunata murnar dawowar Abubakar wasu suna bak'incikin ganinsa da shiga ta alfarma, kowa sai daya bisu da atamfa wasu abayoyi kowa dai da nasa.
Washe gari akayi kiransa a office, sosai ya fuskanci 6acin rai musamman akan watsar dasu da yayi babu kira babu bayani, ya durk'usa ya dinga basu hakuri sbda soyayyar da suka nuna masa,
Kwanansa Uku ya fara tunanin shagonsa daya Bari, tabbas rufeshi babbar matsala ne a gareshi, kwana hud'u da zuwansa ya shirya fita yawo domin ganin gari da ziyarar kakanninsa na gurin uba, yana shikin tafiya wasu y'an mata su biyu suka zo wucewa, da sauri ya bud'e murfin motar ya fito tare da binsu da sauri kafin yace "aslamu alaikum dan Allah ku tsaya" suka juyo dukkansu, a hankali yakai gurin farar wacce take kamar balarabiya ya kalli d'ayar yace "inba damuwa inason inyi magana da k'awarki"
Wacce yakeson magana da ita tace "Babu damuwa kayi sister nace...

Wlhi anyi mana rasuwa ne kuyi hakuri ga tafiya da nayi, insha Allah ina koma gida kamar da read more uku sau biyu a Rana zancigaba sbda muyi saurin gamawa, ku Kara hakuri.

08141799224

Mom Islam
*FALAK🍒*


Mom Islam

39-40

Daga nan ya gabatar mata da koshi waye, cikin ikon Allah ta amince har magana tayi K'arfi a 6angarori biyu, dangin mahaifiyarta da dangin mahaifinta, akan hakan yasa sai daya kai wata d'aya a Nigeria bai koma Germany ba, kasancewar bincike da sukayi suka tabbatar da asalinsa abinka da manya aka yanke dukiyar aure harda sa rana, washe gari jirginsa ya d'aga sai Germany, kafin ya tafi sai daya gina soyayyarsa a zuciyar budurwar tasa mai suna Aisha sannan ya tafi.

Koda yaje jikinsa bai mutu ba.
Yaci gaba da siyarda kayansa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, kusan kullum sai ya kira Aisha sun gaisa,
A hankali- a hankali lokaci ya fara matsowa yana aikawa matar Usman da kud'i ta dinga yi masa soyayyar kayan aure, kasancewar ya jima dayin aure,
Lokacin da wata ya cika shago ya bunk'asa ciniki har wani lokacin sai wajen 12:am Abubakar yake tashi, ranar da bikin ya rage saura two weeks ya dawo gida Nigeria, ansha biki anyi bajinta akwatuna goma Sha biyu ko wanne cike yake da tsadaddun kaya, daga nan aka wuce da amarya gidanta da already yariga da ya siyeshi a gine, gidane tsantsarere mai kyan gaske, kowa ya yaba kyan gidan duk da itama Aishar y'ar masu hali ce amma abin yaso tsorata wasu daga cikin y'an uwanta.
Abubakar sai daya shafe sati uku yanacin amarci ba tare da yayi tunanin halin da shagonsa zai kasance ba, a sati na ukunne ya koma Germany yaci gaba da gudanar da aiyukansa,
Wata ranar Juma'a ya dawo daga masallaci yana shirin komawa gidansa dake nan garin, wannan tsohon yayi masa sallama yana shirin yi masa magana Abubakar yace "baba dan girman Allah kazo mu tafi gidana akwai maganar da nakeso muyi"
Tsohon yace "kayi hak'uri d'ana yin magana a gida ba nawa bane sbda bana iya fad'ar abin k'aruwa a cikin gida"
Abubakar ya fito da tabarma a motarsa suka zauna tsohon yace "hak'ik'a auren da kayi akwai nasara a ciki, babban albishir d'in da zanyi maka shine matarka tanada ciki zata haifo maka y'ay'a har uku ta hud'un ce zata zamo maka tauraruwa mai haska ko ina naka, daga nan kuma aikinka zai koma hannunta saboda tafika jarimtaka fiye da tunani, Allah zeyi mata baiwa Sosai.
Abubakar yayi hamdala tare da fashewa da kuka yace "hak'ik'a Allah ya turoka domin ka zamemin haske a rayuwata tabbas ka zamemin uba Allah gatana kaima gatana ne".
Abubakar yace "duk maganar da nakesonyi anrigada anyi nagode sosai Allah yasaka da alkairi, daganan suka rabu ya koma gida tare da kiran Aisha, kafin yace komai tace "Hubby Albishirinka?"
Abubakar yace "Ina jinki nima akwai abinda nakeson gaya miki"
Aisha tace "inada ciki amma banje hospital ba"
Da sauri yace "meyasa, ya akayi kika gane?"
Tayi dariya tare da katse Kiran.
Shima farinciki yakeyi sosai kamar ya ganta a kusa dashi,
Haka rayuwa taci gaba da tafiya har cikin Aisha ya isa aihuwa ta haifi y'arta mai suna Saudart, Saudart nada shekara uku ta haifi Hibba hibba nada shekara biyu ta haifi Munira, sai da tayi shekara biyar bata sake aihuwa ba kafin ta samu cikin Falak, cikin Falak yazo mata da masifaffen laulayi wanda har ta fara cire rai da rayuwa, lokacin da cikin ya isa wata Tara da kwana goma ta haifi Falak a gida ana shirin zuwa asibiti sai ga aihuwa cikin sauk'i.

Koda Falak take k'arama ta taso da basira da tausayi har tafi yayunta magana kuwa kome aka gaya mata rik'ewa takeyi, tana cika shekara 3aka sanyata a school driver yana zuwa yana d'aukota, lokacin Saudart ta kammala secondary, Hibba ma takusa ganawa Munira kuma tana jss3, Masha Allah family sun had'u da uwa tagari, dukkansu sun taso da tausayin iyayen nasu biyu.

Lokacin k'awar Aisha tanada yara biyu Khausar da Khairat.

Dangim Aisha dasu Hibba suke kiranta da Ummu suna yawan kawo musu ziyara sa6anin na mahaifinsu da suka watsar dasu, sbda cewa sukeyi ya tare a gindinta bata Bari ya yiwa danginsa komai, daga ita sai y'ay'anta.

Beauty y'ace ga Habiba mahaifinta sunansa Hashim, ada yayi tashen nera, da Habiba da momy wato mahaifiyar Arif ubansu d'aya, a danginsu maman Habiba ita kadaice ta musulunta akan soyayyar mijinta daganan danginta sukace zasu kasheta lokacin tanada cikin habiba cikin ya sami kulawa abin takaici shekararsu d'aya batasan danginsa ba, da tayi masa magana zece duk sun mutu har ya zamo ta hak'ura, mahaifiyarta tana gidansu momyn Arif lokacin da cikinta yakai wata Tara mahaifiyarta ta dawo da ita gida a 6oye, lokacin da cikin ya isa aihuwa ta haifo y'arta mace kyakkyawa aka sanya mata suna habiba, daganan ta fara rainonta a gidansu momy, danginta najin halin da take ciki suka kasheta Wanda Babu Wanda zece ga Wanda ya kashe d'in.
Habiba ta rayu a hannun mahaifiyar momy Ummi sun tashi a tare da Momy, lokacin da ta isa aure aka aurar da ita, ashe dangin mahaifiyar habiban ne suketa bibiyarsu sune suka turo mijin habiban, ta aureshi, shikuma babansu momyn bai San da hakan ba, yayi iya bincikensa baiga aibunsu ba ashe sunyi lumbu lumbu ne,

Har yana yi mata ciki lokacin wata biyu, suka kasheta suma din a 6oye sai daga baya aka gano dangin mahaifiyarta ne suke bibiyarta tun akan musuluntar da tayi.
Lokacin momy ta haifi Arif, yayi girma dataji labarin tazo har Egypt ta d'auki Beauty da aka Haifa taci gaba da shayar da ita, kasancewar lokacin Maleek baya bijire mata kamar haka.

Wannan kenan back to story....

Shaikh Abdul-Latif ya rausayar da kansa tare dayin wani shu'umin murmishi yace "kenan dad yanada matsala?"
"Eh yanada ita sosai ma, zuciyarsa zata iya bugawa inhar yaji labarin durk'usar da company, nasan masu shirya abinnan Amma yanzu komai nawa bayayi"
Shaikh Abdul-Latif yace "inhar zaki aureni wlhi zan shige miki gaba akan komai"
A fusace tace "wace baiwa ce dakai da zaka iyar musu ko ka d'auka abin na wasa ne?"

Sheikh Abdul-Latif yace "kibar komai a hannuna inhar an d'aura aurena dake wlhi babu Wanda ya isa ya tunkaro wannan company d'in inhar ba nine nasa ba"
Da sauri ta sake kallonsa kyawawan idanunta suna zubar da k'walla tace "meyasa kakeson aurena kasan koni wacece?"
"Sanin hakan ne yasa nakeson auranki domin mun dace da juna"
Falak ta buga table tace "please ka ficemin zanyi shawara"
Sheikh Abdul-Latif yace "in dawo gobe?"
A hassale tace "eh"
Sai daya fita ta fara tunanin meyasa ma tace ya dawo gobe, bata tsaya had'a komai ba ta fito, mutane nayi mata sannu babu Wanda ta kula abin ya matuk'ar dugulgula mata zuciya ta shiga mota driver nata Shan maaifa abinda ya kasance ba halinta ba...

Masu so daga farko kuyimin magana 08141799224
*FALAK🍒*


Mom Islam


E.O.W

Page 41-42

Tana isowa gida ta wurgar da handbag d'inta a kan two sitter kana ta shige bedroom kana ta fad'a kan gado ta fashe da kuka, ya zatayi ta kasa taimakon dad akan bom d'in da ake shirin tayarwa a company d'insa, da sauri ta fesar da iska mai zafi daga bakinta tana ambaton "innalilahi wa inna ilaihir, me sheikh Abdul-Latif yake nufi dani, yana nufin in aureshi ya zamo me tozartani kokuma ya hallaka dad? no bazan iya ba koda hakan zata faru, sai dai muyi yarjejeniya da dad akan ya yarda in aureshi bayan aure da 5 month sai insa ya sakeni kafin nan nasan na fice masa arai tunda nid'in ba soyayya na iya ba "
Tana cikin magana massage ya shigo wayarta, da sauri ta fito parlo ta d'auki wayar ta koma bedroom d'in ta zauna, tana dubawa taga bak'uwar numberta anrubuta,
Amincin Allah ya tabbata ga zuciyar dake k'aunar cigaban mahaifinta, hak'ik'a banso sanardake zancen dazai d'aga miki hankali ba, a gurguje dai yau saura kwana d'aya bom ya tashi a ma'aikatar mahaifinki shin kin amince da aurena ko in fita daga harkar ki!!?"
Da sauri ta kira number kasancewar ta rud'e, sheik Abdul-Latif na d'agawa kafin yayi magana tace "na amince da

10 / 19