Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

FALAK Book Auren Sirri 1 & 2 By Zainab Habib

Author :  Zainab Habib Category :  African Stories & Novels

Chapter   17 / 19

48K to 51K   out of 54.7K words

ya d'auko meyin makeup gabanta keta fad'uwa ta rasa dalili,
A drowarta ko wanne Kaya sabone babu tsoho a cikinsa haka takalma da jaka sunada yawa ga hijabs suma masu yawa y'an yayi, duk wani kaya na ado ya siya ya zuba ba tare da tasan lokacin ba.
Bayan an gama mata makeup din, da kanshi yaje ya d'auko mata wata doguwar riga wace Tasha ado harta gaji tsabar kyau, ya kawo aka sanya mata, wow kuzo kuga beauty tayi kyau sosai sai ta koma kamar budurwa"
Arif ya dinga d'aukarta a photo yana murmishi, transfer yayiwa mai kwalliyar tayi masa godiya ta wuce.
Da kansa ya d'auko mata takalmi da jaka da hijab harda niqab, abin dai sai ya baka mamaki wai Arif ne yake tattalin beauty Anya lafiya?,
Hannunsa cikin nata suka shiga had'ad'd'iyar motarsa, bai buk'aci driver ba da kansa ya shiga itama ta shiga aka bud'e musu get ya fice a guje...."
Babu editing ayi hakuri
Hhh ana wata ga wata shin wannan lalla6awar da Arif yakeyi na lafiya ne kuwa?
Ga sheik ya zuba iskanci jiya harda wasu maganganu me kuke ganin zai faru??
Shin kunada amsar mafarkin da dad yayi??
Ina labarin Maleek, wane tuggu momy take shiryawa???
Amsarku na cikin book2 wato sabuwar cakwakiya.
Nayi book 1 free saboda soyayyar da kuke nunamin, yanzu 2 zai kasance na kud'i, akan farashin 300 Nima a nunamin so Nagode.
Page 3-4

Daga gobe nefa💃💃🔥
Arif yayi horn a k'ofar gidansu nada da, wanda a yanzu ya zamo mallakin momy, mai gadi ya bud'e masa, yana d'aga musu hannu, kai kawai Arif ya gyad'a masa kana kutsa kan motar ciki,
Tunda suka shiga gidan gaban beauty yake dukan uku-uku, a hankali ta dafe k'irjinta tare da runtse idanunta,
"Babyna fito"
Taji muryar Arif kamar daga sama, a zuciyarta tace "babyn wa Allah ya tsine"
Gidan yayi kyau sosai musamman ma da aka sanya flowers sun haska gidan sosai, bayan yayi parking ya rik'e mata hannu suka fito, kai tsaye suka wuce inda momyn take, da shigarsu parlon beauty taga Cake babba wanda aka zagayeshi da sunanta wato Islam happy birthday Islam, neman bak'incikin da take ciki tayi ta rasa sakamakon farincikin zagayowar ranar aihuwarta.
Momy ta shigo tana sanye da abaya Brown anyi Mata ado da milk color na zare, ga stone da aka mammana sosai momyn tayi kyau gashi ta sake haske, tana ganin beauty ta washe baki tare da cewa "daughter kun iso kenan?"
Beauty ta zame har k'asa ta gaishe da momy, momyn ta dafa kafad'arta tare da nuna mata gurin drinks da kayan ciye-ciye da aka jera akan had'ad'd'en table d'in,
Arif yace "momy ni ko murnar zuwana bakyayi"
Momy tayi murmishi kafin tace "to Naga y'ata na rud'e"
Arif yayi murmishi suka saka momy a tsakiya aka kunna wak'a suka cashe da rawa beauty tana ta dariya, daga nan aka yanka cake tare da shafa mata a fuska duk Arif ya 6ata mata fuska da cake.
Wunin farinciki sukayi a ranar har beauty taji bata son taga tabar gidan momy, saboda sai riritata takeyi kamar k'wai, suna zaune kowanne nacin cake Maleek ya shigo yana sanye da kaya irinna Salman Khan wuyansa rataye da abin da kayan ya taho dasu,shima yayi kyau abin ba'a magana, sometimes abin yana bawa beauty mamaki, tambayarta shine "yaushe sukayi kud'i a tsakanin sati biyu" rayuwar gidan ta sauya sosai, ko wanne burinsa yaga yana faranta wa beauty.
Maleek ya washe baki kana yace "y'ata ashe kinzo Masha Allah ya jikin naki?"
Beauty ta sunkuyar da kanta kafin tace "alhmdulilh dady ya kuke?"
Shima yace "lafiya"
Ya zauna sukasha hira, har wajen k'arfe 8:30 suna gidan momy, Arif da Maleek kuwa tunda suka tafi masallaci sai da akayi isha'i sannan suka dawo, hakama beauty da momy sallahr sukayi sannan suka dawo parlo suka zauna akaci gaba da hira, shigowar Arif da Maleek ne yasa suka amsa sallamarsu momy tace "Arif meyasa bazaka dinga siyo mata fruits ba kasan mai ciki anaso ta dinga ci"
Arif yace "momy insha Allah yanzu muna fita zan siya mata"
Maleek yace "kuyi himmar tafiya gida"
Beauty tace "uhm momy ni anan zan kwana"
Arif yace "ina jiranki a waje" ba tare da yayi musu sallama ba ya fice,
Maleek yace "jeki sai da safe mijinki na jiranki"
Beauty ta mik'e tana tura baki ta wuce inda Arif d'in yake,
Tana zuwa ta d'an harareshi sai kuma ta bud'e murfin motar ta shiga gaban,
Arif ya kamo lallausan hannunta kafin yace "my babyna kullum sake kyau kike"
"Uhm yaushe ka gama bani wahala"
Beauty tayi zancen zuciya Wanda ya fito fili,
Batasan zancen zuci ya fito fili ba ta rufe bakinta gabanta na fad'uwa.
Ami makon taji ya rufeta da faÉ—a sai taji yace "insha Allah bazan sake 6ata miki rai ba, nayi alk'awari, inason kema ki zamo meyin biyayya a gareni"
Beauty ta share hawayen daya kwaranyo mata kafin tace "ashe wannan ranar zatazo, ranar da zanyi farinciki ranar da zan fad'a a ko Ina na samu y'ancin kaina, Ina alfahari dakai"
Wani dad'i ya ziyarci zuciyar Arif har wani shauk'i yakeji, cikin farinciki suka k'arasa gida, suna shiga bayan an bud'e get suka bud'e k'ofar babban parlonsu, beauty tayi d'akinta shima yayi d'akinsa, kwanciya tayi sakamakon gajiyar data addabeta ko Ina na jikinta ciwo yake, ga tashin zuciya.
Bacci ya fara d'aukarta Arif ya shigo yana sanye da sleeping dress na riga Mai dogon hannu da wando marasa nauyi, a hankali ya k'arasa inda take ya kwanta a bayanta tare da rungumeta tsam a jikinsa, gaban beauty ya bada rass sakamakon fargabar sex da takeyi dashi, sam batajin dad'i ko kad'an amma dole zata d'aure karya fahimci hakan.
Idanunta a runtse ya shafo mazaunanta ta baya yana d'aga rigarta yana kiran sunanta a hankali, "babyna.. babyna.."
Cikin siririyar murya ta amsa da "na'am"
"Me kikeso in ta6a miki?"
Cikin sauri beauty tace "babu komai"
Arif ya rad'a mata "k'arya kike"
A hankali cikin hikima ya rabata da kayan jikinta kaf ya kalli cikinta da yad'an fara tasowa, ya shafashi kafin ya had'e bakinsu guri d'aya yana tsotsar harshenta, a hankali ta wani gantsare, ya d'auka dad'i takeji har wani cafko mata kan nipples yana murjawa, ita ko wuya takesha saboda gajiyar da tayi gashi cikinta har wani ciwo yakeyi,
A hankali ya cire bakinta a nashi yakai bakin kan nipple d'in yana tsotsa cikin hikima yana mulmula d'aya,
Abinda bai saba yi ba kenan, Wasa da ita kafin sxx hakan yasa tayi laushi ma'ana tai saurin gajiya dama a gajiye take,
Shigar joyst d'insa da taji a hq d'inta yasata farka tare da zaro ido waje sai Kuma tayi shiru, Arif cewa yake "shafamin bayana tsakiya"
Beauty ta fara shafa masa, ai kamar zai tsaga jikinta ya shige dan dad'i har wani zillo yakeyi ita Kuma har yanzu bata dena ba, sai da ya samu nutsuwa sannan ya k'yaleta, ta mik'e cikin sauri ta tsarkake jikinta kafin tayi alwalah ta fito ta kwanta, shima mik'ewar yayi ya tsarkake jikinsa kana ya fito yasa kaya, itama kayan tasa ta kwanta bayan tayi adu'ar kwanciya baarci.

EGYPT
asubar fari Fadwa ta dinga kwara amai kamar zata amayo da hanjin cikinta, lokacin Abdul-Naseer yaje masallaci, granny ta fito da gudu har tana sulewa, kasancewar dai bataji ciwo ba taci gaba da tafiya harta iso d'akin Fadwa ta bud'e toilet ta shiga, sannu ta dinga jera mata kafin ta mik'a mata ruwa tace ta d'auraye baki,
Godiya Fadwa tayi mata kana ta ra6a ta gefen granny ta fito ta zauna a kan gado tare da fashewaa da kuka,
"Wai akan wannan aman da kikeyi ne zaki fashe da kuka? in tak'aice miki zance ciki kika Sami ina gaya miki, gashi da alamu cikin zai wahalar dake"
Fadwa dai murmishi tayi saboda bata yarda cikinnne da ita ba.
Sai da granny ta tsaftace toilet d'in sannan ta fito tana jerawa Fadwa sannu,
"Yauwa" tace a wahalce dan bakinta mugun d'aci yakeyi mata,
Abdul-Naseer na dawowa daga masallaci ta tareshi a parlo tace "Albishirinka matarka ciki ne da ita yanzunan na gama kwashe amai"
Abdul-Naseer ya ciro kud'i a aljuhunsa ya mik'a mata tare da tafiya bedroom d'in Fadwa, a zaune ya sameta ta jingina kanta da jikin gadon, tace "cikina yana ciwo please zuwa anjima ka kaini hospital"
"To" Abdul-Naseer yace mata jikinsa na rawa,
Acan gurin granny kuwa murna har ba'a magana, burinta shine gari yayi haske suje hospital aji ko wata nawa ne cikin,
Da wuri granny tayi breakfast ta had'a komai gari nayin haske ta ajiye musu a dining ta ajiye nata akan kafet, kafin suzo harta cinye jollof d'in taliyar da ta zuba ta Kora da tea, kafin ta bubbuga musu k'ofa, Abdul-Naseer yace "gamu nan fitowa", bayan su fito sunyi breakfast d'in duk da ita d'in ba wani me yawa taci ba tace ta k'oshi, ya d'auki key d'in motarsa ya rik'e mata hannu tare da zuwa yayiwa granny sallama suka wuce, a hanya sai dariya yake mata Wai tacika raki sai kace ba jarumarsa ba...

Germany
Wani irin juyi tayi tare da rik'e cikinta saboda zanen cikinta na maps din d'akin sirri, a zabure ta fashe da matsanancin kuka kafin tace...
Littafin Falak book2 na kud'i ne akan nera 300
Book2 page 5-6 end🥰

Bonus

"Wannan wace irin masifa ce anya Sheik Abdul-Latif yanada gaskiya kuwa?"
Ta mik'e a hankali lokacin har 12:am tayi a dai-dai lokacin taji ana nocking, da sauri ta k'udundune kanta a bargo, k'irjinta na dukan uku-uku,
Daga can bak'in k'ofar taji yana cewa "Falak ki budemin k'ofa zan d'auki abu ne"
Falak ta runtse ido tare da tsala ihu, saboda ji takeyi kamar ana tsaga mata ruwan cikinta,
sai gabannin asbha sannan ta samu bacci mai nauyi ya d'auketa.
Kiran sallahr asbha da akayi ne yasa sheik Abdul-Latif farkawa yana salati ya mik'e zaune, tare da tashi ya shiga toilet yayo alwalah, a fili ya furta meyasa Falak take guduna?,
Gaskiya nayi kuskure dana barta ta kwana a d'aki ita kad'ai.
Kyara dai-daituwar hannayen rigarsa yayi ya fice da sauri saboda an fara sallah, sai da yayi haske sannan dawo.
Yana shigowa parlo ya sameta a zaune har tayi wanka tana sanye da atamfa super Holland wace tayi mata kyau duk da ba wata kwalliya tayi ba,
Batasan da shigowarsa ba, hakan yasa ta saki jiki take ta danna wayarta hankali kwance,
"Ina son wannan kwalliyar taki"
Falak ta kalleshi da sauri sai Kuma ta mik'e tsaye tace "wlhi na gaji da wannan wasan kwai-kwayon naka, kana nufin ba Kaine me neman hallakani ba?"
Sheik Abdul-Latif yace "haba Falak sau nawa zance miki ina sonki har cikin zuciyata har k'arshen rayuwata tunda nake ban ta6a son wata halittaba bayan ke, meyasa zan cutar dake?"
Amma ai Kaine kazo min jiya da daddare"
Sheikh Abdul-Latif yace "wlhi Allah ban fita ko Ina ba, nida nake ta tunaninki?"

Falak tace "wlhi wannan karya ne akwai wani abu a zuciyarka akwai shirin da kake yi a kanmu nida dad, dama ba tun yau ba wlhi ban yarda dakai ba, sai dana gargad'i Dad amma ya bijire, gashinan na aureka kana neman kasheni Kuma wlhi baka isa ba kayi kad'an"

Bai Bari kalamanta sunyi tasiri a zuciyarsa ba ya rungumota tare da danne zuciyarsa yace "ina son kwalliyar atamfa please ki dinga yimin"
"Mezesa inyi maka kwalliya ashema tsoronka nakeji kenan?"

Sheik Abdul-Latif yace "haba my sweetheart kidena gayamin wad'anan maganganun karfa daga baya kizo ki mutu a kaina"
Falak tace "Allah ya kiyaye duk Wanda ya bawa soyayya gurin kwana to shi a tsakiyar gari zai kwanta, abinda nazoyi gidannan shine ibada sallah abinci ma bai zamemin dole ba"
Rufe mata bakin surutun yayi da bakinsa yana wani tsotsa yana lumshe ido yana d'ad'a matseta a jikinsa kamar wani zai k'wace masa ita, Falak dai ta fara gajiya da abinda yakeyi mata saboda Sam batason takura, ta mintsineshi yaki sakinta, tana shirin cizonshi ya kwanta da ita akan kujerar kasancewar mai zaman mutum Uku ce, yayi mata rumfa da faffad'an k'irjinsa tare da kai bakinsa kunnenta yace "ina sonki please ko sau d'aya ne kice kina sona"
"Cikin masifa tace "aikin banza aikin wofi badan ka danneni ba da na nuna maka aikin hankali nifa ban ganewa wannan abin da kakeyi ba?"
"Soyayya ce fa"
Falak tace "soyayyar taci...."
Ya rufe mata baki.

A hankali ya tasar da ita zaune yace "yau zanje company please kiyimin abinci inason cin girkinki"

Falak ta kalleshi kafin ta juyar dakai saboda tsayawa magana ma 6ata lokaci ne,
"Eh my sweetheart baki bani amsa ba?"
"To mezance maka ko k'arya kakeso inyi maka ina maraba da fitarka adai kula da amanar Allah"
A fili ran Sheik Abdul-Latif ya 6aci yace "kina nufin zanci amanar dad kenan?"
"Wai da haka nayi tsammani"
Ya girgiza Kai ya shige ciki, wanka ya shiga yana gamawa ya fito d'aure da towel kafin yazo ya zauna gaban mirror ya shafa lotion masu k'amshi bayan ya tsane jikinsa, shawarar yasa shaddar da Dad yayi musu a Nigeria yayi, ya d'auko mai ruwan coffee wacce tasha aiki ya sanya ta, ya ciro takalminsa marar nauyi yasa kana yana hula, wow kuzo kuga inda sheik Abdul-Latif ya fito ya d'aura agogon ya feshe jikinsa da turare, kana ya kalli kansa a mudubi, yace "kodai kayan sunfi yiwa y'an Nigeria kyau ne?".
Ya fito parlo tana zaune da waya a hannunta kamar inda ya tafi ya barta d'azu "my sweetheart zan fita"
Falak ta d'ago ta kalleshi sai Kuma tace "jeka kayi kyau"
Iya hakan da ta gaya masa ba k'aramin dad'i yaji ba, har yana wani zama kusa da ita a tunaninsa ta sakko yace "a bani morning kiss "
Falak ta sake baki tana kallonsa kafin tace "shidai wannan abin idan da karatu ne nayi hadda to sai Kuma me?"
"Yauwa tawan dama haka nakeso kiyi haddar soyayyar sheik komai zefi tafiya dai-dai"
Ya mik'e saboda ganin yana neman yin latti,
Harya fita bataje dashi komai ba, shiko yana mamakin Falak wacece irin mutum ce da soyayya bata gabanta duk wannan abin da yake nuna mata har yanzu ta kasa fahimtarsa,

Falak najin motarsa ta fice ta shiga d'akin data kwana ta fad'a toilet tayi wanka, iya mai ta shafa, bata Bari ta shafa man da yake jere akan dressing mirror dinba na cikin hand bag dinta ta ciro, bayan ta gama ta mayar da kayan da ta cire kafin ta fito zuwa parking space "ina drivers d'in gidannan?"
Falak ta tambaya cikin d'aga murya,
Wani mutumi ya fito balarabe wanda zeyi shekaru arba'in yace "mah gani"
"Zaka kaini Berlin"
Drivern ya shiga motar itama ta shiga backside yayiwa motar key, mai gadi na bud'e get d'in suka fice.

Kasancewar tsakanin su day gidansu ita da dad d'in babu nisa hakan yasa basu wani yi tafiya sosai ba, suna isowa anguwar sai da ta fito tayi nocking mai gadin ya tabbatar da itace sannan ya bud'e mata ta shiga, kai tsaye part d'inta ta wuce, Abu na farko data fara dubawa system d'inta cikin sa'a ta gani amma koda ta bud'e babu komai akai, batayi tunanin komai ba, ta d'auka ko saurin da takeyi, ta tattaro ragowar kayanta ta zubasu a bag babba sannan ta fito tana yiwa mai gadin sai anjima,

Bayan ta bud'e k'ofar get d'in ta bud'e motar ta shiga suka koma gida,
Switzerland
Zaune suke a wani bak'in daki da Zagaye yake da jan k'yalle jikin momy da Maleek da Manaf da Arif duk rawa yake, sunaso suji sharad'in da dodo yace zai sanar dasu a ranar 27/3/2023
yau ranar ta cika cif gasu a gabanshi ko wanne ya sunkuyar da kansa, cikin k'araji dodon nasu yace "kuci gaba da rainon cikin da me cikin, alkwarin da zamuyi daku shine duk yaron da ta Haifa ko yarinya dole a dinga bamu jininta"
Momy ta kalli Maleek da yake murmishi,
Dodon ya sake cewa na biyu kuma dole ya zamo dukkanku kuna neman matan waje kema ki nemi wani a waje da zarar kunzo yin sex ku shimfid'a k'yalle abinda ya zubo shi nakeso, na uku zaku dena yin Sallah har na tsawon sati guda bayan haka sai kuje kuci gaba da shagali, tun anan zuciyar Momy ta tsinke mugun kishinta ya mota damuwarta yanzu neman matan da dodo yace Maleek yayi shine babbar damuwarta.
Tunda beauty taga sakin fuskar da momy tayi mata taci gaba da farincikinta da Arif, koda wane lokaci tana k'ok'arin faranta masa shiko zuciyarsa ta kasu gida biyu, amma a fili yana nuna mata so, a ransa kuma abin cikinta shine damuwars,
Yau kwanansu uku da zuwa gidan momy, ta Aiko musu da had'ad'd'en abinci, wanda rabi da jini akayishi a matsayin manja kasancewar abincin manja tayi, Arif ya riga da yasan da zaman abincin dan haka wunin ranar ko lek'owa gidan beyi ba, beauty taci abinci tayi nak ta dinga santi harda Kiran momy a waya wai gobe ma idan tayi abinci irinshi a Aiko mata dashi, momy tayi dariya tace "ashe kinason irinshi dama nayi ne bansan ko zakici ba"
Beauty tayi murmishi kamar momy na ganinta tace "momy wlhi dad'in ma ba'a magana"
Acan gidan momy Maleek na zaune yana jin duk abinda suke cewa, bayan momy ta ajiye waya yace "Maleek ya rungume momy kana yace "yanzu dai beauty itace kud'inmu idan Babu ita muna cikin bala'i?"
Momy tace "tabbas amma fa ni ban yarda kaje ka nemi wata acan waje ba bayan gani"
Maleek yace "kefa da dodo yace kema kije ki nemi wani a waje?"
"Nima ba zuwa zanyi ba wlhi ka share maganarsa har sallah duk muyi abinmu"
Maleek ya dakawa momy tsawa kamar ba shine Mai fara'a ba kafin yace "kinsan waye dodo kuwa? hhh in ma kina mafarki ne kiyi gaggawar farkawa saboda yafi gaban tunaninki yasha gaban kwatancenki har wannan maganar da mukeyi yana jinmu"
Momy ta toshe baki tare da fito da ido waje tace "na tuba bazan sake ba, dodo idan kaji wannan maganar kuskure mukayi"
Egypt
Jiki a sanyaye suka dawo gida, granny na ganinsu tace "Masha Allah kuce ciki harya fara girma dubi inda kikayi haske kika murje"
Abdul-Naseer yayi murmishi itama Fadwa murmishi tayi suka wuce ciki dukkansu, granny tace "oh ni Allah yara basu da kunya ina tayasu murna sun shige?"
Bedroom
Abdul-Naseer yace "please Fadwa ko da Wasa karki sake ki nunawa granny doctor yace Babu cikinnan"
Fadwa ta fashe da kuka tare da fad'awa jikin Abdul-Naseer kafin tace "gara a gaya mata me amfanin boye mata, idan akazo mukayi wata biyar akaga Babu ciki ace naje na zubar ko me kake nufi?"
"Nasan inda zanyi karki damu nidai na gaya miki"
Fadwa ta share hawaye

17 / 19