Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

FALAK Book Auren Sirri 1 & 2 By Zainab Habib

Author :  Zainab Habib Category :  African Stories & Novels

Chapter   15 / 19

42K to 45K   out of 54.7K words

yaga mutum yana halin rashin lafiya, yai saurin isa inda take, ya tallafo kanta da yayi zafi sosai cikin tausayawa yace "Beauty tashi muje hospital"
Babu musu ta mik'e tana sanye da riga da wando ya kamata sosai Arif ya cire mata su yasa mata doguwar riga, Niko nace ashe yana kishinta duk iskancinsa,
Suna zuwa hospital aka bata taimakon gaggawa tare da yi mata gwaji, anan ne aka tabbatar masa da tana d'auke da juna biyu na wata biyu, mamaki ya kama Arif, a zuciyarsa yace "kodai tun lokacin da nayi mata fyd'e shine ta samu ciki?"
Daga k'arshe ya duba takardar da aka bashi, yaje ya biya kud'i kafin yaje ya kar6i magani akayi masa bayanin kar a dinga 6ata mata rai, kana kar ta dinga d'aukar abu mai nauyi daga k'arshe sukace tana buk'atar walwalah a tare da ita,
Koda suka koma gida, yaji soyayyar cikin jikinta na dad'a shiga ransa, har wani shauk'i yakeji, ga kulawa ta musamman da yake bata, ammafa idan buk'atarsa ta motsa sai dai yaje ya sami matan waje haka yakeyi har lokacin da cikin nata ya fara fitowa,
Momy bata sake zuwa gidan ba koda aike ita a dole tayi fushi, haka ma beauty bata ta6a marmarin zuwa gidan momyn ba, burinta bai wuce ace cikin dake jikinta ya 6are ba, da tafi kowa farinci, saboda tsanarsa da Allah ya d'ora mata"
Maleek••
Kamar inda bokansa ya fad'a yau litinin yau zaiyi kud'i naban mamaki tunda sun cika sharud'a, su uku Manaf da Arif dashi kansa, kowa ya kwanta da namiji d'an uwansa kasancewar anyi aikin bokanci dukkansu biyun badan sunso hakan ba, k'arfe 2:pm su Maleek suka fito daga masallaci ya gaiyyacesu zuwa ke6a6en gidansa, suna shiga suka zauna a parlo ya shiga ciki sai gashi ya fito musu da kud'ad'e masu yawa wanda idan suka tsaya k'irgawa sai sun 6ata lokaci, sai dai bank, Manaf ya zaro ido jikinsa na karkarwa yace "a Ina ka samu wannan kud'ad'en Yaya?"
Maleek ya shek'e da dariya kafin yace "bana buk'atar bincike ko doguwar magana, wannan naka ne wannan na Arif kuji dad'inku"
Arif dama ba yanzu bane sabon rik'e ire-iren kud'ad'en a gurinsa, sai dai zai iya cewa "wannan sunfi na ko yaushe yawa"
Bayan sunci sun k'oshi a gidan Maleek d'in suka kama hanyar zuwa gida, ko wanne rik'e da jakar kud'i a hannunsa.
Nigeria, airport..
Ummu Saudart da Munira da Hibba dukkansu sunyo ayari zuwa airport suna zaune a inda aka tanadar,
'Daga idon da Ummu zatayi taga jirginsu Falak na sauka, zubawa mutanen da suketa fitowa idanu tayi tanason taga fitowar Falak,can hangota tana sanye da sari, ba k'aramin kyau tayi ba, ta lullu6e kanta da mayafin tana ta murmishi, kasancewar ta hango mahaifiyar tata nata raba idanu, Su Saudart ma sun hangota, tana isowa da ta kusa zuwa gurinsu ta rugo da gudu ta rungume Ummu tana dariya, wani hawayen farinciki ya kwaranyo wa Ummu suka shiga mota suka wuce gida.
Abin mamaki, an Zagaye gidan da furanni sosai gidan yayi kyau ga walimar cin abinci da aka shirya, ga mamakin Falak taga gidan ya cika da y'an uwan dad da na Ummu duk sun hallara suna jiran shigowarta,
Driver na parking suka fito, mutanen da suka taru sunajin k'ugin mota sukayo waje da sauri ana cewa *"Happy birthday to you Falak* sai a lokacin ta tuna ai yau ne birthday d'inta ashe shiyasa Dad ya matsa ta taho,
Suna k'arasawa ciki kowa ya fara kallonta, sai cewa sukeyi tayi k'iba takara haske Takoma kamar ka ta6ata jini ya fito, a tak'aice dai ta koma kamar balarabiya,
Ko hutawa batayi ba aka fara gudanar da bikin birthday party d'inta aka yanka cake me d'auke da sunanta anci ansha an goge wuya,
Egypt
Har k'arfe 9:pm Abdul-Naseer bai dawo ba, Fadwa ta gaji da jiransa ta koma d'akinta ta kirashi yace "yakusa shigowa tayi hakuri"
Kamar granny tasan lokacin da zai dawo ta d'ibo bargo da pilo ta dawo parlo ta kwanta akan kafet, sallamarsa da taji ne ya sata mik'ewa zumbur tare da cewa "sannu da dawowa, kaga ni dana damu dakai gashi nazo na zauna ita kuwa ko oho tanacan tana sharar bacci"
Abdul-Naseer yayi murmishi kafin yace granny ga kaza please kiyi hak'uri ban taho miki da tuffa ba"
Jikin granny na rawa tace "d'an albarka shiyasa nake sonka, ai akwaika da hankali ga kyakkyawan hali kamar na mahaifinka Allah ya saka da alkairi, ammandai ka siyowa matarka ko?, karta zo ta ganni taji haushi kasan yaran yanzu mugun hali garesu kishi harda iyayen miji nikuma banason wata matsala ta giufta muna zaune lafiya daku"...
*FALAK🍒*

Mom Islam

Arewabook@momIslam11

E.O.W

Page 57-58

Abdul-Naseer yayi murmishi kafin yace "ai Fadwa batacin nama"

"A'a kace tabar dad'i shiyasa duk zuwan da nakeyi sai inga tayi miya ba nama, kumafa ina ga kana siyowa ko tana tattarawa iyayenta ne?"

Abdul-Naseer ya mik'e kana yace "zan shiga ciki sai da safe"

Granny ta wurga masa harar tare da turo baki gaba.

Kai tsaye d'akin Fadwa ya shiga tare dayin sallama ta rungumeshi da sauri ya d'agata sama yana cewa "naji ki fayau Ina tunanin yau bakici komai ba"
"Naci"
Fadwa ta fad'a tanayi masa murmushi,

Tunda taga granny tazo ta dena ajiye masa abinci a dinning sai dai ta shigo dashi bedroom d'inta ta ajiye masa akan table saboda sa ido irinna granny dakuma gani Babu k'yalewa.
Nigeria••
Sai wajen k'arfe 9:30 Hamma Aliyu yazo ya d'auki Saudart suka wuce gida, yana tsokanar Falak.
Washe gari da ragowar y'an uwan Ummu biki ya rage saura kwana biyar, anata hada hadar biki anyi anko yakai kala biyar iyaye da nasu y'an mata da nasu yayu da nasu ka kanni da nasu sai Kuma na k'ananan yara suma da nasu,
A y'an kwanakinnan Sam Saudart dasu Munira basu da zama, Hibba kam rufe shago tayi saboda bama zuwansa takeyi koda yaushe ba,
Sunje kasuwa sun siyo hanbag mai hannu wacce idan mutum ya rataya tsayin hannun zai kai kwankwaso a cikin ko wacce ansa Zobunan azurfa masu tsadar gaske wanda Dad ya Aiko dashi da turare shima ba d'an Nigeria ba, kafin zuwan Falak.
ledar walima Kuma ansa turaren tsinke irin mai guda d'ari sai kasko shima Mai kyau.
Harda ledar fulani day suka bugo Wanda Falak ta aiyyana a ranta bazataje ko guda d'aya ba, bama zata fara gaya musu ba bare hankali ya tashi.
Ana biki saura kwana biyu, Falak ta sake Shan gyaran jiki bayan Wanda akayi mata a Germany sosai ta fito kamar wata balarabiya tsabar kyau, ga haske da fatarta ta sakeyi gunin sha'a wa, a yau Friday sukaje lalle da wani gyaran kai bayan Wanda taje akayi mata, lallen yayi masifar yi mata kyau, mai zanen ja da bak'i har kafarta, ranar asabar dad da Imam da sheik Abdul-Latif da sauran abokan arziki suka sauka a Nigeria, iya dad ne kawai bak'ar fata, dukda shima d'in bawai bak'i bane amma a gabansu dole zai kasance bak'i,
Ummu Tasha ado abin ba'a magana kamar ba ita ta haifo su Saudart ba tayi kyau sosai, su Dad na isowa suka kirata ta tura driver ya kwaso su,kai tsaye dad yace a wuce dasu guest house d'insa kana yasa ayi musu take away na abinci a babban restaurant na garin Gombe, cikin hukuncin ubangiji kafin su isa abincin ya isa, katafaren gidan dad kenen wanda tsakaninsa da gidan Ummu yakai nera d'ari, gidane had'ad'd'e wanda kullum sai anyi mopping an tsaftaceshi, bayan sun isa sun huta dayake su biyar ne, ko wannensu yayi wanka ya sauya Kaya suka nufi dinning room Dan cin abinci, sheik Abdul-Latif yace "Sheik Abdul-Latif ya bud'e Abincin Wanda a k'alla zeyi na 30k sheik Abdul-Latif yace "Imam wanne kakeso?"
Imam yayi murmishi yace "abinci ba kalar namu ba, da yarensu suke maganar shikuma dad yana bedroom yana waya da Ummu.
Imaam yakai lomar abincin bakinsa ya lumshe ido yana Santi.
Acan gidan Ummu kuwa bak'inciki fal Cikin Falak cewa take "meya kawo sheik Abdul-Latif Nigeria wace alak'ar suka k'ulla dazai kashe kud'in zuwa?"
Bata sake Ummmu taji na bare ta fuskanci fad'a da gareta Dan haka tayi shiru da bakinta amma ta ke6e kanta a d'aki.
Washe gari da misalin k'arfe 1:30pm Falak tasha makeup tayi kyau sosai ranar tasa wata riga Tasha ado daga ganin rigar ma zakasan taci kud'i,
A hotel akayi order abinci sai dai adinga kar6owa su Ummu ko tukunya basu Dora ba sai masu wanka da sauransu.
K'arfe 2:pm dubban al'umma suka sheda d'aurin auran Falak da Sheik Abdul-Latif lakadan ba ajalan ba, idan kaga mutanen da suka halaci d'aurin auren sai kayi mamaki saboda yawansu, duk da dady ba mazaunin Nigeria bane, tunda aka dawo d'aurin auren Falak na gidan Saudart gabanta sai dukan uku-uku yakeyi tarasa dalilin hakan, Amma ta rubuta a ranta auren wata biyar zasuyi ko wata uku kafin sheik d'in ya gama dai-daita company d'in dad,
Anyi rabon gifts sosai abin Kuma ya burge mahaifin Sheik Abdul-Latif yasa dad ya rakashi banki ya ciro kud'i ya diga sadakar dari biyar har na dubu ashirin,
Bikin Falak da Sheik Abdul-Latif ya kafa tarihi, kowa yaga bature ko balarabe sai abin ya girgizasu, tambayar tasu anan shine dama balarabe yana auran bak'ar fata?
Acan guest house d'in Dad, iya sheik Abdul-Latif ne ya dawo ya kwanta a bed zuciyarsa nata bugawa da K'arfi kamar zata fito, ya rasa ta inda zai fara misalta ranar yau to shikuma fad'uwar gaban da yakeji na meye?"
Cire kayan da be saba sawa yayi ba, wato manyan kaya ankon shadda Wanda sukayi su shida harda dad, da abokan dad uku da sheik Abdul-Latif da Imaam,
Sallamar su dad da yaji ne yasashi runtse ido kamar meyin bacci Wanda a zahiri idonsa biyu kawai yayi hakanne saboda kunyarsu da yakeji.
Dad yace "wanan wane irin ango ne,Kunga Wai bacci yakeji Allah yasa ma tunda yazo yaga Falak d'in?"
Abokin dad me suna Rajab yace "gashi dai yazo ya kwanta ko hayaniyar ce ta dameshi?" Ikon Allah hausa rangadau a bakinsa,
Kwanansu d'aya dad ya fara nema musu tafiya Germany
Gidan Saudart, Falak ta cika tayi himm wai Dan taji ance da ita zasu tafi, Ummu harda wani yi mata fadan kula da miji itada auran tak'aitaccen lokaci zasuyi.
Abin takaici Wanda ya sake 6atawa Falak rai shine, Wai sheik Abdul-Latif shine zeci gaba da kula da komai na dad, ita Kuma idan aka kunsheta a gida shikenan?
Ummu tayiwa Falak siyayya musamman kayan gyaran da kayan sawa da abubuwan buk'ata wanda ba lallai ta samu akan kari ba tunda ba daga zuwa zata fita ba.
Kwana ukun da tayi kafin su wuce Ummu ta dinga yi mata nasiha akan biyaiyya da sanin darajar miji da iyayensa, itadai Falak ko a jikinta saboda ba sune a gabanta ba, burinta suna komawa ta d'auki system d'inta ta koma bakin aiki tunda an kammala games d'in, saboda duk wasu hidimomi da akayi harda d'aurin aure gani take a drama yake.
Dad shima yayita k'ok'arin nusar da ita tabi mijinta, kasancewar a d'akinsa suke Kuma shi da ita ne kawai yasa ta cewa "dad nifa nagaji da wannan surutan har Ummu tun shekaranjiya abinda take fad'a kenan ko ka mance auran wata uku zamuyi bayan nan ya sakeni in abin yayi yawa ne inyi wata biyar?"
Dad ya d'aga hannu zai kai mata mari, ko meya tuna oho ya sauke hannun yana kallon Falak rai a 6ace yace "aurannan da kikaga anyi wlhi sai dai idan mutuwa kikayi shine za'a fasa wannan auran Kuma kinyishi kenan har abada babu fita sai dai ki kawowa iyayenki ziyara da marmpari"
A zabure Falak ta kalli Dad da idanunsa suka sauya launi tace "dad dan girman Allah ka fahimtar dani ma'anar aurannan? Kaine fa ka yarjemin akan auran wata biyar zamuyi farko ma shida nace, sai Kuma nace uku kace eh ka amince amma yanzu me kake fad'a Dad kana nufin baka sona kenan ka Dena Sona wani yazo ya rabani dakai,Shikenan dad wlhi da kace kadena Sona gara in kashe kaina kafin muje can"
A gigice dad yace " listen to me daughter meyasa zakice haka?"
Ina sonki abinda nakeso ki sani shine, aure ba abin Wasa bane, Ni kaina nasan baki San komai akan aure ba, ni sheda ne, Falak aure yafi gaban tunaninki inhar kinason farincikina dakuma tsawon rayuwata in Allah ya barni ba tare da ciwona ya tashi ba to ki zauna lafiya a gidan mijinki shine magana, inhar kika sa6a masa wlhi ni kika tozarta ni za'a zaga ki zubarmin da mutunci a idon mutane, Falak ta hanyar aure aka sameki Dan me yasa kema bazakiso gudan jininki ta hanyar aure ba?"
Jikin Falak ya gama sanyi, sai ta fara cewa "wato sai yanzu nasan me nake ciki na d'auki soyayya aikim banza na d'auki aure aikin banza meyasa nakasa fahimtar komai akai?"
"Saboda baki da lokacinsu aiki shine abokin aikinki shine abokin hirarki shine komai naki zan iya cewa a abubuwan da suka shafi rayuwa abu biyu kikafi bawa muhimmanci, sallah da aiki, shiyasa koda yaushe bana son rabuwa dake, aikin DSs da mukeyi dake ya zamo ni kad'ai akwai wata mota da oganmu ya baki Ina fatan zakiyi masa godiya idan komai yayi Normal?"
Tayi farinciki da kyautar, sai dai tana cikin hargitsi ba sosai ta nuna farincikin ba, rayuwa tayi mata kunci a halin yanzu batason jin muryar kowa burinta shine ta ganta a d'aki ita kad'ai har na tsawon sati ba tare da wani ya furta mata koda sannu bane"
Washe gari jirginsu Falak ya d'aga sai Germany,
************************
Bayan sun sauka abokan dad da Imaam sukace Sheik Abdul-Latif ya wuce da Falak gidansa, Falak ta kwa6e fuska kana tace "company d'in Dad fa?"
"Akwai ma'aikata a ciki kuje can gidanku idan kin huta kafinnan an kwana biyu sai ki zo ki duba"
Dole tabi abinda Imam d'in ya fad'a gudun gardama, kai tsaye suka shiga mota sai anguwarsu, a mota kowa da tunanin da yakeyi, musamman ma Falak data kasa gane menene auran shi kansa, duk da anyi mata bayani yafi sau ashirin amma ta kasa ganewa.
A wani tangamemen get yayi parking tare da kallonta, kwar da kai gefe tayi, ya danna horn mai gadi ya bud'e ya kutsa motar ciki, bayan sun gaisa da mai gadin ya shige yayi parkin, shi ya fara fitowa kafin yazo ya bud'e mata murfin mota, ga mamakinsa wayarta take dannawa ba tare da tunanin fitowa ba,
"Heart beat ki fito munzo"
Sheik Abdul-Latif ya fad'a cikin siririyar murya,
Ko kawosa akai batayi ba taci gaba da abinda takeyi, batayi aune ba taji ya d'agata sama cak ya shiga da ita, kasancewar akwai mata tsofaffi masu aiki a gidan yasa yana nocking aka bud'e masa, again bata dena danne-danne a wayar ba, ya direta a bedroom d'insa tare da shigewa toilet ya d'auro alwalar magriba ya fita masallaci, alamun rashin caji da wayarta ta nuna ne yasata d'ago kai tana neman inda zata mak'ala chaji, kasancewar tana tafe da cazarta a jaka, mutuwar tsaye tayi, sakamakon ganin wani irin ado tare da flowers da suka Zagaye d'akin sai k'yalli sukeyi, shi kansa mudubin d'akin abin kallo ne ga kayan d'akin farare tass abinda ya kasance purple shine, adon jikin gadon da k'ofar toilet, har cikin toilet d'in shima fari ne,
Itama sallahar ta tashi tayi tazo ta shimfid'a sallahya ta kabbara sallah, tana idarwa tayi adu'oi sannan ta mik'e ta dawo kan gado bayan ta jona chaji, wata dattijuwar mata ce ta shigo zatayi shekaru hamsin a duniya ta ajiye wani babban tirai mai d'auke da abinci masu lafiya da fruits da kayan lashe-lashe, kafin ta gaishe da Falak cikin girmamawa, ba halinta bane wulakanta d'an adam shiyasa ta amsa da "lpy ya aiki"
Matar tace "alhmdulilh"
Shigowar sheik Abdul-Latif ne yasa matar ficewa bayan ta gaishe shi, ya zauna kusa da Falak yace "heart beat please kici wani abu"
Falak ta watsa masa mugun kallo kafin tace "shi bugun zuciyar me yake nufi Banda rashin aikinyi"
Yai saurin matsawa gareta yana rungumota tare da shafa bayanta yace "ya kikeji da muka kasance tare?"
"Mekuwa zanji Banda bak'incikin rabani da Ummu da dad kai munafuki ne wlhi mugu Mai katon kai"...

Gaskiya bazaku dinga samun update akan lokaci ba, inhar kunaso ku dinga ganinsa kullum adinga tayani sharing zuwa sauran groups inba haka ba hhhhh.
*FALAK🍒*

Mom Islam

Arewabook@momislam11


E.O.W

Page 59-60 end of book 1

"Sweetheart ki tattausa kalamanki saboda akwai ranar da zaki so in kasance tare dake"

"Tirr da zuwan wannan rana wlhi sai kayi nadamar aurena da kayi, har yanzu ban gama yarda dakai ba ban gama yarda da cewar kai mutumin kirki bane"

Yau kam ransa ya 6aci, cikin zafin nama ya turata gefe yana huci ya ce" karkiga Ina lalla6aki lokaci yayi dazan gaya miki wanene Sheik Abdul-Latif meyasa na shiga jikin mahaifinki"
Falak ta zaro ido a tsorace tace "cuta ce ta janyo hakan"
"Shittt na aureki saboda d'aukar fansar Aljani Amin Kuma wlhi sai na d'auka zan fita daga rayuwarki"..

Nigeria••
Hankalin dad ya kwanta sosai saboda burinsa a rayuwa shine yaga ya aurar da y'a yansa, gashi bikinsu Munira saura 3weeks an kammala shirye-shirye a 6angarensu, kusan kullum sai yayi waya da Sheik Abdul-Latif sai yazo zai ambaci sunan Falak sai bakinsa ya rufe,
Wata ranar talata kwanansu uku da aure, Ummu tace "ka kiramin Falak rabona da inyi waya da ita na mance"
Har dad ya ciro waya sai ya mayar yace "d'azunnan muka gaisa da ita harda hotonta ta turomin bari idan na dawo zuwa anjima zan nuna miki komai"
"To"
Kawai Ummu tace saboda bata da inda zatayi dole ta hak'ura a hakan.

Saudart, tunda akayi bikin Falak bata samun isashiyar lafiyar da zata kawowa Ummu ziyara bare suyi hira, kullum cikin zazza6i take komai taci sai ta amayar gashi bata k'aunar taga Hamma Aliyu yazo inda take, da ya shigo zata hau kwara amai, wannan abin da takeyi shi ya daukesa a tama gama rainashi kamar taga Kashi zata dinga amai daga ta gansa?, A zuciyarsa kuwa ya aiyana aure zai k'ara inyaso tsabar kishi ta kashe kanta,
A halin yanzu ma sun Dena had'a gado d'aya rabonsu da kwana tare tun ranar da sukaje party suka dawo abin ya faru da ita,
Washe garin ranar yace mata suje asibiti, kasancewarta mai taurin kai tace "Babu inda zata ya barta zata warware, dole ya k'yaleta tunda ya

15 / 19