Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

FALAK Book Auren Sirri 1 & 2 By Zainab Habib

Author :  Zainab Habib Category :  African Stories & Novels

Chapter   18 / 19

51K to 54K   out of 54.7K words

tare da kifa kanta akan bed.
Acan gidan su Ummi wato mahaifiyar momyn Arif, sunata wadak'a da kud'ad'e momy Sai transfer take yi musu daga cunce suna son abu, granny da taji labarin Abba yayi kud'i ta uzzurawa Abdul-Naseer akan dole ya mayar da ita gida, Abdul-Naseer yak'i sai hanya hanya yake yi Mata, da damuwar duniya ta isheta ta nad'a kayanta a d'ankwali ta fito kai tsaye gurin get ta nufa tana zuwa tace "ku bud'emin kofa ai zama a gidan nasa ba dole bane"
Mai gadi yace "Alhji yace kar abar kowa ya fida dan haka ki koma gida, granny tace "shegu munafukai da gemu kamar na wani abu da ake nunowa a TV zaku bud'emin ko sai nayi muku ihu?" Mai gadi yace "na fad'a miki gaskiya kaka ki koma ciki kawai idan Alhjin ya dawo sai ki fita..
Germany
Wani irin kururuwa take sakamakon ganinta da tayi a tsakiyar halittar da batasan sunanta ba, tayi gabas Babu mataimaki tayi yamma nan ma haka, a hankali ta durk'usa tare da rushewa da matsanancin kuka gashin kanta duk ya rufe mata idanu, bamu mukullin d'akin sirri Falak tace....

Ayi hakuri banyi editing ba

Masoya yau zamuyi muku bye bye sai mun hade a paid group.

7-8*
FLK

Juyi tayi a makeken gadon da take kwance, tare da mik'ewa a zabure, tare da share zufar dake bin fuskarta, sai Kuma ta fashe da kuka, a fili tace "wannan wane irin lamari ne da baya riskarta da rana sai da dare, ta fad'a toilet ta d'auro alwalah ta shimfid'a sallahyar data gani a ajiye kan bedside tare da d'aukar mayafinta ta kabbara sallah, tana idarwa ta jingina da jikin bango, sai Kuma ta janyo system d'inta domin ta kunna karatun alkur'ani abin mamaki taga babu komai akai,
Waro ido tayi tare da kashe system d'in ta sake kunnawa har yanzu ma haka take nunawa,
Falak ta sake fashewa da kuka saboda muhimman abubuwanda take dasu a ciki masu amfani wanda duk iya basirarta da rik'e abu bazata iya kawo wasu abubuwan ba,
Tashi d'aya idonta ya k'auracewa bacci ta fara tunanin barin gidan Sheik kota halin ƙaƙa saboda bazata iya jurewa fitinar dake barazana ga rayuwar ta ba, abinda yake matuƙar bata mamaki bai wuce kasa sanarwa da dad halin da take ciki ba, lamarin da yafi ko wanne hautsina kwanyarta kuwa shine a halin yanzu bata isa ta sarrafa abubuwa kamar da ba, koda mutum ne a tsaye ko a zaune idan yazo da niyar cutarwa ne to tabbas sai ta ladaftar dashi amma yanzu tana ganin abin cutarwa bata isa ta yiwa kanta magani ba,
A hankali ta gama Zagaye d'akin kamar me neman wani abu,
Rufewar da idanunta suka farayi ne ya sata neman guri ta zauna, kamar kullum dama sai da asubha baccin yake d'aukarta haka yauma sai gabannin asbha baccin ya sureta, kafin sheik-Abdullatif ya tafi masallaci sai da yazo ƙofofin guda huɗu duk yayi nocking saboda bai san wannene take ciki ba,
Firgit Falak ta farka tare da yin salati ta rufe idonta da tafukan hannayenta kafin ta sauko jiki a mace ta wuce toilet wanka tayi tare da yin brush sannan tayi alwalah ta fito ɗaure da towel jakar kayanta ta buɗe ta ciri riga da skirt na material Wanda duk a Nigeria akayi mata d'inkin, ta ciro hijab tasa tare da shimfiɗa sallahya ta kabbara sallah, bayan ta idar ta ɗauki Alkur'ani wanda ya kasance akan wani ɗan table, ta fara rera karatu, sheik-Abdullatif yazo wucewa ya jiyo zazzaƙar muryarta tana karatu, lumshe kyawawan idanuwansa yayi kafin ya tura ƙofar da yaji saurin karatun, bayan ya shiga da sallama ya zauna har sai da tayi kabbara kafin ya riƙo mata hannu yace "Barka da safiya bugun zuciyar Sheikh-Abdullatif"
Bata ce masa komai ba, shima bai sa ran zata amsa ba, yayi matuƙar riskar kansa a wani yanayi musamman ma da sanyin asubar nan yake ratsa ko ina na sassan jikinsa,
Idanunsa a lumshe ya ce"dan Allah ki saurareni inaso muyi magana muhimmiya idan har zaki amince ɗin"
Abin mamaki sai yaji tace "ina jinka"
Ta miƙa zuwa gaban dressing mirror ta ɗauko Vaseline kasancewar shi kaɗ'ai ta gani a ɗakin sai farar powder, bayan ta shafa man ko kallan inda yake har yanzu batayi ba, har ta shafa powder ta mayar da kayan ta dawo ta zauna kan sallahya, daga nan ta ɗauko wayarta dake hand bag ta kunna tare da shiga game, abin ya bashi mamaki, ya daɗe yana tunanin "Falak wace irin yarinya ce da komai bai dameta ba shin kuma idan aka barta haka zataci gaba da rayuwa kenan?"
Bashi da mai bashi amsar tambayarsa ya kawar da zancen ta hanyar cewa "nayi magana baki ce min komai ba"
"Nace maka ina jinka"
Sheik-Abdullatif yayi murmishi a karo na biyu kafin yace "Falak wlhi ina sonki har cikin zuciyata ina ƙaunarki haka duk wanda naga ya nuna miki so tabbas masoyinmu ne nida ke, mezesa bazamu gina rayuwar auranmu kamar inda sauran masoya ma'aurata suke gina rayuwarsu ba?"
Falak taja dogon numfashi tare da kashe datar da ta kunna tace "am kanaso kaji amsarka ko? first bana soyayya ban taso a cikinta ba, babu abinda na sani banda karatu bansan wani hira mai tsayi tsakanin mutum da mutum ba, koda Dad bana hira ko munyi befi na gajeren lokaci ba, kafihimta?"
Yaji daɗin maganar da tayi masa kuma ya fahimce ta,
Ya ce na fahimci komai kuma naji daɗin hakan abinda nakeson ki sani rayuwar aure ba abin wasa bane, rayuwar aure ba wasan yara bace rayuwar aure ba abin yin ko'in kula bane, yanzu kinsan tulin zunuban da kika ɗaukarwa kanki ta sanadiyar k'in kwana a ɗakina?"
Karo na farko kenan da Falak ta ɗago ta kalleshi, kafin ta ce "ka mance saura wata uku auranmu ya ƙare?"
Sheik-Abdullatif yace "haba ai kin sake ragewa cewa kikayi wata shida ko biyar daga baya kikazo kikace uku"
"Wlhi lokacin na cika zanbar gidannan saboda banga amfanin rayuwar da kullum zaka zauna guri ɗaya kamar mai babban lefi"
Sheik ya ce "munyi alƙawarin nanda wata uku sai na saka miki sona a zuciyar ki ko kina ganin bazan iya ba?"
"Eh tabbas bazaka iya ba saboda soyayya itace kuke cewa rayuwar aure ko?"
Sheik yace "kinyi kuskure k'auna itace gaba akan komai inason ki fahimci hakan"
Tayi shiru ba tare da ta sake magana ko ta sake kallonsa ba,
"Kayanki suna can ɗakinki zomuje in kaiki"
Haka kawai ta tsinci kanta da binsa can ɗin, mutuwar tsaye tayi saboda ganin tsaruwar bedroom ɗin tayi tunanin wanda take ciki shine, a ƙasan zuciyarta tayi farinciki saboda Falak akwai don gayu.
Bayan sun shiga ya kulli k'ofa tare da kunna karatun Alkur'ani a wayarsa ya ajiye gefe, cikin ƙasa da murya yace "Please kin hirani da yawa zuwa yaushe zaki amince inzo gareki bazanyi miki dole ba"
Tabbas tasan zuwa gareta be wuce yace zeyi hugging d'inta ba, bayan haka batasan komai, jakar kayanta da ta hango takai hannu zata zuge zip ɗin ya sanya hannunsa a saman nata kafin yace "Please ki bani amsa?"
"Koda Dad yace min zan aureka bamuyi dashi wani abu zai shiga tsakanina dakai ba kamar inda kakeso, nifa bani da...
A sukwane ya yi mata kyakkwar runguma tare da kamo hannunta ya fara mammatsawa kamar me lalubar wani abun, rungumar dayayi mata bata wasa bace dan haka duk iya k'arfinta data tattara domin ta ƙwace kanta abin ya gagareta,
A wahalce tace "idan har haka ne soyayya turrr wallahi masu yinta sunyi asara"
Da sauri Sheikh yayi saurin sakinta yana kallon ƙwayar idonta,
Wani irin sauke numfashi yakeyi wanda shi kaɗai yasan a halin da yake,
Nigeria
Wani irin kuka saudart ta fashe dashi wanda sai ta baka tausayi, cikin yana matuƙar wahalata gashi duk ta rame taƙi sanarwa da Ummu gudun karta tayar mata da hankali, shi kuma hamma Aliyu a nasa haukar wai ta sauya bata sonsa shi yasa ya dena shiga sabgarta kwata-kwata,
Wata ranar Wednesday da safe misalin 11:30am tun gaisuwar safe babu abinda ya sake haɗashi da Saudart, yana zaune a doguwar kujera mai zaman mutum Uku ya ciro wayarsa a Aljihu ya danna number wanda ni kaina bansan wa zai kira ba, cikin rashin tsammani naji yace "hello mu Khausar, daga can ɓangaren wacce ya kira da Khausar ɗin ta buɗe baki cikin mamaki tace "ashe ranar da nake jira takusa zuwa, Aliyu baƙi aure ina jiran ka na kori samarina kaf dominka yau gashi ina jin Muryar ka cikin farinciki"
Kasancewar a speak out yasa ana jiyo komai yasa Saudart ta ɗago idanuwanta ta kalleshi kafin tayi murmishi yaƙe wanda yafi kuka ciwo, yanayi yana kallon Saudart ɗin ta gefen ido,
Sai da yaɗau lokaci kafin yace "Khausar karki damu Allah ya amsa adu'arki a halin yanzu zan iya ce miki mrs Aliyu"
Khausar ta fashe da dariya tare da buga tsalle kamar yana ganinta, tace "wai da gaske yaushe zaka turo?"
"Gobe insha Allah munyi magana da Bana"
Khausar tace "Allah ya kaimu nima zan sanarwa da Abbana"
Tsabar ya turawa Saudart baƙinciki harda yiwa wayar kiss kafin ya kwashe da dariya,
Saudart dai taga duniya abinda ko a mafarki bata taɓa tunanin zai faru ba, wato kishiya, ina alƙawarin da yayi mata ina son da yake yi mata duk babu kenan?,
Ko da wasa bata bari ta sauya yanayin fuskarta ba bare ya gane abinda ke damunta dole ta kame kanta, ta miƙe a hankali duk da cikin nata bai fito ba, kuma baya ma fitowa sai ta kusa aihuwa cikinta mai bin jiki ne yasata ƙiba,
"Ina big boy ne?"
Hamma Aliyu ya tambayi saudart ba tare da ya kira sunanta ba,
"Yana ɗaki har yanzu be tashi ba"
"Kiyi masa wanka zuwa anjima zamuje gidansu ƙausar"
Hamma Aliyu ya faɗa tare da miƙewa be jira amsarta ba,
Dole ta tashi duk da nauyin jikin da take ji taje ta tasheshi ta kwaɓe masa kaya ta kaishi toilet tayi masa wanka, bayan ta gama masa ta naɗeshi a towel tare da fitowa dashi, ta zauna kan bed kana ta jinginar da kanta ta rasa abinda yake yi mata daɗi a duniya, tabbas tana cikin tashin hankali tunda har aure yake neman yi, kodai ta gaya masa tanada ciki ne? wata zuciyar tace dama can yanada niyar yin aure ƙyaleshi, shawarar ƙyaleshin tabi ta shirya big boy, taje kitchen ta haɗo masa tea ta ɗobo bredi guda biyu mai yanka ta ɗora akai ta kawo ta ajiye masa, bayan ya gama karyawa ta shirya shi cikin sabuwar shadda orange color ta sanya masa babbar riga da takalminsa baƙi mai kyau kafin ta fito dashi ta riƙe da hannunsa, kallon agogon dake manne a jikin bangon parlon tayi, a fili ta furta ƙarfe "12:pm anguwa zakije da dadynka zauna ka jirashi, tana faɗar haka ta koma bedroom ta kwanta, tun tana ɗan wasa da ƙafafunta tana motsasu har bacci ya ɗauke ta,
Hamma Aliyu ya fito yana sanye da lallausan yadi mai kyau brown color kasancewarsa fari sai yadin yayi masa kyau, ya d'ora hula a kansa already yasa takalmi da agogo ya feshe jikinsa da turaruka masu sanyin ƙamshi, yana fitowa yaga big boy yanata tsalle-tsalle akan kujera cikin fara'a yace "my big boy harka shirya kenan?"
"Eh dady momy ce tace wai zamuje anguwa in jiraka anan"
"Okay ai na shirya barinje gurin momyn naka inyi mata sallama sai mu wuce"
Koda yaje bedroom ɗinta ya sameta tana bacci tayi wata irin kwanciya, ya gyara mata kwanciyar tare da ɗaukar biro a loka da takarda ya rubuta, "na tafi Allah ya tasheki lafiya, dan kar kiyimin rakiya shine kika kwanta bacci ko?"
Ya rasa abinda zai sake rubutawa bayan haka, dan haka ya fice tare da riƙe hannun big boy suka fice, yau aikin na manya ne bai nemi driver ba da kansa ya shiga mazaunin driver shikuma big boy yana gefensa suna tafe suna hira, har suka iso wani super market, big boy yace "Dady zaka siyawa momy kayan kwalliya ne?"
Hamma Aliyu yace "eh da second mom ɗinka Dukansu zan siya musu"
Abinka da yaro yahau murna yana dariya,
Siyayya yayiwa Khairat kamar besan zafin kuɗi ba, yana shirin shiga mota wayarsa tayi ring, number ya gani babu suna dole ya nutsu kafin ya ɗaga, zeyi magana akace masa Saudart tana Emergency batasan waye a kanta ba...!
Littafin Falak na kud'i ne 08141799224
*FLK 9-10*
A gigice Hamma Aliyu ya juya kan mota zuwa hanyar gidansu, ya ciro wayarsa a Aljihu ya danna number da aka kirashi tana shiga ya tambayi asibitin bayan an gaya masa ya katse kiran,
"Dady momyce Babu lafiya"
"Eh big boy kayi mata adu'a kaji"

yana isa hospital din kai tsaye ya wuce d'akin da akace an kwantar da Saudart,
A kwance ya sameta an lullu6eta da blue d'in k'yalle, a fili yace "d'azunan fa na baro gida"
Ummu ta fito daga toilet hannunta rik'e da kayan jini na Saudart da aka wanke, cikin rashin fahimta Hamma Aliyu yace "Ummu dan Allah meke faruwa?"
Ummu tace "gatanan ta farka tambayeta" tayi gaba ta barsu.
Hamma Aliyu ya juyo ga Saudart dake yiwa big boy murmishi ta mik'o hannunta muryarta bata fita tace "my boy harkun dawo ne?"
Hamma Aliyu yace "Saudart ba d'azu muka rabu dake ba na barki kina bacci?"
Saudart ta gyad'a kai kafin tace "ikon Allah ya fi gaban wasa jini ne ya 6alle ashe 6ari nayi"

"What!! dama cikine dake?"
Saudart tayi murmishi tare da mayar da kanta ta rufe ido kamar me bacci, nan ko gawaye ne suke ta neman silalowa a idonta, a hankali hawaye suka wanke mata fuska, zuciyarsa a tashe ya fara kiran sunanta ina numfashinta ya fara sama yana k'asa, Hamma Aliyu ya tafi da gudu har yana bigewa ya kirawo doctor,
Bayan doctor yazo yace "please ka jiramu a waje kai waye?"
"Ni mijinta ne"
"Eh to ka jiramu"
Hamma Aliyu ya rik'e hannun big boy ya tsaya jikin bango alamun Babu inda zeje, doctor ya sake cewa "please ka jiramu a waje"
"Kai nifa Babu inda zani kana ganin halin da take ciki ne zaka koreni idan bazaka iya aikin ba ajiyemin kayan aikin mtsw dallah matsa"

Doctor dai yaga masifa zuciyar zaki ta 6aci, Hamma Aliyu ya fara yi Mata gwaje-gwaje kamar shine doctor d'in, sai doctor ya koma jikin bango ya jingina yana kallon ikon Allah,
Can anjima Hamma Aliyu yace "innalilahi wa inna ilaihir raji'un,
Saudart ya akayi haka?"
Ya kifa kansa akan gadon kusa da ita yana kuka, ganin haka big boy shima yasa kuka, daga can waje Ummu ta jiyo kukan ta shigo da gudu, turuss ta tsaya sakamakon ganin doctor da tayi a gefe Hamma Aliyu ya kar6i aikin, batace komai ba taja hannun big boy suka fita, zuwa can wani lokaci naga Hamma Aliyu ya sharce zufar da ta karyo masa yace "malam gashi nagode"
"To kawai doctor ya fad'a kafin ya fice, yaje yana bawa abokan aikinsa labari.
Niko nace da wani ne doctor d'in daya zabgawa Hamma mari ya samu me tsoronsa ne kawai hhh.
Bayan mintuna talatin ta farka tare da bud'e idanunta a hankali,
"Sannu lovely"
"Uhm" Saudart tace kana tace "zansha ruwa"
Ya kai hannu bag d'in ruwa ya bata guda d'aya tare da sake jera mata sannu,
Ganin jikin nata da sauk'i yazauna kusa da ita kafin yace "please ki sanar dani meyasa kika sawa kanki damuwa har jinin ki yahau?"
Saudart tayi ajiyar zuciya kafin tace "aure fa kakeson ka k'ara bayan kasan a yanayin da nake ciki"
Ummu ta turo k'ofa tana cewa "jeka gata can ta tashi"
Sannan Hamma Aliyu ya durk'usa ya gaishe da Ummu sbda yama mance bai gaisheta ba,
Ummu tace "jikinma yayi sauk'i, ya wajensu anty?"
Hamma Aliyu yace "sunan lafiya jiya ma naje tace a gaisheki"
"Wai ni dama Aliyu ka karanci likita ne?"
Hamma Aliyu ya sosa kai kafin yace "Ummu ai shina karanta kin mance Abbana yace sai dai muyi business"
Sai da tayi kwana uku sanan aka sallameta suka dawo gida bayan an rubuta sharud'a wanda ya zamo dole hamman ya bisu,
Switzerland
Ikon Allah kenan hankalin beauty ya kwanta tayi k'iba tayi haske ga cikinta ya fito sosai, yau sunada wata biyar da aure,
Yawancin mutane kowa nata hada-hadar zuwan azumi da siye siye haka fannin Arif ma tab ya cika store da kayan abinci, washe gari Alhamis, kaf girke-girken da y'an aikin da aka ɗauki sukayi beyi mata ba, ta ture abincin tare da fashewa da kuka, Arif dake ɗakinsa yana k'irga kuɗaɗe ya fito da sauri sakamakon kukanta da yaji,
"My baby menene bana son inga kin tayar da hankalinki gayamin kinji?"
"Ni bazanci abincinnan ba na momy nakeso"
Arif yace "Babu matsala zan aika driver yaje ya kar6o Amma kafin nan barin kirata a waya"
Ya je d'akinsa ya d'auko wayar ya danna number momy, tana d'agawa yace "momy yarinyarki ce tak'i cin abinci wai se naki takeso"
Momy ta washe baki kafin tace "lahh aiko driver ya kar6a mata kokuma in Aiko mata dashi, Arif yace "eh momy ki aiko dashi"
Wajen magriba momy ta aiko driver da shinkafa da miya, gaskiya shinkafar Switzerland akwai tsayi lolz
Sai da beauty tayi alwalah tayi Sallah kafin ta gyara zama ta kwashi girki harda had'a zufa, anan gurin tayi bacci, Arif ya lek'o ya sameta a kwance a gefen kwanuka, kwashe kwanukan yayi tare da kaisu kitchen ya dawo ya d'agata sama ya Dora a gado tare da shafar k'aton cikin nata yayi murmishi ya fice.
DUNIYAR ALJANU..
Zaune suke akan wata dank'areriyar bishiya wace misalta tsayinta sai yaba mutum mamaki, Aljn Abdurraman yace "Umar me yasa ka had'a baki da rayuwarmu ake zaluntar mutumin dana taimakawa?"
Umar yace "munyi dakai inhar ka taimakeshi zaka bani alk'awarin da ka kar6a a gurina, ko ka mance zinarai Wanda na baka gudunmawa Amma nace maka duk lokacin dana nemi wani abu a gurinka tabbas koma meye zaka bani?"
Abdurraman yace "Amma ai kasan su bil adama ba kamar mu ba, taya za'ayi kuyi aure tsakaninku da ita bayan kasan hakan bazai yiwu ba?"
"Shine me yuwa da in dinga hanata rayuwar aure ai gara idan taje gurin mijinta nima tazo gurina idan hakan ta kasance zan barsu suyi zaman lafiya, idan Kuma aka samu akasin hakan sai na talauta mahaifinta ruwan Sha ma sai sunje nemowa"
Abdurraman ya girgiza Kai tare da cewa "kai Kuma hukuncinka na gurin Allah Dan kaga ka fini K'arfi shine kake son 6atamin alkairin da nayi?"
Zancen ya fara zama musu fad'a sai ga sarkinsu nan ya fito, ko wannensu ya sunkuyar da kansa

18 / 19