Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Gargadar So Complete Hausa Novel by M Shakur

Author :  M SHAKUR Category :  African Stories & Novels

Chapter   15 / 17

42K to 45K   out of 50.8K words

car key tafito Baba na zaune a tsakar gida yana wanke kaji shi
kadai gaban pampo ganinta yasa yace “ina zaki ya jikin”? Ahankali tace “bari nadan
sayo magani Baba” da dan damuwa ya gyadamata kai yace “toh shikenan kije karki
jima” gyadamai kai tayi tafice shiga mota tayi ta tada tawuce gidansu Ni’ima babu
wani nisa sosai daga layinsu shiga layin tayi har zuwa gaban gidan tai parking
tafito tashiga da sallamanta, Mama na zaune a tsakar gida tana gyara wake itada yar
makotansu da aka aiko yaranta duka sunyi aure yar aikin ta kuma ta aiketa tana
ganin Hawwa tai dan murmushi tace “ahh yau su Hawwa ne agidan” shigowa ciki Hawwa
tayi cike da girmamawa tace “Mama ina yini” murmushi Mama tayi tace “lafiya lau ya
kike Hawwa yasu wajen Baban naki” ahankali Hawwa tace “lpy lau” tazauna awajen tai
shiru takasa magana kaman wata marainiya, Mama ta kalleta sosai tabata tausayi dan
tausayi duktai wani iri, yarinyar dake zaune Mama ta kalla tace “tafi Husna ki
gaida Mamanki kice mata zan shigo anjima” tashi yarinyar tayi tafita, Mama ta kalli
Hawwa tace “sabida Ni’ima kikazo ko?” Gyadamata kai Hawwa tayi, Mama tasauke ijiyan
zuciya tace “Hawwa dagake har Ni’ima ba yara bane, tariga ta sanar dani komi dake
faruwa, she’s just trying to protect her home so I think is best idan kinyi
respecting decision nata and give her space datake so, idan tanaso kudawo da
kawancen zata nemeki, don’t blame her rayuwa yazama abin tsoro, sai ana sara ana
duban bakin gatari fa, kibarta and move on ba dole Hawwa, tunda abu yakai ga haka
kifita daga rayuwanta kinji” sosai Hawwa ke kallon Mama dake maganan irin ko
ajikinta dinnan, wani iri Hawwa taji hawaye na taruwaa idanunta, Mama tace “kidena
nacin nan dan Allah antaba kawance dole? Yo amintan dole ne? Idan kuma kin nace sai
kinyi to kema Hawwa ki yarda da mijin da Baba yamiki mana Malam Kabiru kiyi auren
kowama yahuta kinayi nasan Ni’ima zata dawo gareki, kinji kiyi tunani akan abinda
na fadamiki” Hawwa takarayin shiru zaune awajen akasan simenti, Mama tace “tashi to
kitafi” ko motsi Hawwa takasa yi, Mama ta tabe baki tace “Allah kyauta, tashi kije
dan Allah nima kada ki sake zuwan gida, wacce ta hadamu tace batayi, kowa nasa
yasani aduniyan nan ba’a kuma dole, just don’t take it personal, Ni’ima is
protecting her space ibada take, a musulunce miji yafi kawa sau dubu ko nine mijina
zan zaba bawata kawaba ana zaune lafiya, yanda kikeda wayau da ilimin nan ko kece a
situation din Ni’ima haka zakiyi wlh put yourself in her shoe, y’ata ta samu gidan
hutu yo idan kawa zata mata summun bukumun basai aja mata layi ba kowa yayi
takansa? Kingani saida safe bari nahadama Malam abincin dare” tawuce kitchen
abinta, Hawwa kawai tafashe da kuka da kyar ta dafa bango ta mike bayanta har yanzu
ciwo yakemata fita tayi ta shiga motanta, taja ahankali tabar unguwan takoma gida.
Baba bayanan but tana shiga dakinta taga ya ijiye mata kula zama tayi ahankali
tabude kulan kaza ce ta soyu ansaka kulikuli da yaji gasu cabbage, tana ganin
girkin tasan Baba yadafa mata dama yace dayana saurayi yayi sana’an balangu da su
gasassun kaji, hannu takai ahankali tadauki daya takai bakinta daidai nan Baba yayi
sallama ya shigo yana rikeda leda ganinta zaune gaban kulan yasa yayi murmushi yace
“yauwa Hawwa gashinan naje bakin hanya na sayomiki chivita na grape mai sanyi,
ranan nan na dandanashi yamin dadi zakiso shi”

Yazo yazauna kusada ita yana ijiye karafunan a gefe lumshe idanu Hawwa tayi jin
Baba ya zauna kusada ita tabude su tana ganin yanda duk yadamu yana bude mata juice
din, this is the first time takejinta so vulnerable she’s tired of being a strong
girl, komima na duniya yamata ahankali tadaura kanta jikin hannun Baba gently
tasaka hannunta takama hannunshi ta kankame sosai a kirjinta tafashe da kuka mai
tsuma zuciya, bala’in tashi hankalin Baba yayi dasauri yajuyo yace “Hawwa, ke,
Hawwana? Me akamiki mesa kike kuka haka? Hawwa” sheshekan kuka take jikinta har
rawa yake tarike Baba sosai takasa magana dasauri Baba yadago kanta saikuma yajuyo
da kyau idanunshi sunyi jaa yace “zonan Hawwa zo” yajawota yasata a kirjinshi tai
hugging Baba so tight this is abinda bata tabayiba hugging Baba saidai maybe datana
yarinya, bayanta Baba yashiga bubbugawa yace “ya isa Hawwa ya isa, zakisa hankalina
yatashi, koma menene ke damunki baifi karfin Allah ba, ya isa Jiddalo na, ya isa,
yi shiru yi hakuri kinji, kinada matsala awajen aikinki ne?” Girgixamai kai tayi
alamun a’a tana tsagaita kukan tana sauke ijiyan zuciya ba kakkautawa a kirjin
Baba, ahankali yace “to menene ke damunki”? Murya chan kasa tace “Baba aure nakeso
nayi nagaji da yanda kowa keyi dani sabida banyi aureba” ahankali Baba na buga
bayanta yace “karki damu zaki aure, anmini kwatancen wani Malami na Islamic chemist
ranan asabar tunda ba aiki zan kaiki muje muji ko aljanu gareki dake hanaki aure,
kokice baki sonsu kosu sugudu zamuji dalili kidena damun kanki namiki alkawari
bazan kara takura miki ba, lafiyanki yafi komi mahimmanci agareni Hawwa na,
kiyakuri kinji yarinyana yar albarka kiyakuri da rayuwa, komi tsari ne na ubangiji
kizama mai juriya da hakuri akwai Allah Hauwa’u kinji” gyadamai kai Hawwa tayi,
Baba yayi shiru chan yadago ta daga jikinshi yace “zafin jikinki ya baci kinsha
magani kuwa?” Gyadamai kai tayi ahankali Baba yace “to zai sauka, sha lemon kici
naman bari naje masallaci, kada kuma kisake kuka kinajina” gyadamai kai tayi yadafa
gadonta yana mikewa daukan crutches din tayi tabashi ya karba yafice tabishi da
kallo saikuma ta kalli abincin bata iyaci, wayanta ne yahau ringing da mugun sauri
takai hannunta ta dauki wayan Ammi tagani a screen sanyi jikinta yayi tadauki wayan
Ammi ma sake kwantar mata da hankali tayi sun sade suna waya ahaka bacci yayi gaba
da ita koda Baba yadawo ganin tayi bacci yawuce yana jawo mata kofa duk ya damu
ganin bataci abinci ba.

I KNOW SOME PEOPLE MIGHT BLAME HAWWA ACE KE BAKIDA ZUCIYA NE MENEMENE

LİSTEN I THINK IDAN KANAMA MUTUM SON GASKIYA YOU DO EVERYTHING IN YOUR POWER TO
HAVE THEM BACK IDAN KUN RABU.💔

IDAN SO DA KAUNAN NA GASKIYA NE AT FIRST BAZAKA YARDA LALLAI LALLAI KUN RABU BAFA
SAI REALITY HIT YOU💔

DONT BLAME HAWWA, SHE VALUE NI’IMA, BUT KUNA GANIN ABINDA MAMAN NI’IMA TAMATA SHINE
DAIDAI????
[9/20, 8:00 AM] Halima KW: 💫GARGADAN SO💫


✍🏻M SHAKUR



3️⃣
0️⃣
EPISODE 3️⃣0️⃣

KUNSAN ME AKE NUFI DA INTIMACY CLASS?
CLASS NE DAYA KUNSHI KOYARDA ABUBUWAN YAKAMATA KOWACE MATAN AURE DA AMARE YAKAMATA
SU SANI, TUNDAGA KAN MENENE SHI SADUWA DA IYALI, YA AKE SARRAFA MIJI A GADO, YA AKE
KULA DA MIJI, YAZAKI ZAMA GWANA KIYI FINCINKAU CIKIN MATAN SA🥰
A INTIMACY CLASS BABU KALAN ABINDA BAZAKI KOYABA DAN HAKA JOIN US TODAY WITH JUST
5K SHEKARA DAYA NE CLASS DIN.
MAKESURE KINADA TELEGRAM KAFIN KIBIYA
CHAT ME UP IDAN KINASON SHIGA WANNAN CLASS MAI TARIN FA’IDA

wa.me/+2347012181461
Washegari around 5 ta farka da ciwon kai har bata iya bude idanu da kyau, gashi tai
staining kayanta da wajen abinda bata tabayiba, ta tashi tacire kaya da zanin gadon
batada karfin wanki a basket na laundry tasa, tasake kwanciya ko daga kafa tayi
saitaji akanta, tana ahaka Baba yayi knocking da sallama da katuwan muryan nan nasa
yace “zan shigo” kofan yabude ya shigo dakin yaganta kan gado hankalinshi yakara
tashi ganin sosai Hawwa fa batada lpy, batama iya bude idanu, cikeda damuwa yace
“Hawwa na” yazo wajen gadon yana dagota jikinta kaman fire Baba yace “subhanallahi,
Hawwa zoki lallaba kiyi wanka muje asibiti, kokuma bari kiga nakira Ni’ima” wayansa
yaciro daga aljihu yashiga kokarin kiran Ni’ima Hawwa na kallonshi da kyar harya
katse bata dagaba yace “bata dagaba bari kinsan asuba ne hala bata tashi ba, bari
nasake kira” yasake dialing number saiya cema Baba busy kusan sau 4 yana trying
yace “busy busy yake gayamin” dan murmushi kadan Hawwa tayi ganin shima Baba tai
blocking nashi, cikeda karfin hali muryanta baya fita da kyau tace “Baba karka damu
bari naci abinci zan lallaba naje asibitin nasu adubani” gyadamata kai Baba yayi
yajuya yace “shirya wankan bari nahada miki ruwa” sosonta yaduka yadauka yafita
yana dungura sanda yashiga kitchen Umma na kitchen din ta banka uban tsaki ko
kallonta baiyiba, ruwan da aka ijiyemai nashi na wanka yajuye mata yadauka yafito
yatara na sanyi ruwan yayi dalam dalam dan jikinta akwai zafi sosai yakaimata bayi
sannan yadawo dakin yabuga mata yace “fito Hawwa” fitowa tayi da hula akanta
ahankali take tafiya tana dafe kanta da hannu daya hannu daya tana dafe bango, Baba
yakama hannunta gwanin ban tausayi ya jinginata a bangon wajen yaci bari nakawo
miki kujera, kujera ya dauko yasamata abayin sannan ya shigar da ita yarufo mata
kofa, bata taba sani ana irin ciwon kan nan aduniya ba, kowani motsi tayi sai kan
ya amsa, tadan jima tabude kofan Baba na jiranta, brush yabata daya koma daki
yadauko mata tayi yariketa yakai daki ya zaunar kan gado, Allah sarki da kanshi
yabude sip yazaro mata yar doguwan rigan da yagani na atampa green, ya ijiye mata
kusada ita, tabishi da kallo yanda yake dingisawa yadauko mata mayyukanta yakawo
gadon ya ijiye duka kusada ita murya chan kasa yace “sa kaya ganinan zuwa” yawuce
yafita, da kyar ta tashi tadauko su pad, pant bra tashiga shiryawa ahankali tasaka
green atampan da Baba yadauko, dogon riga very simple yet stylish dinki dan har
collar gareshi rigan, ta zauna ahankali kome zatayi kaman kanta zai fadi, dan
karamin gyalenta green ta dauka ta yafa tasake kwanciya agadon Baba yashigo da
shayi a hannu yazo gadon yazauna kusada ita yace “zoki sha muje” hannu tadagamai
alamun bazata iyasha ba, tana lumshe idanu saikuma dan gajeren bacci yayi gaba da
ita wuraren 7 ta farka, jikinta har kyarma yake sabida zazzabi kaman ana tsinka
hanjin cikin jikinta, idanunta sunyi jajir, gyalen tasake dauka tayafa dan bazata
iya daurin dankwali ba ta lallaba ta mike tana daukan wayanta da handbag da car key
a hannu tasaka flat shoe black tafito, Baba na compound tafito yamike dasauri
yataho da sauri yana kallonta yace “kin tashi” dan murmushin karfin hali tamai tace
“bari naje asibitin su adubani” Baba yace “zaki iya tuki kuwa da ciwon kan nan”?
Murya cha kasa tace “zan iya Baba karka damu” har mota yarakata ganin hankalinshi
bai kwanta ba da fitan ita kadai yasa ahankali tace “Baba ko Ni’ima zata iya dawo
dani kazauna kaji” gyadamata kai yayi ya maida mata kofan yarufe ta tada motan taja
Baba yabi motan da kallo.

Ahankali take tukin, da kyar take iya bude idanu har jiri jiri take gani amman
sabida karfin hali haka tashiga hanya jikinta kaman wuta, ko kadan bata gudu sosai
cus jiri take gani, har layi take, hospital nasu na yan sanda takeso taje tunda
Ni’ima tace tadaina zuwa hospital nasu wanda shine hospital datake using idan
batada lpy, sunkai wajen traffic light na zone 3 ta tsaya tana jiran yakai turn
nasu tawuce, dan tsayawan kawai yasa taga idanunta sun fara ganin duhu, kawai
idanunta suka fara kukkullewa suna firfir, internally taji kaman an kunna wani
engine na vibration a jikinta, kawai jikinta yafara rawan da bata iya controlling
tana fisfisgewa tafara convulsing.
Bakin rigiman Noor yasa yau yatashi da wuri cus tace shizai kaita school, tunda
suka shiga motan nan surutu takemai, ganin an kirashi yafara waya yasa ta barshi
tawuce window tamike tsaye tana kallon hanya ganin sun tsaya chak, motan dake next
to them a layi yar corolla data tsufa ba irin tasu ba ta kalla, ihu tayi tace “Dady
loook someone is sick, Dady someone is shaking, I think is Fairy Angel Anty,
Daddy!” Yarinyar tai ihu dayasa Khaleel yadan dakatar da wayan dayake yazo wajen
yace “Princess menene”? Leko da kanshi yayi shima idununshi suka sauka kan Hawwa
dake convulsing acikin mota ita kadai kanta na karkacewa yawu nabin gefen bakinta,
daidai tawani mike ta sandare ta danna tootle motanta yayi gaba yana arnen gudu
jikake karakakakakap!!!! Motanta yana dukan motocin dake gabanta with full speed…
Dawani irin sauri Khaleel yabude bayan motan yafito yanabin motanta da gudun bala’i
kaman bashiba acikin traffic din nan some people ma nafitowa dan some people anga
Hawwa na convulsing, every gudu da Khaleel yake he’s telling her in his mind don’t
die! Don’t die! Saida motanta yahada 5good cars suna gudu saida sukakai jikin wani
trailer ne akai gwarap!!! Dole motocin suka tsaya hakama nata ya tsaya but still
pushing nata keyi sabida kafanta, glass na gaban motanta ya tarwatse kwasha kwasha
kanta na jini hannayenta na jini, lafiyayyen accident Hawwa ta hada, Khaleel
yafara reaching wajen motanta yana zuwa wajen motan nata dake hayaki sosai yashiga
budewa jama’a nataruwa ana tayashi budewa ana zuwa wajen sauran motocin yana
kallonta yana kokarin bude motan yanda har airbag na motan yafito yatareta tagaba,
bude motan yayi nasaran yi yashigo jini nabin hannuwanta da goshinta ga some
kwalabe ajikinta, ya zare sitbelt dinta, Hawwa tafado jikinshi tana convulsing
kumfa nafitowa ta gefen bakinta da yawu, jini nabin gefen goshinta, dasauri Khaleel
yasa hannunshi yariketa, yakai hannunshi ya zare kafafunta daga tootle flat
slippers nata nafita daga kafafun, lips nata na jini sabida yanda take biting nasu
zata cigaba dasauri Khaleel yakai hannunshi yasa abakinta ta shiga tattaunewa tana
datse hakoran akansu, daidai Salman da bodyguards nashi da mopol dinshi rikeda
bindigoginsu sunzo akahau kallonsu jama’a while ana ciro sauran mutanen da
Alhamdulillah babu wanda ya mutu saidai ciwo, rike Hawwa yayi gam ajikinshi yace
“Salman pay for all damages she caused, I’m taking her to the hospital!”.
[9/20, 8:00 AM] Halima KW: 💫GARGADAN SO💫


✍🏻M SHAKUR

3️⃣
1️⃣
EPISODE 3️⃣1️⃣
KUNSAN ME AKE NUFI DA INTIMACY CLASS?
CLASS NE DAYA KUNSHI KOYARDA ABUBUWAN YAKAMATA KOWACE MATAN AURE DA AMARE YAKAMATA
SU SANI, TUNDAGA KAN MENENE SHI SADUWA DA IYALI, YA AKE SARRAFA MIJI A GADO, YA AKE
KULA DA MIJI, YAZAKI ZAMA GWANA KIYI FINCINKAU CIKIN MATAN SA🥰
A INTIMACY CLASS BABU KALAN ABINDA BAZAKI KOYABA DAN HAKA JOIN US TODAY WITH JUST
5K SHEKARA DAYA NE CLASS DIN.
MAKESURE KINADA TELEGRAM KAFIN KIBIYA
CHAT ME UP IDAN KINASON SHIGA WANNAN CLASS MAI TARIN FA’IDA

wa.me/+2347012181461

3️⃣
1️⃣
EPISODE 3️⃣1️⃣


Wucewa yayi two bodyguards na binshi abaya daya rike da jaka da wayan Hawwa da
Salman yabasu su biyoshi, dayan babu komi a hannunshi, suna zuwa wajen rolls Royce
dinshi suka budemai baya shiga ciki yayi yana rike Hawwa ajikinshi Noor tafashe da
kuka tana kallon yanda jikin Hawwa ke fizgewa, Khaleel yace “sauke glass na motan
kasa she need breeze” saukewa yayi, driver yayi kwana kawai suka fara gudu a lane
din kafin su sami uturn su dauki wani hanya, hannun dogon long sleeve dinshi
Khaleel yakai bakinta gently ya goge yawun dake fitowa daga bakinta yana kallonta
damuwa sosai akan fuskanshi kaman zai kirata da idanu yace ta farka ta farka
tsabagen yanda yake kallonta, Noor na kallonsu tace “she’s biting your hand Dady”
murya chan kasa yana kallon Hawwan dake jikinshi yace “she’s sick that’s why”
dasauri Noor tace “Dady I love her alot can I take her pain away?” Shiru yayi yana
kallon fuskan Hawwan yace “pray for her” yanda Oga yace aje hospital yasa driver
yakaisu hospital din Excellency daya gina, hamshakin hospital ne, kallon Hawwa
Khaleel yake bayako kyafta idanu, suna parking ana zuwa, karbanta akai daga
jikinshi sukai ciki da ita.

Sauka yayi daga motan yabama bodyguard nashi hannu alamun yabashi wayan da handbag
din Hawwa ya karba yace “drop Noor a school” yakalli Noor saikuma ya matso ya manna
mata kiss a goshi ahankali tace “Dady will my FAA be fine?” Gyadamata kai yayi yace
“she can fight! She will fight the sickness trust me” washe baki Noor tayi tace “My
FAA is very strong right Dady” gyadamata kai yayi, ahankali tace “Dady please stay
with her don’t fight like that day at super market” shiru yayi saikuma yace “you
talk too much go to school” yarufe mata kofan yawuce yashiga cikin hospital din
zuwa dakin emergency da aka kwantar da Hawwa, wayanta dake hannunshi ne yashiga
ringing dasauri yadaga yaga suna Baba, jimmm yayi he remembered Salman yagayamai
mutumin baida kafa he’s crippled that means he’s a sick old man idan yatadamai
hankali fa? No! Yafadi ahankali.
Yana tsaye awajen rike da wayan harya katse, daidai Nurse tazo wajen da form a
hannu ta mikamai tace “Sir can you fill the form or you have to call her family”
sabida yagaya musu hatsari tayi yakawota, paper yakalla da nurse din kaman wanda
baiso yayi magana yace “I will call the family”, sannan yadanna screen na wayanta
ganin babu key yasa yashiga call log nata number daya gani da Ammi yayi dialing
ringing daya Ammi tadaga tace “Hawwa na kin dena damuwan ko” shiru Khaleel yayi
baisan yanda ake communication da normal mutane ba sai masu kudi yan league nashi
muryan matan is so calm, “Hello Hawwa” Ammi tasake magana, dan gyaran murya Khaleel
yayi kaman wanda aka bama big task adan hankali yace “she just had an accident
Ma’am she’s in the hospital they’re call for her family” “Innalillahi wa innailaihi
raji’un, Hawwa tai accident, tana ina kace? Wai Hawwa na? Jidda ake magana?”


Dan sosakai Khaleel yayi yajuya kozaiga security nashi yabasu wayan suyi yatuna
yasasu sukai Noor school, murya yar kadan kaman wani bawan Allah yace “yes Ma’am”
sai kawai yaji Ammi tafashe da kuka sosai dasauri yacire wayan daga kunnenshi yana
dan yatsine fuska irin mehaka takeyi saikuma yaji muryan namiji Babba na Hello
Hello maida wayan yayi kunnenshi yace “yes” Baffa yace “bawan Allah awani hospital
take? Ya condition nata yake, idanunta biyu ne kahada mu da ita muyi magana” kai
tsaye Khaleel yace “she’s very sick, she’s unconscio…..” ai kafin yakarasa maganan
yaji kukan mutane dayawa, Baffa yace “ya sunan asibitin”? Ahankali Khaleel yace
“Leadway” “to mungode gamunan zuwa, mu muna zaria zankira Babanta yanzu zai taho”
Baba na zaune a kofar gida yaga number Ammi na kiranshi kin dauka yayi chan saiga
number mijinta Baffa hakan yasa yadauka yana kokarin mai sallama Baffa yace “Malam
yanzun nan aka kiramu da number Hawwa” faduwa gaban Baba yayi sosai bana wasaba
yace “Hawwa, Hawwa? Batajin dadi ai taje asibitin su Ni’ima” Baffa yace “wanda
yakiramu yace tayi hatsari amman ka kwantar da hankalinka tana asibitin Leadway nan
aka kaita katashi kaje ana neman yan uwanta na jini badai musan me ake ciki ba”
salati Baba yafara yana sallallami baima tsaya yakarajin wani bayani da Baffa
keyiba da sauri yamike yakoma ciki yana salati kaman wanda ya haukace duka
kudadensa dabaya kashewa ya tattaro yafito yana salati kawai. “Innalillahi wa
Innailaihi Raji’un, Ya Allah Hawwa na, Ya Allah y’ata, marainiyata Ya Allah,
Innalillahi Wa Innailaihi raji’un, Allahuma ajirni fi musibati, Lahaula walaquwata
illabillahil aliyul azeem” salati kawai Baba yake ko kallon Umma dake tambayanshi
lafiya baiyiba yafito luckily saiga keken daya sauke mutane zai juya taresa Baba
yayi yashiga yafadamai sunan asibitin yashiga still salati yake.

A gate na asibitin aka sauke Baba ya shigo baya hayyacinsa dauriya kawai yake irin
na maza da crutches nashi yake dungurawa yana hoping yana shiga yana kallon
asibitin da tunda yazo duniya baitaba ganin asibiti mai kyau irinsa ba yana kara
tsorata yana addu’a Allah yarufa musu asiri, Khaleel na tsaye a reception din yana
waya Baba yashiga kiciniyar turo Glassdoor dakeda karfi da aka rubuta push

15 / 17