Author : Jamila Umar Tanko Category : Romance
su, ta yi murmushi sannan ta amsa sallamar. Ta na so su juyo su gaisa amma sai ta ga sun dauke kai sun qi dubanta sun wuce. Ta ci gaba da duban wayarta, amma sai wasu saqonnan Usman suka dinga shigo wadanda bata gane kan su ba. Ya sauka daga kan hirar da suke yi dazu ya shiga jero mata wasu tambayoyi akan Jalilah.
Kanta ya daure ta tambaya "kamar yaya? Me yasa kake tambaya?"
Ya ce "Ki na saloon din har yanzu? Su Jalilah sun shigo ciki ko? Toh dan Allah kada ki kula su ku yi fada, na san halinki da haquri da kawaici. Ga ni nan zuwa, wannan fadan ba naki ba ne nawa ne. Ba zan bari kowa ya zo ya ci miki mutunci akaina ba. Na kira Murjanatu a waya bata amsa ba.ku na tare ne?"
Ya na ta jero mata tambayoyi ba tare da jira ta bashi amsarsu ba, sai ya sauka ma.
Kafin ta kira shi sai ta ga mata guda uku sun jeru akanta sun tsatstsaya dukka sun kama qugu su na girgiza. Ta daga ido da sauri ta sake sunansu sannan ta gane Jalilah ce da wasu qawayenta limcy da Husny, tantagararrun 'yan duniya basa jin magana. Daman basu san mutuncin kansu ba ma balle na wasu.
Kafin ta ce wani abu text massage ta turawa commissioner of police ta bada adashin in da take ta ce a taho da motar 'yan sanda.
Jalilah ta fara magana cikin gadara ta ce "baiwar Allah! wajenki na zo wannan ne haduwarmu ta farko bai kamata in zo miki da fada ba, na zo da sulhu da kuma gargadi in kin kiyaye shikenan. Amma idan baki kiyaye ba haduwarmu ta biyu ba zata yi kyau ba."
Jalilah ta juya ta kalli Limcy ta ce "qawata kora mata warning."
Limcy ta lumshe ido ta ce "duk wanda ya san Jalilah ya santa da Usman Aliyu (Handsome guy) sun dade tare dan haka Usman na ta ne ita kadai. Ki rabu da shi."
Husny ta karba ta ce "idan an qi ji kuma zamu dauki mataki, babu ruwanmu da ko ke wacece."
Murmushi Mufidah ta yi ta ci gaba da danna wayarta, kamar ba da ita suke yi ba.
Murjanatu Bibi ce ta fito daga ofis dauke da waya a kunnenta, tana magana da Usman da alama ya gigita ta itama. Ashe kuwa da gaske yake, aminiyarta ta gani 'yan daba sun zagaye ta.
Sai ta qaraso da sauri tana fadin "subhanallah! Jalilah lafiya?"
Jalilah ta dafe kai ta ce "kash! Abinda nake ta gudu kenan, ba na so in tare ta a gabanki dan ina jin kunyarki Murjanatu. Amma ki koma gefe wannan maganar ba taki ba ce."
Murjanatu ta ce "ki taba qawata ki ce ba maganata ba ce? Ke ma da gangan kike yi, har kun bani kunya ma wallahi. Akan namiji ku ka zo za ku yi fada? Kin kasa yaqar zuciyarsa ya so ki, kina ganin in kin yaqi wacce yake so za ki ci riba? It's doesn't make sense, haba kada ku ba da ni mana na dauka ma kun waye ashe har yanzu ku na da buhun kai. Ai Usman za ku tara ba Mufidah ba ita ai sai da yayi kneel down ya na roqonta akan ta kula shi ma sannan ta kula shi. Idan ni ce ke Jalilah babu abinda zan yi da Usman tunda duniya gaba daya sun san baya sonki."
Cabdijam sun ji haushin maganar Murjanatu matuqa amma ita ko a jikinta kawai maganarta take yi.
Jalilah ta fusata ta ce "dole mana ki ce haka tunda kawarki ce, bakinki daya, za ku auri abokai."
Murjanatu ta ce " kin san halina ai idan Mufidah bata da gaskiya zan fada amma yanzu ku ne baku da gaskiya. Kuma kada ku sake ku yi min fada a shagona dan baa taba yin fada anan ba. Zan iya daukar mataki a kanku yanzun nan."
Usman ne ya shigo a gigice cikin shiga ta kamala, baqar suit wacce ta yi masa matuqar kyau, shine babban abinda yake qara burge Jalilah kenan, wato idan ta gan shi fari tas sai ya haska baqar rigar, kai amma ya hadu ya na da kyau sosai.
Idanuwansa akan Mufidah, ya hango ta a zaune tana danna wayarta ko kallonsu bata yi, sai ya ji dadi a ransa. Ita ya tunkara yana isowa ya durqusa a gaban ta daf da kunnuwanta yana jero mata tambayoyi, yana bata baki, yana bata hakuri. Ya tabbatar mata ba zai bari wata ta sake ci mata mutunci akansa ba. Zai dauki mataki yanzun nan kuwa.
Kowacce tana tsaye tana ta girgiza, yayin da kaudin muryar Murjanatu ta cika wajen, ta qi yarda kowa yayi magana. Da alama Hausarta ta qare ta juye zuwa turanci. Ta na ta karanto musu shikashikan sanin darajar dan adam da hukuncin cin zarafin mutum.
Usman ya miqe tsaye a fusace ya harari Jalilah ya ce "ta nan kika bullo kuma? Ki na batawa kanki lokaci fa. Kada ki dauka zan bari ki ciwa matata mutunci."
Jalilah ta harare shi ta ce "yanzu da ka ga sakona na ce zan tafi in daki Mufidah a shagon Murjanatu Bibi ai ka yi reply, ga shi ma har ka taso ka taho, saboda zaa taba 'yar gwal. To ko waye ubanta a garin nan sai na dauki mataki akanta. Su ne masu sharia ko? shine ma alqalin-alqalai na qasa gaba daya ko? Ita kuma lauya ce toh zan dake ta in ga uban da zai taba ni."
Wannan karon saukar mari Jalilah ta ji a kuncinta, kafin ta farfado daga duniyar azaba, ta ji an bangaje ta. Murjanatu Bibi ce ta fusata. Lallai akwai banbanci a tsakanin 'yan dabar Nigeria da na America.
Qawayenta suka yunkuro zasu shiga fadan, jiniyar motar 'yan sanda su ka ji abaki get din wajen, suka tsaya kan ka ce kwabo 'yan sanda mata da maza sun bayyana a falon.
Mufidah ta ce "Murjanatu rabu da su na yi magana da commissioner of police ya aiko da 'yan sanda ga su nan zasu tafi da su, ki bar ta kawai.
Idanuwan Jalilah da qawayenta za ka kalla ka ci dariya, ashe ma basu shirya rigimar ba, nash wasa ne.
Jalilah ta kalli Usman a fusace ta ce "yanzu kai sai ka bari a tafi da mu? Duk halascin da yayata ta yi maka, muka daure da duk wani zagi da matarka ta yi mana."
Ta dauko waya ta kira her excellency, ta ji ta akan waya, tana ta waya daga baya ta lura da Usman suke waya.Ya koma gefe yana ta magana.
Usman ya ce "ga Jalilah a shagon Murjanatu Bibi da qawayenta sun zo su na ta rigima. Su na so su daki matar da zan aura, ita kuma ta kirawo motocin 'yan sanda. Ba zai bari a tafi da su ba saboda shima sun yi masa halacci kala-kala musamman da ta sha yi masa haquri akan zagin da matarsa take yi mata. Amma dan Allah ta jawa Jalilah kunne ta bar wajen nan kada ta sake tare Mufidah a hanya. Duk wani laifi da take ganin an yi mata shine yayi mata ba Mufidah ba, dan haka babu ruwanta da Mufidah.
Her excellency ta tabbatar Usman ya fadi gaskiya dan haka ta yi masa godiya ta kashe waya, sannan ta kira Jalilah, sun dade su na ta magana a waya. Usman ya kira Mufidah gefe, yana yi mata bayani akan ta sallami 'yan sanda ba zai so a kama ta ba, saboda mutuncin yayarta.
Nan da nan Mufidah ta yi magana da 'yan sanda suka juya. Jalilah ta na ta kuka wiwi ta fice a fusace, qawayenta na biye da ita a baya suka shiga motarta su ka wuce.
Murjanatu tuni ta koma ofis ta ci gaba da sauraron baqinta, matar wani minister ce take gayyatarsu zuwa Abuja zaa yi bikin 'yarta. Su na son ayi musu kwalliaya da gyaran jikin amarya na tsawon sati biyu, daga Abuja ma zaa dingumo a dawo azare. Miliyoyin kudin da ta caje su kwakwalwa ba zata iya dauka ba, ba ita zata je ba fa yaranta zata aika. A take suka cake mata rabin kudin.
Ita bata da matsala da kowa, bata da lokacin zaman hayaniya akan saurayin da ko aurarsa baa yi ba.
Usman dai ya na zaune kusa da Mufidah, da alama ya fasa komawa wajen aiki, jira yake a gama wankin qafar ya ce gida zasu tafi.
Murjanatu ta fito ta raka baqinta har wajen get sannan ta dawo take tambayarsu wai mafarki ta yi ne ko da gaske ne? Kamar ta ga Jalilah, ta ga 'yan sanda ana rigima, ta ga kamar ana fada."
Su ka kwashe da dariya su dukka, Mufidah ta ce "ke wallahi 'yar rainin hankali ce, har dambe aka yi da ke fa yanzu amma ki ce kin manta."
Murjanatu ta ce "tsabar in nuna musu cewar muna da abin yi ne, bamu da lokacin fada. Haba, Jalilah ta bani haushi kamar wacce bata taba zuwa makaranta ba."
Usman ya kai Mufidah gida ya shaida mata da yamma zai je gidan su Jalilah yana da magana da ita da yayarta, gara a yi musu tsakani. Da farko Mufidah ta ce ya bar maganar amma da ya nuna mata wasu shaidu da ya tanada akanta, ta tabbatar zuwansa na da amfani.
Da yamma ya isa gidan su Jalilah, daman an san shi kai tsaye aka bude masa get ya shiga da motarsa, sannan ya fito ya shige cikin katafaren falon da ya saba shiga. Ya zauna sai masu aiki suka kawo masa ruwa da lemo su na tambayarsa, ya ce a yi masa sallama da Her excellency ta san da zuwana, sai aka ci saa ma mai gidan yana nan tare suka fito. Jalilah ma ta fito duk da bai buqaci ta zo ba.
Maganar da her excellency ta ke ita ce Jalilah tana sonsa da gaske, idan da kara ina laifin ya hada su su biyu din ya aura. In maganar tattalin arziki ne za su bashi komai da komai.
Usman ya gyara zama ya fara magana sai da gaba dayansu suka Girgiza dauka ji abinda yake fada, har da Jalilah kanta. Su ka cika da mamaki suka rasa a inda ya sami wadannan labarun, kuma har da shaida a cikin wayarsa na bidiyoyi, rubutattun saqonni da kuma muryarta.
Na farko Jalilah bazawara ce aurenta uku haihuwarta biyu suka boye masa. Na biyu bata da kamun kai koda yaushe ana ganin a hotel da maza, har ma ya karanto sunayen otal -otal din da kuma mazan da take bi. Sannan ga muryarta da ta tutturawa qawarta tana cewa, ita a tsarinta bata son talaka, bata son mai mata shine matsalar Usman, ba dan komai take son Usman ba illa dai dan kawai yana da kyau, na fita taro ne. Idan ta aure shi ba a matsayin miji mai cikakken iko zata dauke shi ba, a matsayin yaronta zata dinga juya shi, aurenta ba zai hana ta ci gaba da yin harkokinta da wasu mazan ba.
Qawarta tana da saurayi abokinsa komai suka tattauna da qawar ita kuma sai ta turawa abokinsa shima kuma sai ya tura masa.
Ya ce ko saboda mutuncin da suka yi masa da har ya yarda zai aure ta saboda yadda ya ga tana sonsa, tana ta binsa ta takura, ya dauka da gaske take qaunarsa. Ya yi yunqurin ya aure ta amma wadannan maganganun suka bullo.
Ya ce "a matsayinku idan ni qaninku ne wacce shawara za ku bani? Ku yi mana shari'a."
Her excellency ta yi shiru ta dafe kai ta kasa magana, shi kuwa His excellency albarka ya dinga shi wa Usman ya ce ya je ya auri 'yar mutunci, yayi gaskiya. Yayin da Jalilah ta yi wuqi-wuqi da ido ta rasa abinda zata ce, ga dai muryarta nan da rubutunta har da bidiyoyinta a club, abin ba kyan gani dai.
Har Usman yayi musu sallama ya fita aka rasa wanda zai qara yin magana a cikinsu.
Sai ya ji shi saqayau kamar an cire masa qaya, ya fito yana murna.
Ya iso gida da daddare sai ya iske su a tare, ya bawa Mufidah da Murjanatu labari, su ka sha mamaki sannan su ka yi farin ciki. Tabbas an kashe bakin Jalilah sai mu ga yadda zata je ta yi fada kuma.
BIKI YA YI BIKI
Sai da aka yi mako guda ana shahalin biki kafin ranar daurin aure, wasu ace su ango su zo wasu ace banda angwaye. Su dai duk yadda aka yi da su haka suke bi. Kayan sakawa kawai ake miqa musu su saka sannan a saka su a gaba a tafi.
'Yan uwan Usman mata da maza sun hallara, gidan Mufidah da gidansa aka sauke su, da mata masu aiki da zasu dinga kula da su da dafa musu abinci.
Otal-otal na Bauchi gaba daya babu dakuna sun cika da manyan baqi. Sai a yanzu ma suka san cewa wannan tangamemen otal din da ake ji dashi mai hawa goma na mahaifin Murjanatu Bibi ne, dan haka babu kowa a ciki sai bakinsu.
Mahaifin Mufidah da iyalansa da tawagarsa kakaf sun iso Bauchi. Mahaifan Murjanatu Bibi da 'yan gidansu da wasu daga cikin qawayenta mata da abokanta maza turawa daga america sun hallara.
Mahaifiyar Mufidah da yayanta Umar da matarsa da yaransa, qannen Mufidah na can da suke uwa daya da danginta kakaf, tawagarta su ma sun iso an ware musu dakuna a hotel da dukka abinda zasu nema akwai a hotel din Imam malik ya biya.
Imam malik ma da iyalansa da abokansa dukka sun shigo Bauchi su na su hotel din.
Mutanen gari sun ga taron da basu taba ganin irinsu ba, duk inda ka waiga a garin gilmawar manyan baqi ne cikin galla-gallan motoci.
Usman da Dr.Isa bayin Allah sun ga abin da ya fi karfin tunaninsu saboda tun kafin a zo ranar daurin aure motoci da maqudan kudade ake bawa anylgwaye da amare.
Ranar daurin aure kuwa sai Usman da Dr.Isa suka kusa sumewa dan mamaki. Motocin miliyoyin kudi gwamnoni, 'yan majalissu, sanatoci da sarakuna suke ta miqawa amare, wasu lokutan kuma a hada guda bibbiyu ace na angwaye da amare ne. Sai kiran miliyoyin kudi ake ana cewa kyauta ne daga wajen gwamna jihad kaza ya ce a rabawa amare da angwaye..
Dr.Isa ya hango kansa bayan biki har ya ajiye aiki ya bude na sa asibitin, yayin da Usman ya hango shi ya je ya gama biyan banki bashinsu ya bar aiki, ya bude kanfanin siyar da motoci. Daman irin kasuwancin da yake burin yi kenan a rayuwarsa.
Social media ta dauka, gidajen talabijin da radiyoyi su ma su na ta yadawa. Mutane su na ta zuba sharhi akan amarya da angon da suka fi yin kyau kuma suka fi dacewa. Da yawa an ce Mufidah da Usman sun fi dacewa, wani lokaci kuma ace Dr.isa da Murjanatu sun fi yin kyau a wasu events din. Labarin bikin nan baa garin Bauchi kadai aka tsaya ba dukka Nigeria, sai yada hotunan ake. Daga nan suka gangara zuwa wasu qarshen, ana ta yada hotunan, dan sun yi matuqar yin kyau, biki yayi tsari an kashe kudi ba dan kadan ba.
Angwaye da amare su na zaune akan manyan kujeru wato (high table) ana cikin gudanar da shagulgulan biki. Kamar daga sama basu ga shigowarta ba sai suka ga Fatiti a gabansu.
Yadda ta tsaya ta na kallon Usman ta juya ta kalli Mufidah sai da su dukka suka ji gabansu ya fadi. Fatiti ta yi kyau kamar ba ita ba, kayan jikinta da yadda aka yi mata kwalliya da dauri kamar wata amarya.
Mufidah ta kalli Usman shima ya kalle ta suka juya suka kalli Fatiti, su ka rasa ganewa shin alkhairi ne ya kawo ta ko kuma fada? Dan dai bata yin faraa sannan sai baza ido take kamar mai neman makamin da zata yi bugu.
Da MC ya gane Uwar gidan Usman ta iso sai ya fara sanarwa, yayin da hankulan kowa ya yi kansu, ana so a ga yadda zata kaya.
Maganar zafin kishin Fatiti kuwa ba boyayye ba ne, da yawa sun san labarinta dan haka duk wanda ya ga Fatiti a wajen nan sai ya ji