KISHIN BALBAL BOOK 3 HAUSA NOVELS BY JAMILA UMAR TANKO.doc

Author :  Jamila Umar Tanko Category :  Romance

Chapter   8 / 10

21K to 24K   out of 28.9K words

ya wanke Usman an tabbatar miji na gari ne, wanda kowacce uwa take jin ina 'yar ta ya aura.
Daga nan ta fara yiwa kanta karatun ta nutsu, ita kadai a zaune a daki take lissafi. Ta ga babu ribar da ta ci a cikin baqin kishin nan sai ma asara.
Fatiti ta na hawaye wayarta ta lalubo ta danno Safiya, dan ita kadai ce a duniyar nan take gane yarenta. Safiya ta koma garinsu Misau gidan iyayenta, ta yi yaji akan auren da zai shima. Abin mamaki Dakta ya qi zuwa biko, idan iyaye suka kira shi, sai ya ce aiki yayi yawa zai shigo wani satin. Idan sati ya zagayo sai ya sake dauko wani uzurin.
Safiya ta fayyace mata cewar Murjanatu Bibi zai aura, ya yarda zata zauna a gidanta. Wani tafkeken gida mai kama da aljanna duniya a cikin GRA din garin Bauchi, bayan haka ta sake tafka gida a Abuja idan Bauchi ta yi zafi su tafi Abuja su huta.
Ita kuma Safiya ya ce zai yi sauri ya gama ginin da yake yi ta koma, gida ne mai dauke da falo biyu da dakuna uku. Shine ta ce bata yarda ba, ta yi yaji yanzu ga yaji nan ya kusa komawa saki. Addua kawai take yi kada ya sake ta dan Murjanatu Bibi ta janye hankalinsa gaba daya da na iyayensa da sauran danginsa, duk su na bayanta. Ta zo ta lullube su da ruwan kudi, ga kirki, ga hira wasa da dariya kowa nata ne, ga ladabi. Sabanin irin ukuba da baqin hali da rowa da Sharrin da Safiya ta dinga hadawa dangin mijin basu isa su zo gidan idanuwansa ba.
Safiya ta na magana tana kuka, Fatiti na kuka, dan an riga an yi musu nisa sun makaro, sun rasa ta in da za su kamo bakin zaren. Sai a yanzu suka yi nadamar qin komawa karatun da suka yi da yanzu sun fara aiki su ma su na samun na kansu su huta da wulaqanci. Yanzu komai sai sun jira miji yayi musu basu da komai, basu iya sanaa ba kuma.
Ga mata can irin su Murjanatu da Mufidah sun nemi na kansu, mazan ma kansu shakkarsu suke.
Sai yanzu Fatiti ta sami labarin cewa amma Usman ya qi yarda Mufidah ta zauna a katafaren gidan da mahaifinta ya bata shima a Bauchi da Abuja. Anyi-anyi ya ce ba zai zauna a gidan mace ba sai dai ya yarda zai kama hayar babban gida har Allah Ya hore masa ya yi mata gini.
Fatiti ta san halinsa dan haka bata yi musu ba, ta san ba zai taba yarda ya zauna a gidan mace ba kuma ta san ba zasu iya juya shi ba dan su na da kudi.
Duk duniya Fatiti ce ke yi masa abinda take yi masa, yake yin hakuri bai rabu da ita ba, ta san da haka dan shi baya daukar raini yanzu zai fita harkar mutum kuma idan ya barka ya barka har abada.
Biki ya qarato Usman ya kai kudin komai gidan su Mufidah, har da sadakinsa naira dubu dari sannan da kudin gaisuwa naira dubu dari. An saka rana watanni uku, ba haka sauran suka so ba sai dan kawai Usman ya dage ya ce a bashi lokaci bai gama shiri ba kuma ya na so a jira har sai matarsa ta haihu dan ta kusa. Sannan ya na so ya hada lefe ga sauran hidimomin aure.
Ya cike form din neman bashin banki (loan). Ya zauna da Mufidah sun yi maganar kayan lefe, ta ce duk yadda Allah Ya hore masa ko ya hada mata da kansa ko ya bata kudin. Sannan a hidimar biki ya ce zai hadawa abokansa reception na bayan daurin aure, kuma zai bata kudin walima ta yi ita da qawayenta abinda zai iya yi kenan. Danginsa mata da maza zasu zo Bauchi Ayi bikin su na nan, su ma ba zasu wuce su ashirin ba.
Bikin nan kuwa tunda aka hada da na Murjanatu Bibi an san zaa sha hidima ba kadan ba. Dan haka wancan shirin na su ne shi dai ya fadi yadda zai iya haka ma Dakta ya fadawa Murjanatu, amma ta san wannan tsarin Ustaz Usman ne.
Usman yana ta shawarwari a ransa ko nawa ya kamata ya bawa Mufidah yadda ba zai takura ba, kuma bai takure ta ba. Miliyan hudu ya bata sannan ya kama mata gidan haya qato sabo fil mai dauke da dakuna hudu da falo biyu da babbar farfajiya akan naira miliyan daya.
Ya kashewa Fatiti naira miliyan daya aka hada mata lefe itama na fadar kishiya, akwatuna hudu yayi mata hade da kayan jaririya dukka ya hada sannan ya damqa mata naira dubu dari biyar a hannunta na hidimar biki da suna da dinkuna.
Fatiti sai ta ji gaba daya duniyar ta zame mata sabuwa kamar a mafarki take jinta. Tunda aure ya zama dole ta kwantar da hankalinta kishin ya sauko. Ta na ta murna da wadannan abin arziki, ta yi ta godiya. Yayi mata alqawari zai kama mata hayar babban gida a unguwa mai kyau bayan an gama hidimar bikin.
Wata na zagayowa Allah Ya sauke Fatiti lafiya ta sami 'ya macen da ta dade tana jira. Kyakykyawa kuwa fara tas kamar 'yar larabawa tafi kowa kyau da fari a gidan. Abin mamaki da Usman ya tambaye ta sunan da take so a sakawa 'yar sai ta ce a saka mata suna Mufidah.
Allah mai iko Usman ya tsaya yana kallonta kallo na rashin yarda da mamaki. Ta sake maimaita masa tana so ya saka mata sunan Mufidah. Ya ce ta dauko waya ta kira mahaifinsa da mahaifinta su ji daga bakinta dan ba zai iya isar da saqon nan ba dan saqon nan mai girma ne kwarai.
Ta san abinda yake nufi kawai bai yarda da ita ba ne, ya kasa yarda cewar ta canja yanzu. Ga ni yake wani sharri take so ta kulla masa dan a fara zarginsa cewa tun yanzu ya fara rashin adalci.
Abin mamaki sai kuwa Fatiti ta dauki waya ta kira su, iyayenta da iyayensa har ma da iyayensu mata ta sanar musu ga sunan da ke so a sakawa jaririya. Kowa ya yi farin ciki game da mamaki, aka hada mata da manya-manyan albarka.
Usman ya rasa kalmar da zai furta mata dan murna, kawai sai ya jawo ta qirjinsa ya rungumenta. Ya rada mata a kunne "Allah Ya yi miki albarka na gode. I love you so much. Rayuwata ta zama empty a lokacin da bama tare."
Su dukka hawayen farin ciki suke yi.
Murjanatu Bibi da Mufidah ne a zaune daidai wannan lokacin a falon Murjanatu, sun saka hoton Baby a waya suna ta kallo su na ta sha'awarta. Gaba daya fata suke Allah Ya basu irinta nan da wata shekara. Yarinyar mai kyau da ita kamar su hadiye ta. Su ka kira Usman a waya, ya dauka ba tare da fargabar cewa a gaban Fatiti yake ba,ya tabbatar babu matsala.
Su na masu taya shi murna hade da yabon kyawun baby sannan suka dora da yi mata addu'a Allah Ya raya ya akan sunna. Shi kuma Ya fada musu wani labari da ya basu mamaki matuqa ya daure musu kai har suka shiga kokonto.
Ya ce " kun san daddadan sunan da mahaifiyarta ta zabar mata kuwa?"
Abinda ya fara zuwa zuciyoyinsu shine zaa sakawa yarinya mai Zaa sunan qauyawa tunda aka ce daga wajen Fatiti ne sai yadda Allah Ya yi. Gabansu ya dinga faduwa kafin su ji sunan.
Wai ya yi dariya ya ce " ta saka mata suna MUFIDAH."
Ya ji sun kwashe da dariya su dukka.
Murjanatu ta ce "ka rainawa amaryarka hankali ma wallahi. To ke Mufidah kin san matsayinki yanzu."
Mufidah ta langwabe kai ta ce " shikenan tunda na zama abar zolaya a wajenka gashi har ta fara yi min gori."
Usman ya yi dariya ya ce "wallahi da gaske nake ga ni ma tare da Fatiti, ta fada muku da kanta."
Har ya miqawa Fatiti waya ta yi sallama suka gaisawa basu yarda Fatiti ba ce sai daga baya suka gane muryar.
Ta ce "da gaske yake na saka mata suna Mufidah dan kawai ina son ta zama takwararki kuma in lallashe ki akan abubuwan da na yi miki a baya, ki yafe min."
Allah Ya bamu zaman lafiya. Ina yi muku fatan alkhairi. "
Gaba daya suka yi shiru su na ta kallon-kallo kowa baki a bude daga Murjanatu har Mufidah.
Can Mufidah ta sharce hawaye ta ce " Allah sarki Fatiti har kin saka ni hawaye kin yi min babbar kyauta wacce ban taba zato ba. Na gode, na gode Allah Ya saka miki da gidan Aljanna, Ya raya mana Mufidah akan sunna. Na yafe miki, wallahi komai ya wuce. Nima ki yafe min dan ba ke kadai kika baqanta min ba, nima na baqanta miki musamman da Allah Ya qaddaro zan auri mijinki. ina fatan hakan ya zame mana Rahma da alkhairi."
Fatiti ta matse hawaye ta ce Amin. Na gode."
Su ka kashe waya, Usman ya jawo ta jikinsa ya ce "menene abin kuka? ku dukka ku na ta kuka. Abin farin ciki ne musamman gare ni da ku ka hada kanku tun yanzu."
Fatiti ta sharce hawaye ta ce "da na ji ta fara kuka ne ta saka ni kukan nima. Maganar gaskiya Mufidah tana da kirki ni zan fada maka halinta, babu matar da a duniya ta taba son yarana irin son da Mufidah take yi musu, su ma kuma haka su na sonta soaai. Dan ada ko abincinta bata iya ci ita kadai sai ta leqo ta kira su, sai su je su ci tare. Sannan ita ta taimake ni a lokacin da Godwin ya zo da maza har cikin gidana zai yi min wulaqanci. Wallahi duk boyewa na yi dan kada ka sani ne dai kawai kada ka ji ka na sonta. Ta dinga zayyano wasu abubuwa na kirki da taimako da nuna qauna da Mufidah take yi mata da yaranta amma ta boye masa, sai sharri da gagarumar tsana da ta dasa a tsakaninsu. Amma yanzu da Allah Ya wanke Mufidah da kanSa gashi tana ta fada da kanta.
Allah Abin tsoro mai kowa mai komai. Komai za ka yi a duniya ka yi dan Allah, haka ka damqawa Allah dukkan lamuranka ka jira sakamako.
Usman ya yi shiru yana ta tunani mai zurfi yana jin zafin abubuwan da ya faru tsakaninsa da Mufidah. Ya dinga tsanar ta yana fada mata baqaqen maganganu yana saka ta kuka, ashe ma abar tausayi ce bata da kowa a kusa da ita, ga ciwo ya na damunta. Kwalla ta cika masa ido dan tausayin Mufidah, wani tsananin qaunarta ce ta qaru a zuciyarta ya qudiri aniyyar sai ya saka ta farin cikin da bata taba ji ba idan ya aure ta.
Ya dubi Fatiti cike da takaici, amma ya yi mata uzuri ya ce "Allah Ya na son masu yawan tuba, Allah mai karbar tuba ne. Kada ki damu ta ce ta yafe miki ke ma kuma Allah Ya so ki da rahma da har kika farga kika nemi yafiyarta kuma kika bata tukuici da wata kyautar da ta faranta mata rai. Tabbas wannan tsanar gaba dayanku ta fita daga zuciyoyinku. Alhamdulullah."
Kafin ranar suna saqon Mufidah ya iso zuwa hannun Fatiti da Usman. Danjuma direba ta bawa ya kawo har qofar gidan Usman, ya damqa masa ya ce in ji Mufidah.
Akwatuna guda 2 ne manya a shaqe da kayan jaririya har da na uwar ma da uban.Kaya ne na qasar waje masu laushin auduga. Wata qaramar jaka suka bude, masha Allah gwala-gwalan jaririya ne 'yankunnaye kala-kala da zobe mai hade da abin hannu.
Fatiti ta tabbatar zuwan Mufidah arziqi ne a gare su gaba daya. Sai murna take ta na ta bugawa 'yan gida waya, gaba daya aka dingumo aka taho kallo. Kowa ya na ta yi musu addu'oi kyawawa .
Fatiti da Usman suka kira Mufidah a waya su na ta godiya da nuna mamaki akan yadda ta gwangwaje su haka. Ta ce babu komai kadan ne ma, sai nan gaba ita da takwararta mutu ka raba.
Ragunan suna da yawa Usman ya yanka dan nuna farin cikinsa gami da godiya ga Allah (S W A) da ya bashi 'ya mace da suka dade su na nema. Ya ce kowa ya zo ya ci abinci sadaka, aka dafa kala-kala da abubuwan sha masha Allah.
Bayan suna da kwanaki biyu ya taho Bauchi, Fatiti ta hada masa kayan suna leda leda aka kawowa Mufidah.
Mufidah ta dinga murna dan ta na son cin naman suna akwai dadi, danma Murjanatu Bibi ta kwashe da yawa.
Yanzu kuma Usman Usman ya waiwayo maganar biki gadan-gadan, Lokaci ya qarato. Ana ta sake gyara gidan amarya duk da ma sabo ne amma ana qara qalqale shi.
A bangaren suturun da zai saka a wajen hidimar biki kuwa, kudin ya damqawa Murjanatu ya ce ta yi musu yadda take so.
Haka ma Dr.Isa ya yi, bayan kudin lefenta da ya bata ya bata kudin da zata dinka masa kayan fitar biki dan ba zasu iya da tsarin Murjanatu ba, qaqale ya yi mata yawa.
Amare ne suka tsara komai da suke so a gidajensu. Daman sun kawo komai masu daga qasar waje a kwalayensu, dan haka bayanin yaya kyawu da tsari na gidajen ma b'ata lokaci ne.
Babu yadda zaa yi ka shiga gidajen nan baka dauka a turai kake ba. Sai dai idan ka fito waje ka fara cin karo da bola da kwata sannan za ka tuna ashe a qasa mai daraja kake wato Nigeria.
Labarin auren Usman da Mufidah, da kuma na Dr.isa da Murjanatu ya karade ciki da wajen garin Bauchi. Dan haka Jalilah ta sami labarin komai sai ta hadu da mummunan baccin rai, ta ji zuciyarta na ci da wutar kishin bal-bal kamar zata qone. Babbar matsalar kuma ga Usman baya daukar wayarta, ko ta bi shi ofis baya yarda ya ganta, daman kuma ta tabbatar ba zata gan shi a gidansa ko a hanya ba.
Babu wacce ta tsana a duniya a yanzu irin Mufidah, dan haka ta yanke hukunci zata je ta same ta gaba da gaba ta ja mata kunne akan ta rabu da Usman dan ta riga ta.
Jalilah tana jin nauyin Murjanatu Bibi saboda su na da kyakykywar alaqa da ita, su na girmama juna. Dan haka ta yi ta bibiya ko zata ga Mufidah ita kadai ba tare da Murjanatu ba, amma ina kullum su na tare saboda shirye-shiryen bikinsu. Ta sha zuwa wajen aikin Mufidah sai a ce mata bata shigo ba. Ta sami lambar wayarta Murjanatu amma ko ta kira bata shiga, saboda ta saka wayar a tsarin da sai dai ta kira ka kai ba za ka iya kiranta ba, in dai ba ita da kanta ta zabi ka kira ta ba sannan ta bude ka ba.
Ga biki yana ta qaratowa, tabbas in Jalilah bata yi da gaske ba zaa daura tana can ta na walagigi, dan haka ta yanke shawara ta je ta tare ta kawai ko a gaban Murjanatu ne ayi wacce zaa yi.
A katafaren gidan gyara da kwalliyar mata 'yan kwalisa na Murjanatu, Jalilah da qawayenta guda biyu su ka zo neman Mufidah. Sun kuwa ci saa Mufidah na nan, suka iske ta a zaune akan wata luntumemiyar kujera ana yi mata wankin qafa (pedicure). An jiqa mata qafar a ruwa, a cikin wani baho na alfarma wanda ake jonawa da lantarki.
Su ka shigo a fusace kowa ya gansu ya san ba alkhairi ne ya kawo su ba. Sun yi sallama a ciki-ciki, su na tafe su na ta yatsuna kamar dinga kashi.
Mufidah bata gane su ba ma hankalinta na kan wayarta, tana ta chating da abin qaunarta Usman. Ya na ofis ya yi mata hoto ya turo ya ce gashi yana fama da aiki. Ta yi masa hoton qafarta ta tura masa ta ce ga ta ana wanke mata qafa.
Ya ce "wow wannan qafar mai kyau mai laushi ake sake wanke ta kuma? kada fa jini ya fara kwaranya dan kyau."
Ta ci gaba da tura masa dadadan kalamai na kwantar da hankali dan ya samu nutsuwa yayi aiki cikin farin ciki.
Sallamar su ce ta katse ta daga ido ta dube

8 / 10