KISHIN BALBAL BOOK 3 HAUSA NOVELS BY JAMILA UMAR TANKO.doc

Author :  Jamila Umar Tanko Category :  Romance

Chapter   4 / 10

9K to 12K   out of 28.9K words

bata ma zo ba basu san labarin komai ba ma dan haka ya gaishe su ya fita. Ya je gidan iyayensa nan ma bata nan, su ma ya gaisa da su ya fita. Gidajen su Aunty Rabi ya je da duk inda yake tunanin zata iya zuwa a danginsa da danginta amma ba ta nan sai ya ji hankalinsa ya tashi amma ya fi zaton tana gidan daya daga cikin qawayenta da suka fita daga gidansa dazu.
Da ya zazzagaya gidaje biyu ana ukun sai ya same ta a gidan Samira Abba, daman mijinta abokinsa ne dan haka da kansa ya shiga gidan. Ya ganta a gidan tana zaune yayi lallashin duniyar nan akan ta zo su tafi gida zai yi mata bayani, ta ce ba zata tafi ba. Sai ya rabu da ita ya koma gida, ya iske yara sun ci abinci sun qoshi sun yi bacci.
Kwana yayi yana ta juyi akan gado bai rintsa ba, zuciyatsa ta na ta aiyana masa abubuwa da yawa. Ya gaji da halin Fatiti yayi duk haqurin da zai yi amma kullum abu sai qaruwa yake.
Gari ya waye ya tashi ya taya su Amal yiwa yara wanka da shirya su, ya basu abinci da alewa sannan suka dunguma suka tafi gidan iyayensa su dukka sai shi kadai aka bari a gidan ya rufe qofa ya kwanta dan ana binsa bashin baccin da bai yi ba. Ya na ta bacci har rana, dan ma wayarsa ce take ta ruri, a dole ya tashi ya dauka ya duba ya ga Dr.isah ne.
Wani mugun labari aka fada masa, bai tashi jin labarin Fatiti ba sai kawai ya jiyo ta a Bauchi a gidan Mufidah. Aka saka masa muryarta tana ta zage-zage.
Kuma aka shaida masa cewar ta farfasawa Mufidah gilashin motarta kwatsa -kwatsa amma Mufidah tana cikin gidanta bata fito sun yi dambe ba.
Dr.Isa ne yake ta nishi saboda damben riqe sanduna da duwatsun da take take jifa. Tanimu ma ya kira shi ya shaida masa gidansu ya zama dajin Sambisa.
Usman ya dafe kai yana ta kiran " Innalilahi wa inna ilaihi rajuun."
Ba tare da ya san abinda zai ce ba.
Fatiti ta yi tijara, ta yi zagi, ta yi gori, ta yi tsine-tsine ta ce Mufidah ta fito su yi dambe in ta isa.Ta kira ta da mayya, matsafiya, arniya.Mufidah tana jin ta amma ba ta fito ba.
Munafuka ita ce Safiya tana ta taya ta, itama saura kadan Dr.Isah ya sake ta dan fadan har da shi aka hada. Fatiti dukan qofar gidan Mufidah take yi tana zage zage amma Mufidah ko tari bata yi ba, tana ciki tana ta kuka dan cin mutuncin yayi yawa. Ba ta kira Yayanta ta fada masa, sun yi waya da Umma dai, Umma ta ce mata dan Allah kada ta fito ta zauna a gida.
Da yamma Fatiti ta nemi in da zata sami Jalilah aka ce tana da shagon siyar da takalma da jakunkuna. Nan ma ta je ta iske ta a cikin mutane ta tara mata jama'a ta ja mata kunne, ta yi mata gargadi akan ta rabu da mijinta Usman. Saura kadan a yi dambe aka fitar da Fariti daga shagon dakyar.
Tunda ya ga kiran Jalilah ya ga kiran her excellency ya ji a jikinsa Fatiti ta kai masu ziyara dan haka sai gabansa ya fadi. Ya na amsawa ashe kuwa hakan ne, su ka tabbatar masa sai sun dauki mataki akan ta wannan karon ba zasu yi haquri ba, sai an daure Fatiti. Babu yadda Usamn zai yi illa ya bada haquri. Ya yi ta riqonsu Allah Annabi akan su yi haquri baya gari ne amma zai dauki mataki.
Fatiti ta dawo gidan Safiya har yanzu bakinta bai daina zagi ba, saboda haka ne ma Dr.Isa ya kasa fita aiki a ranar dan Usman ya roqe shi da ya daure ya taimaka kada ya bari wani abu ya sake faruwa. Zai zo garin gobe shima zai dauki mataki.
Da magruba sai ga motar 'yan sanda ta zo gidan. Dr.Isa da Dr.Musa ne suka kashe husumar dakyar, Jalilah ce ta ce ba zata yarda ba sai ta daure Fatiti.
Imam Malik bai yi mamaki da ganin kiran Usman ba, ya amsa bayan sun gaisa Usman ya ce ya bashi lambar Mufidah.
Sai ya bushe da dariya ya ce "au wai baku ma da lambar juna sai ni za ku saka a tsakiya? Dazu ma Mufidah ta kira ni tana ta tambayata wasu tambayoyi akanka, kuma ta ce in bata lambarka."
Su dukka suka yi dariya, Imam ya ce "bari in tura maka."
Usman yayi godiya ya kashe waya, ba jimawa sai ya ji saqo ya shigo wayarsa yana dubawa ya ga lambar ce Imam ya turo.
A gigice yake, ya kira ta cike da fargabar kada ta qi amsawa. Sai ya ga ta amsa ta na magana cikin lallausan murya.
Ya ce "kamar a kwance kike ma ko?"
Ta amsa " eh ina gida ina daki?"
Ya lumshe ido ya ce "me yake faruwa ne anan Bauchi?"
Ta girgiza kai ta ce "babu abinda ya faru sai alkhairi. "
Ya ce "karki boye min an fada min komai, babu abinda zan ce miki sai dai in ce Allah Ya yi miki albarka da baki fita kin yi fada da ita ba. Kuma na gode sosai da karamcin nan. An ce ta farfasa miki glass din mota, ba ki ce mata komai ba kiyi haquri zan zo in sake miki wani."
Ya ji Mufidah ta na ta kuka, ya yi ta lalashinta da wadannan dadadan kalaman na sa, har ta yi shiru. Sannan suka juye da hirar so da qauna tamkar ma babu abinda ya faru.
Hirar yadda su ka yi da Imam Malik Usman ya bata sun tabbatar ya gano su, kuma da alama ya yi amanna da wannan hadin.
Tunda ya ji ta bangaren Mufidah babu matsala sai hankalinsa ya kwanta. Kiran Jalilah ne ya ke ta shigowa tun yana waya da Mufidah. Dan haka da ya gama sai ya kira ta, ko gaisawa bata bari sun yi ba ta fara bambamin fada. Ya sha mamaki da ya ji mugayen kalaman da suke ta fitowa daga bakinta tana kiran matarsa da kalmar mahaukaciya, mutsiyaciya , dabba da sauran maganganun da a fakaice shi take zagi.
Sai kawai yayi murmushi dan ko a yanzu ya qara tantance mace ta gari mai hakuri, mai yin amfani da iliminta, mai kamun kai tsakanin Jalilah da Mufidah. Dan laifin da aka yiwa Jalilah bai kai wanda aka yiwa Mufidah ba, amma Mufidah bata fadi kalma baqa ba ko daya sai ma boyewa da ta yi.
Daman a bangaren Fatiti ma a ajiye maganarta mai hankali da nutsuwa a gefe dan bata da su, an san ta yi laifi sai dai Jalilah ta kasa daurewa ta yi amfani da nata ilimin ta biye mata, kenan su dukka biyun jirgi daya ne ya kwaso su.
Tabbas hada Fatiti da Jalilah a matsayin bishiyoyi abin ba zai yi kyau ba. Mijin ma kashe shi zasu yi.
Usman yayi shiru ya na ta sauraronta ta zage su tas, ta hada da rantsuwa sai ta koyawa Fatiti hankali a garin Bauchi sai dai in baa garin zata ci gaba da zama ba.
Ya yi ajiyar zuciya ya ce "dukka an kira an fada min abinda ta yi amma ki yi hakuri ba dan ni ba, dan Allah Ubangijin da Ya halicce ki, Ya halicce ni,Ya halicci Fatiti. Kuma in ci darajar manzon Allah S.A.W."
Ta yi tsaki ta kashe waya, Usman yayi tagumi ya yi shiru ya rasa abinda yake yi masa dadi. Tuba take yi kawai a wajen Allah ko wataqila wani laifi yayiwa Allah Ya aiko masa da wannan musiba.
Jalilah ce ta sake kiransa, ya zabura ya amsa, wannan karon hirar soyayya take so su yi saboda ta samu dama yau ya kula ta.
Ta yi ta jero kalamanta, ya yi shiru yana ta sauraro zuciyarsa cike da takaici dan shi kansa ya rasa dalilin da ya sa bai taba jin son Jalilah ba. Ga ta masha Allah babu inda Allah ya rage ya, kalar cakulet, doguwa mai hanci mai gashi, gata 'yar asali mulki da sarauta, ga dukiya, ga kwalliya ga tsafta. Sai dai Mufidah ce kadai ta shiga ransa tun lokacin ma da suke tsaka da yin fada a ransa ya ji yana sonta sosai.
Da ya ga dai Jalilahbata da shirin kashe waya sai ya yi mata godiya ya ce babansa yana ta kiransa a waya zasu yi waya gobe, ya kashe wayarsa.
Da gaske ne ma ana ta kiran nasa, ya ga missed call din mahaifiyarsa, ya ga kiran mahaifin Fatiti. Sai ya ji gabansa yana ta faduwa da alama sun ji wani abu akan maganar nan amma kuma ba haka ya so ba.
Hannunsa na rawa ya fara kiran mahaifyarsa yayi mamaki da ya ji ta daram bata yi bacci ba, dan ita mai saurin yin bacci ce. Bayan sun gaisa sai ta jero masa wasu tambayoyi a cikin hikima.
Ta ce " tun jiya su Amal sun kwana a gidanka sannan da safe suka zo gaba daya tare da yara suka wuni ga shi su na shirin kwana, kuma har da mai shan nono ma baa dawo da shi wajen mahaifiyarsa ba. Lafiya kuwa? ina Fatitii? Ba ni ita a waya zan yi magana da ita."
Usman ya gigice, gaba daya ta kasa gane yaren da yake yi. Ya dauko Hausa da turanci ya hada ya maka, ya sake lalubo larabci ya hada da turanci da Hausa ya hargitsa su.
Ta yi masa tsawa ta ce "ka fada min.gaskiya an ce bata gidanka, kuma.bata gidansu. Ta na ina kenan? Fada ku ka yi ta yi yaji? Ko rashin aikin da baka yi ne ta guje ka?. Ba ka iya ci?ar da ita ne?"
Wannan karon sai ya dimauce gaba daya saboda ya boyewa kowa cewa baya aiki ba,sannan ya gargadi Fatiti ta boye kada ta fadawa kowa. Yaya aka yi Umma ta sani? Kenan Fatiti bata ji maganarsa ba? Ita ta yada.
Umma ta rufe shi da fada daman ta tara shi akan labaran da suke ta ji a gari ana ta gulmar akan yadda Fatiti take bashi wahala tana ta musguna masa, shi kuma komai na sa ya qare akanta da iyayenta da danginta. Duk da Umma.ta ce bata damuwa dan su ma yana yi musu komai, kuma daman shi mutum ne mai kyauta ga kowa tun yana yaro ba zata hana shi yin aikin alkhairi ba. Sai dai bata yarda ya zama wawa ana zalumtarsa ba.
Usman yana ta bata haquri ya ce "gashi nan zuwa gidan yanzu."
Ta kashe waya tana ta huci. Wayar mahaifin Fatiti ce take ta shigowa sai ya dauka cike da fargaba .
Baba ya fara ketowa Usman na sa tambayoyin akan abinda yake faruwa.
Baba ya ce "Fatiti ta kira mahaifiyarta tana kuka tana cewa ka ci amanarta kai da makwabciyarta, dan haka ta hau mota ta tafi Bauchi, tun da safe gata a Bauchi. Ta ce matar matsafiya ce, in tana so mutum ya zo ko kana bacci sai ka yi tsafi ka tafi wajenta saboda haka a yanzu ma ita ta yi mata tsafi kawai ta ganta a motar Bauchi, matar ta yi kidnapping dinta a gidanta da kyar da addu'a ta fito daga gidan. Kuma matar ta ce har kai din ma zata yi tsafi ka kai kanka. Ta ci gaba da cewa matar arniya ce kuma mucizai ne dukka a gidanta su take bautawa, ita ta biya muku kudin haya dan ta yi amfani da jininku ta yi tsafin kudi, tana so ta kashe ku. Maganganun shirme dai barkatai mun kasa ganewa. Ga Iyarta ta har yarda, tana ta rangaza kuka."
Takaici ya hana Usman sakat, haushi ya kama shi ya fada a bayyane "ni kuwa me na yiwa Fatiti a rayuwa take so ta dinga tozarta ni, tana tona min asiri akan abinda aka yi da wanda baa yi ba? Baba duk abinda ta fada qarya ne, tsabar zargi ne da kishi."
Baba ya ce " ni kuwa zan tabbatar da cewa na san qarya take dan ni na haife ta na san makaryaciya ce lamba daya. Na kira mahaifinka ma mun tsayar da lokaci, gobe qarfe tara na safe zaa hadu a falon mahaifinka a yi magana. Lallai-lallai ka zo fa."
Usman ya sosa qeya ya ce " Baba ai da asuba zan fita in je Bauchi dan in.taho da Fatiti, tana can ana ta fada da ita, ta ce ba zata dawo ba sai dai a yi biyu babu ko ta kashe ko a kashe ta ko su kashe juna ita da matar. Ina tsoro kada abin ya baci, shine zan je."
Baba ya fusata ya fada cikin gadara ya ce "ita din banza ta isa ta ce ba zata dawo ba, ai na yi magana da ita a waya na ce gobe da sassafe motar farko ta shigo ta dawo. Yadda ta kai.kanta haka zata dawo da kanta ba zaka bi ta ba. Ka kwantar da hankalinka za ta zo kawai ka zo a zauna. Allah Ya yi maka albarka, dukka muna da labarin azabar da take gasa maka amma baka taba kawo qararta ba, shiyasa na cure ka na yarda kai yaron kirki ne."
Mahaifiyar Fatiti ma ta karbi wayar tana kuka tana bawa Usman haquri tana roqo ya ci gaba da hakuri, kada zuciya ta sa ya sake ta.
Usman yana amsawa da "Amin na gode."
Da su ka kashe waya sai Usman ya dora hannu aka ya ya miqe tsaye yana zagaye shi kadai a cikin daki yana ta adduoi yana riqon Allah Ya kawo musu agaji Ya shiga lamuransa.
Dan Fatiti ta bata komai ta ko ina, ta yi laifi kuma ta tona asirin da kanta. Ya na tausaya kansa amma ya fi tausayawa Fatiti a gumurzun da zaa yi a zaman gobe .
Sai ya kwana ya na sallar dare, abin mamaki da misalin qarfe uku da rabi daidai na tsakar dare sai ya ga kiran wayar Mufidah. Ya yi sauri ya amsa, sai ta cika da mamaki da ta ga ya amsa.
Ta ce "baka yi bacci ba ne?"
Ya tambaya shima "ke me ya hana.ki yin baccin?"
Sai suka yi dariya su dukka.
Ta langwabe murya ta ce "na tashi na yi sallah ne ina yi maka addu'a akan Allah Ya yaye maka damuwar da kake ciki dan bana so hankalinka ya dinga tashi. Ni ce na jawo maka duk wannan matsalar."
Sai ya ji ta bashi tausayi hawaye ya cika masa ido, ya yarda sai yanzu ya hadu da masoyiyar gaskiya.
Ya fada cikin sanyayyiyar murya "Allah sarki na gode da kulawa, nima addu'a nake yi mana Allah Ya bar mu tare."
Ta ji dadi wannan maganar tasa, sai ta rufe ido ta ce "da gaske ka ke?"
Ya ce "da gaske nake toh me yayi saura kuma? Fatiti ta sauqaqa min aiki, ta binciko maganar da kanta, ta dauki matakin da zata dauka, kuma ta taya ni fadawa iyayena da iyayenta da sauran dangi. Kin ga ai na huta, abinda nake fargaba duk ya zo min da sauqi. Ke ma za ki iya sanarwa da Daddy da Imam Malik, ki roqe su akan su bar mu mu yi aure."
Mufidah ta ji wani farin cikin da bata taba jin irinsa ba, sai take ganinta kamar a mafarki za ta farka daga bacci.Take tambayar kanta da kanta daman akwai ranar da zan ji irin wannan kalma ta aure akai na? Daman akwai ranar da zan ji ina son wani shima ya ji sonna har mu dukka mu ji zuciyoyinmu sun amince za su yi aure?"
Hawayen farin ciki ne yake ta kwaranya har ya gane cewa kuka take.
Ya tambaya a gigice "Mufidah kukan me kike yi? Ki yi haquri idan maganar nan ta bata miki rai, ba yin kaina ba ne sonki ne ya yi min yawa a cikin zuciyata har na kasa daure in bayyana labarin da

4 / 10