Author : Jamila Umar Tanko Category : Romance
mufida a zaune a falonta tana sanye da hijabi da kofin shayi a hannunta. Ta sauko daga kan kujera ta duqa har qasa ta gaishe shi. Ya ji dadi da wannan sabon matsayi da ya samu dan haka sai ya shiga falon da qarfin guiwarsa gami da yin sallama, ya sami kujera ya zauna ya fuskantarta.
Ya ga alamar kunya a idanuwanta sabanin da take kafa masa ido tana harara. Ya tambayi lafiyar jikinta da yadda take ji yanzu. Ta ce da sauqi, bata mafarkai bata jin komai a jikinta.
Ya fada a bayyane "Alhamdulullah. Allah Ya qara lafiya. Ki qara kiyayewa da addu'a da kuma suturce jiki, da yin turare aljanu na safe da yamma.
Ta amsa da "nagode."
Ya tashi ya fita. Ta bi shi da kallo yayin da ya tsaya zai saka takalmansa, shima ya waiwayo ya dube ta wannan karon da suka hada ido sai su dukka suka yi sauri suka kawar da kai gefe.
Ya sauka qasa ya zauna a cikin mota ya na dumama motar amma kuma ya rasa abinda ya ke damunsa, wani irin yanayi yake ji a jikina, Mufidah tana yawan fado masa a rai. Ya fi kwatantawa da tausayi a baya amma yanzu bai sani ba. Kamar abin ba tausayi ne kadai ba.
Mufidah ta dinga jujjuya kanta dan ta na jin wani irin yanayin da bata san irinsa ba, kuma bata taba jin irinsa a rayuwarta ba. Kwana biyun nan Usman ne yake yawan fado mata a rai kuma sai ta ga komai yayi yana burge ta.
*** *** ***
Usman ya ci gaba da gwagwarmayarsa ta fadi tashi yana neman kudi, yawanci dai bayan typing din da yake yi a unternet Cafe yana daukar fasinjoji a motarsa daga wannan gari zuwa wancan, wataran tafiya mai nisa wataran kuma kusa kusa. Amma ya fi samu a dauke shi shata, manyan mutane ya kai su ya dawo da su su biya shi kudi masu yawa a dunqule kasancewar motar mai kyau ce ga Ac.
Al'amarinsa da Jalilah dai tunda namiji ya shiga ya sami sauqin takura daga her excellency, amma fa Jalilah ta bude wuta binsa take duk inda yake. A cikin rashin saa bata samunsa sai dai idan ya zo a ce yanzu ta tafi. Haka Tanimu ya sha bashi saqon wasiqa ya ce in ji wata mata a baqar mota . Maganar dai ta soyayya ce da aure take so ya zo su yi magana, kuma tana bashi haquri akan abinda yayarta ta yi masa ita ba da yawuna ba.
Mufidah ce da Usman aka hadu a farfajiyar gidan, ya na saka akwatin kayansa a but, ita kuma ta fito zata je wajen aiki.
Su ka gaisa kowannensu cike da faraa, sai ya sanar mata zai tafi kano kuma zai kwana biyu acan.Yadda ya ga yanayinta ya canja sai ya cika da mamaki, alamar kamar bata ji dadi ba.
Ya sake dubanta yayi murmushi ya ce "sati guda zan yi kacal in dawo."
Ta gyada kai ta ce "ba damuwa Allah Ya kiyaye hanya."
Shi bai tafi ba, ita bata tafi ba su na ta kallon-kallo da alama kowannensu kamar ya na so yayi magana .
Ya tambaya "ko akwai wani abu ne?"
Ta gigiza kai ta ce "A a ba komai a gaishe min da su Ahmad, sai dai ban ji dadi ba da baka fada min da wuri na baka saqon alewa ka kai musu ba."
Ya yi dariya ya ce "gaisuwarki ma ta gamsar zan isar da saqonki...."
Bai rufe bakinsa ba sai ga mota ta shigo kai tsaye ta tunkaro su, ta zo ta tsaya agaban motar Usman ta yadda ta tokare motar ba zai iya fita ba. Wata tsalelwiyar mace ce ta fito tana tafe tana yanga sanye take da wani dandasheshen leshi, launin kore da baqi a jikinta, dinkin riga da siket sai dan qaramin gyale kore ta yafa a kanta. Ta na tafe tana karairaya ta iso in da suke tsaye, da ya dube ta sosai sai ya gane ashe Jalilah ce.
Ta zare baqin gilashin da ke fuskarta, sai da ta yiwa Mufidah harara barkatai sannan ta shiga tsakiyarsu ta juya ta fuskanci Usman. Ta na karkada mukulli ta ce "yau dai na ganka kuma babu yadda zaa yi ka guje min.Na gama shirye- shiryena tsaf akan maganar aurena kai nake ta jira."
Mufidah ya kalla da sauri wacce tuni kanta ya sara da ciwo, sai ta riqe kai ta yi can gefe jikin motarta ta jingina. Da kyar ta laluba ta bude motar ta shiga, ta zauna sai ta kasa tuqawa.
Jalilah tana ta magana amma baya gane komai, idanuwansa akan Mufidah. Ya zabura zai je wajen Mufidah.
Jalilah ta sake tare gabansa ta ce "ko a dalilin waccan ka qi kula ni? Mufidah Hamza, ai Mufidah ba zata taba kula ka ba in baka san labarinta ba ni zan baka labarinta."
Ya cika da mamaki ta yadda Jalilah ta san Mufidah haka.
Bai ankara ba, giftawar Mufidah ya gani ta haye sama da sauri, sai ya qara tabbatar da abinda yake ji akanta itama tana ji akansa, amsar ita ce sun fara son juna ne kawai, ba komai ba ne illa kishi take yi akansa.
Ya juya ya dubi Jalilah yayi rantsuwa da wanda ransa yake hannunSa wato Allah in ta sake biyo shi gida ko wani waje duk wulaqancin da yayi mata ita ta jawo.
Ya maimaita mata ya ce shi ba zai aure ta ba, sai dai su kashe shi.
Ta fusata ta fara fadar maganganu tana cewa ita da shi su zuba kuma zai gani ba dai a kan Mufidah ne yake wulaqanta ta ba, zata ga yadda zai zauna da Mufidah. Hawaye face-face a fuskarta ta shiga mota a fusace, ta tafi.
Ashe duk wannan abinda ake yi akan idanuwan Safiya, ta na labe a jikin labulen windon dakinta tana nadewa Fatiti rahotanni.
Ya hau saman bene da gudu, gidan Mufidah yake ta bugawa. Patient ta zo ta bude da sauri.
Ya tambaya a gigice "ina Mufidah?"
Ta ce "ta shiga daki ta kwanta."
Ya ce ta taso ta, ta ce Usman ne. Ya na tsaye a falo yana ta kallon hotunanta masu kyawun gaske. Ya ji ya kasa hana idanuwansa duban kwayar idanuwanta, tabbas ta yi kama da 'yan Ethiopia kyawawa masu hanci da gashi, ga idanuwa dara-dara. Ya kalli halittar falon komai na masu aji tsaf-tsaf,.sai ya tabbatar ashe shi a bola yake zaune ba za ka ta a cewa gidansa da nan iri daya ba ne. Daga shi har Fatitin gidadawa ne ashe babu komai a gidansu sai tarkace. Qamshin da gidan yake yi ne ma ya sake saka shi qaunatar son shigowa akai-akai. Ya shaqi qamshi mai dadi ya lumshe idanuwa, ya na budewa ido ya ga Patient a gabansa.
Ta girgiza kai ta ce "ta qi yarda ta fito da alama kuka ma take."
Ya ji hankalinsa ya tashi sai ya ce da Patient "ki raka ni dakin toh."
Ta na gaba yana biye da ita yana kallon dakunan nan dukka ukun da yake a bubbude suke, kowanne ya sha gyara dauke yake da gadaje na alfarma ga Ac ko ina.
Ta na kwance akan wani danqareren gado wanda ya fi na sauran dakunan kyau, ta juya baya ta na sharce hawaye.
Wata murya ta ji kamar a mafarki ya ce " kin fasa zuwa aikin ne kuma?"
Ta yi firgit ta tashi zauna ta dube shi tabbas Usman ne ba gezau ba ne. Ta rasa abinda za ta ce, a bayyane dai murna ta cika mata qalbi.
Ya ci gaba da cewa "na aiko ki zo kin qi zuwa, ni gani na zo da kaina, duk da bai kamata in shigo har dakinki ba, ba yadda zan yi ne dan haka ki fito falo ina jiranki."
Ta gyada kai, ya fita ya tsaya a tsakiyar falo ya ci gaba da kallon ko ina na cikin gidan. Idanuwansa ya dira a kicin yana kallon kayan dadin da Patient ke dafawa, gashi kuwa yunwa yake ji, irin baqa -qirjin din nan.
Motsin Mufidah ya ji ta tsaya a bayansa, ya juya da sauri. Ya ga ta cire riga da siket din da suke jikinta dazu, baqaqe (suit) ta saka. Wata doguwar riga marar nauyi mai dogon hannu ce a jikinta yanzu, sai dan qaramin hijabin da ta saka akanta.
Ya juya yana kallonta ya ce "kin fasa zuwa aikin ne, kuma saboda me?"
Ta yamutse fuska ta kama kai ta ce "kaina ne ya ke ta ciwo."
Ya tambaya cikin sanyayyiyar murya "me ya kawo ciwon kai a lokaci daya, bayan kin fito za ki tafi aiki lafiyarki kalau?"
Ta yi shiru zata tafi ta zauna sai ya tare gabanta ya ce "sai kin bani amsa fa."
Cikin alamar kunya ta ce "babu komai kawai a lokaci guda ciwon ya sauko."
Ya yi murmushi ya ce "a lokaci guda dai Jalilah ta sauko ta saka miki ciwon kai an ce har kina kuka ko?"
Kunya ta ji kamar zata nutse ta rasa amsar da zata bashi tabbas abinda ya fada gaskiya ne amma bata so ya gane ba.
Ta kalle shi cike da mamaki, ya ci gaba da cewa "na san haka ne ai ba za ki iya yin musu ba. Amma kin san amanarki Yaya Imam ya bani, ba zan so in saka miki ciwon kai ba. Ina so ki kwantar da hankalinki duk yadda kike tunani ba haka ba ne. Ashe ma kin san Jalilah ko? Dan ta ce ta sanki itama."
Mufidah ta yamutse fuska ta ce "ban santa ba ina dai ganinta a shagon Murjanatu Bibi, irin gayyata ce."
Ya sami kujera ya zauna ya harde qafa, itama ta zauna a gefe ta ce " ah ka fasa tafiya kanon ne kuma?"
Ya gyada kai ya ce "nima kaina ne ya sara saboda na ki kan yana ciwo, na fasa tafiya a yau sai dai gobe in na ga kin fita wajen aiki."
Su ka yi dariya su dukka, ta ce "ai gara da ka fasa tafiya."
Ya kalle ta cike da mamaki sai ta rufe fuska ta ji kunya. Ku san wuni suka yi su na ta hira ashe kowannensu yana nan maqare da tsananin qaunar juna tun ranar da su ka fara ganin juna. Mufidah bata tantance ba sai da ta sami lafiya, ta yarda so ne. Shi kuwa daman ya sani kawai dai ya san abinda kamar wuya, ba zai yiwu ba shiyasa ya haqura.
Da kanta ta shiga kicin ita da Patient suka shirya masa abinci kala-kala masu dadin gaske, wadanda bai taba cin irinsu ba. Ya tabbatar ashe an bar su a baya, ina ma ace Fatiti a waye take tana yi masa irin wadannan girke girke a baya, tun sanda yake da kudi yana yin cefane baja-baja.
Wasu tambayoyi Mufidah ta dinga jero masa, amma ya kasa amsawa ta na tambayarsa ne akan yanzu da baya aikin nan me yake yi? Ta ina yake samun kudin da yake kula da iyalansa?
Ta ci gaba da cewa "amma me yasa ka boyewa Imam Malik da ya tambaye ka, ka ce masa ka na aiki? Me yasa ka boye masa? Kuma ya baka kudi ma ka qi karba, me yasa?"
Usman ya ce " eh duk daya ne ai da wata ta biya kudin haya ta mayar da wutar da aka yanke, aka tambayeta, ta ce bata san zancen ba ma."
Ta zuba masa ido tana kallo shima idon ya zuba mata kawai aka hau kallon-kallo, ba tare da wani ya san abinda zai fada ba kuma.
Ya gama cin abincin ya kalli agogo lokacin sallar azhar ya yi ana ta kiran sallah dan haka ya yi mata sallama gami da godiya ya ce zai je masallaci, daga nan kuma zai shiga gari sai da daddare zai dawo gida.
Ta tabe baki ta ce " wajen Jalilah dai."
Da ya tambaye ta me ta ce? Sai ta qi maimaitawa ta rufe fuska. Ya riga da ya ji abinda ta ce, ya yi dariya kawai.
Ta raka shi har qasa tana jaddada masa ya dawo da daddaren fa, za ta ba shi saqon yara.
Nan ma Safiya ta taho a guje tana leqensu har tuntube ta yi ta barje qafa. Ta sami tabbacin Usman da Mufidah soyayya suke yi dan haka dole sai Fatiti ta ji wannan labarin .
Ya shiga mota ya zauna ya kunna sai ya ji kamar ya tafi da ita, itama ta ji kamar ta bi shi. Labarin zuciya a tambayi fuska, yadda suke yiwa juna kallon so da qauna za ka gane labaran da ke cikin zuciyoyinsu.
Ta fada cikin sanyayyiyar murya "ka dawo da wuri fa saboda saqon yara."
Ya yi dariya ya ce "fadi gaskiya dai, saqon na manya ne dai kika fake da saqon yara."
Su dukka suka dariya ya ja mota ya tafi yana takallonta ta mudubi, ta bi shi da kallo sai ta kasa tafiya har sai da daina hango shi, Tanimu ya bude masa get ya fita.
Safiya ta ji ba zata iya daurewa ba dan idan gemun dan uwanka ya kama da wuta ka shafawa na ka ruwa, tana jiyewa Fatiti amma ta fi jiyewa kanta dan idan Isa ya jajibo mata Murjanatu Bibi ta shiga a uku.
Umma ce ta hango Mufidah ta windo sai ta fito barandarta ta suka tsaya su na gaisawa.
Safiya ta yi wuf ta fito bakinta cike da maganganu, sai ta fada dan Mufidah ta san ta ganta. Su ka hau kallon-kallo da Mufidah dan itama basa magana.
Safiya ta gaisa da Umma sannan itama ta tsaya tare da su.Ta harari Mufodah sannan ta ce "cin amana ana ta yi amma dai ayi mu gani."
Mufidah ta yi kamar bata ji ba ko kallo bata ishe ta ba.
Safiya ta ce "Fatiti tana Kano ba wai ta tafi gaba daya ba ne, tana nan zata dawo. Daga nan zuwa sati daya, ai gara ta zo kusa da mijinta kafin 'yan fashin maza su yashe mata miji."
Mufidah ta yi murmushi ta ce " Hajiya Umma zan hau sama lokacin sallar magriba yayi, sannan ina da abin yi ba na zaman kashe wando da sakawa mutanen kirki ido. Duniya ta ci gaba fa kowa ya koma makaranta, gara dai mata su sami abin yi."
Safiya ta fusata zata mayar da martani amma Mufidar ta haye sama, Umma ma ta shige falonta, sai ta ji kamar zata hadiyi zuciya. Tabbas sai ta koyawa Mufidah hankali tunda ta fada mata baqar magana.
Usman ya dawo gida bayan sallar Isha'i ya wuce zuwa gidansa. Bayan ya yi wanka ya saka qananan kaya sannan ya fara tunanin yadda zai shiga gidan Mufidah kai tsaye, gashi bashi da lamabar wayarta.
A dole ya daure ya je ya kwankwasa mata qofa, bugu daya sai ya ga Mufidah ta bayyana da kanta ba saqo ba, ya yi tunanin Patient zai gani.
Ya tsura mata ido masha Allah ta yi masa kyau, kyan da bai taba ganin ta yi irinsa ba. Yanzu ya gasgata yana da matsayi sosai a wajenta saboda don shi aka yi wannan adon.
Ya fada cikin ciki murya mai tafe da shudin qauna "kin yi kyau fa."
Ta yi fari da ido ta ce "na gode sosai. Ka shigo mana ai nan ma gidanka ne."
Sai ya ji wani dadi ya rufe shi, ya ji dadin kalamanta. Ya shiga ya zauna akan kujera. Ta ce "ka qaraso kan dining table, da kai muka yi girkin dare."
Ya yi murmushi ya girgiza kai ya ce "abinci kuma bayan wanda na ci dazu da magrib ai na ci abincin dare sai dai kuma gobe."
Ta ce "in baka ci ba zan