Author : Jamila Umar Tanko Category : Romance
yake cikin raina. In kin ce in janye maganar nan sai in janye har sai ranar da kika bani dama da kanki."
Ta zabura ta ce " kukan farin ciki nake yi Usman ina mamakin wannan rana ranar da wanda nake qauna da bakinsa ya ce zai aure ni ba tare da na roqa ba.Kalmar nan ta aure ta na da girma matuqa, ban taba zaton zata fado kaina ba, shiyasa na ke hawaye ina qara gasgata hikima da jin qai irin na Ubangijinmu. Ya amsa addu'oina da na dangina da suka dade su na yi min, lokacin ne sai yanzu ya zo. Usman na yarda da dukka halayyarka na gasgata kana sona saboda Allah za ka riqe ni da amana. Kai irin mijin da nake mafarkin samun irinsa ne, mijin da kowacce mace zata so ta same shi ni Allah Ya kawo min shi ina kwance daga kan gadona. Na godewa Allah."
Sai ta yi sujjadar godiya ga Allah. Usman ya na ta hello hello.
Ta yi dariya ta ce "wayar na ajiye a gefena na yiwa Allah sujjadar godiya."
Usman ya ce "nima yanzu na dago daga tawa sujjadar ai a lokacin da kike tsaka da fada min kin amince, sujjada kawai na yi. Mufidah na gode da kika karbe ni a matsayin angonki, ta ko ina kin yi min, irin matar da nake mafarkin samu. Kuma na yi alqawari zan yi iyakacin qoqarina wajen sauke haqqinki da kare mutuncinki. Sai dai ina mai baki haquri akan canje-canjen rayuwa da za ki gani, ba kamar irin wacce kika saba ba."
Ta ji yayi shiru, sai ta tambaya a gigice "kamar yaya?"
Ya ce " Usman din na ki talaka ne ya fito daga tsatson talakawa, babu abinda muke da shi, babu abinda muke taqama da shi a duniya sai kur'ani mun koya kuma muna koyarwa.
Mahaifina yana da makarantar islamiyoyi kuma shine limamin masallacin jumaa ta unguwarku. Abinda muka tashi muka gani muka gada kenan. Boko ma a karanbani na yi har na yi nisa dan a gidanmu kaf babu wanda ya wuce sakandire sai yanzu ne ma nake takurawa 'yan bayana nake sa su su ci gaba da karatu, an sami masu diploma da NCE dai."
Ta girgiza kai ta ce "haba Usman yaya za ka yi wannan maganar? Babu abinda ban gane ba, na sanka na san yadda kake ni kai nake so kuma halayyarka nake so. Arziki na Allah ne, na godewa Allah da ka zama mai neman na kanka, baka da kwadayi, baka damu da rudin duniya ba. Na sake cure ka da ku ka riqi qur'ani gam dan shine hanya mai bullewa. Allah Ya yi muku komai kuma Ya so ku da rahma da ya baku qur'ani."
"Alhamdulullah, na gode." Kawai Usman yake ta fada.
Ba su gama waya ba sai da misalin qarfe hudu da rabi na asuba, a lokacin da aka fara kiraye-kirayen sallah.
Ya ce zai fita masallaci, itama ta ce zata jira a kira assalatu ta yi salla sai ta kwanta zasu yi magana bayan ta tashi.
Ta qara da cewa dan Allah bayan yayi sallar asuba ya samu ya kwanta yayi bacci, ya cire duk wata damuwar da matarsa take so ta jefa shi, addua kawai zai yi mata Allah Ya sa ta gane gaskiya.
Ya amsa mata yayi godiya kalmarsa ta qarshe ita ce "I love you."
Ta mayar masa da "Love you more."
Su ka kashe waya kowa zuciyarsa cike da shauqi sai da suka dauki lokaci kafin kowa ya iya motsi kawai su na tunano kalaman juna. Soyayya mai zaqi.
Lokacin da Usman da Mufida suke ta linqaya a cikin kogin qauna. Fatiti na can tana ta linqaya a cikin baqin ruwa mai guba na kishi, mai daci da maqaqi a zuciya. Ta na ta kuka da tsaki da qwafa, zuciyarta ta yi baqiqirin tana ci da wutar kishi bal-bal kamar za ta qone, tana ta sassaqa mugayen hanyoyin da zata bi ta nada masu gadar zaren da zata tsinke da Usman da Mufidah su afka.
Asuba ta gari Fa-Us-Mu.
Bayan ya dawo daga sallar asuba sai ya yi shirin kwanciya dan ya samu ya dan yi baccin awanni biyu kafin lokacin taro, saboda bacci ne a idanuwansa har jiri yake yi.
Ya jawo wayarsa, don ji yake ba zai iya kwanciya in bai turawa Mufidah saqon soyayya ba. Abin mamaki missed calls Fatiti ya gani barkatai.
Ya ja dogon tsaki ya ci gaba da rubutawa abar qaunarsa sakon so da qauna, shigowar wayar Fatiti ce take katse masa hanzari tana kira yana rejecting har sai da ya gama tura saqon sannan ya amsa wayar. Ya daga ba tare da yayi magana ba, ya yi shiru yana sauraronta.
Ta dinga soki burutsunta, hakuri take bashi akan in an je wajen iyaye ya ce bata da laifi sannan tana roqonsa dan Allah kada ya auri Mufidah. Dan idan ya aure ta kashe su zata yi daga ita har yaransu da shi din ma. Ya rufa mata asiri kada ya qara yin aure dan idan ya auri wata mutuwa zata yi.
Ya yi tsaki ya kashe waya, amma ta ci gaba da kira sai ya qi ya dauka, dan shi ya rasa ma da me ma zai kwatanta Fatiti. Me hankali ko tabbabiya?
Saqon Mufidah ne ya shigo, sai ya ji tamkar ya tashi sama dan murna, ya bude da sauri ya karanta. Cancandi ashe na sa kalaman ma wasa ne, wasu zafafan kalaman soyayya ta ambulo masa, sai ya gyara zama shima ya zanbada mata amsa. Wato sun jima su na musanyan kalamai a rubuce, kafin daga baya ya ga gara kawai ya kira ta su yi magana dan baki da kunnuwa su karbi haqqinsu.
Usman ya cire tsoro shakka ko fargabar Fatiti da iyaye, tunda kowa ya sani me yayi saura kuma?
Mufidah ta tabbatar masa da ta damqa masa zuciyarta dukka, ya tabbatar mata ya karba zai riqe ta amana kuma zai kula da ita.
Fatiti ta yi ta kiransa ya qi amsawa, ta ji yana ta waya ba qaqqautawa, sai ta tabbatar wannan wayar ta soyayya ce dan Usman baya son yin doguwar waya, daga nan ta saddakar kogin soyayya ya tafi da mijinta, zai yi wuya ya dawo.
Ta rusa kuka ita kadai a daki har Safiya ta tsorata ta shigo da gudu daga kicin, tana tambayar ta. Ta dauka ma mutuwa aka kira aka fada mata.
Fatiti ta ce "Usman ne a waya yake ta magana da Mufidah tsawon awa guda ya qi daukar wayarta."
Safiya ta yi galala a tsaye ta na kallon Fatiti dan ita abin ma ya fara isar ta, ta gwammace da bata hada wannan husumar ba ga shi har aurenta ya neman mutuwa. Dakta ya yi mata fushi ya fita ko abincinta ya qi ci.
Fatiti ta ja mayafinta ta fice tana fita ta haye sama. Safiya ta na ta kwalla mata kira ta qi dawowa.
Ta na hawa sama ta tsaya a jikin qofar Mufidah ta kara kunnuwanta tana sauraro, wasu kalamai ta jiyo masu kama da tashin bom a cikin zuciyarta.
Mufidah na kishingide akan doguwar kujera ta na waya da abin qaunarta. Gaba daya a narke take idanuwanta da muryarta su na ta shauqin juna. Baa cikin wannan duniyar tamu take ba ta tafi duniyar qauna.
Mufidah ta ce "my dear zai yi wuya in iya yin sati daya ban ganka ba."
Haquri ya ke bata cikin wasu sanyayyun kalamai. Mufidah ta sake narkewa ta marairaicewa, ta ce "gashi ko dan Whatsapp din nan baka yi balle ka turo min hotonka in dinga kallon kyakykyawar fuskar nan taka."
Ya ce "na zaci ke kika ce baki taba ganin namijin da bai yi miki a duniya ba kamar ni, kyawun ma da aka ce ina da shi ki ka ce baki taba ganinsa ba, kai babu ma mummuna a duniya kamar ni."
Su ka kwashe da dariya su dukka ta ce "ka san in ancewa makaho ga ido sai ya ce da wari tunda ya san ba zai samu ba. Ah Usman dina mai kyau ne, mai aji ne, mai mutunci, mai yanga ne dan gayu ne."
Fatiti ta ji wani mugun kishi ya turnuqe mata maqoshi, zabura ta yi zata kaiwa qofar bugun wulaqanci. Sai ta tuna da cewa in ta yi irin wannan mugun zasu gane ita ce ba zasu bude ba, dan haka sai ta buga a hankali cikin nutsuwa.
Mufidah ta tambaya "waye?"
Fatiti ta canja murya ta yi muryar maza ta ce "nine."
Sunan Patient ta kira cikin harshen turanci ta ce ta bude qofa sun yi baqo.
Sannan ta ci gaba da magana da abin qaunarta Usman. Har ya so ma ya ajiye wayar tunda ta yi baqi sai ta ce su ci gaba. Ta san mai gyaran wuta ne, sun yi da shi zai zo ya saka mata wani soket ne da fitulu.
Patient na budewa kafin ta kalli me bugawar, ta ji an yi ciki da ita.
Fatiti Dan Usmanu ce ta bayyana a tsakiyar falo a tsaye akan Mufidah ta kama qugu tana ta girgiza, wata tsutsa ce take ta cizonta ta kishi. Bata qi yau sama ta rufta qasa ba, gaba daya a hadu a tafi qiyama.
Qara-qara-qaqa ga Mufidah ga Fatiti. Ga matar da Fatiti take yunwar haduwa da ita tun jiya ta qi bayyana, sai yau Allah Ya amsa addua'arta.
Abin mamaki Mufidah ko girgiza bata yi ba balle ta razana, ko gyara zama bata yi ba, ta ci gaba da kishigidarta kamar wata sarauniya a fadarta. Da alama itama nesa ce ta zo kusa abinda take nema ne ya kawo kansa har gida. Ta tabbatar ba zata bar Fatiti ta yi mata irin wulaqancin da ta yi mata jiya kuma ta fita daga gidan lafiya ba. Ashe ma ta zama sokuwa, wacce bata san menene shari'a da sanin haqqin kai ba.
Patient ce ke karkarwa tana ta durqushe-durqushe tana bada haquri. Da hannu Mufidah ta yi mata muni alamar ta bar wajen, Patient ta shige kicin da gudu tana kuka.
Fatiti ta yi magana cikin isa da fusata ta ce "Mufidah da mijina kike waya, har kina fada masa kalaman soyayya? Na zo ne ayi ta ta qare ne, ko ni ko ke dan bana jin tsoronki."
Usman ya zabura ya ce "kamar muryar Fatiti nake ji." Mufidah ta gyada kai ta ce "ita ce."
Kan ka ce kwabo Usman ya hada zufa, ya zabura ya miqe tsaye a gigice ya ce "innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Mufidah kada ki kula ta dan Allah ki koma daki ki rufe, amma ina so ki bude mata hand's free ta ji maganata."
Kamar daga sama sai Fatiti ta jiyo muryar Usman yana magana da ita. Sai da ya ambaci sunanta sau uku sannan ya ci gaba da cewa "ki fita daga gidan nan yanzu, na rantse da Allah idan kika yi zagi balle dukka a bakin aurenki. Ki na zaginta toh kin saku"
"Wayyo Allah na." Fatiti ta ambata yayin da ta dora hannu a kai tana ta kai kawo a tsakar falon Mufidah. Sai ashar ya taho kan harshenta yana shirin ketowa ya fito sai ta tuna kalmar saki, sai ta hadiye shi, hadiyar nan kuwa tamkar tana hadiyar garwashin wuta ne, radadi da zugi da daci.
Usman ne akan waya har yanzu, kuma ta bude muryar yayi shiru ya na jiran abinda zai faru.
Ya tambaya ya ce " Mufidah na ji kun yi shiru, ta fita ne?"
Mufidah ta ce "gata nan dai tana ta zagaye a folo."
Kowa ya yi shiru aka rasa wanda zai sake magana. Fatiti ta kafawa Mufidah ido tana harara, kallo na tsana, ji take kamar ta kashe ta. Ta gyada kai ta yi kwafa, sannan ta dora da dogon tsaki ta fice a fusace, ta buga mata qofa da qarfi.
Usman ya sulale ya zauna ya dafe kai yana jujjuyawa, bai daina ambaton "innalilahi wa inna ilaihi rajuun" ba.
Abin mamaki sai ya ji Mufidah tana bashi haquri sannan ta hada masa da dadadan kalamai masu kwantar da hankali.
Su ka yi sallama ya kashe waya, wayar Baban Fatiti ce ta shigo, ya amsa da sauri. Bayan sun gaisa Baba ya sanar masa cewar an daga zaman sai bayan la'asar zaa zauna, gara ayi zaman bayan Fatiti ta dawo tare da ita. Sun yi waya da ita yanzu ta ce tana cikin mota sun taso.
Usman ya amsa da "Allah Ya kai mu, ba damuwa." Amma ya san qarya take ta na gidan ta na neman masifa.
Fatiti na shiga gidan Safiya sai ta baje a falo ta dora hannu akai tana rusa kuka.Ta bawa Safiya labarin wulaqancin da Usman yayi mata har ya kusa ya sake akan Mufidah.
Safiya ma kukan ta ke taya ta dan abinda suka dauka wasa ne, ya fara fin qarfin tunaninsu.
Abincin da ta dafa ma su dukka basu ci ba, Fatiti ta daura dankwali ta yafa mayafinta, basu yi wata sallamar kirki ba ma ta tafi da sauri.
A bakin qofar falon Safiya suka ci karo da Umma zata kawo mata abin karyawa. Yadda ta ga Fatiti tabbas ta ga alamar bata cikin hayyacinta, ta qi ta tsayawa ma su gaisa balle ta karbi abincin da ta kawo mata. Ta wuce tana rusa kuka ta fita daga get din.Tanimu ma ya na ta miqo gaisuwa bata amsa masa ba.
Ta haye babur bata tsaya a ko ina ba sai a tashar shiga motar Kano, ta ci saa motar Danjuma ce akan layi shi ake yiwa lodi sai kawai ta shiga ta zauna.
Hankalinsa ya tashi yadda ya ganta a burkice sai ya koma gefe ya kira Usman ya na tambaya, yaushe Fatiti ta shigo Bauchi? Gata nan ta na ta kuka cikin motata."
Usman ya ce ba damuwa ya kawo ta har gida zai biya shi kudin.
Danjuma ya kawo Fatiti har qofar gidan iyayenta, za ta biya shi sai ya ce "ai an biya ni."
Ta tambaya cike da mamaki "waye ya biya?"
Nan fa ya hau kame-kame ce ya yafe mata ne kawai. Dan bai san me yake faruwa a tsakanin miji da mata ba, ba zai ce mata Usman ne zai biya ba.
Ta yi godiya ta shiga gida.
Da misalin qarfe hudu daidai aka fara zaman, Baban Fatiti ya saka ta a gaba suka isa wajen. Ta sami lungu a qasa akan kafet ta zauna ta yi tsuru sannan ta saka wani qaton hijabi har yana jan qasa. Usman ya zauna a kusa da ita, dan takaici baya son kallonta ma wai rada take yi masa akan ya rufa mata asiri.
Mahaifinsa da mahaifinta da malamansa guda biyu abokan mahaifinsa su ma sun hallara. Mahaifiyar Usman da Mahaifiyar Fatiti ma suka shigo suka zauna a gefe, sai aka tura qofa aka rufe, aka bude taro da addu'a.
Aka ce Usman ya mayar da magana ya fadi duk abinda ya faru. Sai ya rasa abinda zai ce, ya ce shi bai kawo qaranta ba ai ita ce ta kawo qara.Aka ce Fatiti ta fadi abubuwan da suke faruwa, ta hau kame-kame aka rasa abinda take cewa.
Mahaifinta ya fusata ya ce "ki fada mana abinda ya yasa kika fita daga gidanki kika je gidan qawa kika kwana, sannan kuma kika wuce Bauchi washe gari kika yi fada da wata har kika kira ta mayya, matsafiya zata kashe ku, kuma.Usman ya ce zai aura ta?
Fatiti ta fara shirya qarya da sharri ta ce matar ce take sonsa shima yana sonta saboda ita ma ya wulaqanta ni, a dalilinta ya rasa aikinsa. Ta je wajen aikin sa ta hada masa sharri har aka.kore shi. Sharri kala-kala dai, usman ya fusata shi ya yarda ta yi masa kowanne irin sharri amma kada ta yiwa Mufidah dan bata ji bata gani ba.
Mahaifiyar Usman ce ta yiwa Fatiti wata tambaya sai da kowa ya gane Fatiti 1aryan ta ke ta ce " kin ce ita take sonsa, shima ya na sonsa kuma.kin ce ita ta saka aka kore shi daga wajen aiki. Daman